Advertisements
Chapter 5 Reading Diddigar Kaya 1&2 Complete Hausa Novel Hausa Novels
Advertisements

Diddigar Kaya 1&2 Complete Hausa Novel

Author :  Fatima Category :  Complete Novels

Chapter   5 / 29

12K to 15K   out of 86.8K words

yi tunanin akwai fulawa a gidan nan ba"

Fa'iza tace
"kash! Ya kenan Fauxa gashi namu ma babu ya kare"

Mikewa Fauxa tayi tace
"mu je wurin Mammi mu yi, dama wlh tun jiya ban je na gaisheta da ciwon kafan nan nata da ya tashi ba"

Ficewa suka yi Jaddah bata ce komai ba har suka fice, ko da suka isa a Waki suka sameta kwance a ?asa an shimfiWa mata bargo me taushi da pillows, ?ar yayarta da zata Wan girme su da take hannun ta tun bayan auren farida ita ke taimaka mata tunda bata karatu.

Sashukan nan basu da maraba da sashen su Fauxa, se na kitchen da akwai cikin kowanni sashe saSanin nasu, se kuma na yawan Wakuna wadda nan kofa biyu ke fuskantan biyu, na Mammi ne na farko wadda babban parlor ne sossai da kitchen da Wakuna biyu, hakan ne kuma a kowanni Waki, sannan akwai kitchen na waje da kowacce me girki a sashen take girki ranan girkin ta, tsakar gidansu bishiyar cashew ce me ni'imtacciyar inuwa.

"Fauxa yau ke ce a sashen namu? Lallai za'a yi ruwa da kankara"

Fauxa na murmushi ta zube kasa tace
"sannu Mammi ina yini? Ya kafa?"

Mammi tace
"Alhamdulillah Fauxa da sauki sossai har Wazu ma na taka zuwa toilet"

Fauxa tace
"Allah ubangiji ya ?ara sauki"

Da Ameen ta amsa, fai'za ma ta gaisheta.

Fauxa tace
"Mammikina da fulawa? Wainar fulawa nake son yi bamu da fulawa haka Jaddah ma"
Ta karashe tana karya wuya

Mammi tace
"Ah Kice abunda ya kawo ki kenan ba zuwa na musamman da kike cewa ba"

Tana dariya tace
"Allah ba haka bane dama nayi niyyar zuwa"

Mammi tace
"ba za'a rasa fulawan nan ba ku duba a kitchen na cikin nan se kuyi, dama akwai yaji da Zuwaira(kanwar ta) ta kawo min ma jiya da alama ze yi daaWi"

Cikin jin daaWi Fauxa ta mike, fa'iza ta bi bayanta suka yi kitchen.

Anan suka kwaSa suka fara suya se suka fara na manja sbd yadda Fauxa ta hanata sakat Seda suka yi me yawa se suka koma man gyaWa sbd shi fa'iza ke so, suna cikin yi se Fa'iza tace
"ni bani manjan ma in yi mixing kaWan yadda ze bada wani dandano me armashi"

Fauxa tace
"Wallahi bazan bayar ba ka jimin wayau, kowa ya ci da plain abunda yake so"

Musu suka fara, fa'iza ta kai hannu da niyyar fusgan manjan Fauxa ta Salle da gudu daidai kofar kitchen Win taji taci wani uban karo da wani broad chest me yanayi da rock, gabaWaya manjan ya zube a jikin kayan mutumin.

A hankali na kai idanuna bisa mutumin da aka kwararawa manjan Masha Allah, kyakyawar matashi ne me tsawo sossai a kamannin fuska zaka iya cewa kaman an tsaga kara da Fauxa, banbancin nasu kaWan ne shi Win fari ne Kal saSanin Fauxa, haka idanunshi wasu irin Ash ne me wal?iya..

Ko kaWan bashi da rama wani irin tsayayyen namiji ne da yake da jikin every woman dream, daga ka ganshi zaka san cewa ma'abocin workouts ne, yana da dogon hanci sak irin nata da lips wadda suke iri daya da nata kaman an shafa musu cherries yadda suke kyalli, yana da gashin saje gyararre me kyau wadda har zuwa gemu amma be cika yawa ba, a gyare tsab ba?i sidi? se shining yake yi wadda ya kara fitar da ainihin kalar farin fatar shi, daga yatsunshi na hannu zuwa na kafa dogaye ne a gyare suke tsab gwanin burgewa, yana da wani irin kwarjini da farin jini sede fa ma'abocin tsare gida ne, Miskilin bugawa a jarida ne sannan yana da murWaWWen hali da zama dashi se ka shirya.

Sanye yake da Fararen kaya Kal Kal Jean da shirt designers kafafunshi sanye da Dior lufas masu kyau, kamshinshi a take ya baza lungu da sako na kitchen Win, kyawawan idanunshi na kafe kan inda manja ya zube a Rigan nashi kan a hankali cikin tsantsar natsuwa ya Wago birkitattun idanunsa dake cike da kwarjini irin na cikakkun maza ya zuba mata.

Wani irin faWuwar gaba ne ya risketa ga tsoro da ya kusa sumar da ita, cikin da na sanin fara sha'awar wainar fulawa da ta yi a yau ta fara ja da baya, wannan ba?in azzalumin yanzu se ya mata abunda se ta gwammaci kiWa da karatu, ita kanta fa'iza dake tsaye jikin gas a take ta saukar da pan Win sede ta kasa kashe gas Win se rawan tsoro jikinta ya Wauka.

Kokari yake yayi controlling Sacin ranshi sede ganin ko sannu bare yi ha?uri ta kasa ce mai yasa ya Waga kafafunshi ya fara takawa zuwa gareta, a duniya ya tsani ganin yarinyar halayen ta, neman tsokananta, rashin jinta, rashin kunyarta duk ya tsana bata yi mishi don babu fuskan yi Win sede ya kan tsinkaya tana yiwa wasu, sannu be taSa HaWa su ba tana karama in har zata zo kusa dashi se ya mata mugunta tun tana zuwa har ta dena hakan ya dasa mata tsoron shi, Sam baya zama a inda take sbd hakan itama ta koyi kin zama a inda yake, idan kana son ganin Sacin ranshi ka ce suna kama yanzu se ku samu matsala, ya kan yi mamakin yadda kowa a gidan complain Winshi baya wuce Fauziyya har iyayensu maza, shi yana ganin iskancinta wuri ya samu bata sami me saita ta bane, hakan ya sa ya buga Mata tambarin annoba don shi da annoba yake kiranta.

Ganin da gaske nufanta yake ga fuskanshi babu Wigon rahama yasa tayi kokarin gudu, taku Waya yayi ya saka mata ?afa hantsilawa tayi zata faWi, garin neman abunda zata dafe don gujewa kaiwa ?asa ta Waura hannunta na dama bisa kan gas Win da yake kunne, ba wutan bane karafunan da suka riga suka jima da Waukan zafi sossai ne suka aika mata da wani irin raWaWin azaba zuwa kwakwalwanta har bata san sadda ta saki wani ?aran azaba ba tana rike hannun.

Wani mugun murmushi da ko ha?orin shi be bayyana ba ya saki kan ya juya ya fice daga kitchen Win, da gudu Fa'iza ta kashe gas Win kan tayi kanta ta kama hannunta a tsorace tana kallon fuskanta yadda hawaye ke ambaliya kaWai zaka gani ka san tana cikin wani hali ga zufa dake aikin tsatsafo mata.

"Sannu Fauxa! Sannu"

Mammi ce jin ihun Fauxa yasa ta lallaSa ta fito a hankali ta nufe su tana cewa
"Subhanallah me ya same ta? Konewa tayi?"

Cikin kuka Fauza tace
"mammi wannan azzalumin ne ya saka min hannu akan karafunan gas, Wayyoooo hannuna!"

A hankali Mammi tace
"FAIZAN!" Don shi kaWai Fauxa ke cewa Azzalumi.
Da sauri Mammi ta cewa Fauxa
"Wauko akamu yi sauri gashi a chan in saka mata kar ya tashi"

A hankali ta karasa gareta ta Waga ta tare da ri?e hannun har ya tashi gabaWaya tafin na hannunta yayi wani kalar bororo, wani irin tausayinta ne ya rufe Maa sbd ta san zafin wuta ba daaWi amma se ta saSawa Faizan, ashe kaddarar ?one wa ya kawo ta sashen nata da ta jima tana mita akan rashin zuwan nata, da kuwa ta san Faizan ma ze zo yau da bata ma bari sun yi wainar anan ba, wani irin abu ne haka?

Akamun fa'iza ta kawo ta kwaSa ta saka mata har lokacin kuka take, tayi tayi ta ci wainar da saura kaWan ma su kammala ta ?i tace ta koshi, cikin rashin jin daaWi Mammi ke bin ta da ido har ta fice se ta saka fa'iza juye wainar a flask ta bita dashi su je su ci a gida don ta tabbatar ko sashen Jaddah Fauxa bazata kara zuwa ba se an tabbatar mata da baya gari.

Haka kuwa aka yi da fa'iza ta kawo mata ma ?in ci tayi, Allah ya isa kuwa ta ja mishi yayi cikin kwando, gashi Ammin ta bata nan ta tafi kauyensu jiya uncle Winta ya rasu, da magrib ma da kyar ta samu tayi alwala ta tako zata fito zuwa masallaci kenan ta tsaya Chak jin muryar dake tashi a speaker na masallacin, tsaki ta ja ta koma Waki nan tayi sallah har isha bata fita ba, a Cewar ta bazata bi sallar azzalumi ba don Allah ba karba ze yi ba. bayan tayi isha ne ta kunna speaker Winta iya daidai jin kunnen ta ta saka wa?a abunta anan mood Winta ya fara dawowa daidai.

Tana ji su fai'za na cin abinci bata fita ba, idanunta a lumshe take jin Fatima na fesawa fa'iza ita duk yadda take jin karatu bata taSa jin me natsuwa da kwantar da hankali irin na Ya Faizan ba, fa'iza na dariya tace mata

"zaki ce haka ne ma tunda kina son shi"
Fatima ta ce
"ban gane ina son shi ba? Ko de muna son juna?"

Fa'iza tace
"ai ko makaho ya shafa ya san ke ce kike mahaukacin son ya Faizan shi ba take yake ba, ba ta yadda za'a yi yana son ki ne ke karan kanki kan ya miki magana Waya se kinyi hamsin, sannan ya tafi yayi wata da watanni ko a wayan Jaddah baze ce a baki ku gaisa ba idan ma yana jin kunyar Mammi kenan, ni wlh bana son miki kasancewa da ya Faizan ina so ki samu me son ki inda zaki ji...."

Tsawa ta daka mata
"dakata fa'iza! Don ina maganan soyayyata dake ba shi yake nufin ki gayamin duk wani banzan maganan da ze fito daga bakin ki ba idan ma ba kitsa miki aka yi ba don baki da wannan wayaun, to henceforth as from today kika kara min irin wannan maganan wlh se nayi mummunan saSa miki ni ba sa'ar ki bace"

Fa'iza tace
"Ya Fati daga faWar gaskiya?"

"Bana son gaskiyar ki ri?eta"

Daidai lokacin Fakiha ta shigo da gudu tana shelan ya Faizan ya ce a je a karSi tsaraba yana sashen Jaddah.

Da sauri duk suka tashi suka fice daga tsakar gidan.

TaSe baki Fauxa tayi, Fatima na neman magananta ta tabbatar harda shagube a zancen nata, amma ba ta ita take ba yanzu ta samu ta warke shine damuwanta kuma wlh akan Fatima zata rama abunda ya mata tunda shi azzalumin ya fi karfinta.

Chan da yunwa ya fara damunta don ko abincin rana bata ci ba ta sa a zuciyarta zata ci wainar fulawa yasa ta mike ta fito a hankali ta nufi kitchen, ja tayi ta tsaya jin kuka na tashi a hankali....

DIDDIGAR ?AYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuWi ne..
Ze zo muku a Naira Wari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya zuwa wannan layin
09039206763
Ko ki tura katin waya ta layin na sama tare da shedar biya ta what'sapp.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taSa nadama ba>?p?

Karku sake a baku labari.


=???Gureenjoh=???
DIDDIGAR ?AYA
(Mai Wuyar Tsincewa)

(3E DDG 'D1-EF 'D1-JE

FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
And Now..
*Diddigar ?aya... Paid*

*Shafi Na Bakwa*

*PAID BOOK*

?AN?ANO

**WANNAN SHAFI SADAUKARWA CE GAREKI AUNTY HALILLOS GWANATA KUMA MALAMATA>?p?d'?**

"Aunty wallahi son shi ze kasheni! Kin Reneni ne da soyayyar shi hakan ya bani karfin gwiwar kwallafa rai a kan samunshi sede gashi har yanzu shi bana gabanshi, yanzu har fa su fa'iza sun san nice me cusa kai a gareshi shi ba ta ni yake ba! Aunty kinga wulakancin da ya min a gaban su Fa'iza da kannenshi maza?"
Ta karasa tana me kara rushewa da kuka.

Aunty tayi saurin sa mata hannu a baki tace
"Haba Fatima! Me yasa ke kam kullum rashin ha?urinki kara gaba yake? Na faWa miki na kara jadadda miki idan har Faizan be aureki ba to wallahi ba ze auri wata ba, wannan alqawarin da na daukar wa kaina ne tun kan in shigo gidan nan, tufka nake ana warwarewa amma ba matsala ki kwantar da hankali na miki alqawari Faizan ba ze bar garin nan ba tare da an tsayar da magana tsakanin ku ba!"

Wani wawan tsaki Fauxa ta ja kan ta juya ta fice daga gidan gabaWaya, a chan gefe da sashensu inda aka yi wasu kujeru haka masu kyau na tayoyi ta zauna, tana me kallon qonannan hannunta, murmushi ta saki na jin daaWin ba ita ba aikin gida har se ta warke, makaranta ma in ta je ba rubutu ai kuwa za'a sha neman tsokana.

Bata san iya adadin lokutan da ta Wauka a wurin ba, chan ta hangosa yana tahowa cikin tafiyar nan tasa me cike da natsuwa kaman saraki, sanye da wasu kananun kayan still farin Jean da navy blue shirt a ko yaushe Adonshi da shigar shi masu kyau ne da salo irin na burgewa.

Maganan Fatima ne ya faWo mata bata san sadda ta kwashe da wani irin dariya ba har da hawaye, wai amma Fatima tayi asara ta taSe duniya da lahira fisabilillahi ta rasa abun so se wannan? Dariya take tayi tana sakewa wai fa har da kuka Fatima ke yi sbd shi? Ta kara kwashewa da dariya tace
"Taabbb Allah ka rabani da aikin wahala"

Har ya wuce tana babbaka dariyar ta kaman sabon kamu inda Allah ya taimake ta ba Kallonshi take ba don ta san in har ya san dashi take yadda ba kowan nan se na lahira ya fi ta jin daaWi, ji fa yadda yake tafiya, ita wallahi tafiyar da yake yi ko ita mace bazata yi irin shi ba, dariyarta tasha daidai sashensu na samari ta ga ya Wan tsaya ya waigo, daidai itama ta Wago ta kalle shi se suka HaWa idanu, kallon kanki ya taSu ya watsa mata.

Ko seconds biyu be yi ba ya juya ya karasa shigewa sashen, mikewa tayi tana share hawayen dariyarta kaman wacce duniya ta yiwa daaWi ta wuce sashen Jaddah, tana shiga ta narke tana tafiya kaman marar lafiya.

Jaddah tace
"zo ki karbi tsarabar ki na wurin Faizan"

HaWe rai tayi, Fa'iza tace
"ke kinga rikicin da aka kwasa da ya Faizan kan Jaddah ta kwasar miki chocolates Win nan karfi da yaji? wlh ki gode mata ta san yadda kike son chocolates shiyasa, ga su da daaWi kaman zasu tsige kunne"

Kallon chocolates Win tayi masu tsada ne sossai, daga gani ma maybe ba a nan Nijeria ya sayo su ba sede tunda daga hannunshi ya fito basu ba ta sha'awa ba, kau da kai tayi tace
"Jaddah da baki wahalar da kanki ba don ni kam ba sha zan yi ba"

Jaddah ta saki baki zata yi magana kenan Fauxa ta fara kukan hannunta na zugi, da sauri Jaddah ta karSe hannun tana salati tace
"Faozia garin yaya? Me ya sameki haka?"

Ai jin tambayan Jaddah yasa ta kara narkewa tana fashewa da kuka, she's so fragile in tana abu kaman little baby, Fai'za tace cikin damuwa.
"Jaddah ita da ya Faizan ne"

Nan ta bata labarin abunda ya faru tsakaninsu, Jaddah tayi ta masifa ta kuwa ci alwashin se ta saSa mishi wani irin mugunta da bakin hali ne wannan?

A kan cinyar Jaddah ta kwanta tana jin daaWin yadda Jaddah ke ta zuba mitan abunda ya farun, ta kara da
"mutum ne se ba?in miskilanci yanzun nan yasa yarinyar da yake ikirarin buduruwarshi ce kuka amma ko a kwalan riganshi"

Kau da maganan Fauxa tayi don be shafe ta ba, anan ta kwana ma yau..

Washegari Monday ko aiki Waya bata yi ba da taje school ma babu abunda ta rubuta se surutu da neman magana, a ranar Ammi ta dawo itama Seda tayi faWan hannun nata sede baba Alhj be ce komai ba.

Bayan 2days ta Wan samu sauki ta cigaba da aikinta, zuciyarta kuwa na kiyasta mata yadda zata rama abunda ya mata sbd ta sha wahalan qunan sossai.

Yau tana kwance bisa kujerar Jaddah tana danna ?ar karamar wayar jaddahn sbd ita ba kaunar kallon tashoshin wa'azuzzuka da shi kaWai suke dashi gabaWaya gidan take ba, jaddah ta fito rike da tray tana kallonta tace
"Fauziyya don Allah mi?awa Faizan abincin nan kinga yaran duka suna wurin Ibrahim(baba prof)"

HaWe rai tayi tace
"Jaddah eyyah ki jira su in sun dawo su kai mishi"

Jaddah ma rai ta Sata tace
"zan saSa miki wlh Fauziyya, ki wuce ki tashi ki kai in dodonki ne se ya cinye ki, in kuma baza ki je bane ki gayamin"

Hawaye ne ya cika idanunta, ita ba mikewa take son yi ba don ko da yaran suka je wurin baba prof da be ganta ba seda ya aiko fakiha tace mata tace tayi bacci idan kuwa bata ce haka ba se ta kirSa ta in aka dawo sake kiranta, gashi yanzu Jaddah zata saka ta kaiwa wannan azzalumin abinci.

Mikewa tayi ta Wauki tray Win da Jaddahn ta dangwalar ta fito, shiru tayi tana tunani, in ta taSa ji da kyau Jaddah ta taSa maganan rashin son yajinshi sbd muguwar ulcer Winshi ko yaya ya ci yaji se ya kwanta, murmushi ta saki taje kan kujerun tayunsu ta ajiye tray Win da gudu ta koma gidansu taje ta fara binciken drawer Winta akwai wani yaji me zafi da ta daka ranar girkin Amminta sbd an yi mata dole daka yajin shinkafa da waken, kowa da wahala yaci yajin sauran ne ta kulle ta boye a sif Winta.

Da gudu ta dawo ta buWe miyan kubewa danyen ta juye duka, cokalin da ta biya ta Wauko a kitchen ta saka ta juya kan ta ajiye shi a wurin, ta dauki abincin ta nufi sashensu, a gaban site Win ta kalli HaWaddiyar beymach Winshi ba?i siWik se Waukar ido yake da yayi parking a wurin, baki ta taSe ta isa kan motar da sbd yanayin kyaunta mutum kan iya finshi tsawo ta Waura a kai ta juya tayi tafiyar ta.

Tana nan kwance a parlorn na Jaddah har wuraren karfe tara da rabi, wayan Jaddah ne ya fara ringing ta Wauko ganin Faizan ta taSe baki ta mayar ta ajiye tare da lumshe idanu kaman tayi bacci, Seda ya kira sau biyu a

5 / 29