Advertisements
Chapter 11 Reading Goran Duma by Maimuna Idris Beli BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Goran Duma by Maimuna Idris Beli

Author :  Maimuna Idris Beli Category :  Action Novels

Chapter   11 / 28

30K to 33K   out of 82.5K words

yanzu dan mu yi shirye-shiryenmu tare,
bare kina garin me za ki koma gidan ki yi sati biyu ki
dawo?
Haba Rumasa'u me ya yi zafi?"..
.
.
Allah sarki masoyiya, ba dan jikin nata ba ai da nayi
magana an hada bikin mu da ita.lol.
Dan Aunty na Ruma..GORAN DUMA (P 22)
.
.
Nan da nan idonta ya cika da kwalla, ta kawar da kai tana
nad'ewa.
"Ni garin ne kawai ya yi zafi, na tabbatar idan na yi nisa
da shi zan sami sau'kin 'kunan zuciya...
Don Allah Hajiya ki bar ni in tafi, lokacin auren na
dawo..."
Hajiya ta tari numfashinta dan ta ga tana shirin rikicewa.
"Shikenan za mu tattauna maganar da Alhaji zan sanar da
ke zuwa dare, sai ki fara shiri ko?"
Ta kad'a kai, fuskarta ba ta bayyana abin da zuciyarta ta ji
da maganar Hajiya ba; dad'i ko ba yabo ba fallasa?
Alhaji ya 'kurawa Hajiya ido cikin rashin hayyacin batun
da ta gama zantar da shi, akwai alamun ya kasa
hankalinsa fiye da yadda ya kamata ya kasa shi, can ya
nisa ya ce.
"Kin san abin da raina ke raya min game da yarinyar
nan?"
Hajiya ta girgiza kai kawai tana kallonsa, ya 'kara jan
numfashi sannan ya sauke ajiyar zuciya ya ce. "Da kamar
ace ka isa da d'an yau, sai in saka Yusha'u ya maye gurbin
Auwal a yi auren nan kamar yadda aka tsara. Ina cike da
tausayin yarinyar nan ko daya ba na 'kara kaunar ta shiga
hannun da zata wahala, ko hannun da bai san
darajarta ba, samun irin marigayi Auwal wani abu ne mai
gajiyar da numfashi shi yasa na cika da tsoron hannun da
zata fad'a".
Hajiya ta jima kafin kwanyarta ta fanso kanta daga
firgicikin da ta shiga, Yusha'u nata ne, amma ta tabbatar
hada shi aure da Rumasa'u wani ganganci ne,
musamman idan ba da amincewarsu ba, har ga Allah ba
ta shakkar Rumasa'u saboda sau'kin hali da taushin
zuciyarta, mace ce da duk yadda ka kai da ba'kin hali da
wuya ka gundurar da ita, har ka
gani a fuskarta, amma Yusha'u wani irin mutum ne mai
juyayyen hali da kin fahimtar mutane da jujja
ko da gangan. Saboda haka kullum ra'ayinsa yake tfy,
kowa bai iya ba, ita kanta ta san ba don Yushau yy sa'ar
tsayayyen uba ba, da su kansu iyayensa sai sun yi kuka da
shi. Amma da yake babu 'yar musu tsakaninta da mijinta
sai ta binne wannan zargin ta kawo wani da
ta ke jin zai musu ma'ana, wato ta sanar da Alhaji labarin
Hafsat ta baya na yun'kurin hana Auwal
auren Rumasa'u da mahaifinsa ya yi. Ta 'kare da cewa.
"Yanzu babu abin da ya fi tsaye min a rai irin
wannan, auren Rumasa'u nan kusa zai taimaka wajen
mantar da ita Auwalu, ta ya ya hakan zata kasance idan
ana gudun auren sickler?"
Kai tsaye Alhaji ya tare ta da fadin.
"Ni ma daya ne cikin dalilaina na son Yusha'u ya aureta,
'yar uwarsa ce ya san darajarta kuma ya san matsalarta.
Ina ji a raina duk wani da zai yi tattalinta bayansa zai bi,
dalilina na biyu shi ne, kawo 'karshen zaman wannan
tuzurancin nasa ba tare da dalili da 'kosai-kosai da shi. Shi
ba dan zuhdu ba, ba komai ba ballatana a kalli abin a
matsayin ya hana shi aure, kullum maganarsa daya ke
nan bai ga wadda ta yi masa ba. To ga 'yar kirki nan ya zo
ya aura na san duk 'kawar da yake a mace ba zai zarce
hangen irin Rumaisa'u ba... ke ni Allah Ya had'a kansu,
rasuwar Auwal din wata aya ce a cikin fatara".
Hajiya dai sai sauke ajiyar zuciya ta yi ta ce. "Allah Ya
tabbatar da abin da ya fi alkhairi".
Ya amsa da, "Amin". Lokacin da ya ke laluben lambar
Yusha'u a wayarsa, sannan ya ce. "Ki rarrashe ta ta bani
sati daya, zan tattauna da wadanda suka kamata akan
maganar Yusha'u, in akwai yiwuwar hakan ina ganin ba
sai ta koma gida ba ko?"
Hajiya ta yi dariya ta ce.
"To ai ni ban ma san abin da zan ce mata ta kwantar da
hankalinta ba, yadda ta ke nunawa zamanta anan zai ci
gaba da tuna mata Auwalu".
Ya kara wayar a kunne yana amsa mata.
"Ki fada mata na ce sai nan da sati daya, zata fahimce ki".
Da dare Alhaji ya ji muryar Yusha'u a palon Hajiya, ya
tabbatar kuma Rumasa'u na falon tare da Hafsat da
Mubarak, kawai sai ya nufi falon kai tsaye da niyyar sanya
ido ya ga yadda suke mu'amalar juna wata'kila ya san ta
inda zai fara tunkararsu.
Kowa na zaune ana hira cikin sakewa, amma Rumaisa'u
na kwance kan doguwar kujera ta yi dif kukan zuci ta ke,
domin tana hana hawaye zuba a idonta. Duk lokacin da
idonta ya kai kan agogo ta ga karfe tara zuwa goma har
sha daya na dare, sai ta ji wadannan lokutan ne ta tarar
da missed calls din Auwal, daren da zai mutu, kaiconta
shi ne ina ma ta daga ta ji abin da zai fada mata, wanda ta
ke jin ya matsu ya fada mata tunda ya dinga jero mata
kira sama da ashirin duk abin da yake son fada mata ta
tabbatar da ya sameta ya fada matam da
yanzu ya zame mata wani rubutu da zata dinga
karantawa yana rage mata d'imi.
Idanun Alhaji a kanta, ta muskuta ta dan goge kwallar da
ta fi 'karfin zuciyarta ta fito ba tare da ta lura Alhaji na
kallonta ba, ta janyo wayarta ta fara dubo sa'konnin
Auwal a wayar tana goge hawaye
a sace.
Alhaji ya yi gyaran murya ya ce. "Rumaisa'u yaya dai na
ga kina 'yan 'kananan hawaye?"
Ta yi saurin basarwa ta juyo ta dube shi, amma ta rasa
abin cewa, har sai da Hafsat ta dube ta a nutse ta ce.
"Tunani ko?"
Ta yi saurin girgiza kai ta kama ciki, ta ce.
"Cikina ke ciwo". Alhaji ya yi saurin duban Yusha'u wanda
ko juyowa bai ba, yana ta faman ji da kayan marmari,
sannan ya juya ya dubi Rumasa'u cikin tausayawa,
ya ce.
"Ayya kin sha maganinki kuwa?"
Ta kada kai ba tare da ta samu damar maganar ba.
Alhaji ya kuma juyawa ya dubi Yusha'u ya ce.
"To ko asibiti zaku tafi, Yusha'u tashi ka kaita asibiti".
Yusha'u ya ji wani irin takaici ya tokare masa ma'koshi,
da kyar ya sami wani dan sarari bayan ya
hada takaicin da lemo ya hadiye, ya kokarta yana duban
Rumasa'u ya ce.
"Toh, tashi mu tafi".....
.
Ni yau rai na ma ya baci, ya za'a hada Ruma da
mudadden namiji bayan tace ni take so?
Sai bayan sati biyu ma kawai.lol.
Dan Aunty.
.
.
Ta yi saurin girgiza kai tana duban Alhaji.
"Ai bai yi tsanani ba Alhaji, akwai maganin da zan sha".
Hajiya ta shiga maganar.
"Tafarnuwar za a jajjaga miki?"
Dole ta kada kai cikin ajiyar zuciya, Hafsat da ta san aikin
ta ne sai ta mike tana cewa.
"To bari na kawo miki, Mubarak zo mu je ka taya ni
6arewa".
Alhaji ya yi saurin tarewa.
A'a! Debo tafarnuwar ki kawowa Yusha'u ya yi aikin".
Rumaisa'u ta dubi Yusha'u da sauri, amma ba ta iya
karanta komai a fuskarsa ba, amma dai fuskar tasa
ce ta 6oye, domin ya shiga rudanin cewar akwai wata a
'kaasan zuciyar Ahaji saboda haka dagewa
ya yi murmushin karfin hali ya ce.
"Alhaji ai ba na son warin tafarnuwa".
Alhaji ya tsare shi da ido ya, ya ce.
"To ai haka zaka koya ka saba, misali idan ka haifi sickler
zare hannunka zaka yi ka bar matar da dawainiya?"
Da yake Yusha'u ba yaro ba ne, nan take ya kamo tashar,
gumin goshi ya fara masa sallama, dan sanin waye
mahaifinsa akan a'kida, sai ya yi 'kasa da kai kawai yana
hirji a zuci.
hafsat takawo masa tafarnuwa da ruwa da kofi ta zauna
zata tayashi alhji yace tashi ki bar shi.
Haka yagama komai ya ce mata to taso ki amsa taje ta
amsa ta kafa kai ta shanye.yauwa haka ake idan
wani nakusa dakai bashi da lfya taimaka masa zakai..alhji
ya ko ma nashi yushau ya jima yakasa
tashi yaje kiran mahaifin nasa saboda kiran mahaifin
nasa yasan auran ruma ake son likamasa dukda yasan
imma hakan ta tabbata baisa ya bijiremasa ba..ya isa
dakinsa alhji ya ce wani dan sharar fagge naimaka dazo
akan
danwani aiki danake son baka wanda na tabbata zakaji
dadi. dan ALLAH kai wani tunani akan Ruma kasama mata
wata makoma dazata iya zama da zata iya
zama mata masalaha dangane da halinda ta tsinci
kanta..naimaka hakan ne danganin kaine babba
dagani har abbar ruma in muka mutu dawainiyar ya yan
mu zai iya hawakanka..nandai alhi yaitamasa bayanin
yanda zai fahimce shi
amma daga kar she sai yushau ya ce inaga alhji komawar
ruma gidansu yafi mata kwanciyar hankali..
daga kar she dai alhji ya ce kai nakeso ka maye gurbin
auwal.. A dukkan maganar Alhajin babu ga6ar da Yusha'u
zai karya ya shigar da nasa 'korafin saboda haka
ya hau rawar baki.
"An ji, ita an ji daga gare ta ne?"
Kai tsaye Alhaji ya amsa masa.
"Ba na jin yarinyar nan. Ai Rumaisa'u ta haifu". Gugar
zana kawai Yusha'u ya dauki maganar
Alhaji, don haka ya yi 'kunar bakin waken fitowa ya fadi
abin da ke ransa.
"Dan Allah a yi min afuwa Alhaji, wallahi ni Rumaisa'u ba
ta daga cikin irin matar d anake son aure.... akwai na'kasu
da yawa a Rumasa'u da ba zan iya jurewa ba".
Alhaji ya 'kura masa ido fuskarsa ba ta nuna yadda ya
kar6i maganar Yusha'u ba, ya ce.
"Uhum! Lissafo min abin da ta rasa ko wanda ya yi mata
yawa a matar da kake so"..
kodaya bana da ra ayin auran macen da iliminta yadara
na sec. sannan ALLAH yasa banasan shagwababben
mutum.kuma aganina duk kokarin mutum zataga ya
gaza.
cikin tsananin ba cin rai alhji ya ce duk wadan nan
hujojjun naka ba bu wanda yaikama dana addini.alhji
ruma fa tafini zurfin karatu duk yarinyar dataje jamia
idonta a bude yake.ganin mazansu suke kaidaya dasu
basu isa dasuba.kila
kuma kawai ta wafto rigimar kunbi kun shagwabata
ciwon nan nata kamar wani kayan alfarma ya
zamemata.alhji ni ga badayama banasan auran dangi
alhj ya ce yanzu ne na fahimci bada zahiri kake amfani ba
son zuciyakawai.alhji ya ce da zuciya
daya na za barmaka ruma a matsayin iyali bayan na cika
zuciyata dafatan zaku zamewa juna alkhairi kuma idan
ina da hakki akanka abinda na zabarmaka kenan amma
idan kaki sai inSaka maka ido
shikenan alhji ALLAH ya tabbatar mana da mafi alkhairi
badan ransa yaso ba..
awashegarin ranar ne kiran alhji ya risketa hankalinta
kwance dan a tunaninta zaimata nasi hane kamar yanda
yasa ba kila kuma ta bankwana.amma bayansun gaisa sai
yana ta tattalinta tare da kutsamata maganar yusha u
cikin
da bara irin tasa ta manya.
Abba ya ce mata rumaisau yushau ne yazo mana da wata
magana yanaso ya maye gurbin auwal.ayadda ya cemin
ya jima yanasanki ganin kinkarbi auwal yasa ya
hakura.nima kuma dama inada muradin hakan kimanta
da wata ibtila i dakika sami kanki aciki.
rumaisau kizama mai godiya ga ubangiji.ki amince ayi
auran nan kamar yadda aka sanya da mari
gayi.idan rumaisau karkaf abushe take kallon alhji to
mizataima kuka ko tashin hankali.duk wata damuwa ko
abinsanya kuka dazata ci karo dashi a duniyarta mutuwar
auwal ya isa akira shi matakin kar she.idan kuwa wannan
bakincikin
baikasheta ba yakamata kowani tashin hankali ya zamar
mata gada
ta ce masa alhji badan ka bayar da goyo n bayanka a
maganar nan ba alhji dana nemi hanzari.ya ce ina
jinki ruma ta ce masa alhji da baka goyi bayansa ba
harshensa ne yaimazuciyar sa karya takowani bangare
nasan yaya yushau baida tsarin auran irina.baikamata
mutum lafiyayye kamar sa yakare a auran nakasasshiya
irina ba nanda ruma ta bi duk wata hanya tagama aibanta
abinda aka
gani ake son hada auranta da yushau..
alhji ya ce mata duk wata lalurarki ta sikila idan har bata
hanaki auran auwal to bazata hanaki auran yushau
ba.yadade yanai mata nuni
da abubuwa dasuka sanya yakesan ayi auranta da yushau
yanzu kam Ruma tana tunanin KARA,KAWAICI,
SADAUKARWA, yakamatne tsakaninta d.a alhji da hajiya
wadanda suke karramata daidai da mahaifanta..ko
sudasu zata iya dogara ta dubi yushau matsayin mijin
aure
Shirye shiryen biki ya kankama innar ruma ta iso ana
sauran kwana biyu amma kafinhakan tunda alhji
yajizatazo ya tura su yushau rogo saboda bayaso umman
ruma ta fahimcin rashin jituwar dake tsakaninsuhaka
yushau yayarda sukatafi badan yaso ba ahanyarsu ta
tafiya rogo bawanda yaimagana acikinsu.saidai ruma ta
karbi sakonninda take ta suka sata hawaye idan ta shiga
motar auwal sai ya zuge glassai tsab ya rufe, yakuma
kashe A.C sannan a motar sa baya rabo da CAR HEATER
saboda ita,ga tuki cikin
natsuwa,ko da a hanyar da bata da kyau ne saboda kar
tajigata,bugu da kari yakan umarcetatada fito da
hijab a jakarta tasa idan da mayafi ta shiga motar....
.
Dan Aunty.
GORAN DUMA (P 24)
.
.
duk wadannan gatancin sun kufcemata ko kallo bata ishi
yushau ba bare ayi maganar tattali
danhaka taiyi ma kanta gatadakanta ta rufe gilasan.shiko
sai zuba gudu yake a hanya ya cika mata kune da wakar
ala wanda idan ta rantse saurare kawai yake amma baya
duba maanar wakar.
sunkusa karaye aka bugo mata waya wannam karan ya
rage karar wakar ta daga wayar ta sada zumuncine da
gaisuwa daga TAHIR wani member ne a kungiyar su ta
masu sickle cell. yaimata gaisuwar auwal tare da
jajantawa yushau ya ce mata wanene kukai waya da shi?
tajima kafin ta ce sunansa TAHIR TAFIDA MUHAMMAD
tana rufe baki ya watso mata wata tambayar yakuke
dashi?
memberne a kungiyarmu ta sickle
cell acan muka san juna muke zumunci.
ammadai kina da kudurin idan munyi aure zaki bar
kungiyar?
dayake na kwana sanin aurena ba zai rabani da sikila
ba,sai ban ta ba tunanin zan bar kungiyar ba.
amma nasan kin san duk lalacewa
kinsan cewa mijinki yana da ikon hanaki duk wata
muamala da yake da shakkunta ko?
duk yadda kike jin wayewa nasan kinsan mijinki yana da
karfi akanki.
ruma tajima kwarai maganganunsa nayi mata ihu
aka.saidai tayi jarumtaR boye kaico da hawaye,saboda
haka ta shirya magana ma sai ta kori rauni a zuciyarta
wata sha afa da mukai kenan nida kai da iyayen mu a
kaida duk wanda zai auri mai sickle cel ya kamata a zauna
a tattauna dashi bayan gwaji yaji matsalolinsu yaga abin
juriya akai in zai jure din,
yushau ya ce dan na ce ki bar kungiya idan kinyi aure?
ko ruhin ciwon naki makale yake da kungiyar da idan an
hanaki ya tsinke Ranki
duk dai taji zafin maganar amma a sanyaye ta girgiza kai
shikuma ya sami damar dorawa cikin zafin rai
kiyi kokari ki fahimceni karki dinga sauya min magana
kina hada min ita da ciwo.yanzu dai naji kina waya da
wani wanda ba muharraminki bane...
a raunane ta amsa da cewa ban dauki fadan hakan laifi
bane sannan ban shirya karya ta shi ga tsakanina dakai ba
Idan hakane sai ki yanke hulda da abinda kikasan
banaso,dankar kifada min gaskiya inki fahimtarki kiji
ciwo.inkuma karyar kike yimin ALLAH ne shaidata,kamar
yanzu dakika cemin dan kungiyarkune ai bansan
gaibuba,in bayan dangatakarku ta kungiyancin akwai
wata dangatakar yaya zansani kaitsaye ta amsa tana
duban titi.
kobaka sanidinba rashin sanin ba zai cutar dakai ba,ko da
cutarwar ta fargaba ce tunda kasan ciwon
sikila ba kanjamau bane da ake bukatar mai shi ya auri
dan uwansa mai shi shi sikila so ake ya nemo lafiyayye ya
aura dan
dorewar haihuwar yayansu masu lafiya.saboda haka
karkadamu kanka da dangantakata da wani
sickler ko kuma ka saka mana zargin dangantakar
soyayya
afusa ce ya juyo ya dubeta idan na fahimceki umarni kike
minko?kawai saitasami kanta da tuntsi
rewa da dariya tana kare masa kallo kaitsaye ta ce.
"Haba dai, yaushe zan maka umarni?
Na ga dai kamar bai kamata mu dore a gizago da
biyayyar babu ji babu gani ba. Ya wajaba mu tattauna
matsalar ciwona da kai a yanzu kafin nan gaba ka ce an
baka a rufe".
Karkacewar da bakinta ya yi wajen dariyar da take, yasa
tausayinta ya danne takaicin dariya da ma'anar maganar
da ta yi masa. Ya kawar da kai ya bi titi da kallo, sannan
murya 'kasa-'asa ya ce. "Tunda ba fasa auren za a yi ba
idan na ji abin da bai yi min ba cikin abin da za mu
tattauna din ai barin tattaunawar ya fi..."
Ta tari numfashinsa da fadin.
"Me yasa za a kasa fasawa in kuma ka ga ba ka muradi?
Duk sickler ya san a saka aurensa a fasa ba wani ba'kon
abu ba ne, saboda haka babu abin da zai fari dan ka fasa".
Ya jima kwarai yana sa'ka maganar da zata fito bakinsa
kafin ya barta ta fito.
"Da zaki ajiye bokonki waje guda, in sami
kawwamammen matsayi a wajenki irin wanda
nagartattun iyayenmu mata ke ba wa mzajensu, to ina jin
zan zama mai hakuri da tuntuninki ga Auwal.
Dan haka ba kya bukatar 6ata lokacinki wajen yi min
umarnin in aure ki ko in fasa tare da sanin
fasawar tawa ba zata rage ki ba, ko ta amfane ki, tunda
wani za ki aure ba Auwalu ba".
Ta yi shiru kawai tana juyawa maganganunsa, kaasa
fahimtarsu sosai ya sa martaninta ya bi ruwa.
Shi da ya damu da jin ta bakinta sai ya tuna mata yana
mai kallonta.
"Ba zaki ce komai ba?"
A sanyaye ta amsa masa. "Ga6o6in maganganun naka ne
da yawa, yadda kowace na karya za tashi guda in kuma
jata ta yi tsawo, saboda haka kar ka zaci muhimmin abin
da kake son jin bakina a kansa."
Kai tsaye ya amsa mata.
"Kar ki dauki kanki wata tsiyar saboda kin yi zurfin karatu,
ki zauna da ni zaman bauta kwatankwacin yadda kika ga
iyayenmu na yi. In kika yi hakan
shine kika ba ni karramammen matsayi wanda zai wanke
min dukkan tsatsa a raina na auren mai
zurfin ilimi da ban ta6a shiryawa rayuwata ba".
Ta dinga jan numfashi kafin ta amsa masa cikin dakewa.
"Ina jin da taka karramawar zaka sai wancan matsayin da
kake ambatawa, in kuma ka cire zace-
zace da zarge-zarge ka kuma cire garaje cikin mallakar
matsayin da 'karanta rainuw da kuma
sau'kaka fahimta, wannan shi ne".
Ya yi dif kamar ruwa ya cinye shi da harshensa ya yi
niyyar fada mata abin da zuciyarsa ta fahimta a
maganarsa. To abin da zai gaya mata shi ne bokon da
yake gudu ta yi masa.
Bashi da za6i, dole ya yi shiru ya kyale ta, ai a kan
sharafinta take tunda tana da Alhaji me tsaya mata. Har
suka shiga cikin garin Rogo babu wanda ya tanka wani,
suka sauka a gidan kakaninnsu, duk
da tuni kakannin sun 'kar, sai 'ya'ya da jikoki. Haka kowa
ya dinga sanya musu albarka, Yusha'u na
shan albarkar yarda da ya yi ya auri Rumaisa'u da
nakasarta, Rumasa'u na shan albarkar ajiye jimamin
rasuwar Auwal da ta yi a gefe ta yarda ta kar6i dan
uwanta.
Sun wuni a nan gidan, sai dab da la'asar suka nufi gidan
Goggo. A gidanta Yusha'u ya yi mafi rinjayen
zamansa saboda sha'kuwarsa da 'kaunar da 'yan uwa da
Allah Ya zuba mata. 'ya'yan wa da 'kani da mahaifinsu.
Son danginta neyasa duk sa'adda ta kwashi Auwal suka je
Rogo, to a gidan Goggo zata sauke shi, su yi
hira su yi barkanci tare da Goggo.
Wannan dalilin yasa suna shiga gidan yanzu gaba daya
jikinta ya yi la'asar, musamman da Goggo ta baza musu
tabarma wajen da ta saba shimfida musu in ta zo da
Auwal, sai ta kasa zaman kan
tabarma ta koma kan 'karamar kujera ta zauna tana
kokarin hadiye kwallarta.
A haka suka gaisa duk tana rikice, a karshe dauriyarta ta
kai 'karshe lokacin da wasu rukunin zabbi suka gifta, ta
tuno lokacin da suka zo da
Auwal an kyankyaso jariran zabbi fiye da ashirin reras
abin sha'awa, ya daga kai ya dubeta ya ce.
"Don Allah zabbin nan ba su burge ki ba Rumaisa'u?"
Ta bi zabbin da kallo tana murmushi, sannan ta ce......
.
Dan Aunty.
GORAN DUMA (P 25)
.
.
"Ba na jin sun burge nikamar yadda suka burgke ka,
tun dazu fa na ankara kana ta faman

11 / 28