Advertisements
Chapter 10 Reading YAR IYA (Mai Hannun barna) BOOK 1 BY DIAMOND LADY BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

YAR IYA (Mai Hannun barna) BOOK 1 BY DIAMOND LADY

Author :  DIAMOND LADY Category :  Complete Novels

Chapter   10 / 15

27K to 30K   out of 42.9K words

ciki iya tayi tace  Toh shi sukul Win me yake nufi? Ta tambaya cike da aguwa.

Sai da ta juya kai kafin tace

 Makaranta shine sukul Win

Haka suka yi ta shirmen su yayin da cikin gari ya Wauka ai ar Iya ta dawo. Wasu na farin ciki

musamman A'i wasu kuma har sun fara kuka da kansu.

&&&&&&&&&

*ALEE POV*

"Bayan sun isa wurin da suka bar motocin su, kai tsaye suka shige tare da wucewa. Bayan sun isa waWanda suka samu rauni aka mia su asibitin dake can for effective treatment yayin da"

Hamma Zaki yai tsayawa.

"Bai samu kunna wayar shi ba ko da bayan sun dawo, saboda haka ya kunna tare da iran"

"Joseph, cikin mintuna kaWan Joseph ya araso yayi driving Hamma Zaki gida."

"Tun kafin motar ta gama packing gaba Waya mutanen gidan suka iso wurin,p Mom da fuskar ta"

"ke Wauke da tsantsan damuwa da sauri ta shige gaba ganin Joseph ya buWe mishi motar, cikin zafin nama taje tayi hugging nashi tana sakin wani irin kuka."

Zuciyar shi ce ta karye ganin yadda Mom Win shi ke kuka.

"Granny ma ba a bar ta baya ba,"

" Ku bani waje nagan shi don Allah, lafiya alau yake ai koh? ta faWa tana Matsowa kusa da shi."

"Ganin raunin da ya samu yasa jikin kowa yin sanyi. Nan take Mom tace su wuce Hospital, bai iya yi mata musu ba haka suka Wunguma zuwa Hospital. Bayan an yi treating raunukan likita ya"

buaci su koma don yana buatar hutawa.

&&&&&&&&&

"Yammacin ranar kuwa ar Iya tayi wanka har da wanke baki da gawayi da kuma alimun, aka"

saka kaya masu kyau ita ala dole an je birni.

"Ko sallama bata yiwa Iya ba ta fito abun ta tana taku tana yaui kamar wata kuSaiwa. Kai tsaye gidan su Aminiyar ta A'i ta wuce, kafin isar ta kuwa duk wurin da ta gifta sai anyi gulmar ta wai"

ar Iya taje birni baku ga har sauya tafiya tayi Baneh irin ta an birni?.

Sai da suka sha hirar yaushe gamo da kuma labarin bayan rabuwa a nan A'i ke faWa mata tsiyar

da an garin suke mata bayan tafiyar ta.

" Hmm awata dai tunda kika sa afa kika bar Gallara shikenan an gari suka tsaneni,  Ban gane ba "

 Ina faWi miki Aradu har duka na wasu suke yi wai zasu huce tsiyar da muka tsula duka a kaina Mamaki ne ya kama ar Iya jin abun da an garin suka yi wa Aminiyar ta kuma ta Waukar mata

alawarin Waukar mata fansa.

"Daga haka suka fice don yawata gari. Gulma ko ina ar Iya annoba, ar Iya mai hannun Sarna"

"ta dawo, wasu wurin kuma gulmar su bata wuce yadda ar Iya ta sauya tafiya ba ga kuma kaya masu kyau da suka gani a jikin ta saSanin da da sai tayi wata da kaya a jikin ta."

"(Nace ah toh, don ma makaranta taje da ace wani gidan an gayun taje da tafi haka)."

A dai-dai wata corner suka ga wani yaro Wauke da kaji a hannun shi alamun sayar da su zai yi.

ar Iya kuwa murmushin mugunta tayi sannan ta dakatar da shi.

 Dauda ina ne zaka je haka a yammacin nan da kaji?

Dauda da duk ya tsorata ya duburburce saboda ya san karon sun da ar Iya mai hannun Sarna ya fara magana cikin iina.

 da...da...dama...innnn...innna ta...ce...ta..ta...ce..na..je ka...ka..kasuwa na..sa..sa..yar da...kajin...sai...na.auno...geron tuwa .

Murmushi kawai tayi tace shikenan jeka abun ka ammah kace kada a ara aiken ka da kaji kaji ko?

Kai ya gyaWa daga nan suka bar shi ya wuce.

Nausawa cikin kasuwar suka yi still ar Iya na kwalmaWewa kamar wata kara tana ara gyara

tafiya.

Dai-dai wurin Bala Mai kifi suka tsaya ganin lokacin yake soya kifin.

Fari ar Iya tayi da ido sannan ta gaida Bala wanda take zuciyar sa ta fara wani irin bugu.

 Ina wuni mai kifi

Cikin arfin hali Bala ya amsa yace

" Ina wuni ar Iya ya gida?, Kin dawo ashe "

" Eh wallahi mun dawo jiya da Yamma, akwai kifin ne? Ta faWa tana ara lea kifin dake zube kan teburin."

Bala ya amsa mata da

 Eh akwai

Ai da tunda suka zo bata ce uffan ba ta ce

 Mai zafi zaka saka muna

Da  Toh  ya amsa sannan ya jawo leda ya cika ta da kifi daga nan ya mia musu. Godiya suka yi

mishi sannan suka ja afafuwan su sai gidan Iya.

"Bayan sallar maghrib A'i ta yi sallah a Wakin Iya, don ita duk tsiyar ta tana yi ne idan mai tare mata tana nan kuma ba laifi tana bubbuga sallar ta duk da cewa ba yadda ake yi ba abun ku da"

mutanen auye.

Kai tsaye gidan wata Halima suka shiga. Duk da cewa basu taSa shiga gidan ba ammah haka

ar Iya ta jagoranci A'i zuwan cikin gidan saboda ta jiyo amshin dahuwar da ke tashi ta jikin zana.

ar Iya ce ta fara kwaWa Salama

" Salamu Alekum, Salamu Alekum ga bain maghriba "

Halima da bata san waye ba ta amsa tana gyara murya da alamar a makewayi take.

Shigowa suka yi suka zauna kamar mutanen kirki a kan taburmar da ta shimfiWa kusa da

murhun.

"Halima mace ce mai son gayu, fara ce kakkaura kuma ba ar cikin Gallara bane, daga Azare aka auro ta. Da yake tayi zama cikin birni kuma irin matan nan ne masu kutsawa cikin manya babu wahala ta san abubuwa da dama. Sana'ar ta a nan Gallara shine sayar da maganin mata iri iri kuma babu laifi ana siya saboda kowa so take ta zama gwana wurin mijin ta. Hakan yasa Halima ta saba da an garin cikin ananin lokaci, da wuya kazo gidan ta baka tarar da bai ba"

wasu sun zo ayi musu irin dahuwar nan ne wasu kuma siyan maganin mata suke yi.

aure da zani a irjin ta ta fito daga makewayi tana kallon su ar Iya da suka make a kan taburma tana aika musu kallon tambaya.

 Sannun ku da zuwa an mata

 Yauwah sannu ar Iya ta amsa tana ara kame kanta wuri guda kamar ta warai.  Bari na sako kaya sai nazo

Bayan mintuna 30 sai ga Halima ta fito cikin wata koWaWWiyar atamfa sai dai tas-tas take babu alamun datti. Tayi kwalliyar ta ta kuma shafa janbaki har da eyeshadow. KO ifta ido ar Iya bata yi ganin irin adon da matar ta caSa. Haka nan taji matar ta burge ta kuma tana son su ulla

zumunci.

" Kuyi hauri an mata na Wan Sata muku lokaci, wacce ce amaryar a ciki? ta faWa tana yin wani"

murmushi tare da zama kusa da su bisa taburmar.

Kallon mamaki ar Iya ke bin ta da shi jin wai wacece amarya?. A'i da yake an riga an sanya

bikin ta bayan tafiyar ar Iya birni saboda dama tun kwanaki aka fara auren sa'annin su.

Sunkuyar da kai asa tayi tace

" Nice, Ina wuni "

Murmushi Halima tayi tace

 Lafiya alau ai na Wauka wannan ce amaryar Ta faWa tana nuna ar Iya da yatsa.

Kamar ta Allah ar Iya bata ce komai ba sai murmushi kawai take saki nace anya kuwa wannan

murmushi babu biyu a asa kuwa?.

Bayan sun gaisa tace

" Bari na saue dahuwar nan don Allah, kema ya kamata ki fara shirin auren nan fa, in kin je gida ki cewa Innar ki ta fara shirya ki kuma ki ce mata ina gyara sosai da kuma bada magungunan mata masu kyau "

Caraf ar Iya tace  Gyara kuma na me?

Halima da yake irin matan nan ne marasa kunya kuma babu ruwan su da yaro ko babba tace

 Bari na saue na dawo

Saue tukunyar tayi tare da Waura wata tukunyar da alamar abincin dare zata girka. Wurin su ta dawo

ta zauna sannan ta maida kallon ta ga ar Iya.

 Yauwah awar amarya kike tambaya kan batun gyara koh? kai ar Iya ta gyaWa tare da maida hankalin ta ga Halima.

 Toh kafin nan dai ya kamata na san sunan amarya da awar ta ko?

A'i tace

" Ni suna na A'i wannan kuma Aminiya ta ce ar Iya, halan zaki ji ana labarin ta ko da yake mu"

ma kan mu bamu san ki ba a auyen duk irin yawon mu

Murmushi Halima tayi tace

" Yoh ai dole na san ar Iya mai hannun Sarna, ai naji ance ma taje birni, halan yaushe kika dawo? "

"Duk irin tsiyar ar Iya da yake nema take bata ce komai ba sai ma murmushi da tayi tace  Jiya na iso, ammah nima na kusa yin auren ai tunda awa ta zata yi, sai dai ina son ki min"

bayani akan gyaran da kuma maganin mata da kike magana a kai

Halima ta gyara zama tace

" Babu damuwa zan miki bayani kamar yadda kika buata sai dai bari na kammala girka mana abinci muci, idan muka yi sallah sai mu fara bayanin don zamu kai zuwa gobe bamu gama ba. Tunda mai gidan baya nan ai zaku jima koh? "

GyaWa kai ar Iya tayi haka nan A'i ma.

Halima ta tashi ta gyara wuta ganin ruwan ya riga da ya tafasa yasa ta wuce Waki ta Wauko

"taliyar murji mai Wan yawan gaske, zubawa tayi a tafasasshen ruwan daga nan ta gauraya da muciya."

"Har taliyar ta dahu cikin su babu wadda yayi magana, da kan ta ta kwashe taliyar cikin matacin"

ta na arfe.

Sai da ta soya manja ta Wauko yaji sannan ta fito. A tray Win silver ta juye duka taliyar sannan ta

"saka musu manja da yaji, nan aka hau taliya aka cinye ta tsaf....."

(Masoya littafin ar Iya ina matuar godiya da irin haWin kai da kuke bani ta hanyar suburbuWo

comments don arfafa min guiwa.

"Ina godiya sosai awayen ar Iya, su AMEERAN MAMA, HINDATU HASSAN, da sauran da ban ambace ku ba, ina fatan samun haWin kan ku har abada, Allah ya bar auna."

ME KUKE TUNANI GAME DA ALAAR HALIMA DA AR IYA? MENENE

DALILIN TAMBAYAR AR IYA GA HALIMA?

SHIN WANE IRIN SALO NE AR IYA TA DAWO DA SHI GALLARA?

MU HAU DA SAFE IN SHA ALLAH DON JIN CIGABAN LABARIN.

"DUK AMSOSHIN KU NA TARE DA ALALAMIN DIAMOND LADY , KU CI GABA DA BIBIYAR ALALAMI NA DON YANZU NE ZA'A FARA WASAN!"

"TAKU HAR KULLUM, DIAMOND LADY "

"[5/5, 7:13 PM] Diamond Bhatool :"

NAZARI WRITER'S ASSOCIATION

[Marubuta masu aiki da zallar fasahar zamani tare da bin a'idojin rubutun Hausa cike da

kyakkyawan nazari don kawo sauyi cikin Al'umma]

*KYAWAWAN NAZARI DOMIN AL'UMMA*

AR IYA

(MAI HANNUN

ARNA)

[Labari/Rubutawa] FADIMATU ADAMU HASSAN

DIAMOND LADY

{GARKUWAR NAZARI WRITERS}

"&Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart"

touching love &

I DEDICATED THIS BOOK TO NAZARI WRITER'S ASSOCIATION.

BOOK 01 PAGE 29%



*ALEE POV*

"Ana kaishi asibiti kuwa aka fara bashi kulawa, kwanan su Waya suka koma can gida da shi"

"saboda yadda an jarida suke sintiri a bakin asibitin, ga kuma mutane kamar tururuwa safe, rana yamma, dare basu bar asibitin ba."

Kulawar da ya samu yasa cikin two days ya warke sumul da yake dama ciwon a iya jiki ne

zuciyar na nan alau.

"Kowa nan da nan yake da shi kamar wani wai, duk irin yadda yake takurawa annen sa hakan bai sa sun gajiya wurin yi mishi addu'a ba. Musamman waWanda suke jin kaunar shi daban cikin"

zukatan su.

"angaren kulawar nan ba'a bar kowa baya ba, Granny, aan ta, jikokin ta da sirikan ta"

"musamman Nenne ga kuma Sarah da itama take iyawar iyawar ta, Allah these ko Allah zai sa Hamma Zaki ya so ta ne."

"ira kuwa ta ko ina, wasu na iran Mom wasu kuma Daddy yayin da wasu ke iran wani daga cikin"

ahalin suna tambayar jikin sa don tuni labari ya karaWe Nigeria ta ko ina zancen ake.

"In ka hau facebook, IG har da Tiktok kowa abun da yake wallafawa a shafin sa kenan. Dr. Faruq ne yayi Video Win a lokacin da suke kan aiki. Ai kuwa a ranar da suka dawo ya wallafa Video Win a shafin sa na Facebook, Instagram, Twitter, YouTube, da sauran su. Kafin kace me kowa sai tofa albarkacin bakin sa yake. Kowa na yabawa wannan zarton matashi da yake aikin sa babu"

akkautawa.

"Comments Win wasu kuma bai wuce kan yanayin shi ba, wasu na faWin wannan ai baindiye ne irin waWanda ake nuna su a indian film Win nan. Ashe dai da gaske akwai masu irin arfin nan."

"Kowa dai da abun da yake faWa, an uwa mata kuwa santi ne kawai ke jansu."

"Videon nan fah tun da mata suka gani suka rikice, su ba jarumtar shi ce ta burge su ba kaWai"

siffar shi kawai ita taja hankalin su.

"Daga nan batun zai fara, an mata a ko ina a faWin asar mu Nigeria burin su yanzu bai wuce su"

mallaki wannan Lion Win ba. Ga kyau ga kuma jarumta.

"Tuni aan mommy da Daddy (Ina nufin an gayu, shagwaSaSSu aan manya) suka fara yiwa iyayen"

"su daru su fa ga wanda suke so, sun ji sun gani in Babu shi ba zasu rayu ba."

Ana wannan drama ne kuma hukumar sojoji ta asa ta shirya gagarumin bikin cin nasara da

suka samu bisa jajircewar Commander da ya jagoranci aikin wato Hamma Zaki.

Flyer na taron ma kar ku so kuga yanda yake trending a yanar gizo. Ai kuwa mata fa sunyi shiri tsaf don halartar wannan taro kowa da irin tata aniyar don jawo hankalin samSalen saurayin

nan.

"(Wannan kenan, nimah gaskiya na haWa sabbin kaya na don ina so nimah nasamu matsuguni a"

zuciyar Hamma Zaki na).

*AR IYA POV*

Bayan sun samu cinye taliya da manja kowa tasha ruwa aka wanke hannu.

"Halima tace  Toh sabbin abokai na, da farko zan fara amsawa ar Iya tambayar ta. tayi shiru"

tana maida duban ta ga ar Iya.

" Tabbas akwai gyara na musamman da ake yiwa amarya idan zata yi aure. Wannan gyara kuma ana yin sa ne dai-dai al'adun kowa. Gyaran nan na da matuar muhimmanci musamman saboda shi kanshi ango ya son amarya tayi, yana don ya ji ta daban. Ana gyaran jiki, tun daga"

"fuska zuwa afa, gyaran gashi da kuma sauran gyararraki."

"Kin gane, misali da zan baki yanzu saboda baki kai Waukar bayanan ba shine, kamar ke yanzu in Zaki yi aure, ni da kai na zan gyara ki fes, kinga fatar nan taki da gani Allah ya zuba mata kyau da haske datti ne kawai ya Sata ta, To zan gyara ta ta koma fes da ita irin ta an gayu ko"

ba komai ango ya gani zai yi mamakin hakan.

Sannan wannan bakin naki ma da kike gani in Zaki yi aure tas zai koma in yasha gyara 

Haka Halima ta fayyace musu gyaran jiki da ake yi.

" Sai kuma batun maganin mata, ku da yake ananan yara ne ba zaku fahimta ba amma dai zan faWi muku abu kaWan "

Halima ta faWa musu batun sex idan anyi aure tare da muhimmancin da ayyukan waWannan

magungunan matan.

Daga haka suka koma normal hirar su. ar Iya tace

" Oh Ni Halima kika ce za'a iya gyara baki na?, To da me za'a ke gyara shi? "

" warai ar Iya Tun yanzu ma ki fara,idan kika samu gawayi, ko don ashe ku da kara kuke girki, to in kun tashi tafiya ga gawayi a nan sai ki tafi da shi."

"Ki daka gawayin nan da gishiri da kuma lalle, sai ki daka kanunfari da kuma alimun ki haWe da"

"wannan dakakken gawayin, kullum sai durje bakin ki, ina tabbatar miki bazaki jima ba zai koma fes kamar farin wata "

Sai da dare ya fara duka suka yiwa Halima sallama tare da alawarin zasu ke shigo mata.

"angaren Angel ar Iya kam ba'a magana, haka kawai taji tana son yin sana'a cikin auyen, tou"

yanzu tunda an mata bayani kan maganin mata shi ta yanke zata fara siyarwa ba tare da ta san menene da menene constituents na maganin matan ba.

"Sassafiya kamar kullum ar Iya ta tashi, bata, tana miewa ta fito daga bukkar ta, bata tsaya ko ina ba sai wurin kiwon Baffi, kashin shanu ta tsinta akan faifayin busa, ta hau kan turmi ta Waura"

shi bisa bukka.

Tana Waurawa ta diro tare da Waukar langa ta fice abun ta. A dai-dai gonar wani mutumi da yake kiwon tumaki da awaki ta tsaya. Ciki ta tsallaka saboda an riga an kewaye wurin da fence. Sai

da ar Iya ta kusa cika langar nan da kashin tumaki da awakin nan ta fito abun ta.

"Gida taje shima ta Waura shi a sama daga nan ta ara fitowa, wannan karan ciyawa taje ta tsigo a"

"buhu, ta sanya ta kamar yadda tayi wa sauran abubuwan."

Gidan su A'i ta wuce suka fita yawon su. Suna fitowa ar Iya tace wa A'i

" Ke A'i yau kwaWayin mangwaro da kashu nake yi, muje lambun Baba Haro mu ciro "

"Bata Musa ba su ka Webi afafuwan su suka wuce lambun Baba Haro. Sun ci Sa'a kuwa kamar baya nan har da murnar su don sun riga sun san Bala'in wannan tsoho, don duk maitar ka ko zata fito tayi rawa ba zai bayar ba."

"Sai da suka kewaye ko ina suka tabbatar Baba Haro baya nan suka Wale bishiyar kashu tare, suna tsinkowa suna Waurewa cikin kwalayen su. Da yawa suka tsinka sannan suka sauo suka"

ajiye ullin a gefe.

Basu tsaya Sata lokaci ba suka hau bishiyar mangwaro. Tun akai suke Sha in sun sha sai su

wullo asa.

Suna cikin haka ko tarawa basu yi ba Baba Haro ya shigo lambun. A dai-dai lokacin ne kuma

ar Iya ta wullo wallon mangwaron da ta lashe shi har ya zama fari sol.

Bai yi aune ba kawai yaji wallon mangwaro akan sa. Duk tunanin shi irin wanda jemagu suka

sha ne shi yasa bai samu ya duba wallon ba.

Ba zato babu tsammani yaji wasu wallayen har biyu da suka iso kan sa lokaci Waya.

" Ashh"" ya furta tare da sunkuyawa asa. Arba da lasassun wallayen yayi ai kuwa ya Waga kai sama. Mutane biyu ya gani kan bishiyar mangwaron. Nan ya fara musu magana kan su sauo.  Ku sauo yanzu ko na hawo na ci ubanku "

Dariya suka kwashe da ita ar Iya tace

" Kaji tsoho da wani zance, har ya bani dariya...hhhhhhh..to ka hau Win mu gani ina zaka iya "

Haushi ne ya cika Baba Haro Jin Muryar yarinya tana masa baWala a bishiyar da ke cikin lambun sa.

" Wallahi in na hau

10 / 15