Advertisements
Chapter 20 Reading A Rubucetake Book 2 Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Rubucetake Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Complete Novels

Chapter   20 / 33

57K to 60K   out of 97K words

akayi mata da dukka favourite colors na abbas din don saboda shi din, kome zatayi tana yin sa da colors ko yanayin da tasan zabinsa ne,bata taba duba nata choice din,wannan ya sake sawa ta kama zuciyarsa da kyau.

Fahad ta bawa kwandon,ita kuma ta kulle sashen nata,ta saka affan a kafadarta ta fito.

A seat din baya yasa fahad ya saka kwandon,karon farko da ya rasa duk wata sha'awa na cin abincinta,bama abincinta kawai ba,gaba daya yayi loosing komai da yakeji a kanta,sanda ya daga ido ya hangeta tana takowa,gaba daya ta haske farfajiyar gidan da wani irin kyau da qamshinta daya fara aika saqon tahowarta kowanne sashe na gidan,ita da yaron sunyi wani kyau na kusamman kamar fure,saiya dauke kansa ya maida gefe,yana jin zuciyarsa na masa matsanancin bugu kamar zaya fado daga qirjinsa,abubuwa hiyu suna gogayya cikin qirji guda daya lokaci guda SO YAYYA DA KIYAYYA,soyayyar nason tasiri,amma wani abu mai nauyi yana tasowa ya danneta yana baiwa qiyayyar damar wanzuwa a farfajiyar qirji da zuciyarsa,zuciyarsa na kwadaita masa ya sake kallonta,don ta fito a kamar da yakeso,amma tsananin haushinta ya danne wannan muradin da ransa ke dashi,don haka kafin ta qaraso ma ya shige cikin motar yana haki qasa qasa.

Mamaki ya sake cikata,da kansa a irin wannan lokacin yake takowa ya karba affan daga hannunta ya bude mata motar ta shiga sanan ya miqo mata shi,jiki a sanyaye ta qarasa motar ta bude ta shiga ta zauna, qamshinta ya qarasa baibaye ilahirin motar

"Ina kwana uncle" ta gaaidashi tana dan rusunawa,ya amsa a taqaice ya miqa hannu yana karbar affan,tsam ya rungumeshi a qirjinsa hana jinjina hukuncin da zai yanke wanda har yaron zai shafa,amma dai wannan shine maslaha a wajensa,don yana ji a zuciyarsa bazai taba iya zama da fasiqar mace ba

"Why widad why?,ta ina na gaza?" Ya fada can qasan ransa yana jin wani ciwo,saiya sunkuya a sanyaye yayi kissing goshin yaron ya saka masa dariya kuwa,sai zuciyarsa ta karye,ya miqa mata shi ba tare daya sake kallon fuskarta ba,don kallon fuskarta na gaya masa wani fa ya taba tabata,wani ya taba rabar wanann jikin nata,wani ya taba kwanciya da ita yadda kakeyi,tunanin da yake sakashi jin kamar zaiyi bindiga.

Duk yadda taso yaci abincin ya qiya,dole ta qyaleshi,tayita sako hira a hanyar tafiyar amma yana banzatarwa,ta jinjina kai tana mamakin wacce damuwa ce haka ke damunsa?,don kada fa takura masa daga qarshe sai tayi shuru itama, motar kamar ta kurame,tafiya mara dadi data fara yi dashi tsahon rayuwarsu dashi,har daga qarshe bacci ya dinga daukarta,dama yau din bata samu tayi baccin nata data saba ba.

Lokacin da zasu gifta kano sai taji kamar ta sauka yaje ga ummunta,amma dole ta danne,koshi bata cewa komai ba,batason ta dameshi da magana,tunda ta fahimci a yanayin rashin son magana yake.

Sai bayan azahar sannan suka isa magariba,ta ware idanunta sosai tana jin kewa da shauqin mommynta,tana jin dama ya ajeta wajenta duk da rakiyar aiki tayi masa,ga mamakinta sai taga ya dauki hanyar gidan nasu,ta kasa haquri sanda taga sun shiga unguwar su

"Na gode uncle" kansa kawai ya daure ya gyada mata ba tare da yace komai ba.

A qofar gidan yayi parking,cikin sa'a usama daya daga cikin qannenta maza da mamarta ta haifa a gidan ya fito,cikin zumudi da murna ya qarso wajen,suka gaisa da abbas sannan ya fidda mata kayanta

"Kakaimin jakar kazo ka karbi affan" saboda yadda taji qafarta da mararta duka sun riqe mata gam.

Yana shiga ya fito ya karbi affan din suka shige ciki suka barta,ta buda murfin motar,saidai har a sannan abbas din baice mata komai ba,sai ta dakata da fitar ta waiwayo

"To sai yaushe kenan?,sannan a nan zaka sauka?" Kai ya girgiza mata alamun a'ah,ya bude bakinsa da yakejin kamar ya manne yace

"Ki zauna kawai,sai lokacin dana gama aikin,zanzo na daukeki" duk da yanayin da yayi mata maganar yana saka mata rashin jin dadi a ranta,saboda ba yanayin daya saba mata mu'amala dashi bane,amma jin zata dan zauna a gidan ya mata dadi,tanason kasancewa sosai da mamarta,don tana jin dadin haka,uwa uba tana qaruwa da abubuwa masu yawa,sajta jinjina kai

"Allah ya bada sa'a,yasa a gama lafiya, zamuyi kewarka nida affan" ta fadi a sanyaye da wani abu dake bugun zuciyarta wanda batasan meye ba

"Ameen" ya fada muryarsa a qasa

"Ba zaka shiga ku gaisa ba?" Tayi masa tayi,abinda bata taba ba kenan sai yau

"Later" ya fada a gajarce,saita jinjina kai kawai,ta saka qafarta ta fice a motar jikinta a mugun sanyaye kamar wadda aka zarewa laka.

*H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Part 02

Page 29

Murmushi fal fuskar mommyn nata,fuskartata cike da rahama da qauna irin ta uwa ta amsa sallamar widad din,affan yana hannunta kamar zata maidashi cikinta cikin wani irin tattali,harta fara rabashi da pampers takalmi da socks din jikinsa wai ya sake,shigowarta yasa sauran qannenta guda biyu da ganin affan ya hanasu fitowa suka sake hautsina falon da murna

"Anty don Allah kiyi kwanaki,daddyn affan kada yazo yace ku tafi yadda ya saba" saleem ya fada yana dariya, dariyar itama tayi,idan tazo sam basu so ta tafi

"Aiki dai yazo yi,nasan kuma yana gamawa zaiyi zancan tafiya,mommy yana gaidaki,yanata sauri amma yace idan ya dawo zai shigo ku gaisa"

"Babu Komai,Allah ya bada nasara"

"Ameen" ta amsa mata.

Wunin ranar taga kulawa da tattali daga mommyn nata da qannenta,gaba daya sai suka dauke hankalinta da kuma damuwarta,saidai duk da haka lokaci lokaci abbas na dawoma tunaninta,tana ta tambayar kanta me ya faru?,wacce damuwa ce fa canzashi haka?,batayi tunanin akwai damuwar da zai shiga da har zata jawo rashin kulawa daga gareshi ba,to amma koma meye tana fatan Allah ya warware,ya kawoshi da sauqi.

Lafiyayyen dakin data saba sauka anan ma yau din ta sauka,bayan ta gama komai zata kwanta ta sake duba wayarta,abun mamaki babu kira ko saqon abbas din,abinda bai taba faruwa ba a tsakaninsu,cike dai da mamakin da har a yau ya kasa sakinta ta soma lalubar layinsa,mamakinta ya sake ninkuwa sanda wayar taqi shiga,tayita gwadawa harta gaji ta haqura ta kwanta.

Sai da tayi kwana biyu a cikin wannan yanayin,saidai ko kusa ko alama bata gayawa mummy ba,abinda yadan rage damuwarta a kwana na biyun taga miscal dinsa,koda tabi saita kasa samunsa,saita haqura,tayita zuba ido ko zata sake ganin kiran nasa.

Washegari da safe ta gwada kirannasa,cikin sa'a ta sameshi,tun kafin ya daga ta sauke ajiyar zuciya,ta koma gefan gado ta zauna,dab da zata tsinke ya daga,lallausan muryarsa ta daki kunnenta cikin sallama,ta lumshe idanunta sannan ta budesh,a mugun shagwabe tace

"Uncleeeeeeh.....hmmmm" har cikin jininsa yaji wani abu ya tsarga masa amma wani abu mai girma yazo ya ture komai

"I will call you ina hanyar bauchi" murna ce tadan kamata,ko ya koma ne ya barta daga bisani zai dawo kenan ya dauketa?,bata gama tunanin ba ya yanke wayar,saita sauke wayar itama tana murmushi,daga lokacin ta zama kusa da wayarta don batason tayi missing kiransa,amma har wasu awanni suka shude Shuru ba kiransa babu alama.

A nutse ta bude k'ofar toilet din ta fito daure da babban towel fari sol,lallausar farar fatarta mai santsi da sheqi tana ta daukan idanu,wadda hakanan take koda yaushe saboda bata wasa da gyaran jikinta.

Gaban dressing mirror din dake dakin ta isa,ta ja kujera ta zauna tana kallon fuskarta a ciki,gaba daya jin ranta da jikinta takeyi babu dadi,fuskarsa ke gilma mata cikin idanuwanta,sam jikinta bai bata ba,zuwa yanzu ta fara shakka,zuciyarta ta fara mata kokwanto,ta kasa nutsuwa gami da gamsuwa da wannan tafiyar da ya qirqirar mata bagtatan lokaci guda,tana tsaka da hidindimunta,tun daga yanayi fuskarsa da kuma yadda ya dinga tuqi daga bauchi zuwa katsina takejin kamar ba abbas dinta ba,tabbas akwai abinda ke faruwa,akwai wani muhimmin abu dake gudana,tayi tunani har babu iyaka,ta laluba dalilin tas tun daga randa ya sanya qafa ya fita daga gidan zuwa dawowarsa da kuma isowarsu katsina......tayi zagaye cikin tunani da abubuwan da suka wanzu kaf! Ta kasa gano abu guda daya farun.

A iya saninta sun rabu suna masu kewa da kuma shauqin juna kamar ko yaushe,hakanan koda yana hanyar sokoto safiyar ranar sun jima ita dashi akan waya suna hira,wata irin hira irin wadda ke fallasa sirrin zuciyar masoyi zuwa ga dan uwansa,yana ta mata qorafin a takure yake acan din tare da mita tana lallabashi tana kuma masa dariya,har suka rabu kyawawan kalamai ne bisa fatar baki da zuciyar kowannensu,to amma me ya canza hakan?lokaci guda ya dawo bauchi a hargitse?,ya kuma tsirar mata tafiya katsina a dare daya?.

"AKWAI WANI ABU" ta fada murya qasa qasa tana motsa tausasan lips din bakinta tare da zare idanunta daga kallon da take qarewa fuskartata,ta dauki lotion dinta mai taushi da qamshi ta fara shafawa fatarta cikin kasala taraddadi da kuma damuwa.

Duk bayan wasu mintuna saita kalli wayarta dake gefe tana tsammanin kiran,saboda ta sani haka suka sabarwa juna,duk inda zashi cikin nigeria..... matuqar tafiyar mota zaiyi itace abokiyar hirarsa har ya isa inda zashi,idan kuma hakan bata kasance ba.....zaiyita kiranta har ya isa din,amma wannan karon ko gilmawar miscall dinsa bata gani ba bare kiransa,bayan ya gaya mata zai kirata din,sanann a qididdigen da tayi a yanzun kuma, tabbas koda baije gida ba yana gab da isa

"Waishin meke faruwa?" Ta sake jefawa kanta tambayar wata irin damuwa tana tabata tun daga qasan zuciyarta.

Cikin dauriya ta shirya kanta cikin doguwar rigar atamfa,ta fidda ainihin kyanta da surarta sosai,duk da yanayin da take ciki sai data tsaya gaban mudubi ta kalli kanta,lokutta da dama takan dubi kanta da kanta tana tuna WACECE ITA A SHEKARUN DA SUKA SHUDE,a yanzun sai taga kamar ba ita ba.....komai yana zuwa yana shudewa da wani irin sauyi mai ban mamaki.

Lausasan slippers ta zurawa qafarta,sannan ta isa bakin qofa ta kama handle din ta bude tabi siririn corridor din da zai sadaka da ainihin falon gidan.

Tun bata qarasa ba ta hangeta zaune cikin falon,mommynta......halittace mai girman matsayi a wajenta,halitta dake sahun farko cikin halittu mafi soyuwa a wajenta,a duk lokaci irin wannan da zatayi balaguro ta taho takanas saboda kasancewa da ita.....duniyarta kan cika da farinciki,takanji a duniya yanayi irin wannan bashi da tsaara a wajenta.

A jikinta taji tahowarta,saita dauke idanunta daga kan tv din da take kalla ta maida kanta,kusan lokaci daya suka sakarwa juna murmushi,ta kuma rigata magana

"Wannan nauyin wankan naki dai yana nan,affan ya fara kuka har sai da aka fitar dashi" cikin karaya da rauni da takeji cikin gangar jikinta da zuciyarta ta qaraso dab da ita ta zauna,tana shirin amsa mata.....kamar me kiran yana jiran dai dai lokacinne kira ya shigo wayarta,a hanzarce ta daga wayar tana duba me kiran, zuciyarta cike da fata da burin ganin wanda ranta ke darsa mata.

Batasan sanda murmushi ya subuce mata ba hadi da fitar siririyar ajiyar zuciya ba

"Ina zuwa" tace da mommie,ba zata iya amsa wayarshi a gabanta ba,ita kadai tasan hottest words da suke gayama junansu,kuma muddin aka samu mishkila mommie taji daga ita har shi sun gama tafka abun kunya.

Kai tsaye dakin ta koma,ta samu gaban madubin data tashi dazu ta zauna tana yunqurin daga wayar

"Assalamualaikum" ta fada a shagwabe tana karyar da wuyanta gefe,abu mafi soyuwa kenan da tasan yana so tattare da ita,har yau kallonta yake cikin madubin da yake kallonta shekarun baya da suka shude,bata canza a idanunsa ba

"Wa'alaikumus salam" mummunar faduwa gabanta yayi daka jin sautin muryarsa me taushi da sanyi da yake mata magana da ita koda yaushe ta juye zuwa wata iriyar murya,irin muryar da yake magana da cirminals a yayin da aikinsa ya biyo ta kansu.....irin muryar da yake magana da juniors dinsa a yayin da suke hurumin aiki......irin muryar da yake magana da ita a duk sanda ya shiga qololuwar bacin rai da fushi akan wani,muryar da bata taba jin yayi mata magana da ita ba.

Kowacce gaba ta jikinta tayi sanyi,tayi namijin qoqarin tattaro nutsuwarta da juriyarta tace masa

"Ka sauka lafiya?,ya kaje gida"

"Me yasa zaki aikata min haka?" Ya fada muryarsa tana ninka ta da kaushi da ban tsoro,daga cikin wayar tana iya jin hucinsa,da alama a matuqar bacin rai da kuma fusata yake, tambayar tasa kuma ta dilmiyar da ita kogin tunanin ina ya nufa ne?,kafin ta lalubo amsa kunnuwanta sun fara isar mata da saqo mafi muni cikin rayuwarta,daga bakin halitta mafi soyuwa a gareta

"Ashe haka kike?,ina miki kallon saliha ashe mayaudariya ce ke?,maciyar amana ce?,macuciya ce ke?,na baki dukkan yarda,na damqa miki rayuwata ashe zaki wasa da rai na da lafiyata?zaki wasa da mutunci na?" Wani irin tashin hankali ne ya sauko mata,me abbas ke fada ne

"Me nayi maka?,abban affan me ya faru?,kasan me kake fada kuwa?"

"Na sani!,nace miki na sani, tsahon yaushe tsahon kuma wanne lokaci kika dauka kina cin amanata kina kuma ha'intata WIDAD?wadanne watanni kika dauka kina aikata cin amana a gareni a sanda ni na baki yarda!" Kasa zama tayi,ilahirin jikinta ya dauki tsuma,sai ta miqe tsaye qafafuwanta suna rawa

"Kana cikin hankalinka kuwa abban affan?,a ina kake yanzu?" Ta tambayeshi don ta tabbatar da cewa he's safe,ba gusar masa da hankali akayi ba yake gaya mata hakan

"Har kinyi wayon fara bin maza?,ki kwana a hotel?,hakan bai isheki ba har sai kin dauko gardi kin kawomin gidana?,kin kuma kaishi har gadona na sunna widad?,wane laifi na aikata miki haka dana cancanci irin wannan hukuncin?" Yayi maganar ta qarshe muryarsa a wani mugun karye,saidai zafi da kaushin nan suna nan taf a muryarsa

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ta fada a bayyane,qafafuwanta suka hau rawa,gabanta yayi wani irin bugawa da zuciyarta ta hasko mata abinda yake magana a kai.

"Hotel kuma?" Ta tambayeshi muryarta na wata mugun rawa,irin rawar dake bayyanar da zallar daburce wa a sanda aka ritsaka bisa wani abu na rashin gaskiya

"Bakije bane?,ko zaki sake shiryamin qaryar da kikayimin a lokacin da na tambayeki?"

"Naje,tabbas naje....amm......"

"Ya isa!!!!" Abinda ya fada kenan a tsawace

"Abinda nakeson ji kenan kuma naji,kije ke da Allah,bazan taba yafe miki ba,amanata da kikaci ubangiji ne kawai zaiyimin sakayya,Allah ya isa ban yafe miki ba!!!" Kit! Wayar ta katse

"Abban affan,daddy!!!" Ta fada a gigice,saidai tuni ya katse layin

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ta sake maimaitawa jikinta na wani irin kyarma tana yunqurin binsa,saidai a take kamfanin sadarwa suka gaya mata is switched off,saita saki wayar ta sulale a wajen tana sakin wani azababben kuka,wani abu mai tauri da zafi yana tokare mata qirji.

"Waye ya ganta?,waye ya gaya masa?,waye???" Ta soma nacin gano daga inda maganar ta fita

"Hafsah" taji an bata amsa daga can tsakiyar zuciyarta,kukanta ya tsaya cak na wasu sakanni,sai ta sake rushewa da kukan tana jin kanta yana sara mata,tana son miqewa amma ta kasa,idan tayi kamar zata tashi sai jiri ya maidata ya kayar,a haka aka turo qofar dakin,ta daga idanunta da taji kamar basa dauko mata hoton komai da kyau ta tsurawa qofar idanu tanason tantance mai shigowar.

*H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Part 02

Page 30


Mummy ce dauke affan da yake faman tsala kuka,kukan nasa daya dinga shiga kunnuwan widad kamar a duniyar mafarki

"Karbeshi ki bashi yasha,kamar bacci yakeyi" mummyn ta fada tana miqa mata shi,saidai ko motsawa batayi ba bare tayi azamar karbarsa,abinda yaja hankalin mummyn kenan

"Ke widad.... widad lafiya?" A hankali ta ajjiye affan ta zauna tana jan widad din cikin jikinta gami da ambaton

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Hasbunallahu wani'imal wakil" ganin kamar tana neman fita a hayyacinta,addu'o'i ta soma karantawa tana shafa mata a fuska,a hankali sai nutsuwarta ta fara dai daita,ganinta ya fara dawowa dai dai,ta zubawa mummyn idanu wasu hawaye masu zafin gaske suka fara zarya akan fuskarta.

"Meyake faruwa?,me ya sameki?"

"Mummy cikina ne yakemin wani irin ciwo"

"Ya subhanallah" ta fada wani sashen na zuciyarta yana mata wasi wasi,yanayin da taga ta shiga baiyi kama da yanayin ciwo ba,yafi kama da wanda yaga wani mummunan tashin hankalin

"Bari na kira saleem sai mu muje kiga likita,ai bai kamata a zauna ba" kama hannun mummyn tayi

"Aah mummy,addu'a zakici gaba da yimin,ko yanzun da kika yimin na samu sassauci" kai ta jinjina badon ta yarda da widad da abinda yake damunta ba,a haka ta sakata ta shayar da affan saita sake karbarsa ta fita,saidai fiye da rabin hankalinta yana kan widad din,duk bayan wani lokaci saita leqata tare da tambayarta ya jikin?,akwai abinda take buqata?,saidai tace babu.

A ranar yadda taga baqar rana haka taga baqin dare,baqin daren daya zame mata baqiqqirin,yayi mata kuma tsaho tamkar daren mutuwa,tayi dukka Wani qoqari na fahimtar da abbas abinda yake zato ba haka bane amma yaqi saurararta,ta kira har

20 / 33