Advertisements
Chapter 16 Reading Goran Duma by Maimuna Idris Beli BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Goran Duma by Maimuna Idris Beli

Author :  Maimuna Idris Beli Category :  Action Novels

Chapter   16 / 28

45K to 48K   out of 82.5K words

gurina ki yi iyakar son ranki ran da na
kawo wadda zata bi ni sai 'kila ta zame miki darasi"
.
Allah sarki Ruma.
Mata Allah Ya raba ku da na miji irin Yushau,
Aamiin.
.
Dan Aunty
GORAN DUMA (P 36)
.
.
Ta hadiye dun'kullallen ba'kin cikin da ya tokare mata a
'kirji, da murmushin 'karfin Hali ta ce.
"Ba na tuna Auwal a hurimin muzguna maka Yaya
Yusha'u, domin ban aure ka ta silar so ko kuma ta dole
ba, na aure ka ne dan na yi bautar aure wato bautar
Allah, saboda haka ban ta6a hada zaman gidanka da wani
'kyalli ba.
Halin da na sami kaina a cikin gidanka da irin ri'kon da
kake min wani nufi ne daga ubangiji. Yadda kake nuna
munin halina da kasawata a cikin rikon da nake maka
Allah Shi ne shaidata ina kuma ro'konSa kafin Ya dau
raina ya nuna maka 'kir'kirarmin munin hali kawai ka yi
ba dan ya cancance ni ba.
Sai dai duk yadda na ke da 'karfin halin tsayar da zuciyata
a kanka kar na tuna baya in wuya ba na kasa tuna Auwal
tunda MUTUM DA ZUCIYARSA bashi da iko da ita, sai dai
ina ro'kona wata alfarma, ko
ma dai menene, Auwal ya mutu babu komai tsakanina da
shi, sai fatan alkhairi. Ina ro'kon ka
janye shi daga cikin al'amuranmu, mu muka saura a
duniyar muke taka irin rawar da muke so a
cikinta, kuma ha'ki'katan ta ishe mu riga da wando...."
Cikin kuka ta tashi ta bar masa dakinsa, in da ta bar shi da
shanya baki yana kallon wajen da ta tashi.
Ya yi niyyar ya share ta, amma da ya tuno tashin hankalin
da suka yi har ta kai ga 6ari sai ya sauya shawara, ya
gaggauta shiryawa ya sameta a dakinta.
Hankalinsa ya dan kwanta da ya same ta ba cikin kuka ba
kamar yadda ya yi zato, sai ya same ta a
zaune bakin gado tana murza confo a gwiwar hannu tana
cije le6e, akwai alamun hannun ne ya motsa.
Ya zauna kan sofa yana binta da kallo fuskarsa babu yabo
babu fallasa. Ya jima yana shan 'kamshi
kafin ya taro abin da zai ce.
"Ki yi hakuri na daina sako Auwal a lamuranmu, amma
magana ta gaskiya ba zan ta6a lamintar..."
Ta yi saurin dakatar da shi cikn muryarta da ke sha'kewa
saboda son fashewa da kuka da kuma alamun zafin ciwo.
"Yaya Yusha'u ka taimake ni ka tashi ka koma dakinka
ciwon hannuna ya kori ciwon da zuciyata ke ji saboda
takaicin da kake 'kunsa mata. Bai kamata ka biyo ni ka
kuma daga min hankali ba, in dai baka dokantu da na bar
maka duniyar a yanzu ba"
Bai yi mamakin yadda ta ke magana cikin fada ba. A sanin
da ya yi mata in dai tana ciwon hannu ko 'kafa ya ta6ota
harshenta kan yi kaifi a wadannan lokutan, Allah basshi
idan ta warke sai ta ba shi
hakuri ta ce zafin ciwo ne.
Sai ya yi shiru ya tsaya yana kallonta, ta ci gaba da
mur'kususu tana 'kugi, nan da nan ta hada gumi
sharkaf! Dole zuciyar musulunci ta sanya shi zuwa ya
ri'keta yana mata sannu yana ta faman shafa
mata confo a hannun.
Sun fi awa daya suna abu daya, ba ita ba ba shi kansa sai
da ya yi muguwar jigata saboda ri'kon da
ta ke masa. Ya tambayeta ta sha magungunanta na
kullum?
Ta nuna ba ta sha ba, ya nemi ya bata sai wajen karfe
daya ta samu runtsawa a cinyarsa ta barshi
da sa'ke-sa'ke da 'kare mata kallo, har ta kai shi ga lissafin
tsawon lokacin rabonsu da kusantar juna
kamar haka, lissafin kuma da ya tuna masa kishinta har
ya kai ga farkar da ita. Amma Rumaisa'u 'yar halak duk da
gajiya da baccin da ya cika mata ido ba ta 'ki amsa
tayinsa ba.
Sai dai tir! Lokacin da ya fara gigicewa sai ya ke ambaton
sunan wasu mata.
"Sumayya, Sumoli, Ummi".
Tuni ta kwaci kanta da ambaton. "Lahaula wala 'kuwata
illa billah".
Ta barke da kuka lokacin da ta tattaro bargo ta tashi
zaune.
Ya bi ta da kallo cikin fuskar mamaki ya ce.
"Kan ki daya Rumasa'u, lafiya kike?"
Ta ci gaba da kuka cikin tsare shi da ido, sannan ta kattse
shi cikin shesshekar kuka, ta ce.
"Abin da ka yi yau ba ka da sanin yana daga nau'in zina?
Wace ce Sumayya, Sumoli, Ummi? Mene ne hukuncin
kawo mana su a shimfida?"
Zuciyar Yusha'u ta yi wani mugun bugu da ya fahimci
abin da yake rayawa ya fito fili, amma da yake ya iya
fargar jaji, sai yayi fuffukar borin kunya.
"Kin ga malama bana son sharri, wacce mace na sani
bayan ke?
Kawai ki ce min kin zaci kowa ma
irinki ne da kike suffanta ni da na kabari...."
Ta toshe baki ta tashi tsaye cikin tsananin tashin hankali
tana kallonsa.
Da sauri ta juya ta shiga bandaki ta turo 'kofa ta fashe da
kuka.
*
Bakwai safiya bata cika ba, Yusha'u ya silale ya buga mota
ya bar gidan inda ya doshi gidansu kai
tsaye. Ya kamata ya ture shakka ya bude kwanjinsa dan
yin abin da yake so ba wanda ake so masa ba,
wanda ya dace da shi ba wanda aka datar masa ba.
Kai gara ma ya tunkari Alhaji kai tsaye ya sanar da shi zai
yi aure tun kafin kwa6arsa ta zaureye tunda a yanzu dai
ta fara ruwa.
"Alhaji ina neman amincewarka ka yarje min na 'karo
aure, ina da muradin hakan sannan na kamu
da son wata yarinya, bugu da 'kari auren zai taimake ni ya
taimaki Rumaisa'u a matsayinta na mai yawan larura ba
ta ko iya daukar nauye-nauyen kanta balle ta dauki na
wani".
Ran Alhaji ya 6aci gaya, sai dai ya hadiye shi a ciki.
Ya yiwa Yusha'u wani kallon wulakanci ya ce.
"Cikin dalilai ukun da ka gabatar min wanne ne kake jin
ya fi gamsar da kai na lallai ka yi aure?"
Cikin karfin hali Yusha'u ya ce.
"Duk Alhaji ina son in 'kara auren, ina son yarinyar,
sannan dan in taimaki ita Rumasa'u"
Nan da nan Alhaji ya ci mur, ya tare shi.
"Ni karya ce ba na so, kawai dai kana muradin ka yi aure
yanzu ne ka sami matar da kake so ba wadda ake so
maka ba, kar ka 'kara sako Rumasa'u a cikin dalilanka".
Yusha'u ya dauko buhun rantsuwa ya fara saukewa,
Alhaji ya tare shi.
"In ka rantse min zan iya kwada maka mari a banza a
wofi Yusha'u, kana son taimakonta ka kasa nemar mata
'yar aiki?
Hajiya ma ta yi zuciya ta kai muku 'yar aikin, ka ke neman
korarta da mugun hali?
Duk halin da kuke ciki ina sane Yusha'u zuba maka ido
kawai na yi na ga iyakar gudun ruwanka,
in gani shin da gaske kasheta kake shirin yi, ka sami
sararin auro wata.....?"
Yusha'u ya tari numfashin mahaifinsa da doguwar
rantsuwa.
"Na rantse da Allah Alhaji ba 'karamin hakuri nake da
munanan halayen Rumasa'u ba...."
"Kafin ya sauke huci Alhaji ya sharara masa wani
bahagon mari, Yusha'u ya dafe kuncin, wani irin radadi
ya isa har kwanyarsa ya hadu da bakin da zuciyarsa ta yi
suka sabbaba masa zubar hawaye.
Yaushe rabonsa da dorar da zafin duka gemai-gemai da
shi?
A dake shi akan matar da yake
zaman laurara da ita?
Sai ya ji ya 'kara tsanar Rumaisa'u, zuciyarsa ta 'ke'kashe,
ya dubi mahaifin nasa cikin kwalla ya ce.
"Alhaji ni na san matsalolin da nake shiga a cikin auren
Rumaisa'u, idan dai ina da damar in auri wata
bayanta to don Allah ka amince min auren nan..."
.
.
Yushau dai dakikine inji wani a gidan nan,
idan kuna so ku bani dama na sheke shi kamar yadda
nayiwa Awwal kowa ya huta da bakin cikin sa...
Abbas Abdulkadir Hada Hada (Dan Aunty)
GORAN DUMA (P 37)
.
.
Alhaji ya hadiye rud'anin da ya shiga cikin zafin murya ya
ce.
"Ba ka da damar! Ka tashi kuma ka bar min gida, sannan
ina maka godiyar halaccin da ka yi min. Na
aura maka Rumasa'u dan ka ji 'kanta ashe kai auren je-
ka-na-ka ka yi da ita, kake zage 'karfinka
da iyawarka kake muzguna mata dan ta gaji da kanta ta
ce ba ta aurenka ta jure, sai kake son kinkimo aure dan
ka nuna mana iyakarmu. Auren da kadan ya haure
shekara daya kake shirin dan'kara mata kishiya?
To ban laminta ba, in kuma ka ga na laminta to ciki
aikinka ka yi ka sako min Rumaisa'i, fa'kat! Ka 6ace
min da gani na gaji da ganin mummunar fuskarka".
Yusha'u bai wami karfin gwiwar wucewa kasuwa ba
saboda zafin zuciya, fushi, 6acin rai da radadin a
fuskarsa ta ke.
Ya shiga gidan shiru babu motsin Rumasa'u ko na
talabijin dinta, sai Adama da ke kara-kainar aiki a
kicin, ya yi tsaki 'kasa-'kasa ya wuce dakinsa cike da dokin
Allah Ya kawo Rumasa'u ta ta'kalo shi ya sauke mata
kwandon rashin kirki.
Amma fiye da awaya biyu babu ita babu motsinta,
ga yunwa na addabarsa saboda ko karyawa bai yi ba, ga
ciwon kai da zafin mari ya sabbaba masa.
Amman fiye da awa biyu babu ita babu motsinta,
ga yunwa na addabarsa saboda ko karyawa bai yi ba, ga
ciwon kai da zafin da marin ya sabbabasa masa.
Da kyar ya lalla6a da azahar ya je sallah ya dawo ya kuma
kwanciya yana sanyo idon shigowar Rumaisa'i. Da gangan
ya dinga kaki da gyaran murya a tsakar gida dan ta san da
zuwansa, amma har la'asar ba ta shigo ba.
Bayan ya dawo sallar la'asar sai ya wuce dakinta kai tsaye
cike da fushi.
Ya same ta a zaune gaban sofa tana jinyar hannunta
wanda ya yi ciwo jiya, yau ya kumbura suntum, da ya
kalli fuskarta sai da gabansa ya fadi saboda yadda ta yi
wata muguwar rama idonta kuwa ya jeme da kuka.
Sai dai yana tuno yadda ya sha mari a kanta a wajen
Alhaji sai ya ji kamar ma ya yi mata Allah Ya 'kara.
Ya nemi guri bakin gado ya zauna ya dubeta fuskarsa a
daure.
"Ki tashi ki dafa min abin da zan ci yunwa na ke ji".
Cikin wahalallen kallo ta dan tsura masa ido, muryarta a
dashe.
"Yau daya Yaya Yusha'u.... ina neman alfarmar ka ci
abincin Adama, lallai ina takaicin kasa tashi in girka maka
abinci. Ba zan iya ba Yaya Yusha'u, dubi hannuna ya
dame ni da matsanancin ciwo kamar na cire shi na
jefar..."
Ya tareta cikin halin ko'in kula.
"Wallahi ba zan ci girkin Adama ba, dole ki tashi ko abu
mai sauki ki dafa min. Taliya ko ki soya min dankali da
kwai, na ba ki minti talatin."
Bai ko saurari hanzarinta ba ya fice ya barta. Dole ta mike
tana kuka ta sami dankwali ta daura a wuya,
ta tare hannunta ta nufi kicin.
Ta dinga aiki da hannu daya cikin matsananciyar wahala
da zubar da hawaye, in ciwo ya ishe ta ta tsaya ta yi
mur'kususu da 'kugi har sai ya lafa sannan zata tashi ta ci
gaba.
Da yake jalob din taliya babu wahala ba ta dauki wani
dogon lokaci ba ta gama, ta iske shi daki ta kai masa.
Ya nuna mata firji. "Ki dauki fura ki dama min".
Ta daure hawayen da ya cika mata ido tana duban
hannunta ta ce.
"Sai dai in da hannun hagu zan dama maka, kada furar ta
samu matsala.... hannuna yana ciwo."
Ya kawar da kai yana ta6e baki. "Yaushe za ki dama min
fura da hannun hagu?
Yanzu duk girkin nan da hannun hagu kika yi?
Damun fura sai ya gagare ki....?"
Da ta dan tsura masa ido ta ga ya soko maganganu a
'kasa sai ta fahimci shi kansa bai yarda da kansa ba. Ba ta
ce masa komai ba dan haka ya kuma samun
ta cewa.
"Ina son in sha furar nan da gaske, ki lalla6a hannnun ki
dama min..."
Cikin 'kufula akan rashin tausayinsa ta tare shi da cewa.
"Ba zan iya ba wallahi".
Ya dago kai cike da haushi da 'kufula ya dube ta amma ba
ta bashi sararin cewa wani abu ba, ta
tashi ta bar masa falon.
Wannan abin da ta yi ya 'kara 'kufular da shi. Ya fito zai je
sallar magriba ta fito tsakar gida cikin hawaye ta tare shi.
"Don Allah Yaya Yusha'u in ka yi sallar ka dawo ka kai ni
asibiti..."
"Ba zan iya ba wallahi".
Ya tari numfashinta da irin furucin da ta yi masa dazu
yana ta faman hura hanci.
Cikin raunin murya ko zai tausaya mata ta ce. "Don Allah
ka taimake ni Yaya Yusha'u".
Ya yi gaba cikin fuffuka ba tare da ya tanka mata ba. Ta
ce.
"To na je ni kadai...?"
Ya sake tare ta da fadin.
"Allah Ya ba da sa'a". "To ba ni kudin magani".
Ta fada cikin tsananin tausayin kanta. Ya fice abinsa yana
cewa.
"Ba ni da su".
Kawai sai ta dur'kushe a wajen ta rushe da kuka ta jima
tana yi sannnan ta koma daki tana kuka tana ambaton
Allah, babu halin ko Hafsat ta kira a waya ta taimake ta
saboda al'kawarin da ta yi na ba zata 'kara sanar da wani
halin da ta ke ciki ba ko zata mutu.
Har sha daya na dare tana cikin tashin hankali, sannan
Yusha'u ya shigo amma shi da kansa ya san bai kyauta ba,
tare kuma da tsoron 'kila Rumasa'u ta kira wani ta sanar
da shi yadda suka yi, 'kila
Alhaji ya la'ance shi, yana kuma cike da tsoron wannan
dan rikicin da suka yi kar ya yi sanadin zubewar cikinta
kamar yadda ya faru a cikinta na baya.
Wadannan dalilan suka sa bayan ya gama shirin bacci ya
doshi dakinta ya same ta cikin mawuyacin halinta.
Girman kai da masifar haushinta da yake ji ya hana shi yi
mata kulawar kirki, ya dai yi mata sannu, ya ajiye wayarsa
kan durowa ya haye gado ya ja bargo.
Rumaisa'u na zaune har sha biyu da rabi sannan ta samu
hannunta ya rage zogi, zuciyarta kuma ta dau
nata ciwon na zama da ma'kiyi wanda ba ya tausayin dan
Adam, duk hawayen da ta ke a yanzu
na wannan takaicin ne. Cikin haka ta ji take shigowar
sa'ko a wayar
Yusha'u, haka kawai ta ji ta cika da dokin ganin sa'kon.
Ban da tana cikin halin ciwo wanda kan mantar da ita
tuna wasu tunane-tunanen duniya babu yadda
za a yi ta kasa lissafinta da Sumoli, Sumayya, Ummi. Duk
lokacin da ciwo ya sake ta tunanin matan nan da ala'kar
da ke tsakaninsu da mijinta ta ke.
Cikin sand'a ta janyo wayarsa ta budo sa'kon cikin doki
da dukan zuciya ta bud'a.
'Ya Habibi, wani mafarki na yi mai 'kayatarwa, mun yi
nutso cikin burikanmu, mun tabbatar da mafarkanmu na
mallakar juna.
SUMOLINKA'.
RUMAISA'U ta maimaita karanta sa'kon nan ya fi sau
ashirin masa'ki, hade da kallon 'keyar Yusha'u da ya juya
mata baya yana sharar baccinsa.
Yanzu tunaninta ya fi tafiya juya maganganun sa'kon tare
da misalta daga irin macen da ya kamata su fito.
Sumoli! Sunan ya yi kama da na wadanda ba Hausawa ba
'kila kuma ba musulmai ba.
To karuwa ce?
Tana shakkar in karuwa ce dan Yusha'u ba shi da
kamannin neman mata ko ta ina aka juya shi.... .
.
To da ganowa idon ta, shi yasa yanzu naji ance an daina
yiwa mata padan komai idan za'ayi auren su sai padan
''kiyi hakuri, banda duban wayan sa' lol.
Dan Aunty.GORAN DUMA (P 38)
.
.
In Sumoli ba karuwa ba ce mecece? Ba ta ta6a kawo
matar da Yusha'u zai nema da aure zata zo da irin
wannan sunan ba bare a same ta da irin wadannan
maganganu a tsakiyar dare haka! Abin ya daure mata kai
matu'ka.
Ana cikin haka sai ga lambar sa'kon ta kwado kira,
Allah Ya sanya wayar a silent ta ke, kawai sai ta suri wayar
ta yi falo, ta daga wayar ba tare da ta tanka
ba.
Sai mai kiran ce ta fara magana cikin yau'ki da sautin
'karamar dariya.
"Yi hakuri na tashe ka bacci ko? Zuciyata ce ta kasa
hutawa da begenka.
Ka ga sa'kona?
Wani mafarki mai dad'i na yi mana tunda na farka na
kasa komawa....."
Zuciyar Rumaisa'u ta dinga bugawa fat-fat! Hannunta ya
dinga karkarwa ri'ke da wayar, amma
da yake tana da dauriya sai ta amsa muryarta tar!
"Ayya! Shi kam kin ga har ya fara jan rago, amma idan ya
farka da safe zan sanar da shi".
Ba ta jira cewar Sumoli ba ta kashe wayar ta zube a
kujera cikin haki tamkar wadda ta yi gudun famfala'ik,
abin da ya cunkushe mata numfashi ta ma rasa ta inda
zata kwashi wannan 'kalubalen
yadda zai zame mata maslaha.
Da safe Yusha'u bai sami sararin fita kasuwa ba saboda
kansa da ya matsa masa da ciwo.
Da Adama ta iso kasancewar da safiya take zuwa, ta zauna
har la'asar, yau da ta zo sai Rumasa'u ta
sallame ta da cewa sai gobe yanzu zata je asibiti daga can
kuma ta wuce gida sai dare zata dawo.
Ta sami Yusha'u da maganar asibiti kamar jiya dai ya
furje.
"Ki dawo lafiya, ni ma ba lafiyar ce da ni ba in zan sami
mai kai ni asibitin albarka zan sa masa".
Ta yi murmushi kawai ta yi masa sallama ta fice duk da
kuwa dari da hamsin ne a jakarta, ko cikakken
kudin a daidaita sahu ba ta da su daga Sallari zuwa
asibitin Nasarawa, ga shi safiya ce bare ta je banki ta fitar
da kudi. Amma dai da yake gidan zafi yake mata sai ta
jefa katin ATM dinta a jaka ta fito daga gidan ta kama
tafiya a 'kafa zuwa titi ta sami adaidaita sahun da zai kai ta
asibiti a kudin jakarta.
Akwai tazara tsakaninta da titi saboda haka hutunta hudu
a hanya, tana na hudun ne kan wata kwalbati kamar daga
sama Hafsat ta tsayar da motarta kusa da ita tana matsa
mata hon.
Cikin farin ciki da goge gumi ta mi'ke ta nufi motar Hafsat
ta bude mata cike da mamaki tana tambayarta.
"Daga ina zuwa ina?"
Bayan Rumaisa ta shiga motar ta daure cikin murmushin
ya'ke tana cewa.
"Daga gida zuwa asibiti, ke kuma daga ina kika fado mana
da sassafe haka, ko ba gidana za ki ba?"
Hafsat ta juya motar rabin hankalinta na kan Rumaisa ta
ce. "Daga gida nake, jiya Mubarak ya sanar da ni ba ki ji
dadi ba, da ke na kwana a raina shi yasa na doko
miki wannan sammakon".
Rumaisa ta yi murmushin jin dadi ta ce.
"Kin kyauta wallahi, kin ceci rai, ina Sani da ya bari kika
fito da safe haka?"
Hafsat ta amsa mata tana dariya.
"Ya fita shi ma, da dai ya kwaso min mita sai kuma ya
mayar da ita gori, wai gara na dinga zuwa ina
ganinki ko na yi zuciya in taya 'kokarinsa in karb'i baby".
Rumaisa ta tayata da dariya ta ce. "Sani ba dai ba'a da
zare-zaren magana ba".
Hafsat ta murgina kai, ta ce. "Ai fa.....
Hafsat ta murgina kai, ta ce. "Ai fa, me kike zaune kan
waccan kwalbatin?"
Cikin son a basar da maganar Rumaisa ta ce.
"Hutawa nake, wai 'karfe nawa?" Hafsat ta dan kalleta da
kyau sannan ta mayar da kallonta ga titi ta ce mata.
"Tambayar da na so in miki kenan, da sanyin safiyar nan
kika fito a yanayin jikinki kuma har da
tafiyar 'kafa, ina Yaya Yusha'u?"
Cikin hadiye 6acin rai Rumaisa tta ce. "Yana gida, kansa
ne yake ciwo..."
Da sauri hafsat ta tare ta.
"Yadda har ba zai iya tu'ki ba kuma ba zai iya fitowa ya
nemar miki adaidaita sahu ba?"
Sai Rumaisa'u ta kasa amsawa, wannan ya sabbaba shiru
a tsakaninsu, saboda kowa da abin da zuciyarsa ke
sa'kawa.
"Mu 6ulla ta zoo road ko zan samu fitar da kudi a Sahad".
In ji Rumausa'u cikin rashin nutsuwa dan ta san fada
kawai ta yi dan kar kai tsaye ta roki Hafsat
kud'i, amma ta san yanzu ba zata iya fitar da kudi ba.
Hafsat ta dan harareta ta ce.
"Da wannan safiyar?"
Rumasa'u ta yi shiru kawai, ita kuma Hafsat ta dora cikin
zafin rai da 'kufula.
"Mubarak ya fada min hannunki ke ciwo har ya fara
kumbura, mu gani".
Rumaisa'u ta janye hijabi

16 / 28