Author : Maimuna Idris Beli Category : Action Novels
son
nuna gazawa da ta tsaya kawai ga bayyanawa ta
hanyar 'kura masa ido cikin hawaye.
Haka suka tsaya ita kuka, shi hawaye, har daga
'karshe ya zagaya mota ya shige yana cewa.
"Zo mu je asibitin".
Ta yi saurin duba agogon hannnunta da ya nuna
'karfe sha daya da mintoci sha hud'u. Ta bude
motar ta sunkuya a tausashe ta ce masa.
"Bari na sanar da Hajiya".
Ya yi saurin tare da fadin.
"Rumaisa'u kar ki sanar da kowa matsalarmu fa,
umarni ne da kuma kokarin kwantar da
hankalinku ke da Abba zai kai ni gwaji, ba dan na
yarda da iya raba ni da ke ko ya yi wani abu a
cikin sonki ba. Ya kamata ki ri'ke wannan kada ki
yi 'kokarin raba ni da kanki, son da nake miki
mutuwa ce kawai zata iya raba ni da shi".
Ta sororo cikin sanyin jiki tana kallonsa. Ta
hadiye kwallarta ta ce masa.
"Auwal wai me yasa ka damu da kira mana
mutwa? Ai ba sai ka kirata zaka bayyana min
kana sona ba,.."
Ya tareta cikin kyalkuala dariya.
"Me yasa ba kya so na kirata? In akiranta ne dan
na sna ita ce mai YANKE 'KAUNA, duk yun'kurin
raba mu da kuke ni dai na tabbatar ita kadai ce
zata iya raba ni da son da nake miki. Amma na
san ba ni da karfi ko dabara a cikin aurenki
yadda Ubangiji Ya so haka zai yi".
Ta murza yatsu tana dariya, ita ma ce.
"Shikenan. In Allah Ya so ni da kai mutu ka
raba".
Ba ta jira cewarsa ba ta wuce. Ya bi ta da kira,
ta tsaya ba tare da ta juyo ba, ya dan daga
murya.
"Na fa gaya miki kar ki fad'a".
Sai kawai ta kad'a kai ta wuce tana dariya.
.
Allah sarki soyayya... Sai gobe in shaa Allahu.
Dan AuntyGORAN DUMA ****9
Akwai wani lokaci da Alhaji ya sanya shi kai
ta taronsu na masu cikon sankarar jini
(sickle cell) ya jirata har aka tashi taron. A
hanya sun taho yana faman cikarsa da
batsewa, har ya fashe da cewa.
"Inda za ka san ciwon shifcin gizo ne har a
wata 'kungiya, wai dan tsabar lalacewar
zamani ciwon ake wa 'kungiya, kowa ya san
ba ciwon ne ya dame ku ba, wata hanyar
neman kud'i kawai kuka mayar da ciwon!"
Rumaisa'u ta yi murmushi tana kallon tagar
motar kafin da kyar ta samo abin cewa.
"Yaya Yusha'u kamar yin 'kungiyar zai fi
rashinta amfani. Ni dai nan na 'kara min
imani da godiya ga Allah wanda Ya halicce
mu yadda Ya so ba dan 'kiyayya ba, sai dan
Ya zamo jarrabawa a gare mu. Kawai dai ka
yi mana fatan ya zamo kaffara".
Yusha'u ya yi wani gajeran tsaki, sannan ya
tsuke bakinsa.
Shekararta ta 'karshe a B.U.K, Hafsat ta
kammala N.C.E har ta fara aiki, mahaifanta
sun dawo Abuja da zama. A wannan
shekarar ne ta hadu da gwarzon masoyin
da ta ke jin har duniya ta nad'e ba zata yi
irinsa ba.
Ba wai tana rasa masoya ba tuni, sai
soyayyar ba ta wani nisa sabo rashin goyan
bayanta, ko kuma in sun san matsalarta su
kauce.
Sun hadu a wata laraba ne tana tsaye a bus
stop cikin B.U.K ner site tana jiran motar da
zata kai ta old site, ita kadai ce tsaye a
wajen, sai fama ta ke da ri'kon tafkekiyar
lema (umbrella) a hannu saboda hadarin da
ya fara d'aurewa, zai iya zubar da ruwa
bagatatan, saukar ruwa a jikinta kuwa wani
tushen tashin hankali ne da zai iya motsa
ciwonta.
Dai-dai wannan lokacin AUWAL ya zo
giftawa ta gabanta da motarsa.
Ta bi motar da kallo cikin tunanin yadda
suke kwashe da Mominta a hutun da ya
gabata.
Wani Uziri na son tsaida ni, Amman zan yi
'kokarin kammalawa da wuri naci gaba....
Shekararta ta 'karshe a B.U.K, Hafsat ta
kammala N.C.E har ta fara aiki, mahaifanta
sun dawo Abuja da zama. A wannan
shekarar ne ta hadu da gwarzon masoyin
da ta ke jin har duniya ta nad'e ba zata yi
irinsa ba.
Ba wai tana rasa masoya ba tuni, sai
soyayyar ba ta wani nisa sabo rashin goyan
bayanta, ko kuma in sun san matsalarta su
kauce.
Sun hadu a wata laraba ne tana tsaye a bus
stop cikin B.U.K ner site tana jiran motar da
zata kai ta old site, ita kadai ce tsaye a
wajen, sai fama ta ke da ri'kon tafkekiyar
lema (umbrella) a hannu saboda hadarin da
ya fara d'aurewa, zai iya zubar da ruwa
bagatatan, saukar ruwa a jikinta kuwa wani
tushen tashin hankali ne da zai iya motsa
ciwonta.
Dai-dai wannan lokacin AUWAL ya zo
giftawa ta gabanta da motarsa.
Ta bi motar da kallo cikin tunanin yadda
suke kwashe da Mominta a hutun da ya
gabata.
"Rumaisa'u da zaki iya tu'ko a Kano sai na
sai miki mota, saboda yau da gobe, duk
safiyar Allah da yammaci sai na tuno yadda
za ki fita, ko za ki dawo gida. Sai na dinga jin
kamar zan yi tsuntsuwa na zo na dauke ki,
na san wahalar da d'alibai suke sha".
Ta dubi mahaifiyarta cike da so da 'kauna, ta
ce.
"Momi ai kina min addu'a in Allah Ya so ba
zan ta6e ba".
"Duk da haka zan iya siyen motar?"
Ta kad'a kai ta ce.
"In hankalinki zai fi kwanciya ki siya mana..."
Momin ta tareta da fad'in.
"To wacce iri kike so, fad'a min idan kud'ina
ba su kai bai in nemi taimakon Daddynki".
Rumaisa ta yi dariya, ta ce.
"Ta daidai kudinki nake so".
Momi ma ta sake yin dariya ta ce.
"Shikenan, zan ba ki mamaki".
Auwal ya kula da kallon da Rumasa'u ta bi
motarsa da shi ta madubi, kasancewar shi
ma ya sa mata ido, kawai sai ya taka birki,
sannan ya yo baya ya risketa.
Ganin hakan ya sa ta dauke fuskarta zuwa
kallon wani guri daban. Ta ma ajiye lema ta
bude jaka ta ciro golas ta 'kwama.
Auwal da ta 'kara jan hankalinsa, sai ya bude
mota ya fito ya zagayo wajen tana share
fuska. Ya dubeta sama da 'kasa ya ce.
"Mece! Mace akwai waskiya, yadda kika yi
fuskar nan ba dan na ga sanya kika zubo
minido ba, in na kwana dubu ina rantsewa
babu wanda zai yarda idan na ce kin
'kyasa".
Da sauri ta dago ido ta dube shi, sannan ta
dubi motar a ta'kaice, ta ce.
"Ba kai nake kallo ba..."
Ya tareta da sauri.
"Wa kike kallo?"
Ta nuna masa motar tana cewa.
"Ga ta, ai ta fi ka kyau".
Ya dan ja da baya baki bude na alamar shan
mamaki. Ya kalli motar tasa, sannan ya dubi
kansa yana gyara kwalar riga tare da
gilashin idonsa, cikin dariya sosai ya dafa
motarsa ya ce.
"Yanzu wannan ta fini kyau don Allah" dube
ni fa ki gani son kowa 'kin wadda ta rasa, ni
ba dogo ba, ni ba gajere ba, ni ba fari ba, ni
ba ba'ki can ba. Ga ido, ga dogon hanci,
shape d'in ba irin na maza, komai ya ji fa kar
ki bari ki yi asara yarinya. Mota ki kyaleta in
kina raye sai ki ga kin yi wadda ta fi ta... Ni fa
na ma tsaneta daga yau... Dan kishi ne da
ni..."
Yanzu ta daga kai suna duban juna ita da
shi, kai tsaye ba za zummar komai cikin
ranta game da shi ba, sai game da
maganganunsa, kasancewarta mai sanyin
hali tana son mutum mai barkwanci. Ba ta
sami abin cewa ba, ya rigata da fadin.
"Ya ya na ji zaki d'an yi manejin tafiyar da
ni?"
Karon farko ta yi murmushi ta girgiza kai.
"Ka yi ha'kuri a fatar bakina kawai kalmar ta
tsaya, na bi motarka da kallo. Amma zahiri
ba ita din nake nazari ba, wata duniyar
tunanin na tafi daban ka san ana haka ko?"
Ya kada kai yana murmuashi.
"Na sani, amma dai kin ji na ce bana son
kishiya".
Ta sunkuya tana murmushi ta dauki lemarta
ta mi'ke tana fadin.
"Ko dai kishiyi?"
Suka yi dariya su duka.
Ya kar6i lemar hannunta.
"Zo mu tafi kin ga ruwa na shirin sauka, kar
ya daki fuskarki ya yi mata illa".
Ta girgiza kai tana murmushi.
"Na gode kwarai, amma ba na hawa lift.."
Da sauri ya tareta.
"Wa ya fada miki lift za ki hau? Ke da
motarki... Na ramtse zaki iya shafe komai a
duniyata saboda haka ke ce alfarmar tawa
ba ni zan zama alfarmarki ba".
Ta 'kara dubansa da kyau, a sanyaye ta ce.
"Wannnan dokin fa? Daga ganin sarkin fawa
sai miya ta yi..."
Ya sake tare da fadin.
"Wata 'kila ina daga masu afkawa rijiyar so
farad' d'aya. Tun daga nesa fa na hango ki
inuwarki kawai na kalla na ji wata
'kwa'k'kwar zumunta ta sar'kafe zuciyata,
da na 'karaso na kalli fuskarki sai kawai na ji
mun zama JINI DA TSOKA d'aya.
TA Sake dubansa da kyau tana dariya, abin
da ta ke ji a ranta game da shi, shi ne ya iya
dad'in baki, da ba ta dandani shekaru da
yawa a duniya ba, farat d'aya zai wafce
imaninta.
Ta lumshe ido kai tsaye, ta ce.
"Ba na son 6ata maka lokaci ko juyar da
karramammun kalamanka. Ga shi ciki dole
na za6i daya".
Kai tsaye shi ma ya amsa.
"Kin za6i 6ata min lokacin in dai ba kishiya
ne da ni ba, karramammun kalamaina kar ki
wani kalli karamcinsu, yadda ya kamata su
fito a kunnenki, wallahi ban tsara su dan in
burge ki ba, zo mu tafi don Allah".
Bai jira cewarta ba ya bud'e mata 'kofa. Ta
d'an yi jim, sai ta kasa tankwa6ewa ta shiga
motar.....GORAN DUMA
******10
Ya rufe sannan ya zagaya ya shiga yana
mi'ka mata lemarta ya tashi motar. Har suka
zo bakin gate kalma daya ta had'u su.
"Mene ne sunanki?"
Kai tsaye ta amsa masa.
"Rumaisa'u Aliyu Ahmad".
Ya ce, "Sunanki mai dad'i. Ni sunana Auwal
Ibrahim Hadi".
Ba ta tanka ba, shi ma bai kuma tankawa ba
har suka zo bakin gate, wata iska mai 'karfin
gaske ta taso da alamun yanzu ruwa zai
sauka. 'Kirjin Rumasa'u ya fara dukan uku-
uku cikin matsananciyar fargaba. Ta dubi
maza da matan da ke tsaitsaye cikin tashin
hankali. Ta tatabar duk yadda hankali zai
tashi bai fice fargabar za su yi mura ba, ita
kuwa in ruwa ya daketa zai wahala ba ta yi
ciwon da ya kusantarta da ita da kabari ba.
Rage gudun da Auwal ya yi ya sa fargabar ta
'karuwa, saboda zaton sauke zai yi, amma
sai ta ga ya nufi titi zai haura. Ta sauke ajiyar
zuciya, muryarta na sar'kewa ta dube shi ta
ce.
"Da ka taimaka ka dauki matan can, na san
ba za a rasa wad'anda za su yi hanyar da
zaka yi ba. Za ka sami lada idan ka taimake
su".
Ya d'an ja fasali yana duban titi, ba tare da
ya dubeta ba. Ya ce.
"Allah Ya kawo mai taimakonsu, ni ba na
daukar mata a motata".
Ta d'an juma tana dubansa, duba na rashin
fahimta, sannan ta ce.
"Ni ba ka gane nawa jinsin ba ne?"
Ya yi murmushi ba tare da ya dubeta ba.
"`Ka'k'karfar ala'kar da zuciyata ta 'kulla da
ke ya kori wancan 'kudurin nawa daga naki
jinsin. Kin zama 'yar gida a zuciyata da duk
wani abu da na mallaka".
Ta gaji da kallonsa ta kawar da kai, ruwa ya
fara sauka da 'karfi. Cikin sauri ta 6alle
jakarta ta fito da rigar sanyi ta saka tana
'kumbiya-'kumbiya.
Bai tanka mata ba, amma dai hankalinsa na
kanta duk da idonsa na titi, tana bayyana
alamun jin sanyi, amma kawaicinta ya hana
ta 'karasa zuge gilashin 6angarenta, kuma
da hakan yasa ya yi mata aikin da ta kasa
yana cewa.
"Na lura kunama ce ke, kawaicinki kuma na
son hana ki abin da kike so..."
Ta yi 'yar dariya ta amsa.
"Ni da na zo ci rani har ga Allah bai kamata
in za'ke ba".
Ya watsar da wannann batun nata, ya ce.
"Ina zan kai ki?"
Ta yi dira-dira alamar canki-canki, sai ta kasa
za6ar gurin zuwa ta yi shiru kawai sanyi na
kad'ata.
Hankalinta ya yi gida, amma ta ina zata bi ta
je? Ina za ta fake ta sami motar?
Ya juyo ya yi d'an nazarinta, cike da mamaki
ya ce.
"Ina zaki je?"
Muryarta na rawa ta ce.
"Ai na kasa za6a ne. Bana son santi, ruwa in
ya dake ni illa yake min. Da makaranta zan je
amma na fasa saboda sanyi. Yanzu in ka
sauke ni kafin na sami motar ma ruwan ya
yi min abin da ya ga dama".
Ya ci gaba da kallonta cikin nazari, bai
fahimci abin da yake son fahimta ba. Ya
kad'a kkai ya ce.
"Ni ma ba zan iya ajiye ki ruwan ya dake ki
ba. Ina da ganawa 'karfe uku, sai dai a yi
min uzurinta. Ina ne unguwarku?"
Muryarta ta ci gaba da rawa, saboda laifin
da ta ke jin zata yiwa kanta da gidansu. A
ganta saurayi ya auketa kamar zubar da
mutumci ne, amma kamar wannan za6in ya
fi dukan ruwan.
"Na gode Allah ya saka maka da alkhairi, a
Gandun Albasa nake".
Ya ce, "Hanyarmu daya ke nan, ni a Na'ibawa
nake, ziyara na kawowa wani malamina,
shekaru na biyu da barin makarantar na yi
digiri na a nan na fara aiki a 'karkashin
gwamnati. Ya kamata na ajiye iyali Allah bai
kawo ba, sai yau Allah Ya yi min katarin
d'aura d'amba".
Rumaisa'u ta yi d'f! kamar ruwa ya cinyeta.
Tausayin kanta ne ya hanata nazarin amsar
da zata ba shi. Ta ji 'kaunarsa a ranta, sai dai
ta 'ki yarda irin 'kaunar da ta ke d'orewa da
aure ce, 'kauna ce kawai irin wadda d'an
Adam ke wa wanda yake zaton mutumin
kirki ne, ko kuma wanda ya yi maka alkhairi?
Ta yi sororo tana kallonsa kawai yana jin
kallon da ta ke masa a jikinsa, amma ya
had'iye sn ya juya ya kalleta.
Ta juya a hankali ta bi shi da kallo tare da
sauke ajiyar zuciya, ba ta ce komai ba.
"Ba ki da abin cewa akan abin da na fad'a?"
Ta girgiza kai a nutse ta ce.
"Kar ka 6atawa kanka lokaci na san ban
cancanta zama iyali ba".
Ya yi saurin yi mata duban rashin fahimta,
amma ya ta'kaita zar6a6i wajen ce mata.
"Ai ina tsammanin ba a yin komai babu hujja
ko? Ki fada min dalilin zan duba na gani".
Ta muskuta ta ce da shi.
"Don Allah ka yi ha'kuri".
Ya ya yi kasa'ke yana kallonta, sannan ya ce.
"In dai ba laifi zan wa Allah ba, to ba zan iya
hakura ba..
Ta tare shi ta fadin.
"Ina fatan nan gaba ba zaka zarge ni da
rufa-rufa ko yaudara ba?"
Ya 'ki daukar maganarta da muhimmanci. Ba
tare da nuna damuwa ba ya ce.
"Ina saka rai Alkhairi ya biyo baya, idan
kuma akasinsa ya samu zan dogara ga Allah,
amma ki sani akwai laifinki ciki Allah ne ba
za barki ba, musamman da yake a rufe kike
ba ni uzirinki".
Ta yi shiru kawai shi kuma ya share wannan
maganar ya shiga tambayarta karatu da
wasu abubuwa da yake jin suna da
muhimmanci a cikin ala'kar da yake son
'kullawa da ita.
Cikin ikon Allah sun wuce Gadon Kaya babu
ruwan babu iska, ko hadarin ma babu,
saboda haka ta ji ranya ta afu da son ta
sauka ta hau motar haya ta 'karasa, amma ta
kasa yi masa magana har sai da aka kira shi
a waya ana nemanta wajen taro ya bayar da
uzirinsa, yana sauke wayar ta ce.
"Kawai ka sauke ni a nan na shiga mota na
'karasa, sai ka wuce sabgoginka".
"Da yake tun farko na ke kika 'kirkirar min
sabgogin ba, kar ki yi mamakin in na 'ki bin
umarninki".
Dole ta yi dariya ta share zancen.
Ya tsayar da motar a harabar gidansu yana
d'an zuba mata ido saboda yadda ya ga
kamar ta kad'u da ganin wani da ya tsaya da
motarsa kusan lokaci daya da su.
Da sauri ya kalli motar dan ganin tana rawar
jikin ficewa. Ta juyo ta dube shi da duban
rashin fahimta. Ya nuna Yusha'u yana fadin.
"Wane ne wancan?"
Ta dubi Yusha'u sannan ta dube shi, a
takaice ta ce.
"Yayana ne".
Ya yi zuru yana kallon Yusha'u, haka kawai
ya ji hankalinsa bai kwanta da shi ba. Ya
kad'a kai bisa dole ya bude 'kofar suka fita
lokaci guda. Da sauri ya nufi Yusha'u da ke
'kokarin rufe mota ya yi masa sallama tare
da mi'ka masa hannu. A wula'kance Yusha'u
ya amsa idonsa na kan Rumaisa'u, sannan
ya ce.
"Yaya kuke da wannan?"
Auwal ya yi zuru yana kallon Yusha'u da
Rumasa'u yadda Yusha'u ya yi mata magana
fuskarsa babu walwala ne ya ba wa Auwal
damar nutsuwa ya karance shi.
Akwai alamar nutsuwa a tsaiwar Rumasa'u,
sai dai a rikice ta d'ebo masa amsa.
"Dan ajinmu ne... Ya taimake ni ne saboda
ruwan da ya tare ni.. Hanyarsa ke nan shi
yasa ban nemi sauka ba da muka wuce inda
ake ruwan.
A gadarance Yusha'u ya ce.
"Kina fad'a min hanyarsa ce dan kin shirya
kullum ya dauko ki yana kawo ki ko? Ban
san iyakar tsawon lokacin da zan dinga
fad'a miki nan Arewa ba kamar can Kudu ba
ne. Babbar 'kazanta ce mu a nan mace ta
dauki namiji aboki..."GORAN DUMA
*****11
Ganin yana neman tsinkata ta tare shi.
"Lalura ce yaya Yusha'u, na yi gudun dukan
ruwa ne".
Yusha'u ya yi tsaki tare da yin gaba yana
cewa.
"Duk illar da dukan ruwan yake da shi, ai bai
kai na sarayar da mutumci ba, koda yake
wayewarku ta halatta muku haramci".
Rumaisa'u ta yi suguri ranta ya yi mugun
6aci. Ta san Yusha'u bai iya magana ba sam!
Haka yake yinta kamar kashi, amma a yau ta
fara shakkar dan ta zo cin arzi'ki gidansu ne.
A sanyaye ta dubi Auwal da ya yi shiru
rungume da hannu yana kallon 'kasa, ta ce.
"Na fa gode zan shiga ciki".
Ya dago da alamun tunani ya dubeta.
"Me yasa kika 'ki fad'a masa gaskiyar
matsayin da na za6a mana? Sai kika
ala'kanta mu da jabun dangantaka?"
Ta dan ja numfashi, sannan ta amsa.
"Har yanzu kai kake kid'a da rawarka. Da
zaka bi ta tawa za mu yi sallama ne mu rabu
har abada. Karatu ya kawo ni garin nan, ya
kamata na ji da shi shi kad'ai... Mts! Ni bana
son hargitse-hargitse wallahi".
Ya fahimci cikin 6acin rai ta ke, saboda haka
sai da ya shirya kalaman da zai mata.
"Kina da wanda kika tsayar?
Ta girgiza kai, fuskarta a daure. Ya numfasa
ya ce.
"Idan haka ne na tabbatar kin zo KANO ne
dan mu had'u mu auri juna ba tare da na yi
gi6i a karatunki ba, ki daina gaggawar
yanke hukunci akan lamarin rayuwa. Da
hakan gara ki zama mai dabarar tsara
al'amuranki, ina neman alfarmar kar ki kore
ni, kuma ban matsa miki ki so ni ba, amma
ki ba ni dama mu fahimci ko zamu iya tafiya
tare".
Yanzu idonta cike yake da 'kwalla saboda
takaicin kalaman Yusha'u, gidansu kawai ta
ke tunowa da yadda ta ke da kima da
mutumci a cikinsa.
Auwal na ganin kwallarta ya dan shiga
damuwa, amma a nutse ya tausasa murya ya
ce mata.
"Idan akwai matsala dan Allah ki fad'a mi
kuka na nufin damuwa. A kalamaina ban ga
abin da na fad'a da zai 6ata rai ba".
Ta 'kir'kiro murmushin 'karfin hali dole ta ce
masa.
"Babu komai, Allah Ya yi mana jagora".
Tun daga wannan ranar Auwal ya zame
mata wani 6arin rayuwa, ya 'kware da
samar da muhallan farin ciki a zuciyarta da
kirkinsa da kuma yadda yake kula da ita da
damuwa a cikin abin da ya dameta.
Tun daga wannan ranar Auwal ya zame
mata wani 6arin rayuwa, ya 'kware da
samar da mujallan farin ciki a zuciyarta da
kirkinsa da kuma yadda yake kula da ita da
damuwa a cikin abin da ya dameta.
Kullum sai ya zo gidansu, tare da cewa yana
6ata mata da yawan lokutai a waya, haka
kuma takanas yake binta makaranta ya
daukota, babban zunubinsu da ya tsayawa
Yusha'u a rai ke nan saboda imanin da ya yi
na cewa, duk yarinyar da ta je jami'a sai ta
lalace. Ya rasa yadda zai fahimtar da Hajiya
da Alhaji a matsayinsu na wadanda kamar
su ke waliyantar da Rumasa'u saboda kyan
hali.
Rumaisa'u ta fara nisa cikin abin da ba ta
za6a tsarabarsa a rayuwarta ba, wato SO,
tana ji a ranta ita nakasashiya ce duk yadda
so zai zama in ta amince masa wata rrana
zai zame mata mad'aciya, amma a yanzu
Auwal ya ture wannan tsarin a ranta, sai ya
barta da zulumin