Advertisements
Chapter 16 Reading Diddigar Kaya 1&2 Complete Hausa Novel Hausa Novels
Advertisements

Diddigar Kaya 1&2 Complete Hausa Novel

Author :  Fatima Category :  Complete Novels

Chapter   16 / 29

45K to 48K   out of 86.8K words

fadeela saide yana iya tunawa vividly yadda baya barin sashen se da kuka, har ya girma yayi wayau Ammi bata taSa kaunar shi ba, gashi yanzu ya auri ?arta.

Fita yayi yana shirin kashe wayan hannunshi ya danna gallery, Jan kalar riganta ne ya saka shi sake kallon hotunan da suke jeren, hannu ya sa ya danna Waya, dariya ne ya kama shi ganin yadda ta tura baki wai ita nan tana style amma tayi kyau ba laifi, kallon hotunan yake yana dariya marar sauti daga karshe bayan ya gama ya girgiza kai yace
"this girl is crazy"

Ajiye wayan yayi ya kwanta tare da lumshe idanu bacci ya sureshi.

Washegari da safe aka kawowa husna kayanta, duk inda zata Fauza zata ajiye kafa husna na biye da ita, ga surutu tun tana amsawa har ta gaji, yamma likis husna tace se sun yi game.

"Toh faWi wadda kike so se ayi"
Fauza ta faWa don ta addabe ta da maganan game Win nan

Husna tace
"muyi wasan Suya Aunty"

Dankwalinta ta cire ta daurewa husnar suka hau wasan Suya duk sun cika Wakin da hargowa Dukda su biyu ne kachal, bayan husna ta kamata da rigima da satar kallo itama aka Waura mata ta fara laluben husna..

Sam bata ji sallamarshi ba se jin mutum tayi da hanzari ta cabki hannunshi tana cewa
"yeeeeeyyyy wa na kama...?"

Dib dariyar ta ya Wauke jin taushi da sanyin hannun ba na husna bane, da sauri ta zare kyallen dankwalin tana Kallonshi kaman yadda shima yake kallonta...

DIDDIGAR ?AYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuWi ne..
Ze zo muku a Naira Wari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taSa nadama ba>?p?

Karku sake a baku labari.


=???Gureenjoh=???

D?

20

Ihun da husna ta sa na yeeey an kama uncle shine ya dawo dasu daga wata duniyar da suka tafi, da sauri ta matsa baya tana saukar da kanta ?asa, shi kam basarwa yayi ya ri?e husna dake cewa shima a Waura mishi yayi tunda an kama shi yace
"A'a husny zan yi amma Ba yau ba, baki ga yanzu na dawo ba?"

Tace cikin yarantarta
"eh uncle, ina tsarabata?"

Ya kalli Fauxa yace
"Auntynki ta zo ta karSa miki"
Yana kai nan ya juya ya fice.

Husna taje da gudu wurin Fauza tace
"Aunty fauza uncle wai ki je ki karSa min tsarabata"

Fauza tace
"Toh husna"

Husna tace
"Aunty in kallo MBC kan ki dawo?"

Kai kawai Fauza ta Waga, kan ta Wauki hijab Win sallarta ta zura tare da fitowa, baya parlorn don haka Wakinshi ta wuce tayi knocking aka bata izinin shiga.

Ta tura a hankali ta shiga, this is the first Time da ta shigo Wakin, tsaruwa da haduwar Wakin ya tafi da ita kasancewar shi me son fari hakan yasa komai na Wakin fari ne, sossai tsarin rashin hayaniyar Wakin yayi mata kyau, a kan kujera yake zaune ya tankwashe kafa, hannunshi wani daily trust ne yana dubawa.

Ta Wan rusuna tace
"ga ni yaya"

Da hannu ya mata nuni da ledojin da suke kan table wadda Fatima ce ta ajiye ta je kuma Wauko plates da sauran abubuwan da zasu yi anfani dashi ne, yace
"Ki dauka muku Waya"

Tace
"An gode Allah ya saka da alkhairi"

Se a lokacin ya Wago yana kallon face Winta da ya fito fess a onion hijab Win nata, daidai lokacin kuma Fatima ta shigo Wakina gabanta ne yayi wani irin faWuwa wadda seda cikinta ya nemi kullewa, a makogoronta taji wani abu ya ti?e ta me take yi a Wakin nan? Ta tambayi kanta kan ta karasa daidai lokacin ita kuma Fauza ta Wauka ta juyo.

Da wani irin banzan kallo Fatima ke bin ta, ta san duk sbd wannan Husnan nan ne har Fauzan ta samu shigowa Wakin mijinta, daga yarinyar har Fauza ji take kaman taje ta sa musu wuta a Wakin su mutu, sbd yanzu bayan shigan asuban shi duk in ya dawo se ya shiga, gashi Faizan mutum ne da babu fuskan kawo mai wargi ko tace zata hana shi abunda yayi niyya, gaskiya bazata iya hakuri ba kaman yadda take aika mata da harara haka itama ta rama tare da jan tsiririn tsaki wadda ya sake hasala Fatima har bata san ta furta

"kan uba!"
?agowa Faizan yayi yace

"lafiya?"

"Baby yarinyar nan wai ta buge ni kuma ko sannu babu tayi wucewarta?"

Yace
"Fauza?"

Haushin kiran sunan tan ma ya sake mamaye ta tace
"ita fa"

Shi har ya manta da ainihin halinta don yanzu yana ganin babu shiru shiru irin ta, sannan ga saurin bada hakuri wadda wannan na daga cikin abunda yasa tunda ta zo gidan faWa me tsayi be taSa hada su ba don duk Sacin ranshi da zaran ka ce mishi yi hakuri shikenan, fauza bata san shi ba bare ta san lagon shi.

"Tunda har ta fita bata sani bane na san da ta baki ha?uri, yunwa nake ji zo yi serving Wina"

Wani haushi ne ya sake turnike Fatima, yau Faizan ke kare Fauza? A kufule tayi serving Winshi ta mike yana tambayarta bazaki ci bane? Ko bata juya ba tayi ficewarta, girgiza kai yayi yana mamakin halayyar da take nuna mishi tun daga shigowanta gidan, tabbas ba don shi jajirceccen namiji bane da se abunda Fatima tace a gidan za'a yi, ita in har ba'a yi ra'ayinta ba tayi ta fushi kenan tana kumbure kumbure?

Abincin shi ya ci ya koshi ya wuce toilet yayi brush da wanka ya zo ya sauya zuwa kayan bacci, kwanukan ya fitar da sauran abubuwan makulashen da ya sayon ya kai fridge Win kitchen, daga nan ya wuce Wakinta ya samu wai har ta kwanta be tanka mata ba ya fito ya nufi Wakin Fauza.

Suma ya sa mu sun kwanta kuma har ma sun yi bacci, fitowa yayi kawai ya koma dakinshi ya kwanta shima don yana da flight 8 zashi Lagos amma around 9 na dare ze dawo..

Washegari yana idar da sallah yayi sauri ya watsa ruwa ya shirya kan ya fice bayan ya le?a Fatima da bata tashi Bama, don ita wai don ze yi tafiyar sassafe ta samar mai abinci bata san wannan ba sede in yaje airport ya karya a chan kan ya wuce, be damu ba sbd dama chan haka yake yi.

Tana jin fitan motan shi ta mike zaune, tare da sauka daga gadon dama tayi wanka kawai ta saka kaya ta yafa gyalen ta ta fito, tun wata biyun farkon aurensu ya koya mata mota kuma ya saya mata wata karamar Hyundai, direct kitchen na sama taje ta rufe da key, ta sau?a kasa ma ta rufe ta haWe keyn ta watsa jaka kan tayi ficewarta daga gidan.

Bayan su Fauza sun tashi tayiwa husna wanka itama tayi suka gyara gidan tare duk bata lura kitchen a rufe ba se bayan ta gama taje ta murWa kofan ta ji shi a rufe, kitchen na sama ta dawo taji a rufe, da mamaki take kallon kofan kan ta wuce kofan Fatima ta murWa shima a rufe, ajiyar zuciya ta sauke kan ta kama hannun Husna suka koma Wakinta da Tunanin Fatima ba nisa tayi ba Dukda dae ita bata taSa gani an rufe kitchen Win ba duk zamanta a gidan.

Sauran kazan jiya ta turawa husna da Admiral 'A Dukda yayi sanyi sossai haka dae ta lallaSa husnan ta ci, bata san lokacin da zasu dawo ba hakan yasa bata ci ba ita gudun kar kuma basu shigo da wuri ba husna ta sake jin yunwa.

Wasa wasa har azahar babu wadda ya dawo a cikinsu gashi lokacin yunwa ya fara kama Fauza da babu abunda ta saka a cikinta, sauran kazan ta sake baiwa husna ta cinye.

Tun suna kallo har taji bazata iya cigaba da kallon ba sbd yunwa da yake shirin yi mata illa, bayan sun yi la'asar ta duba jakanta ta fiddo kuWin da Jaddah ta sanya mata ciki tun randa za'a kawo ta tare da sanya hijab ta kama hannun husna suka fito, saide me gadin wadda yoruba ne yace mata oganshi ya mishi umurni kar ya barta ta fita daga gidan ba tare da izininshi ba.

Rokon shi ta fara saide tsoron rasa aikinshi yasa be kula ta ba, don Sam be san ita Win matar Faizan bace ba ma, haka suka hakura ganin tsayuwar baze yi musu ba suka koma ciki amma fa ganin magrib yayi ga dukkansu biyu yanzu sun jikkata don husna har ta fara kuka yasa ta sake fitowa ta roke shi ko ze kira mata ogan nashi da Wayanshi don ta san dae duk muguntar Fauzan in har ita ze iya mata to baze iya yiwa Wiyar kaninshi ba, unfortunately layinshi baya wucewa.

Haka suka sake dawowa parlorn kasan tana jin yadda ?asan cikinta ya ri?e kam kam kaman zata mutu, daurewa take tana rarrashin husna da yanzu ta fara kiran iyayenta se tausayin yarinyar ya kama ta, fita tayi ta fara duba gidan, ba irin gidansu bane bare ta iya zamewa ta fita, ba kuma zata iya faWawa me gadi abinci babu zata je su saya ba sbd ta san hakan kaman wani tonon asiri ne ga Faizan wadda be kamata gida kaman nashi ace babu abinci ba me gadin ma ba yarda ze yi ba.

Hawaye ne ya gangaro mata ta sa hannu ta share, bata da waya bare tayi order a kawo mata har gida.

Komawa sama tayi zuwa dakinshi banda sassanyar kamshi shi babu abunda yake tashi, duk irin dubawar da zata yi bata samu wayan da ya ara mata jiyan ba. Kuma Sam bata kula da lockers Win gefen fridge ba waenda snacks ne a ciki da su dangin cereals tunda ta san ita nata babu komai ciki.

A ?asa ta saka gwiwowinta ta Waura kanta a kan gadon hannunta dafe da mararta dake wani irin kugi, husna ce ta biyo ta tana kuka sossai ita tana jin yunwa, mi?ewa tayi ta kama ta tace
"mu je mu yi isha se mu koma ko mai gadin ze yarda mu fita"

Komawa Wakinta suka yi ta bar Wankwalinta anan a Wakinta suka yi sallah shima ba natsuwa, ko da suka sake fitowa neman yiwa mai gadin bayani take saide be kula ta ba, masifa zata fara mishi saide bata da karfin hakan kasancewar bata bar ko ruwa ne ya shiga cikinta ba.

Rarrashin husna kawai take suna tsaye kaman marayu se suka ji horn, da sauri me gadin ya karasa ya duba ganin oganshi ne yasa yayi hanzarin wangale gate Win.

Wutar motar shi ne ya haske mishi su yadda suke tsayen yasa gabanshi faWuwa.
"Peter, me ya kawosu bakin gate?"

Peter yace
"Sir tun da afternoon suke ta so su fita kuma ka ce kar in yarda in bar kowa fita bayan madame, ta sakani nayi ta kiran phone naka saide baya shiga sir"

Ganin hawaye a fuskokinsu duk su biyu ya sa ya san ba lafiya ba, da hanzari ya karasa da motan tare da buWewa ya fito yana kallon su yace
"Fauziyya lafiya? Me kuke yi a nan? Ina Zaku je?"

Kasa magana tayi se hawaye, da gudu husna taje ta rungume shi tana cewa

"uncle yunwa muke ji, tun safe Aunty bata ci komai ba nima sauran kazan da ka sayo mana jiya tayi ta bani kuma ya kare nima na fara jin yunwa, gateman kuma ya hana mu fita mu sayi abinci... Ina ta kuka amma Aunty tana ta rarrashina dukda itama tana kukan bata so na gani"

Wani irin yanayi marar misaltuwa ya shiga, yana rike da yarinyar yace

"yunwa? Fauziyya?? Me ya samu kayan abincin gidan?"

Kanta ?asa tace a hankali
"tun da muka tashi suke rufe"

Kokarin controlling bacin ran da ya shiga yake yace
"Fatima fa?"

"Itama mun tashi bamu sameta ba"

Ze yi magana se ga knocking na Fatima, me gadi yaje ya buWe ta shigo tana ganin Fauzan tace
."Oh baby ashe ka dawo? Ina ta kiranka tun six bana samunka, ka ga ban dawo da wuri ba ko? Wlh na fito lectures 6 mota na ya lalace masu gyara suka ta Sata min lokaci yanzu haka ma na bar musu ne na biyo bo....."


"Fatimaaaa!"
Ya daka mata tsawa muryarshi with so much anger yace
"me ya rufe kitchens Win gidana tun safe?"

Zata yi magana ya sake daka mata tsawa
"don't you dare lie to me, me yasa kika rufe kitchen kika tafi da keys alhali kin san akwai mutane a gidan? Kisa kike son yi? Fatima a gidana har a yini da yunwa??"

Kuka ta fashe dashi tana rasa abun faWa don kwakwalwanta rasa irin karyar da zata yi tayi, in ina ta fara daga yadda fuskanshi yayi turning red ka san ranshi ya kai makurar Saci.

Kallon Fauza da bata sake Kallonsu ba yayi yace
"Fauziyya shiga mota muje"

Wucewa Fauza tayi ta buWe back seat Win motan shi ta zauna yayinda yake rike da hannun husna yana nuna Fatima da hannu wacce ta fara cewa

"A'a ina zakuje? Ga fa keys Win na dawo dasu..."

"Ki tabbatar kin tanadi furucin kare kanki a gareni kan in dawo don wallahi wallahi ranki se yayi mummunan Saci akan wannan abunda kika aikata, ko babu aure Fauziyya da husna sun fi karfin yunwa a gidana Fatima..."

Yana kai nan ya zagaye da husna ya buWe mata gaba ta shiga, ya dawo side Win driver ya ja motar ya fice da gudu.

Hannu Fatima ta Waura a kai tace
"na shiga uku!"
Da gudu tayi cikin gidan don kiran Auntyn ta ta nemi mafita kan ya dawo, garin neman gira tana shirin rasa idanu, ita da ya kamata ta nisanta su gashi tana shirin kawo kusanci tsakaninsu, ina zasu je? Me zasu je suyi? Shine kawai tambayar dake ta mata kai kawo.

Driving yake yana sauraron sheshekar kukan da fauza ke yi, husna ganin Fauza bazata yi shiru ba yasa itama ta fara kuka tana waigawa ta kalli Fauza da ta Waura fuskanta a tafin hannunta ta kuma kwantar bisa cinyar ta tace
"Aunty yunwa kike ji ko? Kiyi ha?uri yanzu zamu je mu ci abinci ko uncle?"

Shima Fauzan yake kallo a kai a kai ya gyaWa kai yace
"in shaa Allah Husna"

Restaurant mafi kusa ya kaisu, husna na fita ya zagaye ya buWe mata kofan.

A hankali ta sanya kafa ta fito yace
"kukan nan shi ze kosar dake ne?"

Bata tanka shi ba suka nufi ciki tana tafiya a hankali sbd cikinta da ya kama, tea me zafi ya fara ordering Allah ya sa VIP Winsu room ne so in ka shiga babu me ganinka, suna shiga ta nufi zubewa yayi saurin tarota suka karasa kan lallausan shimfidun dake wurin ya ajiyeta ta zame ta kwanta, sake kiransu yayi a landline dake wurin cikin mintuna se gasu da shayi kan ya basu ordern abincin da zasu kawo musu.

Da kanshi ya Wagota ya mi?a mata shayin, kurbi biyu zuwa uku tayi se amai.. Da gudu ta karasa washing hand base dake wurin ta fara kwala amai, yana ri?e da kafadanta hannunshi Waya na shafa bayanta cikin tsantsar tausayi yake furta
"sorry! Sannu am so sorry"

Daga ka ga aman ka san na wahala da yunwa ne, bayan ta gama suka sake dawowa ya bata tea Win ta sha, bayan ta shanye ya matsar mata da abincin da aka kawo Win tuwo ne da miyar vegetable, yatsina fuska tayi tana kallon tuwon, husna har tayi nisa a cin nata.

"Bakya so?"
Kai ta gyaWa don ita bata son tuwo, janyewa yayi ya sake kiransu tana ta Kallonshi da idanunta da suka kara girma, yadda duk tausayinsu ya kasa boyuwa a fuskanshi kaman ze yi kuka, tambayarta yayi tace rice and stew with plantain. Nan take ya faWa musu suka kawo.

Zama yayi yana kallon yadda take cin abincin Dukda yunwa da take ji amma cin ba wani sauri ko hargagi a natse take kaiwa bakinta, ganin zata Wago yasa ya Wauke kai ya fara cin tuwon da taki ci Win.

Ba su suka dawo gidan ba don ya biya dasu sahad sun sayi abubuwa snacks masu yawa dangin su biscuit da su drinks da kayan tea su custard da oat, golden morn, coco pops ba abunda be saya ba.

Don anan ma yaga laifinshi da be ajiye musu abubuwa haka a Waki ba, tunda daga dakinshi har na Fatima akwai snacks da drinks kuma a fridge.

Pizza da shawarma spot suka je ya sake saya musu kan suka nufi dawowa gida, duk abubuwan da yake yi Win sede suyi hira da husna amma ita kam tak bata ce ba, tana jingine da jikin motar daga karshe ma bacci ne ya kwashe ta.

Ko da suka dawo gidan a gate ya tsaya ya cewa gate man Win ya janye maganan da ya faWa duk sadda Fauza ta nemi fita ya barta ta fita.

Daga haka suka karasa ciki, zata Wauki kayan yace ta bari.

Haka ta wuce ta Barsu da husna, bata ko kalli Fatima dake zaune a parlorn kasan ba ta haura abunta, kayanta kawai ta sauya ta kwanta akan gado sbd wani irin bacci da take ji.

Shi kam dashi da Husna suka kwashi kayan zuwa sama saida ma yayi sawu biyu, da kanshi ya shirya abubuwan inda suka kamata, kan ya kama hannun husna suka yi Wakinshi tana cin shawarma.

"Yaya..!"
Fatima ta kirashi ko kallonta be yi ba, tayi saurin binshi Waki ya juya ya daka mata wani hargitsatsen tsawa
"get out of my sight tun baki sanya ni yin abunda zamu zo duka muna dana sani ba.."

Zata sake magana yace
"outt!"
Ya sake daka mata tsawa, da sauri ta fice tana kuka.

Duk abubuwan da ya kamata yayi yayi har wanka yayi ya sauya kaya kan lokacin husna tayi bacci, Waukanta yayi ya fito zuwa???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? dakin Fauza.

Saida ya sauya mata kaya kan ya nufi gadon da ita ya kwantar idanunshi kan Fauza dake bacci peacefully, Adu'a yayi musu kan ya fito.

A hankali ta buWe idanunta ta bi bayanshi da kallo har ya maida kofa ya rufe, ajiyar zuciya ta sauke kan ta gyara kwanciyarta cikin nazarin yadda zata ci uban Fatima na abunda tayi mata...

DIDDIGAR ?AYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuWi ne..
Ze zo muku a Naira Wari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad

16 / 29