Advertisements
Chapter 3 Reading Diddigar Kaya 1&2 Complete Hausa Novel Hausa Novels
Advertisements

Diddigar Kaya 1&2 Complete Hausa Novel

Author :  Fatima Category :  Complete Novels

Chapter   3 / 29

6K to 9K   out of 86.8K words

Yaya Fadeelah da wata ?ar uwar su Baba prof zasu tafi, Kallonsu yayi yace
"ku je ku shiga mota ga mijinta ze zo da ita yanzu"

Kanta ?asa tana shesheka duk masu rakiya suna tsaye cike da tsakar gidan ana ta mata Adu'o'i.

Hannunta baba prof ya ri?e ya sanya cikin hannunshi a tare suka Waga suka kalli baban se suka kalli juna, dukkansu suka Wauke kai, gyalen ta baba prof ya sake ja ya rufe mata goshi yace
"Allah yayi muku albarka! Allah ya tabbatar muku da farin ciki a wannan tarayya ku je kuna cikin adu'o'inmu a kullum, Fauziyya karki manta duk abunda na ce miki kinji?"

Kai ta gyaWa, hanya ya nunawa Faizan se ya juya ri?e da ita suka nufi mota, dole ya biye mata suna tafiya kaman ba zasu taka ?asa ba don haka tafiyar ta, idanun mutane da Baba ya sanya ya saka hannu ya buWe mata gefen ta shiga ya gyara mata kayan ta kan ya rufe kofar fatima dake gefe Waya ta ja tsuka me karfi, gaban motan ya shiga Farhan ya ja suka fice kan na su yaya fadeela ya biyo bayansu.

Basu tsaya ko ina ba se Airport, suna parking ya fita ya shiga ciki yana waya kaman yadda tun da suka fita daga gidan waya yake, Fatima fushi take dashi kaman shine ya Sarar mata da ciki hakan yasa itama be kula ta ba, yaya fadeela ce ta zo ta ri?eta suka shiga ciki Fatima da Ya kaka suka biyo su cikin mintuna ya gama komai, ya zo ya Mikawa kowa tickets nashi suka wuce suka yi checking suka shiga jirgi.

Banda ajiyar zuciya babu abunda take saukewa, ba wannan ne karonta na farko shiga jirgi ba Dukda duk gidansu babu wadda ya sani sede tana yawan zuwa Abuja da friends nata kuma da jirgi hakan yasa bata ko nuna alamar tsoro ba, jirgin na daidaita a sama ta yaye gyalen ta sbd zafi, daga inda take tana hangar yadda Fatima ta kwanta a jikinshi yana ri?e da hannunta da alama rarrashi yake.

Kau da kai tayi tare da tsaki tana kallon window ta fara Tunanin rayuwata Daki-daki....duk me ya jawo waennan abubuwa da suke faruwa? Shin wacece ita tun daga farkon fari?
A take tunaninta ya daka tsalle yayi baya daga inda ta fara sanin wacece ita...

DIDDIGAR ?AYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuWi ne..
Ze zo muku a Naira Wari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya zuwa wannan layin
09039206763
Ko ki tura katin waya ta layin na sama tare da shedar biya ta what'sapp.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taSa nadama ba>?p?

Karku sake a baku labari.


? ? ? ? ? ? ?? =???Gureenjoh=???
DIDDIGAR ?AYA
(Mai Wuyar Tsincewa)

(3E DDG 'D1-EF 'D1-JE

FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
And Now..
*Diddigar ?aya... Paid*

*Shafi Na Uku*

*PAID BOOK*

?AN?ANO

**WANNAN SHAFI SADAUKARWA CE GAREKI MRSJMOON GWANATA KUMA SHUGABATA>?p?d'?**

*SOME YEARS BACK*

"Fauxa! Fauxa!!"

Muryar ke fitowa daga tsakar wawakeken gidan yana amsa kuwwa a duk sa?o da sa?o na cikin gidan, har matsakaiciyar matar ta iso kofan Wakin tare da yaye labulen sbd kofar dake wangale bata fasa kiran sunan ba.

Turus! ta ja ta tsaya tare da wara ido Kalmar

"kan uban chan!" Ya fito daga matsakaitan laSSanta.

"Fauziyya! Ashe sunanki daaWi yake min da zan kama in yi ta kira kina ji ki min banza? Ni sa'ar ki ce? Ko kin maida ni irin su fa'iza ne?"

Kyakyawar matashiya ce me Wauke da coffee colour skin, irin skin Win nan da ake kira glass skin da ake wa magana na zaune saman bed me yanayi da gadaje irin na hostel hannunta chocolate ne na bounty tana sha, a hankali ta Wago manyan idanunta? da kwayar suke kalar Grey ta watsawa matar tare da motsa kyawawan siraran lips Winta wadda ya saka cikakken girarta me cike da gashi suka haWe wuri guda cikin kunkuni tace

"Ai an san inda mutum yake ba se a zo a same shi ba, sai an yi ta mishi kiran kasuwa!"

Ta karasa da murguWa baki.

Wara idanu matar tayi tace
"Me kike cewa?"

Da karfi tace
"ni ban ce komai ba, gani..!"

Tayi maganan tana dirkowa ba tare da ta bi matakalar da aka tanada don hakan ba ta je gaban matar ta tsaya kerere, tsiririya ce me kananun shekaru bata da kauri da matukar wuya ta haura 16yrs karamin shape da take dashi ya haWu da tsawon ta ya bata wani kyaun sura na musamman, manyan idanunta da dogon hancinta zuwa lips Win ta sun taimaka wurin fitar da ainihin kyaun da Allah yayi mata musamman in ka HaWa da yanayin skin color Winta.

"Ki wuce ki je ki yi min wanke wanke tunda zuwa Islamiyya ya gagareki, Fatima bata samu tayi ba sbd lokacin islamiyya da ya shiga"

Baki ta turo tace
"ni ba zan yi wanke wanken da ba na rana na ba fa! Me anfanin rabawar to in an san za'a zalunci mutum? Ni de! Ni de......"

?assss haka karar Marin da aka yiwa bakinta ya bada sauti da sauri ta Wago don ganin waye ne ta sauke mishi tijarar ta da be bar kan kowa ba, se suka HaWa idanu da Ya Farhan zaro mata idanunsu iri Waya yayi yace
"fitsararriya ana magana kina yi, ki wuce ki je maza ki kama wanke wanken nan tun ban sauya miki kamanni ba.."

Baki ta zumburu tana kunkuni
"mugu, azzalumi..!"

"Me kika ce?"

Tace
"cewa nayi to bari na fito"

Ta RaSa ta wuce tana ci gaba da kunkuni musamman da taji Aunty Amarya na cewa
"da baka kai mata hannu ba ai Farhan, yaran ne se Adu'a yanzu"

"Munafuka, guntuwa..!"

Ta faWa bayan ta sauka tana bin kan interlocks da suka zagaye sashen wadda har daga wajen karamar kofar da nake hange a buWe su ke zube.

Tsakar gidan an yi kaman roundabout na interlocks inda tsakiyar kyakyawar bishiyar Almond wacce aka fi sani da umberalla ta kawata gidan, chan gefen kitchen da store Winsu aka yi wurin wanke wanken dake lailaye da tile, Fatima ta riga ta gama HaWa wanke wanken har ruwa da komai, farawa tayi tana me cin alwashin wlh ranar wanke wankenta baza tayi ba sede Fatiman tayi.

Tana wanke wanken tana ta bubbuga kwanuka har Seda Ammi ta le?o tace
"ke kam lafiyanki kuwa?"

Kallon farar matar tayi wacce suke Wan yanayi ta tsawo da hanci tace
"?alau Ammi"

Girgiza kai tayi ta koma tana sauke labulen ta duk ta ji abunda suka yi da Amarya, bata mamakin halayen Fauxa don kowa ya kwana ya tashi ya san wacece Fauxa a gidan, zama tayi cikin kujerun parlorn nata tana ta tufka da warwara wadda bata rabo da shi a kullu yaumin na kwanan duniya.

Har Fauxa ta gama wanke wanken ?an islamiyya basu dawo ba, hijab Winta ta janyo daga saman igiya dake Waure a tsakar gidan ta saka tana me ficewa kar wannan guntuwar Amaryar ta HaWa ta da aiki.

Masha Allah, tsakar gida ne me matukar yalwa, shimfiWe da interlock ?awace da flowers kama daga koraye, jajaye, ruwan Woruwa da kuma farare chan gefe parking space ne, se parts babba guda Waya, wadda nasu ne na biyun girma se wani ?arami a gefe, da kuma wadda be kaishi ba daga gefe. daga cikin gidan wani babban masallaci ne da yafi gidan ?awatuwa, babban kofan ta waje ne sede akwai wasu kofofin kama daga na maza har mata ta ciki.

Karamin part Win tayi tana shiga ta fara ambatan
"Jaddah! Jaddah!!"

"Maza to cire min dodon kunne Fauziyya se ki huta"

Baki ta chuno wadda kaman Wabi'ar ta ne na lura, tana shiga parlorn matar bayan ta cire takalman ta daga bakin varendern tiles dake shimfiWe daga kasan kofan.

Parlor ne madaidaici sede ya wadatu kwarai da kayan more rayuwa, cikin Waya daga cikin kujerun ta kalli dattijuwar wacce kamanninsu har ya Saci da yarinyar tace
"Haba jaddaty ai ni dake Bama ?ar haka"

Jaddah na jin haka ta san wani jarabar Fauxa ta kwaso, tace
"Toh ina ji yanzu kuma me ke tafe dake?"

Fauza na zama daga kasa ta kama mammatsa kafafun tsohuwar tace
"Ban je islamiyya da karatu ba kuma kin san anjima se Baba Prof ya aiko kirana"

Ta faWa a marairaice
"in ba'a yi sa'a ba se ya sa su Faisal zazzane ki"
Jaddah ta karasa mata.

Raurau tayi da idanu ga tsoro ga neman rigima, babu abunda take tsoro irin bulala kuma tana dakuwa kam sbd rashin jinta da neman rigimar ta babban shine rashin kunya.

"Ki taimakeni jadda kar baba prof ya san lafiya ta ?alau ?in zuwa nayi, wlh na gaji ne kullum kullum abu Waya bawa baka da hutu ko kaWan"

Sallama aka fara daga Wan harabar na jadda wadda ya sakata saurin cewa
Fauza
"yi maza hau kujera ki kwanta ki kuma rufe fuskanki da hijabi, maza maza"

Da gudu kuwa ta haye tare da janye hijabinta ta rufe fuskan nata.

"Wa'alaikumussalam waye ne kaman Farhuddeen?"

Saurayin ya karaso yana sanye da blue riga da wando me taushi tare da hular taSani kaji hadisi yace
"nine Jaddah dama baba prof ne ya aikoni in kira masa Fauxa se kuma Aunty Amarya tace min yanzu ta gama wanke wanke baze wuce nan tayo ba"

Jadda tace
"eyyaa ai kuwa nan ta shigo zazzaSi ya rufe ta kwab Waya dama wanke wanken ma da kyar ta gama shi sbd kawai Amarya ta matsa ne, ka ce mishi bata jin daaWi"

Ko rantsuwa ze yi baze yi kaffara ba lafiyar Fauxa ?alau tsabar sonta da jadda ke yi yake sa take goya mata baya lokuta dayawa irin wannan, kwafa yayi yana hararanta kan ya juya ya fice.

Seda ta tabbatar ya fita kan ta wanckalar da hijabin tana saukowa hakwaranta farare Kal da kaman jera su akayi a waje.
"shiyasa nake matukar yinki tawan, shege ya Farhuddeen ina Kallonshi yana harara ta ta wuyan hijab kawai ba yadda ya iya dani ne"

Hira suka cigaba da yi da jadda sbd duk jikokinta kowa ya san mutane biyu ne mafi soyuwa a wurinta se kuma aka samu akasi suka kasance WUTA DA AUDUGA.

Dab magrib suka Wauro alwala a harabar na Jaddah suka fito don zuwa masallaci, Wabi'ar gidan dole duk me kake yi kan magrib ka tabbatar ka gama daga mazan har matan a kira sallah kana cikin massallaci ana kira kuna amsawa kaman yadda addini ya koyar daga karshe ayi Adu'ar bayan kiran sallah se a yi sallah, in an idar za'a yi azkar bayan an gama za'a yi nafila kan kowa ya Wauki Alqur'ani daga ma'ajiyar Qur'anai na massallacin a hau karatu har zuwa lokacin da za'a kira isha a gabatar ayi nafila karfe takwas na dare kowa ze koma gida don cin abinci da sauran hidimdimu haka da asuba kiran farko dole kowa ya mike ya hau shirin massallaci har yaro ba'a bari, Wabi'a ne da suka tashi suka tarar ana yi wadda basu san iya tsawon lokacin da aka Wiba ana yi ba.

Tun kan su isa massallacin suka hango ?an mata wacce zata Wara Fauxa Waya se kuma waenda basu kaita ba su uku se wasu guda biyu da zasu yi sa'anni da ita duk tafiyar daban dabance.

Kau da kai tayi ta cigaba da hiranta da Jaddah, bayan sun shige kowa ya zazzauna chan se ga Aunty Amarya da Ammi sun shigo sanye da hijab, daga bayan su mata ne guda huWu ras, a kallo daWWaya zaka iya faWin kai tsaye biyu Fulani ne, sbd yanayin haskensu se biyu ba?a?e waenda kuma suke da zane wato tsaga irin na kanuri.

Duk gaban jadda suka du?a suka mika gaisuwa, ta amsa da fara'arta kaman kullum, Fauza ta kalli wata babbar mace daga ciki tana da dirin jiki Dukda tsufa da ya fara bayyana mata kuma fara Kal me yawan fara'a wadda be Soye hakwara biyu na hajji dake bakinta ba tace

"Mammi sannu, ya ciwon kafan?"

Da tsantsar kulawa Mammi ta kalleta tace
"sannu Fauxa, kafa da sau?i idon ki kenan tun asuba ko?"

Murmushi kawai tayi, ta juya ga sauran matan kaman dole tace
"maami, umma da dada sannunku"

Ba don idanun Jaddah dake kansu ba babu wacce zata amsa a cikinsu sbd haushin rainin wayaun Fauxa da a kullum kaman kara karuwa yake, gyaran muryar loudspeaker da ya karaWe ilahirin unguwan da kiran sallah yasa duk kowa ya samu sahu ya natsu suka fara amsawa.

Har zuwa na karshe wato;

Laaa ilaha illallah!

A lokaci Waya duk suka amsa da
(laaa ilaha illallah Muhammadurrasulillah sallallahu alaihi wa salam, Allahumma rabba hazihida'awatit tammah, wassalatul qa'imah, aati Muhammadu Al wasilata Wal fadeelah, wa ba'athhu maqaman mahamuda Allazee wa'ad ta.
Allahumma Salli ala Muhammad wa'ala aali Muhammad, kama sallaita ala Ibrahim wa ala aali Ibrahim innaka hamidun majeed, wa barik ala Muhammad wa'ala aali Muhammad kama barakta ala Ibrahim wa ala aali Ibrahim innaka hamidun majeed)

"ya ke ?ar uwa shin kin san falalar amsa kiran sallah kuwa? Ko wani irin yanayi kike ko wani irin nauyi ne a gareki in har bakinki ze iya motsawa manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gareshi ya ce 'idan kuka ji me kiran sallah to ku faWi irin abinda yake faWi, sannan kuyi salati gareni, domin wadda yayi salati Waya a gareni Allah zai yi salati goma a gareshi".

Bayan an idar da isha duk gida kowa yayi anan aka fara haramar cin abincin dare, ita kam dae Fauza ko kallon inda su Fatima suke bata yi ba suma ba wadda ya mata magana saboda tuwo ne kuma miyan kuka ko shakureta ake ba ci zata yi ba.

Mp wadda kowa da kowa ke dashi personal a gidan me Wauke da memory 32Gb cikinshi karatuttuka ne na malamai daban daban da kuma riwayoyi kala kala sede fa Fauza nata harda wakoki kala daban daban na mawaka mabanbanta, memoryn take cire wa ta kai school wata friend Winta ta saka a wayanta su tura wakoki duk ta harhardace rabi da kwata yanzu ma wakar Auta waziri na Kewa ta saka tana ji murya chan kasa kasa, Sam bata ji shigowar shi ba se jin kiran sunanta tayi cikin kaushin murya wadda ya sakata saurin mikewa tana zare idanu zuciyarta na bugawa, yau idan wa?ar nan ne ya shiga kunne Baba ta shiga uku!....

DIDDIGAR ?AYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuWi ne..
Ze zo muku a Naira Wari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya zuwa wannan layin
09039206763
Ko ki tura katin waya ta layin na sama tare da shedar biya ta what'sapp.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taSa nadama ba>?p?

Karku sake a baku labari.


=???Gureenjoh=???
DIDDIGAR ?AYA
(Mai Wuyar Tsincewa)

(3E DDG 'D1-EF 'D1-JE

FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
And Now..
*Diddigar ?aya... Paid*

*Shafi Na huWu*

*PAID BOOK*

?AN?ANO

**WANNAN SHAFI SADAUKARWA CE GAREKI MRSJMOON GWANATA KUMA SHUGABATA>?p?d'?**

Da wani kalar sauri ta amsa tana me mi?ewa tace
"Na'am Alhaji! Sannu da dawowa"

Be amsa ba se idanu da ya zuba mata, duk cikin yaranshi itace yake jinta na karshe a cikin zuciyar shi, Allah ya gani babu yadda ya iya ne yake zaune da ita amma ya gaji iya gajiya da halayyarta babu randa za'a wayi gari a yini ba'a kirashi kan case Win Fauxa ba, a gida babu irin rashin kunyar da baya ji da kunnuwanshi tana yiwa yayyun ta, duk gidan babu wadda baya girmama na gaba dashi se Fauxa, dokarsu kuwa ba a bakin komai yake ba a gareta.

"Ki je Baba Prof na kiranki"

Daga haka yayi gaba sbd sa?o ne Yayan nashi ya bashi Idan ya shigo ya tura ta, mikewa tayi da hijab Winta dogo har ?asa kaman ta Allah ta fice, harabar gidan tar kaman rana har ta isa babban parlorn na Baba prof dake gefe da shiga kofan sashen nashi da na matanshi, akwai hanya da ze kaika Wakunan baccinshi kuma akwai wadda ze kaika cikin gidan nashi ta cikin parlorn.

Da sallama ta shiga, babban parlor ne me Wauke da kujerun alfarma, carpet ne me taushi da tsananin kyau malale bisa parlorn duk girman parlorn Seda ya Wauke tsab, ga kujerun alfarma na asalin royals, chan gefe shelf ne na littatafai har ba zasu kirgu ba.

A tsakiyar kujera ta ganshi zaune yana nazarin wani littafi, ta karasa kusa da kafafunshi ta zube tace

"Barka da dare baba"

Ya kalleta kan yace
"yauwa Fauziyya"

Fuskanshi ba alamun wasa yace
"me ya hana ki zuwa Islamiyya yau?"

Wuri wuri ta fara yi da idanu cikin in ina tace
"baba... Am dama.. Dama tunda na dawo makaranta ne na fara ciwon ciki shiyasa ban je ba"

Yace
"kin san Allah yayi mana hani da karya? Ya kuma kwaWaita mana ri?e gaskiya a kowanni hali? Karki kasance cikin makaryata sbd daga furucinki zan iya cewa kai tsaye ba gaskiya kike faWi ba, me yasa baki son karatu daga na boko har na Arabi?"

Kanta dake kasa ta girgiza tana forming hawaye tace
"kayi hakuri"

Yace
"na ha?ura, na san ki da tsanar karya hakan yasa farar Waya na gane ki, Fauziyya karatu na da wani irin muhimmanci a rayuwarmu daga boko har arabi, barin ma arabi da ya zama dole wajibi a garemu mu nema, duk girmanka da tsufanka dole ne ka cigaba da neman ilimi sbd shi ze zama haske a rayuwar duniyarka da lahirarka, Allah SWT yace ku sanni kafin ku bauta mini idan har baku sanni ba to ta yaya Zaku bauta mini? Haka kuma Ayar farko da ta fara sauka da Kalmar 'Iqra' ta fara to meyasa bazaki dage wurin gyara gobenki ba?"

Nasiha ya cigaba da yi mata da misali

3 / 29