Author : Maimuna Idris Beli Category : Action Novels
shi dai bai kamata yaci ba,
hapsat ma bata son tsawaita wannan maganar akan layi
dan ta san makoma abin. Saboda haka tayi saurin tare
Rumaisau da cewa anya kuwa ba Yusha'u bane?
sai kawai Rumaisau tayi zuru tana kallon haprsat kamar
wadda hankalinta baya jikinta tace ko a tatsunia bai
kamata kiyi zaton yaya Yushau ba, me ya ani da yaya
Yushau zai bata lokacinsa a kaina?
Ko kin manta ne ?
Ai ko a layin mutane nake zaton mai turo min sako bai
kamata ki kawo yaya yshau ba.
Hapasar ta rausaya kai cikin sallamawa tace haka ne wai
dama da ake zargin mai wayar a cikin dangi..
A dan kupule Rumaisau tace ko mun rage mu biyu daga
ni sai shi ya kamata in pita waje neman mai turo min
sako.
Hapsat tayi shiru saboda rashin abun cewa,
kamar amsa ga abin da sukayiwa tagumi suna tantama
sai ga taken shigowar sakon mahaukacin masoyi..
Rumaisau na dubawa ta gashi ne, sai ta mikawa hapsat
wayar ba tare data karanta ba. Ta mike da hannu dunkule
tana dukan hannun hagu tare da pareti a palon.
''Rumaisau akace mutun mutun gida ne da rabin mutun
da wanda ba komai ba, wanda yake mutun shine mai yin
shawara da al'amuransa, kuma mai ra ayin madaidaici
wanda yake rabin mutun shine mai shawara amma bashi
da madaidaicin raayi ko kuma yana da madaidaicin raayi
amma ba shawara, wanda yake ba komai ba shine mara
shawara, kuma mara raayi.
Wani babban sahabi yace mana ''kuyi shawara da
mutanen kirki na gama yi miki sanin raayi madaidaici
wato tuni na san cikar rabautarki ashe ke guda ce naji a
raina kina son kiyi shawara akan harkar soyayyata haka
ne?
Ina sauraron abunda hukunci zai yanke min,
mahaukacin masoyi.
A pili Hapsat ta karanto sakon, zuciyarta na harbawa ,
hannunta sai karkarwa yake ...
.
GORAN DUMA 4.
.
.
a pili Hafasar ta karanto sakon zuciyarta na harbawa,
hannunta sai karkarwa yake idon ta cikin na Rumaisau
bakin ta na rawa tace da wa kikayi zancen zaki zo neman
shawara a gurina?
Babu tsoro a puskar Rumaisau ta kebe baki tace da
harshena dai ban pitar da sautin zan nemi shawarar wani
ba dazun nan a freedom na zanta da zucia ta ina pitowa
kuma kai tsaye na nupo gidan ki.
Mun shiga uku, hapsat ta pada tare da wurgar da wayar a
dan tsorace cikin jikinta yasa da sauri Rumaisau ta isa
gareta ta ruko kapadarta tana daria matsalata dake tsoro
Wallahi, baki san babu abin da zai iya samun dan Adam
ba sai abin da Ubangiji Ya kaddaro maka ba?
Bana tsammanin wani katon Al'amari cikin sakonnin
mahaukacin masoyi, kawai dai na gajia da bacin lokataina
da tunanina ne wajen wassapa shi yada sakonninsa.
Hapsat tayi kasake sai nan take ta dawo hakalinta ta mika
hannu ta dauki wayar ta sake duba lambar, nan take ta
dannan maballin kira, ta gama bincike dab da zata shiga
sai ta katse, kusan sau goma tana gwadawa hakan na
paruwa a karshe ta kwape lambar a wayarta ta jira nan
ma hakance ta paru suka dubi juna kowacce puskarta da
jarumta tace ina horonmu da addua da mayar da lamari
ga Allah Rumaisau karmu raya wani mugun abu a cikin
sakonnin nan mu kwantar da hankali mu kuma dauke su
ba komai ba ki bani kwanaki biyu nayi wani dan bincike
idan kin amince zan sanar da sani.
Rumaisau tayi saurin girgiza kai ban amince sani yaji ba
kin san sanida surutu maganar tana iya zuwa kunnen su
hajia ba tare da mun shirya mata ba,
cikin saduda hapsat tace hakane amma dai surutun sani
mai maana ce ki daina suppanta shi da wani aku...
Ta kare da zolaya duk kuma suka yi daria suna pitowa
harabar gidan suka ci karo da sani mai gai ya wangale
masa kopa ya shigo.
Suka tsaya jikin motar da Rumaisau tazo da ita suna jiran
karasowar sani . rumaisau ta rungume hannu a kirji tayi
puska ma'ana ta shiryawa shegantakar da sani mijin
hapsat zai zo yayi mata, tunda ya saba,
lallai kuwa idon masu hidima da ke karakaimar yi masa
maraba da xuwa bai tsure shi ya kasa girgije su ya nupi su
kai tsaye ba.
Hapsat na dan boye puska tana satar daria tayi masa
sannu da zuwa hankalinsa na kan rumaisau yana mata
kallon sama da kasa a karshe yace a'a yau mutanen
zuhdu ne suka tuno da mu?
Ta tuno da ita dai Allah Ya sani ba dan kai nazo ba.
Ta tare shi tana nuna masa hanyar wucewa ya tuntsire da
daria yace matsalata dake kenan sai ki dinga dagewa sai
kinyi pada kuma da yake ba dabiarki bane sai ba yayi miki
kyau har tapia ke nan.
Bazaki zauna mu gaisa ba gashi naga puskarki da abin
karatu...
Wannan kalaman nasa suka sata daria kawai ta bude
kopar mota ta shige suna dan barkwanci har ta pice...
Ta tattara duk wata sabga da zata iya dugunzuma mata
hankali a ratuwarta ta watsar, in sako ya shigo wayarta ta
daina budo shi inta hau fb ta share inboz sai komai nata
ya dawo dadai.
Sati daya a tsakani sai mahaukacin masoyi ya dawo
kwado mata kira a waya da parko share kiran ta dingayi
amma daga bisani sai ta yanke shawarar ta daga wayar
suyi ta ta kare ita da mai kiran, amma idan ta daga sai
iska shuuuu...
Babu motsin murya sunyi haka ya zarce sau goma a
karshe kawai sai tayi blockin din layin sa gaba daya a
wayoyin ta ba tare da jin cewa zata yi nadama ko kaico
ba.
Sati na biyu akayi rasuwa a kauyen su Rogo hajia nada
ganawa da liyitanta a Egypt daidai wannan lokacin bisa
larurar ciwon sugar da take pama dashi, alh kuma tare
dasu tapi saboda haka ta wakilta Rumaisau taje gaisuwar.
16/02/2013
tana zaune cikin yan uwa a gidan gaisuwar har bayan
sallar azahar sannan ta tapi gidan Goggonta karpe uku
take jira ta karasa ta dauko hanyar dawowa gida saboda
haka ta kimtsa komai tana zaune kawai.
Goggonta ta shigo tana mata wani irin kallo sannan tace
Yushau bai san ke hajia ta turo ba sai yanzun nan nake
pada masa.
Rumaisau ta daidaita maganae goggo a memory dinta
amma ta rasa gane ta inda maganar ko wani abu a cikin
ta zai ampaneta, saboda haka ta hadiye a sanyaye tace
ashe yazo?
Goggon ta amsa mata eh tun sape yana nan ai ina
tsammamin ma ya riga ki zuwa.
A dai ci gana da hakuri Ubangiji Yana son bayinSa masu
hakuri, rayuwar dai kina ganin yadda take hutsirewa kana
tsaka da kara mata burika, wadanda kake kokaawar
imma a sannu ko wadanda kake son sawa karpi rauwar
Garbati nan ta isa mutun aya Ruma, shekaru goma sha
shidda bai leko gidan ba yana can kudu da kyar akayi
masa kiranye ya dawo gida anata parin ciki da murna har
anyi masa matar aure kinga duka duka bai hada sati 2 da
dawowarba Allah Ya karbi abinSa , ai wannan gudun
dunia wajibi ga mai son cikawa da imani
rumaisau jinta kawai take ta san waazi take mata abin da
take waazi a kansa ma ta kasa tantancewa musamman da
yake akwai batun yushau da aka yi shimpidar waazin a
kasan ta kasa gane me goggo take son nusassheta akan
hakuri da yushau, wanne tawaye take da bukatar ta yi
hakri akan sa?
Amma dai da yake baya da jayayya sai ta rausaya kai tace
Allah Ya samu cika da imani.
Goggo na amsawa hakan yayi dadai da shigowar Yushau
cikin daikin puskar Rumaisau babu yabo ko pallasa ta
taishe shi sannan ta mayar da hankali akan wayarta, tana
dube dube goggo ta sa musu ido a pakaice yushau na
satar kallon rumaisau yace nansan bada mota kika zo ba
ko?
Ta dago sarato tana kallon sa amma yanayin puskar
hakurinta ta hana a gane yadda ta karbi batun muryarta
na rawa tace hakane motar haya na hawo.
Yadanyi dariar da yake tunanin zata sami matsuginni a
zuciyarta yace aina sanki da tsoron tukin daguwar hanya.
Ta share daria da batun nasa hanyar muyar da hankali a
wayar ta tana nazarin sakonnin makaranta rubutun ta a
jaridar Aminiya,
karpe nawa zaki tapi?
Ya pada kamar bai damu da yadda ta share shi ba ta dago
agogon hannunta ta duba ba tare da ta bude shi ba tace
ina jiran karpe uku ta karasa ne sai na komai shima ya
duba agogon yana padin nima ita nake jira sai mu koma
tare ta danyi kasake bukatar tasa na mata kururuwa a
kwakwalwa sai pamar kwakwalwar cetayi aikin da
zuciayar nata ta kasa, wato ta girgiza kai tace nayi
alkawari da dan mashin zai zo ya kaini tasha,
kai tsaye ya amsa mata sai na biki na dauke ki.
Bai jira cwarta ba ya pice abinsa. Sararo ta hada binsa da
kallo da sauraron wayarta mai take shigowar sakon
murya, sai da ya pice ta sauke idon akan wayarta cike da
rudani da mamaki shakarunta nawa da yankewar samun
sakon murya a waya.? A lokacin da take samun sakon
wayar ma daga wani muhimmin mutun ne a duniyarta.
Wasa! Tana budewa sai ga lambar mahaukacin masoyi
kawia sai ta mike ba tare data shawarci kanta ba , goggo
ta dan bita da kallo ita kuma ta tsawaita muryarta tace
goggo yau na manta banje hawa dutse ba, mintina
ashirin bari naje na dawo.
Goggo da yake ta san rumaisau da maganar son hawa
dutse bata zargi komai a ranta bam ta santa duk sanda
tazo ta kan ware lokaci ta shiga daji ta hau dutde shi yasa
yanzu ta amsa mata da cewa ai da yake ba zuwan
nustuwa yau kikayi ba kiyi sauri to ki dawo kije gidan
gausuwar kizo ku tapi kar ya gaji da tsumayinki ya tapi.
Ga yamma ga wahalar mota kinga babu dadi.
Rumaisau na kokarin picewa tace idan ya gaji da tsumayi
kawai yayi tapiyarsa dama ina da ajandar kwana idan hali
yayi.
Goggo bata samu amsa mata ba ta kule.
Ba zata iya tantance yadda akayi ba ta isa wajen dutsen
ba, ta sulale a sanyaye ta haye samansa sannan kamar
yadda ta saba ta siga juyawa a hankali tana hango
karshen gari (harizone )
wannan aladar muhimmiyar gaske ce a rayuwarta dan ta
kan kara mata imani da tsoron Allah wanda Ya halincci
wannan makekiyar duniyar da take zagayawa a cikin ta,
duk kuma da girman nan nata sai ta zama bata isa abin
iya kallo ba cikin abin da Ubangiji ya halitta amma sai ya
kebance ita kankanuwar duniyar d niimomi masu tarin
yawa, Ya karrama dan Adam a cikin ta sannan Ya bashi
zabin makomarsa a hannun sa, a cikin ta aljanna ko wuta,
wanda yabi Allah cikin ta yayi kunci a gare shi to
muminancinsa ya bayya na, wanna ya ki yarda da
AllantakarSa ko ya zama pandararren bawa to tayi masa
yalwa rabonsa kenan.
A yanzu hawaye ne ke diga a puskarta ba kuma wannan
karatun kadai ya sanyata hawaye ba har da tuna yadda
duniyar nan ta shude mata da mutun muhimmi a cikin
ta, kamar yadda ta tabbatar ita ma wata raba zata shude.
Rauninta kuma ke raya mata ba zata taba samun wanda
zai maye mata gurbinsa ba, wannan tunanin ne ya pado
mata da na sakon mahaukacin masoyi, a rikice ta zauna
dandamalin dutse ta dauko wayarta a jaka cike da doki
hannunta na karkarwa ta danna muryar...
Rumaisau kin taba nazari akan zucia?
Harumin gaske ne ke rike akalarta ya ja sabanin ta jashi,
tawa zuciyar kamar ni take ja. Ma'ana ban cika jaurimi
amma na kasa yarda ni rago ne dan na rike hujjar
zuciyata na ja ne ga alkhairi ne wato ke.
Zuciyar tawa na da karpin hali ko?
Bana ganin bakinta ni kuma dan ta gamsu kin hada
dukkan alkhairan da idan anyi paputuka a kanki ba a
sarayar da lokutar a wopi ba, dan ma duniar nada abun
tsoro ko?
Gangancin shigar haske cikin duhu da shigar duhu cikin
haske ya isa kada zuciyar mai imanin mutuwa wadda
bata bukatar imani cikin sharudanta, ga wanda ya yarda
da ita da wanda bai ma yarda da ita bam duk ba wanda
take ragewa
duk sanda na yi tsaye cikin lambu ina kallon sararin
samania sai na cika da shakkar anya kuwa ozone layer da
akce yana kekkecewa ne yake kara gudun dunia ba
waccan mutuwar ke kusatoni ba?
Duk sanda na tuna haka sai nayi kwalla ina ganin kamar
zanyi mutuwar da babu gata, wato wadda na ke so bata
yarda ina son ta ba.
Mukwana lapia.
Bata gama tantance matsayin da zuciyarta da azancin ta
suka karbi sakon mahaukacin masoyi na yanzu ba ta
hanga yushau ya nupo ta kai tsaye yana ta sauri kamar
mai shirin tashi sama..
Ambaton MUTUWA wadda take da kishiyar rayuwa
asakon mahaukacin masoyi ya sata kallon Yushau na
tahowa garau!
Saboda tunaninta da yake son tino rayuwar ta ta baya.
Yau da gobe a rayuwarta.
Mutuwa a cikin rayuwarta.
Kaddarori marasa dadi na rayuwarta.
ASALIN RUMAISA'U.
Mahaipin ta...
.
in shaa Allahu gobe zamu ci gaba daga inda muka tsaya..
.
Dan AuntyGORAN DUMA 5
.
.
ASALIN RUMAISAU
Mahaipinta Aliyu Ahmad dan karamar hukumar Rogo ne
a kano. Mahaipiyarta Khadija inyamura ce mutumiyar
Enugu wadda ta musulunta a hannun mahaipinta sukayi
aure da zama a garuruwa daban-daban kasancewarsa
dan sanda.
Mahaipinta dan dangi ne sosai a kauyen Rogo da cikin
garin Kano duk da cewa su biyu ne kacal a gurin nasu
mahaipan wato shi da kuma yayansa Usman mahaipi ga
Yusha'u da kannensa mata hudu sai Mubarak auta,
mahaipinta da mahaipiyar ta akwai zama na soyayya da
pahimtar juna mai kwari a tsakanin su, Allah bai wadata
su da iyali masu yawa ba daga yayarta Balaraba (Aisha)
sai ita auta har a halin yanzu wajen uwa da uba.
Bayan rauni na kasanxewarta a jinsin mata masu rauni
sai wata jarrabar Ubangiji Yayi mata na kasancewarta
daga masu pama da larurar nan ta sankarar jini (sickle
cell ) cutar da gatan da iyayenta ke nuna mata bai hanata
tasowa cikin wata irin mawuyaciyar rayuwa ba , alal
alakka sun karbi kaddarar haihuwarta da Ubangiji Ya
nupe su dayi suna godia a gare Shi tare da rashin gazawa
ko kosawa cikin tarin dawainiya gare ta yadda ya kamata,
duk wani sikila ya samu.
Iyayenta naji da ita suna tausaya mata suna tattalinta
ninkin yadda suke tattalin yayarta Balaraba sun jure duk
wani alayi na ciwonta, kai karewa saboda ita innarta ta
koma karatu bangaren lapia bayan tayi digirinta na parko
akan Na'uwa mai kwakwalwa (computer engr.) kapin
aure, bayan sun haipeta da shekara daya ta karkade
zaninta ta koma makaranta inda ta karanto wanda ya
kara taimaka mahaipiyar kwarai wajen yadda take kula
da rayuwar ta.
Tayi karatu a tape kuma cikin gata kamar yadda ya
kamata har matsayin kammala babbar sakandire ta pito
da sakamako mai kyau, saboda haka ta sa ran shiga
Jami'ar Bayero ta kano dan karanta aikin jarida.
A daidai wannan lokacin mahaipanta zaune a enugu
saboda haka ta debo zaman karatunta ba dan son ran
iyayen ba ta dawo wajen yayan mahaipin nata Alh Usman
wanda ke zaune a kano kuma shahararren dan kasuwa a
kasuwan kantin kwari.
Daidai wannan lokacin Balaraba yayarta ta auri Mukhtar
ma'aikaci a garin Abuja , shima Alh Usman Ya aurar da
yayansa mata uku, Atika, asiya, maimuna sai Hapsat kadai
wadda take tsararta sannan Mubarak sai ko babban
yayan su Yusha'u da ya tasamma zama tuzuru babu aure.
Yushau ba a gaban iyayensa ya girma ba tun daga yaye
kakarsu ke rike dashi a Rogo har bayan rasuwarta ma sai
yaci gaba da zama inda yapi wayo , can yayi firamare da
sakandire yazo gidan su kano yayi NCE a FCE kano bayan
kammalawan sa saboda sabo da rogo sai ya kuma
komawa can ya kama aikin koyarwa amma idon kudi da
ya gani lokacin zaman karatunsa a kano yake zuwa
kasuwa gun mahaipin sai ya hana shi mayar da hankali ga
koyarwar inda bai hada shakaru biyu cikinta ba ya ajiye
ya dawo kano yaci gaba da harkokin kasuwanci.
Duk sauran kannensa ma sunyi karatu daidai gwargwado
na iyakar sakandire suka yi aure, Asiya da Atika da suka
auri yan boko sun sami damar ci gaba har sun para aiki,
amma Maimuna na zaune a gida da kasuwancinta,
albarkacin Rumaisau yabawa hapsat damar dorawa daga
sakandiri bayan nacin ta sami B.U.K ta gaza sai ta bige da
sa'adatu Rimi collage.
Hankali da nutsuwar Rumaisau tare da rashin kuzarinta
wani abu ne da sam baya dada yushau da kasa, yana
mata kallon wata muguwar shagwababbiya kuma mai
shegen raki, wadda yake ganin ba a kanta aka para ciwo
ba amma akwai alamar tapi kowa kururuta shi, kullun ita
ke nan cikin ciwo da neman uzuri ayadda ta baro gidan
su suke kirkirar mata shagwaba da mayar da kai baya
haka anan gidan nasu babu wanda ta rage, alh da Hajia ,
hapsat da Mubarak kuma suka pi kowa taya bera bari a
wajen su komai na Rumaisau na musamman ne kai
saboda Rumaisau sun hakura da yawa daga jin dadin
rayuwar su,
saboda Rumaisau Alhi ya cire duk wani A.C a cikin gidan,
panka idan Rumaisau na guri cikin su hudun nan babu
mai shan iskarta, in kuwa shi ya guntse ido zai kunna duk
zasu taso kansa da korapi.
Duk wani aikin gida na mata babu ruwan Rumaisau da shi
ko ta sa kanta zatai hajia kan hana, abincinta na
musamman ruwan wankanta na musammam, duk inda
zata pita kuma sai anyi dawainiyar da ba zata yi tapiar
kasa ba,
ba ta da aikin da ya wuce taci ta sha ta pita yawon
makaranta, anjima kuma ta ishe su da rakin ciwo.
Ba wannan ne kadai abin da ke damun Yushau akan
rumaisau ba, har da matsayin karatunta wanda sam baya
kaunar wata mace ta taka matsayinsa, in kuma har ta
taka din to yana mata kallon wata gagara kundila a duk
wani nau'in halin tsiya.
Wadannan dalilan ne suka hana shi iya boye kin da yake
wa rumaisau wanda ya hada da hapsat saboda tattalinta
ga rumaisau da kuma kama turbar rumaisau na zurpapa
ilimin boko.
Hakurin Rumaisau da zaton alkhairinta yasa bata taba
hasashen yushau ya tsaneta ba, pahimtar da tayi masa
kawai shine shi daban ne a cikin gidan mai wani
murdadden hali da kake kasa passarawa, yana da pushi
yana kuma da halin sauye-sauye, saboda haka ta koyi
zama dashi, bata cika nuna shigarta wani hali a gaban sa
ba dan gudun yaki bata muhummanci taji haushi, bata
daguwar hira dashi , bata neman taimakonsa ko wanne
iri, kuma idan hajia ko Alh sunyi masa umurnin kaita
makaranta ko asibiti yana paman kumburi ta kan bashi
hakuri tare da karawa kanta nustuwa dan kai yaga
giggiwarta, amma duk da haka bata tsira ba,
akwai wani lokaci da Alh ya sanya shi kai ta taronsu na
masu ciwon sikila ya jirata har aka tashi taron, a hanya
sun taho yana paman cika da batsewa har ya pashe da
cewa '' inda zaka san ciwon nan shipcin gizo ne har da
wata kungiyam wai dan tsabar lalacewar zamani ciwon
ake wa kungida ko ya san ba ciwon ne ya dame ku ba
wata hanyar neman kudi kawai kuka mayar da ciwon.
Rumaisau tayi murmushi tana kallon tagar motar kapin
da kyar ta samo abin cewa '' yaya yushau kamar yin
kungiyar zai pi rashin ta ampani, ni dai tana kara min
imani da godia ga Allah wanda ya halicce mu yadda Ya so
ba dan kiyayya ba, sai dan Ya zamo jarrabawa a gare mu
kawai dai kayi mana patan ya zama mana kappara.
Yushau yayi wani tsaki sannan ya tsule bakin sa.
Shekararta ta karshe a BUK hapsat ta kammala NCE har ta
para aiki, mahaipanta sun dawo Abuja da zama a wannan
shekarar ne ta hadu da gwarzon masoyin da take jin har
dunia ta nade baza tayi irin sa ba.
Ba wai tana rasa masoya ba ne, sai soyayyar bata wani
nisa saboda rashin goyon bayanta, ko kuma in sun san
matsalarta su kauce.
Sun hadu a wata laraba ne tana tsaye a bus stop