Author : Mamuhgee Category : Complete Novels
gami da jan wayarta ta fara dubawa,saidai zuciyarta adan hargitse take kadan,don bugunta ma ya sauya ba kamar yadda yake a qa'ida ba,kuma ita kanta batasan dalili ba.
Tsaye yayi kawai a wajen kusan minti biyu yana duban hanyar,sai ya dauke idonsa yana sauke ajiyar zuciya,gaba daya a wannan lokacin bazaice yana jin dadin duniyarsa ba,duk yadda yaso ga qaryata hakan da gayawa kansa komai dai dai yake,amma yasan ya fada dinne kawai bawai don dai dai din yake ba.
Gurin affan ya qarasa,ya dauki yaron yayi masa wasa sosai sanann ya wuce dashi dakinsa,ya cikashi da kayan wasa ya shiga bandaki ya sake wanka, sanda ya fito harya bingire saman gadonsa yayi bacci,da alama dazun dama kukan rigimar baccin yakeyi,ya saki murmushi yayi kissing goshinsa a hankali ya gyara masa kwanciya yana jin qaunar yaron har cikin jininsa,sai ya tsaya gaban madubi ya shirya cikin qananun kaya,ya shafe jikinsa da turare sanna ya fito.
A falo ya fara zama,amma kamar wanda magnet ke jan hankalinsa zuwa ga dakinta saiya kasa samun sukuni,bayason shurunta,kasheshi yakeyi,a qalla ko fada yana da buqatar su dinga yi,duk sanda tayi masa shariya irin wannan baya iya jurewa,bashi da juriya akan abinda yakeso,sai ya taka a hankali ya saka kai zuwa cikin dakin.
Tana tsaye gaban wardrobe tana fidda wasu kaya,sau daya ta waiwayo ta kalleshi ta mayar da kanta kamar batasan da wanzuwarsa ba,ya tsaya daga bayanta yana dubanta
"Ina abinci na?" Kamar ba zata amsa masa ba,saita zuqi numfashi ta fitar ta bakinta a hankali, zuciyarta tafasa kawai takeyi amma batason tayi wani abu da zai nuna bata ganin qimar uncle muhsin,ta saki kayan hannunta ta juya ta fice ba tare data tanka masa ba,yabi bayanta sai ya sameta saman dining tana serving dinsa.
Kujera yaja ya zauna yana bin dukka motsinta da kallo,ko sau daya taqi duban inda yake,kamar ma ita daya ne cikin falon,wani irin fushi ne kwance saman fuskarta ba tare da ita kanta tasan da hakan ba,yaja ajiyar zuciya me nauyi ya sauke a hankali,dai dai sanda ta gama zuba abincin ta motsa da niyyar miqewa tabar wajen
"Dawo ki zauna" ya fada a tausashe cikin muryar bada umarni,bata musa masa ba,kamar yadda bata kalleshi ba,ta kauda kanta zuwa wani sashen daban,yaja abincin gabansa ya fara ci,saidai gaba daya girkin kamar ba nata ba,ta cika masa yaji sosai,abinda tasan yafi tsana kenan,ya lumshe ido yana jin yadda yajin ke ratsa harshensa har kwanyarsa,ya sakeyin loma ya biyu ba tare da ya bari ta gane tsananin yaji da yakeji ba,saidai idanunsa suna kanta,ya tsatstsareta dasu ya hanata sakewa gaba daya,cikin jikinta takejin laifin data masa,amma zuciyarta taqi amsar haka.
"Karomin" ya fada yana tura mata plate din,sai ta daga kanta da sauri cike da zallar mamaki ta kalli plate din ta kuma maida dubanta gareshi suka hada ido,idanun nasa da suka dan canza launi saboda tsananin zafin yaji,sai kuma ta janye idon nata ta basar,tasa hannu ta dauki plate din ta qara masa ta tura masa hadi da bashi qeya.
Spoon ya sake sakawa ya kuma cinyewa,sanda ya sake cewa ta qara masa sai data zauna sosai ta dubeshi da kyau,bakinta yadan motsa kamar zatace wani abun sai kuma ta fasa,ta sake janyo plate din ta fara zuba masa
"Wannan karon ki zuba yafi sauran yawa,muddin ta wannan hanyar zuciyarki zatayi sanyi......zan jurewa ci har sai kince na barshi haka"
"Kayita ci,bazance ka barshi ba" ta gayawa zuciyarta hakan.
Ta gefan ido ta dinga satar kallonsa ganin yana hanyar cinye uban abincin data sake loda masan,tun tana satar kallonsa harta koma kallonsa kai tsaye,ko sau daya bai kalleta ba yaci gaba da ci,ta kalli idanunsa zuwa sannan sun canza launi sosai,tasan yadda yajin abinci ke masa illa,musamman ulcer da yake da ita wadda idan ta tashi ba qaramar wahala take bashi ba,batasan lokacin data riqe hannunsa ba
"Ka barshi haka" ta fada da sauri muryarta tana rawa.
Jajayen idanunsa Ya daga ya kalleta dasu,sai ta gaza jurewa kuka ya qwace mata,ta saka dukka hannuwanta biyu ya rufe fuskarta dasu tana sakin siririn kuka.
Tsam ya miqe daga inda yake zaune ya iso gabanta ya tsaya yana dubanta zuciyarsa na wani irin tafasa,kafin yace komai tayi hanzarin bude fuskar saboda wani irin amai mai zafi daya danno mata,yana qoqarin riqeta tana qoqarin zamewa,saboda tasan muddin yaci gaba da riqeta zata wankeshi da aman.
Bata iya riqeshi ba kuwa ta fara kwararashi,bai damu da yadda ta batashi ba saboda gaba daya hankalinsa a tashe yake,dama bata da lafiya?,tun yaushe?,duka bashi da wannan amsar,ya riqe hannuwanta sosai daya hannun nasa ya dafe mata bayanta yana jera mata sannu kamar zai ari baki.
Shi ya gyara wajen,ya hada mata ruwan dumi ta gyara jikinta da ta bata shima ya gyara nasa jikin,tana kwance tana maida numfashi idanunta a kulle ya qaraso dakin,ya canza kayan jikinsa, boxer ne kawai a jikinsa,qaqqarfar kuma lafiyayyar surarsa ta fita sosai,ya dawo gaban gadon ya durqusa dab da ita ya kama lallausan hannunta ya riqe cikin nasa
"Tun yaushe ne baki da lafiya?"
"Kada ka tambayeni" ta fada muryarta tana rawa
"Why?" Ya tambayeta a mamakance,sai data zame hannunta daga nashi sannan tace
"Saboda baka damu dani bama gaba daya bare lafiyata"
Tashi yayi ya haye gadon gaba daya,ya jawota cikin jikinsa dukkaninta ya rungumeta tsam,bata da qarfin da zata qwace a jikinsa dole haka ta zauna,a hankali sai taji yadda zuciyarsa ke bugawa da Wani irin qarfi n da ya wuce qa'ida
"Tun daga wancan lokacin da abun ya faru haka kullum zuciyata take bugawa,ban taba zaton zankai wannan lokacin ban kamu da ciwon zuciya ba,komai nina aikata miki shi,amma bisa wani umarni da bansan daga inda zuciyata take karboshi ba.......kiyi haquri da dukkan abinda ya faru,ki kuma yafemin,amma nayiwa zuciyata alqawarin bazan bar wannan abun ya wuce a haka ba, kowanne irin tunani nasan zaki iyayi a kaina,dai dai ne bazan hanaki ba,amma ki bani dama......i need a chance don Allah don kuma affan bawai don ni ba" daga wannan maganar ya zame jikinsa daga gareta,ya barta da tunani.
Hijab ya dauko mata sannan ya dauko affan
"Muje kiga likita,bai kamata ki kwana hakanan ba" shi ya taimaka mata har zuwa bakin mota,sai data shiga ya kwantar da affan a baya sannan ya shiga ya tayar da motar suka fice daga gidan,dukkaninsu zuciyoyinsu babu dadi.
Idanunsa qyar akan allon computer din sanda likita yake mata scanning,yara biyu ne gasunan kwance a mahaifarta har zuciyoyinsu sun fara bugawa.
Da sauri ta dauke kanta gefe hawaye yana sauko mata,ta yaya zata iya rainon cikin 'yan biyu?,bayan ko yaye affan batayi ba,a wannan yanayin da take ciki bata jin tana da qwarin gwiwar da zata iya rainon cikin ma gaba daya
"Satin cikin sha biyu gashinan,congratulations" Dr anwar likitan mai matuqar kirki da barkwanci ya fada.
Abbas dake jinsa kamar a duniyar mafarki ya miqa masa nasa hannun,Allah me yadda yaso a lokacin da yaso,cikin yanayin da yake na daukewar dukkan wani farinciki daga rayuwarsa sai ga hasken farinciki ya ratso daga ubangiji,ya maida dubansa ga widad hankalinsa ya tashi da ganin hawayen da take zubarwa,ya matsa saman kanta yana jera mata tambayoyin akwai abinda ke mata ciwo ne?,saita gyada kai
"Bari ina zuwa" Dr anwar ya fada yana fita a office din,hakan ya bawa abbas damar dagata,ta zauna sosai yana riqe da hannunta,saidai ya kasa zama,yana tsaye ne tsakiyar qafafunta yana kallonta
"Bani da qwarin gwiwar rainonsu da haifarsu" ta fada tana zubda sabbin qwalla,sai ya dora yatsantsa saman labbansa
"Zan baki duk wani qwarin gwiwa da kika rasa,zan baki dukan hope,zamu rainesu tare na kuma tayaki naqudarsu,don Allah ki kwantar da hankalinki na roqeki,ina da buqatarsu,burin kuma hajiya kenan kullum taga tarin jikoki daga wajenki" furta sunan hajiya da yayi ya sake sanya damuwa da karyewar zuciya a zukatansu su duka biyun,sai ya matso ya sanyata cikin qirjinsa yanason saukar mata da nutsuwa.
Tun daga wanna lokaci gaba daya ya maido hankalinsa akan widad din,ya bata dukkan lokacinsa ya rage ranakun fita aikinsa,ya hanata yin komai,komai shi yake mata,yayi nata yayi nasa yayi na affan,sai daya gama karantar komai da takeso naci sha da sauransu,wani lokacin har tausayi yake bata,duk da har yanzu ta kasa warewa yadda suke a baya,abinda yake qara masa damuwa cikin qirjinsa kenan,yake ganin kamar komai bai wuce a wajenta ba.
Tun randa yaci wannan abincin qirjinsa yake yawan riqe masa da ciwo,amma sam bai nuna mata ba,don so yake ya dawo da dukkan farinciki da walwalarta.
*H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Part 02
Page 35
Wannan shine babban damuwarsa kafin ya tunkari abinda yake gabansa.
*******Qarfe daya na tsakiyar dare ya farka da wani irin mugun gumi da yake karyo masa,saboda riqewa da qirjinsa yayi da wani irin mugun ciwo,da qyar yake iya jan numfashi,ya laluba hannunsa ya kunna fitilar gefan gado,haske ua gauraye dakin nasa,shi daya yake kwana,bai taba takurata ko sau daya akan su hada makwanci ba,hasalima ta lafiyarta yake,ya sauko daga gadon ya fita waje don ya samu ruwa mai sanyi yasha ko qirjin nasa zai sake,ya tabbatar ciwon da yaketa dannewa ne yau yaci qarfinsa.
Haki ya dinga yi sosai bayan yasha ruwan,ya samu hannun kujera ya zauna yana riqe da qirjinsa,a hankali ya fara kiran sunan Allah ganin ciwon yana neman yafi qarfinsa.
Tana yawan fama da qishirwar dare,tsakiyar baccinta ta tasheta,ta farka a hankali tana mutsitsike idanu sannan ta zauna sosai tana kallon sashen da abbas din ya zauna dazun,wayam babu shi,ya zauna ne yana karanto mata wasu laifuka cikin system dinsa da wasu suka aikata ya kamasu ya kaisu kotu da hukuncin da kotu ta yiwa kowannensu,batasan sanda bacci ma ya dauketa ba.
Ba ruwa a dakin,dole ta gyara farar hular data dora kan sassalkar sumarta ta zura bedroom slippers dinta ta fito.
Da farko tsorata tayi jin alamun mutum cikin parlor din,amma kuma sai sautin muryarsa dake tashi can qasa ta gaya mata waye,cikin tashin hankali sosai ta iso gareshi.
Gaba daya ta rude da yadda taga ya fita a hayyacinsa,tana ta son ta kira wani cikin mutanensu na nan amma ya riqe hannunta gam ya hanata motsawa,batasan sanda hawaye ya fara zaryar saman fuskarta ba,yanayin yadda yake riqe da qirjinsa ta tabbatar ulcer dinsa data jima bata tashi bace a yau ta tashi,kuma ko bai gaya mata ba ta tabbatar abincin data bashi ne yaci.
Sosai hankalinta ya tashi,gani take kamar mutuwa zaiyi a daren,kamar bazai kwana ba,indai hakan ta kasance kenan itace ajalinsa?,abinda ya sake daga mata hankali ta fashe da wani irin kuka mai tsuma rai.
Duk da cikin ciwo yake amma hakan bai hanashi jawota cikin jikinsa ba yana dan bubbuga bayanta
"Kayi haquri daddy,ni na jawo maka"
"Shshshsshsh" kawai yace da ita,sai tayi lamo cikin jikinsa,cikin ikon Allah zufar jikinsa ta fara raguwa,kasa sakinsa tayi,har zuwa sanda taji numfashinsa yana sauka a hankali da alama bacci ya fisgeshi.
Har zuwa lokacin bata bar share hawaye ba,ta sake qanqameshi cikin jikinta tausayinsa ya kamata a karo na farko,hajiya ce ta fado mata,tayi imani inda tana raye ko meye zai faru bazaikai tsananin wannan ba,ta tuna maganarta ta qarshe akan abbas da affan
"Allah ya baki ikon riqesu gaba daya" har maganar ta bawa widad din mamaki,ashe kusan wasiyya hajiyan ke bata.
Dukkansu kukan affan ne ya tayar dasu,da tafiyarsa daya fara koya ya qaraso wajen,sai abbas din ya miqa hannu yana daga kwancen ya daukoshi cak ya azashi saman ruwan cikinsa yana kallon yaron fuskarsa dauke da murmushi
"Am sorry son.....na hanaku bacci kai da mamanka ko?" Ya fada a karye,saita miqe ta zauna sosai tana masa sannu kafin ta kalli agogo,an riga an idar da sallar asuba,dole sai hakanan suka yita a makare.
Yau din musayar aiki akayi,ta hanashi yin komai tayi dukkan wani aiki kamar yadda ta saba a baya,yana kwance yana binta da kallo,duk inda ta gifta sai wani abu ya motsa ransa,zuciyarsa bata masa dadi da yadda ya zargeta ya dasa bacin rai a ranta,ashe yaransa har biyu suna kwance a mahaifarta.
Wuni sukayi ranar a tare,har bayan la'asar tana ta hidimar hada musu abincin dare,affan yana kwance saman cikinsa,tayi tayi ya dagashi saboda qirjinsa amma yace
"Ki qyaleshi,yayi missing dina shima" tasan akwai magana a bakinsa amma ta shareshi.
Cewa yayi tazo ta dauke affan din,tana isowa yasa hannu ya janyota jikinsa,sannan ya sauke affan a gefe,sosai ya sakata cikin jikinsa yana kallon fuskarta
"Da gaske widad....bagarar dani kiketa yi,yau kwanaki nawa da dawowarki,da gaske bakiyi missing dina ba?,hala kin daina sona?" Ya fada murya a karye,hannu tasa tana ture fuskarsa daga tata,saboda wani nauyi yake sakar mata da manyan idanun nan nasa
"Daddy bamu da lafiya dukkanmu,ka barmu mu warke cikin salaama" ido yadan lumshe sannan ya budesu ya zubesu fes kan fuskarta,saita janye idanunta tayi kamar bata ganshi ba
"Alright.....jibi nakeso na wuce bauchi" ta daga kai a hankali ta kalleshi,ranta yadan quntata kadan da zuciyarta ta tuna mata da hafsat,wajenta zaije kenan?,kamar yasan me take rayawa sai yace
"Wani aiki ne mai muhimmanci ya tasomin"
"Amma daddy,su office din basusan har yanzu baka gama warkewa ba?"
"Saun dauka na gama warkewa sumul,tunda sunsan ina da jarumar mata dake bani kulawar dake warkar da zuciya da gangar jiki,basusan wannan karon ta zama raguwa ba" kanta ta kawar kawai,tasan jan magana yakeso,ya saki boyayyen murmushi,wannan boyayyen fushin nata ya barta ne kawai,yana jiran lokaci,zai sauke mata shi tassss,a yanzun taci albarkacin abinda yake jikinta ne,amma itama ta sani,yasan lagonta fiye da yadda take tsammani,ya kauda shurun da ya wanzu a tsakaninsu
"Aikin yana da muhimmancin da bazai iya jikirtuwa ba,saidai kiyimin fatan nasara kawai" ya fada yana lumshe idanu,yana tuna wayar da sukayi dazu da umar dinsa,wadda a qalla ta kwashesu kusan awa guda.
"Allah ya bada sa'a ya kuma bada nasara"
"Ameeen ya hayyu ya qayyumu".
Bayan ya kwantar da affan sai ya bita kitchen suka kama aikin tare,ba wata doguwar hira a tsakaninsu,amma lokaci lokaci tana kamashi yana satar kallonta,kallon da batasan na meye ba,daga bisani ya gaza jurewa,ya zagayo ta bayanta ya riqe qugunta sosai ya jawota cikin jikinsa, ya dora habarsa saman kafadarta
"Wannan cikin yayi miki kyau fiye dana affan,ina fatan zaki bani baby girls masu kama dake this time around" murmushi ta saki tana jin saukar numfashinsa har cikin kunnenta,hakan kuma ya fara tayar mata da tsigar jikinta,saita zame a hankali
"Eheeennnn.....gwara ma ka fadi gaskiyar ka,koda baby girls dinne masu kama dakai kakeso,ka dauka ba'a gayamin ba,sanda na haifi affan yadda ya deboka ya dinga maka dadi har baka iya jure fada" siririyar dariya ya saki,ya koma ya jingina da kitchen cabinet yana kallon kyakkyawar fuskarta
"Bakisan kin fini kyau ba?,affan namiji ne,duk munina idan yayoni ba matsala,kinga kenan dama baby girls din ne yafi kamata su dauko ki ko?" Yadda ya kira kansa da mummuna ya sanyata dole ta daga kai tana sake dubansa da kyau,suka hada ido yayi wani kalar tausayi kamar ita zata zana masa yaran,sai dariya ta qwace mata.
A sirrance ya sauka a bauchi,ba wanda yasan ya iso bauchi sai umar,ya kuma gana da manager din hotel din a ranar bayan ya kama daki a wani hotel na daban.
Duk wani dauka na cctv camera dake hotel din saida yasa aka sauke masa,tun daga kwanan watan da kwanyarsa zata iya riqe masa na sanda suka fara zuwa weekend shi da widad,ya wuce dasu dakin hotel dinsa dasu.
Sai da ya gama komai ya nutsu sannan ya fara bibiya,komai tiryan tiryan,bayan ya bawa umar wasu yace ya tayashi,amma ya tabbatar sai yana kebantaccen waje kamar haka.
Aikin ba wani sabon aiki bane a wajensa ba,yana da kafiya da jajircewa akan aikinsa,idan yasa qahon zuqa akan abu sai ya ganoshi,saidai idan baiyi niyya bako bai sa kansa ba,wannan na daya daga cikin sirrin samun qarin girmansa akai akai,dom haka kuma zama bibiyat dukka motsin hotel din na watanni bai wani jigatashi ba,daren gaba daya ya sadaukar yayi wannan aikin,sai coffe kawai da yake makawa cikinsa.
Ya tsaya ya jajirce yayi aikinne bawai don har a sannan akwai sauran zargin widad a ransa ba,a'ah,yayi hakanne saboda ya zamana shima yana da hujja kamar yadda