Author : Mamuhgee Category : Complete Novels
daina ji na wasu sakanni kafin su dai daita, bakinta da dukka ilahirin jikinta ya fara rawa,Allah ya taimaketa ta kama kalmar
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" kuka mai tsananin qarfi ya qwace mata,sai kuma numfashinta ya fara sarqewa,ta fara kokawar qwatarsa,daga haka kuma saita daina gane komai.
Sanda ta farka cikin setting room ta samu kanta ita da hajjaa nujood da bilkisa matar suraj,suna mata sannu amma sake tanbayarsu take da gaske hajiya ta rasu ko kuma mafarki tayi?.
"Allahn da ya fimu sonta ya dauki abarsa,addu'a ce kawai zata nuna zallar soyayyar da muke mata ba koke koke ba" nasihar da suka dinga mata kenan cikin kwantar da kai, saita fashe da kuka sosai tana jerawa hajiya addu'o'i har kamar ba zata tsaya ba,a haka suka miqo mata affan daketa rigima ta soma shayar dashi,amma hawayen fuskarta yaqi tsayawa,duk sanda ta kalli affan din sai taji zuciyarta ta sakeyin rauni,yayi rashin kaaka,kuma masoyiyarsa,wanda tun yana ciki take qaunarsa da begen ganinsa amma Allah bai qaddara hakan ba.
Ba shakka hajiyan ta dace,domin dukkan wata siffa dake alamta kyakkyawan qarshe hajiyan ta sameshi,kama daga yanayin yadda ta mutu da cikakkiyar kalmar shahada a bakinta,zuwa yabo data dinga samu daga wajen mutane,gidan kamar xai tsage da jama'a,har maqwafta a cike yake babu masaka tsinke.
Ta idar da sallar la'asar tana zaune saman abun sallah,har a sannan qwalla bata bar fita daga idanunta ba,tuni kanta yake sara mata da matsanancin ciwo,husna 'yar nasmah qanwar abbas ta shigo mata da abinci,ta kalleta ta kalli abincin
"Ina abbansu mimi ne?"
"Ni tun safe ban qara ganinsa ba" hankalinta sai ya qara daukuwa a kansa,tasanshi sarai,tasan irin soyayyar dake tsakaninsa da hajiyan,ya kamata a duba halin da yake ciki,itama tunda tazo bataji an ambaceshi ba,don haka ta miqe ta goyawa husna affan sannan ta canza hijabin jikinta zuwa babban daya saukar mata har qasa ta fita a dakin.
Da qyar aka gano mata shi a dakin su umar,sanda tayi sallama ta shiga dakin kasa ganinsa tayi saboda duhun da dakin yake dashi,ta laluba makunnin fitilar dakin ta kunna,haske ya wadaci ko ina,mamaki ya kamata ganinsa zaune saman abun sallar, idanunsu suka hadu waje guda,sai taji wani rauni ya ziyarceta,kuka take da muradin yi amma kuma zuciyarta na gaya mata ba haka ya kamata tayi ba.
Takowa tayi a hankali zuwa inda yake zaunen har yanzu idanunsu na manne da junna,fuskarsa ta fada wuni guda,sai wani irin jigata da idanunsa sukayi,dab da zata iso ya shafa addu'a sannan ya miqa mata hannunsa,ta dora nata hannun akai,zai mata masauki saman cinyarsa ta zame ta zauna daga gefansa tana kallon qwayar idanunsa dake cike da wani irin tashin hankalin da ba kowa bane zai iya karanta,tsananin jarumtarsa ya boye komai
"Yaushe kukazo?" Ya tambayeta da wata irin murya dake cike da sanyi da jigata,ta danyi gyaran murya kadan don kada ta fashe masa da kuka
"D'a.....d'az......" Kasa qarasawa tayi,dukkan wata jarumta ta qare,saita fashe masa da kuka harda sheshsheqa,baice komai ba illa rungume kanta da yayi a qirjinsa yana shafa bayanta,yadda kanta ke qirjinsa haka take jiyo yadda Zuciyarsa ke wani irin bugawa a hagunce.
Mintuna kusan biyar ta dauka a haka sanann ta fara qoqarin saita kanta,ta daga kai tana dubansa da idanunsa da suka sauya kala,hannu biyu yasa yana goge mata hawayen sanann yace
"Nasan ba wannan ne kukan da kika fara ba,pls karki qara yin wani kukan,hajiya bataso,kiyi mata addu'a" kai ta jinjina cikin aro jarumta,ta gaidashi tare da yi masa gaisuwa,don ya fita cancantar ayi masa gaisuwa,duk kuwa da cewa itama kallon uwa takewa hajiyan,ba zata taba mantawa da gudunmawa da soyayya qauna da kariya data baiwa rayuwarta ba.
"Amma uncle,me kakeyi a nan kai kadai a duhu?"
"Sallah nayi,baki gani ba sanda kk shigo?" Kai ta jinjina
"Na gani,amma idan ka shiga cikin jama'a kamar sai yafi,a nan din tunani zaiyi maka yawa ne" kai ya jinjina kawai
"Kaci abinci?" Ya sake girgiza mata kai,saita ajjiye masa affan ta shiga cikin gida ta samo masa abinci me kyau,saidai gaba daya ya kasa ci,ya ture plate din yace
"Samomin coffee kawai ya isa" haka ta koma ciki ta hado masa coffee din,a hanya ne suka hadu da hafsat tana shigowa goye da yusra,yadda ta dauke mata kai itama haka ta bawa banza ajiyarta ta shige.
Coffee din ya shige cikinsa da qyar,ya kama hannuwanta ya riqe cikin nasa yana cewa
"Allah yayi miki albarka" don badon tazo ba yanajin azumin yini biyu zaiyi,don shidai ko qyallin hafsat bai gani ba,duk da ya tabbatar tana gidan,don suna gaban gawar hajiya ta shigo gidan tana runtuma ihun da sai da akayi mata magana.
Bata barshi shi kadai ba sai data sashi gaba ya fito daga dakin ya koma cikin mutane,duk bayan wasu lokutta kuma tana sawa ana duba mata shi da yadda yake.
To rashin mahaifiya wani rashi ne mai mugun ciwon da fadin radadinsa bazai misaltu ba sai wanda Allah ya jarabta dashi, rasuwar hajiya rashine na dukka dangi dama mutanen unguwa,kowa yaga tsananin jarumtar abbas,don ba wanda baisan irin shaquwa da qaunar dake tsakaninsu ba.
A gidan yake kwana shi da widad din,amma daki daban daban,hafsat kuwa yaran take diba su wuce gidan iyayenta su kwana,sai kusan azahar take zuwa har akayi kwana uku.
Randa akayi sadakar ukun da safe ne tsananin ciwon kai na rashin bacci da kuma damuwa suka sanya abbas a gaba,dole ya buqaci tafiya gida don ya kwanta ya huta,duk da bashi da tabbacin yiwuwar baccin.
Farko hafsat yasa widad ta nemo masa su wuce tare,don yasan gidan kansa yayi qura,sanann widad din tana jego ga kuma mutuwar itama yadda ta bugeta tilas tana buqatar hutu,to amma sama da qasa babu hafsat din ba alamarta,dole yasa widad ta shirya suka wuce gidan.
Sosai ta gyara masa bedroom dinsa irin yadda tasan yana so,sannan ta shirya masa dan abinda zaici mai dadi da ruwa ruwa,ta kuma hada masa ruwan wanka mai dumi sosai da qamshi,yayi ya canza kayan,ta sashi a gaba yaci abincin ya kwanta sannan ta baro masa dakin bayan ta sanyashi yayi addu'a.
Falon ta dawo taci gaba da gyaranshi,tanayi tana duba affan dake kwance yana watsal watsal da qafa,ya cusa yatsunsa biyu a baki.
Doko qofar falon akayi lokaci guda ba zato ba tsammani,har affan dake kwance yadan firgita
"Subhanallahi" widad ta fadi tana duban bakin qofar.
*H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Part 02
Page 19
Hafsat ce a wani birkice sanye da hijabi ruwan qasa,fuskar nan cike taf da bala'i,tun sanda ta dawo taji sunyo gida da abbas din hankalinta yatashi,kullum fatarta da addu'arta yarinyar ta tafi kenan,sai gashi ta dawo rayuwarta tsundum
"To mayya natacciyar dole,da kika tashi dawowa ai saiki jira girki yazo kanki,bawai ki biyomin miji kihau aikin da ba naki ba" sosai maganar tata tayi mata ciwo,kamar ba zata tanka mata ba,amma saita dago daga gyaran throw pillows din da takeyi ta kalleta
"Maita da naci ga miji inajin isace wannan,wadda bata isa ba ko tayi babu riba,mukan da mukeyi alhmdlh akwai riba, miji kuwa babu wata rana da na kebe da zan tsame hannuna daga bashi kulawa saboda na girkina bane muddin yana da buqatar kulawata,ke meye ya hanaki tsaiwa ki bashi kulawar idan har kin damu dashi?" Ta fadi kanta tsaye tana kallon idanun hafsat da mamaki ya kasheta.
Turqashi!,anzo wajen,yau ta samu dama,tanajin babu abinda zai hanata cin uban yarinyar yau abinda ta jima tana buri,kamar widad din ta karanci hakan,kuma bataso tayi abinda zai tada abbas di daga bacci,don haka tayi hanyar kitchen da dan saurinta
"Dawo mana qaramar mara kunya kiga yadda ake yinta yau a fidda raini" hafsat ta fada tana bin bayan widad,dama abinda widad din keso kenan,don haka tadan daga qafa,tana shiga kitchen din ta tsaya tana ajjiye plate din hannunta,dai dai sanda hafsat ta qaraso ta dora hannunta a kafadar widad da nufin damqota.
Tankwabe hannunta widad tayi cikin fushi tana kallonta
"Sakeni,karki sake gigin riqeni,idan raini kikeso a fidda ki bari ya gama baccinsa ya fita a gidan ya zaman dagani sai ke,a sannan zan nuna miki cewa jaa da baya ga rago ba tsoro bane,shashasha wadda har yau batasan ta girma ba" ta dire maganar da tsaki mai mugun qarfi.
Tsananin mamaki ya sanya hafsat din mutuwar tsaye tana kallon widad,cikin fushi ta yunquro a karo na biyu kafin tace komai widad ta rigata yin magana
"Kika sake kika dora hannunki a jikina.... wallahi tallahi sai nayi miki wanka da wannan ruwan zafin,sauna kawai,shashasha"tayi maganar tana fidda manyan fararen idanunta waje a kan hafsat din.
Abu makamancin wannan bai taba hadasu da wida din ba,don haka furucinta ya tabata sosai,sai taja da baya tana tafa hannuwa
"Ashe da 'yar kalare nake zaune?,dama kanawa 'yan sara sukane mazanku da matanku?,to shi wanda ya baki daurin qarqashin yimin rashin mutuncin bari na tasoshi" saita juya tana haramar fita a kitchen din.
Ai widad bata barta takai qofar ba ta sanya hannu ta fincikota saiga hafsat warwas a qasa,ta isa bakin qofar kitchen din ta tsaya riqe da qugunta
"Azzaluma mara imani,wanann baccin dai yau sai ya yishi wallahi duk baqincikinki da baqin halinki" sai kawai taja qofar kitchen din ta kulleta aciki,bata da wata hanyar fita kuma saidai tabi ta qofar baya ta kitchen din ta fice,saita isa qofar part din nasa shima ta kulle,sannan ta saki ajiyar zuciya tana jan tsaki a ranta.
Sam ta daina ragawa matar,zata nuna mata ita din bakanuwa ce,duk da ba jininsu bace amma kuma cibiyarta na bunne anan,tana jjn surutanta da zage zagenta sama sama har ta daina ji,da alama tabi ta qofar bayan ta fice.
Yayi bacci kuwa sosai,don bashi ya tashi ba sai dab da magariba,a sannan widad din tayi wanka a nan sashensa ta sauya shigarta da wani sky Blue din material me kyau,ta daure kanta da band ta kuma dora dan yalolon mayafin material din,affan na kwance daga gefe cikin farar overall yana bacci abinsa shinfide cikin farin towel.
Tunda ya fito yaga dukansu sunyi masa kyau uwa da dan nata,karon farko da ya fara ganin mai jego mai tsafta irin haka,abinda bai saba gani ba,idan hafsat na jego idan kaji ana jaga jaga ko itace,duk wani kalar qarni da bashi bashi zaka jishi,idan anyi magana takance jego take,dama wannan ai shine jegon inji hausawa,sallamawa sassanta dama yakeyi gaba daya,saidai tazo nashi da ziyara ta wuce.
Ta daga kai daga wayar dake hannunta tana duba saqonnin watsapp suka hada ido,ya sauke mata murmushi yana jin zuciyarsa tana yin sanyi,ya samu nutsuwa kaso hamsin cikin dari daga qunci da rudanin da zuciyarsa ke ciki,ya durqusa a hankali yayi kissing affan dake baccinsa cikin qauna, qamshin da jikin yaron keyi ya ratsa hancinsa,ya daga kai yana sake kallonsa
"Kullum kamanninmu da muhammad sake fitowa takeyi" ya fada da sassanyar muryarsa,ta saki dan murmushi
"Sosai.......kun nunamin son kai ai" ta fada tana dan masa hararar wasa,sai ya saki murmushi yana cewa
"Ba komai,next time by now ya samu yaruwa,ita na tabbatar zatayi miki karar" ido ta fidda sosai tana kallonsa sannan ta langabar da kai
"Habba mana uncle....." Kai ya jinjina yana tarar numfashinta
"Yes.....inason yara da yawa babyn uncle,mutuwar hajiya tasa naji ina son in tara yara masu yawa sosai,just pray Allah ya bamu nagari da zasuji qanmu"sai ta jinjina kai tana cewa
"Ameen".
Bai fita sallar magariba ba sai da yaci abinci ya sake wanka,kafin ya dawo ta sake gyare komai,ta budade falon da qamshi yadda zai masa dadin zama.
Sai da akayi isha'i ya dawo,ya zauna a falo suna taba hira,yana kan kujera tana zaune a qasa,qafarsa saman cinyarta tana matsa masa qafafunsa a hankali cikin wani salo da ya sake saukar masa da nutsuwa,kamar an jehota saiga hafsat ta sake shigowa falon tana kumbura.
Kallo daya widad tayi mata ta dauke kai kamar batasan Allah yayi ruwanta ba a wajen tana ci gaba da tausawa abbas qafarsa,yayin da abbas din ya tsirata da idanu yana kallonta ba tare da yace komai ba
"Daddyn mimi,zuwa nayi na gaya maka ka jawa matarka kunne sanna kayi mana tsakan........"
"Dakata da Allah"ya fada da kakkausar muryarsa yana daga mata hannu
"Bana buqatar wata hayaniya ko tashin hankali,idan ba zaman lafiya bane ya kawoki ba..... please stay away from here" yadda yayi maganar yana nuna kamar ta gundureshi yasa ranta ya quntata sosai
"Adalcin da zakayi kenan?,ba zaka tsaya kaji abinda akayimin bama.....dama kaine kakar daure mata gindi shi yasa kullum take kallon mutane sa'aninta,to wallahi......"
"Shut up" ya miqe tsaye a zafafe yana nuna mata hanya
"Fita banason hauka" hawaye ne suka balle mata
"Yanzu a gabanta kakemin haka abbas?,na rantse da Allah......" Wani mahaukacin mari yakai mata wanda widad ta tabbata inda ya sameta saita rasa haqoran gaba,Allah ya taimaketa ta goce,ba shiri ta juya tana fita daga falon,hannunta dafe da kuncin nata cikin kuka kamar wadda marin ya sameta.
Hannunsa cikin kana ya zauna yana yamutsashi,ya samu ciwon kan ya ragu amma tana neman maido masa bara bana,miqewa widad din tayi tayi mazauni gefans kamar zata shige jikinsa,da kalamai da hikimomi data koya ta samu nasarar saukeshi,ya dinga sauke ajiyar zuciya yana matsa hannunta dake cikin nasa,ba shakka mace ta gari rahama ce,inda bai samu widad din ba ashe da haka zai qare rayuwarsa cikin wahala da baqinciki?.
A daren tason ya barta ta kwana sashenta ta kira hafsat din ta kwana tare dashi,tunda ita din na abinda zata iya masa amma yace bata isa ba,muddin ta tafi ranta sai ya baci,shiba wani abu yake buqata ba a situation din da yake ciki ba,koda batayi masa komai ba kasancewarta a damansa yafi komai kwantar masa da hankali.
Kwanan daga fuskanci widad din tayi ya sake ingizata sosai,wutar qiyayya ta sake ruruwa a zuciyarta,ranar tayi kukan fili tayi na boye,ta kuma tsinewa duk wata kishiya dake duniya.
Washegarin da akayi addu'ar bakwai suka shirya komawa kaduna bakin aikinsa,yabar widad a nan don ta gama arba'in dinta,taso komawa kano amma muhsin yace tazo kenan,dan tsoho alhj salim ya goya masa baya,hakama abbanta,don dole ta zauna a nan,amma ta koma gidan hajjaa ne saboda yadda gidan har yau yake bata tsoro.
********To sannu a hankali kwanaki suka ci gaba da tafiya,al'amuran rayuwa kuma sukaci gaba da gudana yadda suke a baya,duk da ciwon rashin hajiya yana zukatansu,amma dole a yadda da hukuncin ubangiji a kuma rungumi rayuwa a duk yadda tazo.
Zamanta gidan hajjaa taci gaba da samun kulawa,tana kuma sake gogewa da rayuwa da sanin makamarta.
Sanda sukayi arba'in affan yayi wata qiba gwanin sha'awa,yaron kamar ka saceshi ka gudu saboda kyau da wani kwarjini da yake dashi,farat daya yake shiga ran kowa,hakanan itama widad din,kana kallonta zakasan lallai girma da hankali ya soma gameta,ta samu hutu da nutsuwar rai sosai a tattare da ita,ta zama wata big madam,ta kula da jikinta da kyau ciki da waje.
Ranar da sukayi arba'in ranar abbas da yammaci ya diro,da safen sunyi waya da tace masa basuyi arba'in ba sai jibi,saboda batason yace mata zaizo,akwai abubuwan da takeson qarasawa,to ashe yana lissafe tsaf da kwanakin.
Dariya nujood ta dinga yi mata sanda aka saukeshi a setting room,tana zaune dafa'an a qasan carfet sanye da wata riga me qaramin hannu mai kama jiki kamae robber,sai palazzo pants daya zauna mata sosai ya kuma bude yadda ya kamata daga qasa.
Harara ta watsawa nujood din ta miqe tana cewa
"Karki bari aji kanmu dake wallahi" tayi maganar tana zare ribbon dinta da yayi sakwa sakwa tana gayara gashinta,duk da cewa itama taji dadi qasan ranta,don ba qaramin kewarsa tayi ba,to amma kuma taso ta kammala komai ne
"Bani nakar zomon ba" ta gama gyarawa tsaf ta duqa zata dauki affan nujood ta rigata tana cewa
"Rufa masa asiri,kada a jawo masa a matse dan bawan Allah,ku gama gaisawar tukunna sai na kawo miki shi" ta fuskanci jan magana nujood din keji,sai bata sake ce mata komai ba ta juya ta fice.
*H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Part 02
Page 20