Advertisements
Chapter 15 Reading Goran Duma by Maimuna Idris Beli BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Goran Duma by Maimuna Idris Beli

Author :  Maimuna Idris Beli Category :  Action Novels

Chapter   15 / 28

42K to 45K   out of 82.5K words

a yanzu rashin dabara ne ya
jagula mata rai, sai ya daure kamar wani soko
ya ce. "Shikenan sai ki duba sauran".
Ta mayar da maganin 'karin jini cikin ledar, tana cewa.
"Ka yi hakuri Yaya Yusha'u, babu maganin da zan iya sha
a ciki, in na sha na jefa rayuwata cikin hatsari".
Yanzu Yusha'u ya kasa hadiye 6acin ransa, dan har ga
Allah yana ganin Rumasa'u amfani ta ke da zurfin iliminta
tana nuna masa iyakarsa, komai ya yi bai iya ba dan
tsabar rainin hankali ita da ta karanci
jarida wai ita ce zata kushe wanda ya karanci lafiya.
Ta kushe wannan ta kushe wancan komai cikin gadara
kamar wata uwar mutane.
Ya yi kokari ya rage zafin 6acin ransa a muryarsa, ya ce
mata.
"Amma dai idan kin yi min haka ba ki yi min adalci ba,
kawai dan ki nunawa duniya kina iko dani,
kina kallo in kawo mutumin duk ba ki musa ba sai bayan
tafiyarsa ki ce ba kya son aikin in mayar masa da
magungunansa?
Wannan ai ya yi kama da wulakanci..."
Ta katse shi a sanyaye.
"Yaya Yusha'u idan na katse hanzarinka a gabansa shi ne
wulakanci, gara in bari ya tafi muyi komai mu biyu... wai
ma don Allah Yaya Yusha'u har sau nawa zan fada maka
ba na shan magani kai tsaye?
Tsawon zama a gidanku ka ta6a ganina a kyamis...?"
Shi ma ya tare da tsawa.
"Ban sani ba! Ni dai kin wulakanta ni, abin da nake ta
gudu ke nan, duk mai zurfin karatu ta 'kalubalanci
mijinta, ta yi jayayya da shi, ko ta raina masa azanci
sunnarta ce, kamar ni ma ban ta6a allin nan ba.... Haba!
Ban da kaddara me zai kai ni?
Ba gara ma mutum ya tafi kauye ya auro ba".
In dai da sabo ya kamata Rumaisa'u ta saba da wannan
gori da cin fuskar, duk kuma 6igiren son
zuciya da rashin gaskiya.
Tun kafin abin ya yi tsawo ai ta mi'ke ta bar masa falon ba
tare da ta ce ci-kanka ba, ta shiga bandaki
ta wanke baki, sannan ta bi lafiyar gado tana addu'ar
Allah Ya sa ma ya yi zuciya ya tafi dakinsa ta huta.
Sai dai addu'ar tata ba ta kar6u ba, dan ko mintuna
ashirin ba ta yi da kwanciya ba ya shigo ya sauya
kayan kwanciya, ya zauna bakin gado ya ce mata.
"Yanzu ya ya kike so a yi?"
Ta dan zura masa ido sannan ta ce.
"Da me?"
Ya ce, "Da maganar 'karancin jinin bana son a kai ga
maganar sai an 'kara miki jini".
Ta yi murmushin gajiya da abu daya, ta ce.
"Idan ba zan yi laifi ba kuma ba zai zama umarni na ba ka
ba, asibiti ya kamata na je gobe".
Ya janye mata abin rufa ya fara murza tafin kafarta yana
cewa.
"To ya ya zan yi?
Ai kawai na zama mijin ta ce sam-sam ba na yi miki
kwarjini. In Allah Ya kaimu gobe sai mu je asibitin."
Ta janye kafarta tana 'karamar dariya.
"Allah Ya kai mu goben. Yanzu sai ka tashi ka tafi
dakinka..."
Ya tare ta lokacin da ya fara nade su cikin bargon.
"Haba yarinya kin ma isa, ai rashin kwanjin nawa bai kai
nan ba".
Da sapiyar ranar sai ya nemi hanzarin cewa na manta yau
akwai ni da zuwa rogo, satin da ya wuce Alh yayi min
maganar kaddamar da wata rijiya da yake a waya ne bai
min cikakken bayani ba, sai naje naji, ki bari idan na
dawo da yamma sai muje asibitin,
ta kada kai da sauri cikin bugun zuciya , rijiyar Awwal ce
ta kuma tabbatar idan Yushau ya jiyo gaskiyar maganar
Allah ne kadai ya san yadda zai tashi hankalinsu.
Saboda haka ta wuni cikin zullumi da tashin hankali gami
da pargaba,
lallai kuwa' yushau ya shigo gida karpe goma na dare
puskar nan tasa kamar an saukar masa sakon mutuwa ko
hutawa baiyi ba ya para surparta da bala'i irin wanda bai
taba yi mata kamar sa ba, tun tana kokarin kare kanta har
ta zubo masa ido tana kallo cike da tsabar bakin ciki a
tsukun wannan lokacin da za a kawo mata tayin mutuwa
babu abin da zai hana ta amsa,
sai sha daya da kusan rabi ya hakura ya tapi dakin sa yana
ta mita, wai don me tana auren sa tana auren soyayyar
wani har da irin wadannan sadaukarwar da ya rantse
kuma ko kwatar abin da tayiwa Awwal shi bazata iya yi
masa ba,
lokacin da yake bala'in idon Rumaisau a kekeshe yake
babu alamun kuka saboda masipar bacin rai, sai bayan
pitarsa ta samu kukan ya goce mata,
ta dinga yi babu kakkautawa dan ta hakkake duk rashinsa
ya jepata cikin wadannan masipun auren Yushau ke wa
sila. Da akwai Awwal kila da yanzu tana daga cikin matan
da za a lissapa su a sahun parko na jin dadi da sa'ar miji,
amma yanzu ratuwarta da lapiyarta na wani hali na tsaka
mai wuya,
wajen karpe biyun dare ta nupi dakin kwana saboda jin
numpashinta na shakewa, da zummar tilasta kanta bacci
dan ta manta wadannan bacin ran ko dan kai lapiyarta ta
sami nakasu.
Sai dai da alama ta makara dan numpashinta yaci gaba
da shakewa lokaci daya kuma cikinta yayi wani irin
juyawa tape da ciwo sai ga damshi-damshi ta sami kanta
a ciki,
nan da nan ta para ambaton Innalillahi wa inna ilaihi raji-
un . Ta san lallai tana cikin tsaka mai wiya, bari zatayi, zata
bubar da jini alhali dama bai ishe ta ba,
ta barke da kuka ta isa bandaki kamar dama ana jiran ta
shiga bandalin ne jini ya balle , tun tana tararradin rasa
gudan jininta (wato danta) har ta dawo pargabar tsira da
ran ta,
saboda yadda xiwon ciki ya addabe ta ,jini kuma yaki
tsayawa har numpashinta na neman daukewa.
Da rarrape ta sawo dakinta ta janyo waya sai ta rasa ma
wanda zata buga ta sanarwa , ko yushau bai gargade ta
sanar da iyayen su halin da take ciki ba, ita kuma tai
alkawarin ko zata mutu ba zata kuma sanar da su din ba.
To idan ta kira wani a yanzu ta pada masa wannan
mummunan labarin sai sun tuhumi ina yushauu ?
Ko wacce irin laya za a yi musu sai sun parke.
Numpaninta na kokarin kubucewa ta dinga kiran yushau
yana kallon kiran yana sharewa, kusan sau goma sai da
kyar ya daga cikin tsaki sai dai a wannan lokacin ta para
pita hayyacinta sai ta kasa magana illa wata irin
sheshsheka,,,, nan da nan yushau ya dawo cikin azancinsa
da gudu ya watsar da wayar ya doshi dakinta ya same ta
kwance gaban gado cikin jini a sume.
Halin da ya same ta shi kansa ba dan yana jar zuciya ba
kila ya sume cikin tsabar rikita da barin jiki ya dago ta
yana padin na shiga uku zan kashe yar mutane,babu bata
lokaci ya janyo durowa ya dauki ID card dinta na shaidar
kasancewarta sikila da gudu ya pice ya pita da mota,
sannan ya dawo ya dauke ta ya nupi asibitin nasarawa,
da yake akwai group din jininta a jikin Id card dinta ba a
tsaya jiran diban na yushau ba aka makala mata wani.
Har azahar na washegarin ranar Rumasa'u tana cikin
wani hali na kasa gane kai, Yusha'u ya yi
nadamar abin da ya yi matu'ka, musamman da ya sami
tabbacin cikin Rumasa'u ya zube, hannun
agogonsa ya koma baya a matsayinsa na mai dokin ganin
dan kai. Tun sha biyun rana Mummy ta sauka cike da
tashin hankali wanda ta yiwa Yusha'u kallon tsana a
fakaice ba, babu wanda ya san tana yi idan ka dauke shi
Yusha'u.
Da azahar da suka sami damar shiga dakin kowa cikin
jimami, Hajiya da iyalanta kaf in ka dauke Mubarak da
tilas ya je makaranta, ga Alhaji ga Mummyn Rumasa'u
tare da Balaraba.
Ko zama Mummy ta kasa yi tana tsaye rungume da
hannnu ta 'kurawa ledar jinin da ake 'karawa Rumasa
ido, idon Mummy ya fara fitar da kwalla saboda tsabar
tausayin 'yarta. Ta ji a ranta akwai sakaci cikin hatsarin da
ya faru da 'yarta, sakacin da ta
tabbata ba 'karshensa ke nan ba, za a kuma wani dan
Yusha'u mutum ne mai taurin kai da wasa da al'amura
cikinsu har da rai.
An dai gaya mata silar hatsarin daga bakin Hajia iya ma
kamar yadda Yusha'u ya fada mata cewa. "Ana dan zafi,
ita kuma kin san ba a kunna mata fanka, sai na ce ta tafi
dakinta ni ina son kunna
fanka. Ina bacci kwatsam ta kira ni a waya na ji muryarta
cikin wani hali kafin na 'karasa dakin na tarar da ita a
sume."
Sam Momi ta kasa gamsuwa da wannan fatawar. Ranta
kuma ya yi mugun 6acin da ta ke jin lallai sai
ta bude kwanji a kan 'yarta in ba haka ba Yusha'u zai yi
mata sanadinta ko da yake cuta ba mutuwa ba ce, amma
zai iya yiwuwa ta 'kare rayuwarta cikin
wahala saboda rashin kulawa.
Idonta cike da kwalla ta sauke ganinta a kan Yusha'u da
ke zaune kan kujerar da ke gaban gadon Rumaisa'u, ta ce
masa.
"Yusha'u me ya faru ne wannan tsausayin ya afku?"
Yusha'u ya kasa hada ido da ita, ya kwaso in'ina. "Wallahi
Mummy... Muna kwance ta tashi ta.... shiga bandaki kawai
ta fara kwala min kira kafin na farga ta fadi a nan
wajen..."
Hajiya da su Atika suka ware ido suna kallonsa, tun daga
nan jikin Hajiya ya yi sanyi ta tabbatar akwai
wani abu da Yusha'u ke 6oye wa tunda har ya yi baki biyu
haka, Alhaji ma ya dan kalli Hajiya ya basar cikinsu babu
wanda ya tanka.
Mummy ta 'kara tayar da ganinta sosai akan Yusha'u, ta
ce.
"Shin kun je asibiti kuwa kamar yadda na ro'ki
alfarmarka a waya?"
Nan ya shiga kame-kame cike da borin kunya. "Ranar ban
koma gida akan kari ba. Jiya kuma mun je bikin bude
rijiyar nan... Damadai yau na ke shirin ta je asibitin..."
Alhaji da takaici da fargaba ya fara kaiwa bango ya tare
shi ta hanyar shiga maganar ya cewa Mummy.
"Wai me yake faruwa da kika sanshi kina Abuja mu ba
mu sani ba?"
Kai tsaye cikin raunin murya ta fada masa.
"Lokacin da cikinta ya yi wata biyu ta kira ni ta fafa min,
amma da sigar neman shawarar yadda za a yi ta je asibiti
kasancewar sickler kullum cikin na'kuda suke, na ce ta
sanar da mijinta da kanta, sai ta nuna min tana jin nauyi.
Ni na kira Yusha'u a waya na fada masa, na kuma sanar
da shi dukkan hatsarin
da ke tattare da rashin zuwanta asibiti ya amsa min za a
je, amma har tsawon sati kusan uku ba a je
asibitin ba. Rannan na kirata ina bincikar lafiyarta,
sai tana kuka ta sanar min a halin yanzu ma jininta ya yi
'karanci. Na kuma kiran Yusha'u na gargade shi. Yau
kwana uku ke nan jiya kwana biyu wannan hatsarin ya
faru, Yusha'u bai nemi asibiti ba ni ban san wanne irin
sakaci ba ne wannan".
.
To zamu shiga hutun sallah daga yau, sai kuma bayan sati
biyu.
Dan Aunty.GORAN DUMA (P 35)
.
.
Ran kowa a dakin ya 6aci, musamman Alhaji da Hajiya,
Alhaji ya yi kwafa cike da takaici da 'kunar rai kamar ya
hadiye zuciya, ya ce. "Sakaci ko ganganci, 'kila so ya ke ya
kasheta
tunda na aura masa ita bisa tilas".
Dannewa kawai Mummy ta yi ta amsa cikin sanyin
murya.
"Alhaji maganar duk ba ta yi zafin haka ba, amma dan
kyautawa gaskiya Yusha'u ba ka kyauta ba. Ba a kan
wannan lamarin ba Yusha'u na sha sanar da kai irin
hatsarin da yarinyar nan ke ciki, dan na yi wasa da
hankalinka ba zan dinga fada maka 'karya ba.
Yarinyar nan na bukatar taimako ba na komai ba na taya
ta kiwon kar ciwonta ya tashi. Ko ba 'yar uwarka ba ce ba
kuma matarka ba ce ai ka yi mata taimakon musulunci,
wanda ya hori musulmai da taikamon juna da yaye
damuwar juna".
SABODA tsabar takaici Yusha'u kasa magana ya yi, sai ya
yi kwafa kawai ya kawar da kai, Hajiya ce ma ta cika shi
da kallon tuhuma, Hafsat kuma take satar harararsa, dan
ita kadai ta san wanne irin zama Yusha'u ya ke da
Rumasa'u, gidan Rumaisa'u gidan zuwanta ne kwarai da
gaske, tana kallon
rashin shakuwar dake tsakaninsu tana kuma kallon yadda
Rumasa'u ta ke fama da dawainiyar aiki tana da lafiya ko
ba ta da ita, shi babu abin da ya shafe shi. Bayan wannan
ta kula da jarabar ma'kon da Yusha'u ke yi ko a wajen
abinci da
kayan masarufi ballantana a sami Rumasa'u da kudi, bare
a yi batun ta bugi kirji ta kai kanta asibiti.
Yusha'u bai ta6a tsanar auren Rumasa'u irin yau ba. Ya
fahimci Rumaisa'u ake so ta mallake shi ta dinga shimfida
masa doka ba, a'a danginta ma so ake suna daga
nesa su za su dinga tsara masa yadda zai yi a gidansa, shi
yake hakuri da Rumasa'u ta ke juya shi
son rai, ya ke hakuri da masifar laulayinta, ya ke hakuri
da ita ya ke mata adalci alhalin ya san ba shi ne cikin
zuciyarta ba.
Duk wadannan manyan aibu ne ya ke jurewa sun kuma
isa ya ci fuskar Rumasa'u a kansu, amma bai ci din ba ya
ke kawar da kai amma duk da haka ana nuna gazawarsa,
ba a dangin Rumasa'i ba ba kuma
a nasa dangin ba. Wannan abu da yawa yake mutuwa ta
je kasuwa!
Rumaisa'u ta yi kwana biyar a asibiti aka mayar da ita
gidan Hajiya, ta yi sati uku a can ta warware sosai ta
kuma murmure kamar ba ta yi cuta ba.
Sannan aka mayar da ita gidanta bayan Alhaji ya wanke
Yusha'u tas da nasiha da gori, ya nuna masa lallai Yusha'u
na shirin ba su kunya a wajen iyayen Rumasa'u, kunyar
da ta fi tun karfo ya tubure ya ce
ba zai auri 'yarsu ba.
Zaman ya sauya salo da wata irin rayuwa mara dadin
labari, Yusha'u ya bude kofar zuwa asibiti da kashi saba'in
cikin dari sai dai shigen je-ka-na-yi- ka, wato ba ya bayar
da kwabonsa zuwa asibiti bare a kai batun siyo magani,
ya kuma toshe
dukkan kofar da zata iya tambayarsa saboda tsabar
gizagonsa ya camfa Rumasa'u ta raina shi,
kuma matakin da zai iya dauka a kanta shi ne ya toshe
kofofin rainin ta daina ganin hakoransa a waje balle ta
nemi kawo masa wargi.
Ai kuwa sai ya kwana bakwai Rumaisa'u ba ta ga
hakorinsa da sunan dariya ba, babu doguwar hira
sai dai numfarfashi da bayar da umarni, in ta debo masa
dogon batu sai ya numfasa da kyar ya ce
mata, "To". Ko kuma, "Na ji". Gaba daya rayuwar
Rumaisa'u ta kuntata, jikinta babu dadi, zuciyarta babu
dadi sai gaba daya gidan ya zame mata kamar kurkuku,
duk da tana iyakar
kokarinta wajen ganin ta ribato Yusha'u. Cikin haka ta
kuma wayar gari da ciki bayan watanni uku da
komawarta gidan. Wannan karon ta yi jan namijin
tuknararsa da
maganar cikin tun kafin ya cika watanni biyun.
"Allah Ya inganta, Ya raba lafiya. Ina fatan za a yi min
hanzarin mu wayi gari lafiya kafin mu je asibiti?"
Abin da ya fada mata ke nan cikin rashin walwala ba tare
da ya dubi idonta ba.
Sai dai fa yana neman shayar da ita mamaki, dan yanzu
ya 'kara sauya taku na mayar da ita aljihun
baya, kuma ba a bakin komai ba, sannan yanzu kullum ya
dawo kasuwa zai fesa wanka da sabon
dinki ya feshe jiki da turrare ya cife kullm cikin sabon
dinki da daure fuska ya ke, sai kuma ya kai goma na dare
har zuwwa sha daya a waje babu halin ta nemi ba'asi
yanzu sai abin ya zame musu rigima, domin kuwa sai ya
hau kanta da bala'i.
"KO KE da nake da ikon in hana ki fita ban sami wannan
sararin ba bare ni da duk lalacewa ba ke kike ciyar da ni
ba balle ki iya saka wa 'kafata kwado".
Ba'kar magana a tsakaninsu ta zama abin adon da kamar
alfajari Yusha'u yake idan yana ya6a mata,
komai na laifi da korafi ne, duk kuwa yadda ta zage masa
da kyautatawa kullum bakin cikinsa ta ke hadiya tana
korawa da ruwan hakuri, amma tamkar zuga shi ake yana
'kara gadara da izza tare da munana mata.
Rannan ya dawo gida karfe goma kamar yadda ya saba,
da sauri ta cimmasa a dakinsa ta yi kwalliya kamar 'yar
tsana, amma bai ko yarda ya 'kare mata kallo ba, sai wani
kawar da kai yake yana hura hanci.
Ta yi masa sannu da zuwa ta gaishe shi, sannan ta ce.
"Wanka zaka fara ko in kawo maka abinci?"
Ya yi kicin-kicin ya daure fuska ya ce. "Wannan wacce irin
tambayar rowa ce Rumasa'u?"
Ta dan dube shi a sanyaye ta kawar da kai, ta kasa cewa
komai, shi kuma ya ci gaba da mita.
"Ina jin haushin tambayar nan da kike min kullum!
Ki kawo min mana idan ba na bukata ba sai na barshi
ba?"
Ta jima kanta a sunkuye, sannan ta yi murmushin takaici
ta ce.
"Allah Ya ba ka hakuri".
Jiki a sa6ule ta wuce ta kawo masa abincin sannan ta
nemi guri ta zauna har ya gaji da hararar abincin
sannan ya zauna ya fara ci. Ita kuma ta ci gaba da satar
kallonsa tana tuna yadda suka yi rannan. Ya
dawo da yamma ya fito da kudi yana kirgawa ta kawo
masa abinci, kawai sai ya hau ta da masifa.
"Wallahi matsi ne ba na so. An gaya miki babu abin da na
zo yi duniya sai cin abinci?
Ke babu arzikin da zaki yiwa mutum sai dai ki yi ta tura
masa abinci?"
Idon ta rau-rau ta ce.
"Yaya Yusha'u kamar me zan yi maka yanzu?
Ka dawo na yi maka sannu da zuwa, na kawo maka ruwa
kai da ka fita tun safe sai in kasa kawo maka abinci?
Haba Yaya Yusha'u!"
Ya kara tarar numfashinta a 'kufule. "Amma dai lissafi
kika tarar ina yi ko?
Idan abin kirki ne sai ki zauna ki taya ni ba wai ki yi ta tura
min abinci ba".
Ta dube shi da kwallarta ta ce.
"Ka tuna ranar da ina hada kayan wankinka na ciro kudi a
aljihunka na ajiye maka ka zo kana tuhumata da cewa, ba
su ke nan ba?
Har kana min gargadin kar na 'kara ta6a maka kudi?"
A nan sai ya yi zugudi, kuma da yake uwarsa ba ta rasuwa
ita kadai sai ya yi fuska ya ce.
"Ni ba na son 'kullaci".
Dan haka yanzu da ya yi mata maganar rowa ke sa ta yi
masa tayin abinci ya sa ta tsaya tana ta faman satar
kallonsa, shi dai wanda ke 'kinka babu abin da za ka yi ka
iyar masa.
Zuciyarta ta 'kara rauni da ta kula da yadda yake ta faman
muzurai kamar mai zaune da mayya, kawai
sai ta ji hawaye ya su6uce mata, can ma sai shesshekar
kuka.
Ya dago ya dubeta cikin muguwar 'kufula, ya ji ransa ya yi
mugun 6aci dan babu abin da ya kaddara shi ne, ta tuno
marigayi Auwal. Ya jima yana mata kallon tuhuma me
kuma ya tuna? Oho!
Sai ya sauke kai murya a sar'ke ya ce. "Haka Allah Ya
'kaddaro min, Alhaji kuma ya jaza min, ina aurenki
zuciyarki na auren wani ko?
Hmm MUTUM DA ZUCIYARSA ko?
Ba zan gaji da gaya wa Allah neman Ya bi min ha'k'kina
ba".
Ta tsayar da kuka ta zuba masa ido kamar numfashinta
zai dauke saboda takaici ta motsa baki da niyyar magana
sai kuma ta hadiye abarta ta yi 'kasa da kai tana girgizawa.
Sai kuma ya sha jinin jikinsa ya dan kafa mata ido,
sannan ya ta6e baki ya ce.
"Ki fadi duk abinda ranki ya raya miki, kar ki 'kullace ni.
Abin da na fada gaskiya ce idan kina da wadda zata
tankwa6e ta ba sai ki kawo ba, in ma rashin kunyar da
kika saba za ki yi min ai ba wani
saban ba ace a

15 / 28