Advertisements
Chapter 18 Reading A Rubucetake Book 2 Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Rubucetake Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Complete Novels

Chapter   18 / 33

51K to 54K   out of 97K words

yin sallama.

Maimakon ya amsa sai ya fadata da fada,ta runtse idanunta tana jin kakkausar muryarsa har cikin zuciyarta,sai ta miqe tsam ta wuce daki riqe da wayar tabar aminatu da affan a nan.

"Ke dawa kuke waya?" Ya tambayeta bayan ya gama fadan rashin daga wayar da wuri

"Nida ummu,sai kuma anty fanna"

"Shine har kusan awa daya da rabi?" Mamaki ya sake cikata,to meye a ciki?,yasansu kuma dukkaninsu dama idan tana waya dasu tana dadewa

"Eh lissafin kaya mukeyi da ita,ummu kuma dama kasan hirarmu ai" Shuru ya danyi sannan yaja tsaki ya kashe wayar.

Duk yadda taso danne zuciyarta amma ta gaza saida hawaye ya silalo mata,wai meye hakan?,me yake faruwa?.

Sai data dan koka kadan zuciyarta tayi sanyi sannan ta shiga toilet ta wanke fuskarta ta shafa farar powder sannan ta fito.

Har yanzu suna falo ita da yaron,ta bata wayar tace ta maida masa,sannan ta zauna ta dauki tata wayar tana dubawa.

Tex ta rubuta masa na ban haquri,duk da abun naci mata zuciya sannan ta tura masa,saita koma ta zauna jikinta gaba daya babu qwari.

Falon shuru saboda aminatu ta fita da affan,zuzzurfan tunani ta shiga tanason gano ainihin abinda ya kawo wannan lamarin tsakaninta da abbas din amma ta gaza gano komai,cikin haka ta kwashe awa kusa biyu,ta daga idanunta tana kallon qofa sanda taji ansa key ana qoqarin bude qofar.

Tasan waye,don shi kadai keda key din gidan,miqewa tayi cak da nufin shigewa bedroom dinta,motsinsa da taji kadai ya karya mata zuciya,bata kuma so tayi kuka a gabansa,saidai ta makara,bata kai ga isa dakin ba ya shigo,kuma ya ganta,yana dauke da affan,da alama ya tsaya ya karboshi ne.

Daga nan inda yake ya tsaya bayan yayi sallama yana kallonta,ta amsa amma bata juyo ba,sai ya tako a hankali ya iso bayanta ya rungume ta ta baya,saita sake masa kuka kawai.

*H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Part 02

Page 25


Kasa cewa komai yayi,sai zuciyarsa dake wani irin tsinkewa,sun jima a tsaye a haka har affan ya fara kuka,sai ya miqa mata yaron ya juya ya koma dakinsa yana jin wani yanayi mara dadi cikin ransa,yanason bata haquri ya kuma lallasheta ya kasa,sai bayan ya zauna cin abincin dare yake sake jadda mata

"Ina tsananin sonki,ina kuma tsananin kishinki" bata da amsar bashi,amma batasan wanne irin kishi ko soyayya bane daya rikide yake son komawa ZARGI.

Tun daga ranar data fuskanci haka saita daina doguwar waya don kada ya kirata bai sameta ba,hakanan ta daina nisa da wayarta,idan zaiyi kira dubu zata daga,don don kiyaye faruwar wata matsala da take gani kamar tana shirin kunno kai,da tayi hakan sai taga kamar abubuwan sun ragu,kira dai tana jurar dagashi,to amma ta barwa ranta hakan shine maslaharta.

Ya koyi dawowa gida akai akai,sabanin baya da abincin rana kawai ke dawo dashi,a yanzu sai yazo gida sau hudu biyar kafin lokacin tashinsu a aiki yayi,tun abun yana mata wani iri har ya koma bata mamaki,tako ina ya koma wani irin tsauri da yake mata kama da ZARGI don yafi gaban kishi,amma tayi qoqarin dannewa,tare da bashi uzuri.

Tafiya ta kamashi katsina ta kwana biyu,har sunyi sallama dashi kan aminatu zata dawo gidan ta zauna har sai ya dawo,amma bayan awa uku sai gashi da fahad,dan yayansa ne shima

"Zai tayaki zama har na dawo" da to kawai ta amsa masa,don abubuwan nasa sun fada daure mata kai.

A tafiyarsa ta kwanaki biyu ya dage da addu'ar Allah ya sassauta komai,ya kawo qarshensa,cikin sa'a daya dawo din sai taga abun ya ragu,satinsa daya da dawowar suka shirya zuwa weekend yadda suka saba,daga nan zasu maida fahad gida.

*R U B U T A C C I Y A R K' A D D A R A II*


Shigar yammaci suka yiwa bauchin,sanda motarsu take shiga gidan duka yaran suna farfajiyar gidan suna wasa saman kekuna,hafsat na tsaye da wata baquwa da alama sallama takeyi tayo mata rakiya ne.

Dukka yaran suka kwaso a guje sukayo kansu suna murna tare da kiran sunan affan,harda yusra dake rarrafe,duka tyai budu budu da jikinta da qurar dake farfajiyar gidan,widad bata barta ta qaraso ba ta isa gaban yarinyar ta dagata tana mata waqa

"Allah rayan.....rayan 'yar nan" sai kuwa ta bangale mata baki tana dariya,ta sanya yarinyar cikin jikinta itama tana dariya,duk da ajiqe jikinta yake,fitsari ne ko ruwa itama bata sani ba,yarinyar akwai fara'a sosai,shi yasa take sonta.

Ga mamakin widad da hafsat ta dawo daga raka baquwar sai tayo wajensu

"Sannu da zuwa daddy" ya daga kai da murmushi yana kallonta

"Yauwa sannu da gida maman yara" ta saki murmushin jin dadi kadan,sai widad ta taka kadan ta gaidata.

Ba yabo ba fallasa ta amsa mata sannan ta maida kanta ga mijinta suka fara hirarrakinsu,har widad taji tadan qosa da tsaiwar ta dauki qaramae jakarta ta cewa fahad

"Shigomin da sauran kayan don Allah" sai tayi gaba ta barsu a wajen.

Sai bayan kusan awa guda aka shigo mata da affan,a lokacin har tayi nisa wajen gyaran sashenta,ta karbeshi tana tambayar fahad ina duka yaran

"Mamansu ta tafi dasu bagaren abbansu" saita gyada kai kawai tana cirema affan pampers dinsa,don ba kasafai take barinsa dashi ba don ba mai yawan fitsari bane.

Ta kama kanta sosai game da lamarin hafsat dama tun ba yau ba,don sai ta gama zamanta a bauchi su koma bata bari hanya ta hadasu ba,to wannan zuwa hutun ma haka ya kasance,hatta dasu mimi ta janyesu,wannan bai damu widad ba,tunda koba komai itama Allah ya bata nata,affan ya isheta suyi sabgarsu a sassansu,ga kasuwancinta dake dauke mata hankali,wani lokacin saita share awanni tana lissafin kaya dana kudade.

Uwa uba wannan zuwan ma da sukayi sai takejin jikinta duka babu dadi,yawan bacci da kasala gaba daya,ranar da ta karba girki washegari abbas din yana saman dining tana shirya masa breakfast yana riqe da affan yana masa wasa,ta kammala taja kujerar ta zauna ta fara saving dinsa,idanunshi a kanta harta gama ta daga kai suka hada ido

"Lafiya yallabai?" Sai ya dage mata girarsa dukka biyun

"Sonki nakeyi" maganar ta bata dariya har sai data murmusa

"So na nawa kuma ranka ya dade?"

"Na babu adadi,malala gashin tunkiya,ina sonki sosai,ina kuma kishinki widad,da ina da hali ko quda bazan bari ya sauka a kanki ba" ajiyar Zuciya ta sauke mai nauyi tadanyi rolling idanunta tana kallonsa,ta yarda kai idanma akwai abinda yafi yarda ta yishi akan irin soyyyar da abbas keyi mata

"Amma jiya kinsan kinci bashi na,kikayi baccinki kina barni da kewa" murmushi ta sakeyi tana dan rufe bakinta

"Amma yallabai,ina jinka fa ka rage zafi sosai fa" fuska yadan bata

"Hakan bai gamsar dani ba madam.....bana wani ganewa rage zafi,na ji na kasance tare dake kawai shine magana,kwanan nan kin koyi lalaci da dogon barci,ko so kike na qara aure oho" ya fada yana dan shan mur kamar da gaske.

Idanu ta fiddo,saita fara bubbuga masa qafa cike da shagwabar nan tata tana masa kukan qarya

"Haka kace uncle?,haka kace?" Dariya ya saki

"Wasa naki miki wuddu na" ya dora affan saman dining din yana cewa

"Idan na biyewa mamarka bazan fita ba,ina da aiki masu yawa,gobe ma kuma sokoto zan tafi daurin aure,zai yiwu ma mu kwana can sai jibi"

"Allah ya nuna mana"ta amsa tana qarasa tura masa sauran breakfast din.

*W A S H E G A R I*


Tunda wuri ta gama masa komai na tafiyan yana kwance yana bacci,hatta da breakfast da ruwan wanka,sai data kammala ta shiga dakin,suna cikin duvet shi da affan suna baccinsu hankali kwance,ta saki murmushi har qasan ranta tana jin dadi idan ta kallesu,su din sanyin idaniyarta ne,kamarsu kullum qara fitowa takeyi da juna,kana ganinsa basai ka tambaya ba kasan mahaifinsa ne,tadan dora hannunta saman pillow din da yake kai ta soma bubbugawa a tausashe,ya motsa kadan saiya dora hannuwansa saman kunnensa ya rufe.

Murmushi ta saki,ta gane ya farka tashi ne bashi da niyyar yi,saita gyara zama ta zame duvet din gaba daya daga fuskarsa,ta kamoshi ya maida fuskarsa,ta sake zamewa,sai kawai ya cakumota gaba daga ya mirginata ya danneta da dukka qarfinsa,sannan ya kama fuskarta ya riqe a tafin hannunsa saitin tasa,ya fara bude manyan idanunsa da suka qara girma kadan saboda barci cikin nata qwayar idanun,suka kuma dan canza launi kadan.

"Na meye zaki dameni da tashin sassafe,bayan ke kika gajiyar dani jiya?" Ya fada da muryar bacci wadda tayi mata dadi qwarai cikin kunnuwanta,saita saki murmushi tana girgiza kai

"Banda sharri uncle,ka fadi gaskiya" girarsa ya daga mata

"Wacce gaskiya ce da tafi wannan,ni wani irin zaqi naji kina......."

"Wayyo uncle,don Allah kada ka fada" ba shiri murmushi mai kama da dariya ya qwace masa,sai ya hade goshinsu waje daya

"Don Allah ki barni na fadi irin abinda naji,da gaske nake widad,kullum sake dad......" Bata da zabi illa hade bakinsu da tayi waje guda,shi kuma hakan ya zamana kamar ta sake bashi dama ne,sai kuwa ya manne mata da kyau.

Da qyar ta qwaci kwanta tana sakin numfashi,ta nuna masa agogo da yatsantsa

"Lokaci yana tafiya, everything is ready" tayi tsalle ta fice daga bedroom din don kada ha biyota.

Binta yayi da kallo yana murmushi,sai ya waiwaua gefan inda affan yake,sun tula masa pillows basu sani ba,ya gyara masa kwanciya sosai sannan ya fada toilet.

Komai ita ta taimaka masa ya gama shi,yayi kyau cikin Wani lallausan yadi ruwan zama,wanda ya sake fitar da haibarsa da kwarjininsa.

Widad dake tsaye tana qare ma kwalliyar tasa kallo,tana sake jinsa har cikin jininta tayi.magana qasa qasa,ya waiwayo yana dubanta bayan ya ajjiye tissue din da ya gama goge sauran maiqon abincin da yaci,saiya zube hannayensa a aljihun wandonsa ya fara takowa inda take idanunsa akan fuskarta

"Me kika ce?" Dariya take qoqarin dannewa

"Bance komai bafa" da wani irin zafin nama ya kamota ya sakata sosai cikin jikinsa yana sansanarta

"Kayi kyau da kwarjini,idan ka fita kamar ba kai ba,kamar ba kaine ka gama danne 'yar mutane dazu dazu ba,ko ba haka kikace ba?" saita zaro ido sosai,batayi tsammanin yaji abinda ta fada ba,girgiza kai ta fara yi

"Don't say no.....na riga naji" juyo da ita gabansa yayi

"I love you,ina kishinki sosai" ido ta lumshe tana mamakin yadda yake jaddada maganar kishin nan koda yaushe

"I love you too" ta amsa masa a sanyaye.

Har gaban mota ya rakoshi,tana tsaye suka fice daga gidan bayan ya leqa ya yiwa hafsat sallama,ita din dama can batasan rakoshi ba,saidai idan wani abun zata amsa tayi mantuwa ta biyoshi,ko kuma abinda zata karba din yana cikin motar tasa.

*B A Y A N A W A H U D U*


Misalin qarfe hudu na yammaci,tana kwancw a falo tana chart,affan yana kwance saman cikinta yayi bacci kira ga shigo wayarta,data duba da kyau sai taga abubakar ne,dan uwa ga mahaifiyarta wanda yake kamar mazaunin uba a wajenta,yana da matuqar kirki,ya kuma dauketa kamar diyar cikinsa.

Kwantar da affan tayi,ta zauna sosai tana amsa wayar,suka gaida dashi sannan yace

"Muna garinku,amma bamusan inda zamu iso gidanki ba,don wannan shine shigowarmu ta farko bauchi" sosai dadi ya kamata,iya zuwan da takeyi wajen mummynta kawai ta fahimci yadda sukeson mommyn nata,bama ita kadai ba,har su da suka fito daga cikinta

"Ta wanne guri kuke?"

"FAAZ hotels"

"Bansan gurin ba kawu,amma zan tambaya saina taho daku" ta fada cikin murna,karon farko wasu daga dangin mahaifiyarta zasu kawo mata ziyara gidanta.

Suna gama wayar ta kira abbas din don ta gaya masa zata taho dasu,saidai cikin rashin sa'a dukka layukansa is switched off,ta kira rose tace ta yiwa samuel magana ko tare suke ya cewa ogansa ya kirata,to amma shima ba tare dashi sukayi tafiyar ba,ta kusa minti talatin tana kira bata sameshi ba,sai ta miqe ta gyara yafen mayafinta ta fito farfajiyar gidan.

*H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Part 02

Page 26


Hafsat da lawal ta hango tsaye jikin motar hafsat din suna magana,da alama fita zasuyi ko kuma sun dawo,ba kasafai takeson shiga sabgarsu ba,amma yanzun dole tayi tambaya taji ta inane wurin yake tunda ba garinta bane,saita sauya akalar tafiyarta zuwa wajensu.

Dif sukayi sanda suka ganta a wajen,hafsat ta dauke kai kamar bata ganta ba

"Don Allah lawal ta ina faaz hotels yake?" Tambayar data fusgi hankalin hafsat,saita waiwayo ta zubawa widad din ido

"Faaz hotel kuma?"

"Eh nayi baqi ne zan taho dasu"

"Okay" ya fada sannan ya fara mata kwantance inda yake ya qarashe da cewa

"Kibi ta nan ahmadu bello way"

"Aah,ta sa'adu zungur road kaman yafi" hafsat ta tsoma bakinta,bata kawo komai a ranta ba,cikin tsarkakakkiyar zuciya tace

"Yauwa na gode" kamar tace lawal din ya kaita ganin suna rufe motar sun gama uzurinsu da ita amma saita fasa,ta shige part dinta da sauri ga sauya kayanta zuwa abaya wadatacciya tayi rolling,saita saba affan a kafadarta ta dauki key dinta da kudin napep da zai kaita ta fita,tasan ba zata jima ba,duka duka da zuwa da dawowar ba lallai ta wuce awa daya tunda basu da wani nisa sosai.

Wani irin duumm yaji kansa yayi,ya sake daukan wayar jikinsa yana rawa ya kuma buda hotunan,itace dai..... widad dinsa ce dai babu canji, itace dauke da affan dinsa,yaron dake tsananin kama dashi

"Hasbiyallahu la'ilaha illa huwa alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azeem" ya fada wannan karon har bakinsa yana rawa,kansa ya sara masa yasa hannu bibbiyu ya dafe,wani sashen na zuciyarsa yanata qoqarin kawo uzuri da kariya a gareta,amma wani sashen kuma yana qaryata haka hadi da sukan duk wani hanzari da zuciyarsa ke badawa,sashe mafi qarfi kuma mafi rinjaye kenan.

A hankali sai zuciya ta fara ayyano masa irin abubuwan da suka faru a jiyan,ita tafara tashinsa a bacci,ta kuma shirya masa komai na tafiyar tun lokacin tafiyar baiyi ba,ta dameshi kuma ya tashi ya shirya kada yayi latti,hakan yana nufin dama akwai abinda ta shirya zatayi a ranar shiyasa take Allah Allah ya tafi?.

Bayan nan yayi kiranta da yammar kusan miscal uku,bata biyoshi kiran ba,har sai cikin dare bayan bacci ya daukeshi,sai da safe yaga miscal,bata kuma sake nemansa ba,me hakan yake nufi,duka wadan nan abubuwan da ido yake gani ya zama gaskiya kenan?, innalillahi wa inna ilaihi raji'un ya sake fada kansa yana qara sara masa sosai yayi qas da kansa yana jin yadda zuciyarsa ke masa wani masifaffen zafi.

Yafi awa uku cikin matsanancin halin da baisan dame zai kwatantashi ba,kafin daga bisani wata qaqqarfar zuciya ta yunquro masa,ya miqe ya fara hada kayansa,abinda sam baiyi shirinsa a sannan ba har sai zuwa gobe da safe.

Bashi da kuzari ko qarfin halin da zai iya tuqi daga sokoto zuwa bauchi,dole ya nemi daya daga cikin yaransa da sukayi tafiyar tare ya bashi driving din.

Tunda suka dauki hanya bai iya katabus din komai ba,sunci rabin tafiyar saiga kiran widad din ya shigo,ya kalli wayar sosai kamar widad dince a gabansa,zuciyarsa na wani irin bugawa,wani sashe na zuciyarsa na bashi izinin dagawa,wani sashen kuma yana hanashi tare da tuna masa girman laifinta a gareshi,daga qarshe daya sashen yayi rinjaye,sai yayi rejecting kiran,yama kashe wayar gaba daya,ya maida kansa jikin kujera ya kwantar yana lumshe idanunsa,kanshi yana ci gaba da sara masa

"Widad fa,widad" abinda zuciyarsa keta maimaitawa kenan cike da wani irin zulumi tashin hankali tsoro da kuma fargaba.

Cikin mamaki ta sauke wayar tana kallon fuskar wayar sosai,zuciyarta na gaya mata rejecting kiran nata yayi amma ta kasa gasgatawa,saita katse shakka da mamakinta ta sake yunqurin kiransa a karo na biyu,saidai computer ta gaya mata wayar tasa a kashe take.

Jim ta danyi,to kodai wayar tasa babu charge ne,ya qare sanda take kiran nasa?,bata sani ba,amma

18 / 33