Advertisements
Chapter 2 Reading YAR IYA (Mai Hannun barna) BOOK 1 BY DIAMOND LADY BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

YAR IYA (Mai Hannun barna) BOOK 1 BY DIAMOND LADY

Author :  DIAMOND LADY Category :  Complete Novels

Chapter   2 / 15

3K to 6K   out of 42.9K words

in na zo ki ara min rashin kunya ki gani, bari na ira dogari Waya ya sanar da"

sarki matar sa ta karye ta faWa tana kashewa da dariya sannan ta fita.

A bakin afa ta sanar da dogarin cewa Saratu matar sarki na neman sa daga nan ta cika bujen

ta da iska.

"Bata tsaya ko ina ba sai gidan su A'i Aminiyar ta wacce take take mata bayar kamar bafadiya. A'i ma ba baya ba a rashin ji shiyasa duk auyen babu wacce ar Iya ta zaSa matsayin abokiyar ta irin A'i, tare suke tsula tsiyar su, su tsokali wannan su zagi wannan in sun ganshi su duka"

wannan aikin su kenan cikin gari ini suke suna yawo kamar udaje daga nan sai can.

Tun daga bain soron gidan su A'i ar Iya ke wala iran ta.

 A'i A'ilo kan kaza Amadu ya siyo mata kaza taci wannan shine kirarin da ar kewa Aminiyar ta tuni zaki ga ta fito da yake ita ma duk ta ishi gidan su har Allah Allah suke ta fita. Yau da bata

fita ba tsiyar da ta tsula musu ba'a magana.

A'i na fitowa daga gida ta dubi awar ta tace

" Kutt ar Iya dama kina cikin Gallara yau ko kallon ki banyi ba, ko dai kin samu kaso ne shiyasa "

 Dallah ni ba magana nace ki min ba ki zo muje gida yau na samo babban rabo

Nan ta bata labarin kifin Bala da ta kwaso da kuma Naman Iya Uwa Maman sarki. Suka yi ta

dariya suna shaiyyancin su.

Har sun kama hanyar gidan su ar Iya A'i tace  ah ar Iya wallahi mu bi ta dandali ta wurin

Bayero mai balangu nasan zamu dara. Tafa hannu suka yi suna dariya ar Iya tace  Ke A'i yau kam dai sai cikin mu ya cire don ciwo mu dai wuce.

"Tafiya suke suna taWe-taWen su har suka iso dandali, duk da cewa dare bai yi ba lokacin ne ma ake kiran sallar Ish ammah yara da manya, an mata da samari sun cika mail ga kuma"

Sangaren Bayero da yake sayar da balangu sai kai kawo ake a wurin.

"Ganin kowa hidimar shi yake yasa ar Iya wallah ihu ita da A'i Suna faWin,"

" Wallahi Sakse ya biyo ta hanyar nan, kowa ya gudu ya tsira da kansa don kuwa har da wua a hannun sa Nan wasu suka fara gudu yayin da ar Iya da A'i suka ci gaba da ihun"

 Wallahi dagaske ga nan Sakse mun shiga ukuuuu

"WaWanda suka Wan ja gefe tuni sun fara neman wurin Suya, Bayero kuwa da Mai Salisu mai shayi duk sun watse sun shige kiosk Win Baaba Mai trader, tuni wurin yayi tsit babu almaun motsi kowa yayi shiru don tsira da ransa shi, hakan yasa ar Iya da A'i nausawa kai tsaye tsaye wurin bakangun Bayero. Tas suka kwashe shi cikin ledodin da ke ajiye bisa teburin balangun, har sun lallaSo zasu tafi ar Iya ta hango wasu Sula-Sulan breads kan teburin Salisu, tuni ta wuwuro biyu"

ta rie.

"Juyawar su da niyyar tafiya suka ji motsi a bayan su, waye kuwa in ba Sakse ba ai tuni suka"

"arta a na kare Sakse na biye da su. Dama bread Win a hannun ar Iya suke , sai da suka ja Sakse ta lungun arashi kukan ka ar Iya ta faki ido ta damo asa ta watso masa sai ciki idon sa, ta ara dama ta watsa sai da ta tabbatar asar ta masa illa ba zai iya gani ba ta tsokalo karen Baushe tuni suka yi siWaf-siWaf suka gudu suka bar Sakse da kare ga kuma ido car"

asa.

Gudu suka ara har sai da suka iso gidan Iya tukun suka tsaya suna haki suna mayar da numfashi. Tun daga lungun da zai sada ka da cikin gidan suka jiyo Muryar Baffi.. ata fuska ar Iya tayi saboda ta san halin Wan tsohon sam baya Waga mata kuma duk iya shegen ta bata isa

tayi masa musu ba in yace abu.

"Da yake su an duniya ne sai suka haWa plan, ar Iya ta shiga da gudu zuwa Bukkar ta kamar an biyo ta sai A'i ta biyo bayan matsayin wacce ta tsokalo. Hakan kuwa suka yi tuni ar Iya ta arta A'i na biye da ita basu ko kalli Iya da Baffi basuka shige, dariya suka yalyala suna tafa"

hannaye.

Baffi da ya lura da su kuma ya gane shiri ne irin nasu bai bi ta kan su ba kawai yayi musu addu'a ya mie zuwa tashi bukkar. Har Iya zata bi bayan shi ta tsinki Muryar ar Iya

" Ina kuma zaki je Iya baki bani aikin da nayi miki ba? ta tambaya tana wani yamutsa fuska. Iya da dam tuntuni take jiran dawowar jikar tata saboda ta bata ita ma ko ta maida aan yasa tayi murmushi ta nufi Wakin ajiya ta Wauko naman kajin da ta soya, ba tare da ta Wauki ko afa ba ta mia mata."

 Gashi nan ar Iyan ta

"Cinya da fuka-,fukai ta zaro da mia wa Iya tuni ta amshe kamar sabuwar mayya sai wani wage Baki take ita ala dole zata ci nama."

Wani abun mamaki tas suka cinye kajin da zasu kai huWu kuma ba anana ba sannan suka ara da

balangun Bayero na yi tunanin zasu bar bread Win zuwa safiya ai kuwa sai ar Iya taja Waya ta buWe A'i taja Waya ta buWe tuni suka lamushe su tasss....

Suna gama cinye wa suka ara fita waje ammah wannan fitar ta satar mangwaro ne kuma

bishiya zasu hau.

(Nace sai kun je aljanu sun wurWo ku ai ehmana)

Gonar da ke kusa da gida suka nufa. Bayan sun tsinko mangwaro suka dawo.

Duk da cewa dare ya tsala hakan bai hana su yawata cikin auyen ba don farauto wani abun

su ara a cikin su kafin kowa ta wuce gida don huce gajiya.

*WACE CE AR IYA*?

"Mu haWu gobe don jin wacece ar iya, tabbas akwai Soyayyen al'amari a tattare da ita ku ci"

gaba da bibiyar alalami na don jin ya zata kaya.

COMMENT PLEASE!!!

"[4/26, 8:45 PM] Diamond Bhatool :"

NAZARI WRITER'S ASSOCIATION

[Marubuta masu aiki da zallar fasahar zamani tare da bin a'idojin rubutun Hausa cike da

kyakkyawan nazari don kawo sauyi cikin Al'umma]

*KYAWAWAN NAZARI DOMIN AL'UMMA*

AR IYA

(MAI HANNUN

ARNA)

[Labari/Rubutawa] FADIMATU ADAMU HASSAN

DIAMOND LADY

{GARKUWAR NAZARI WRITRS}

"&Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart"

touching love &

DEDICATED TO NAZARI WRITER'S ASSOCIATION



BOOK 01

PAGE 05%06



*WACECE AR IYA?*

Malam Umaru Gallara haifaffen auyen Gallara ne da ke cikin aramar hukumar Shira da ke jahar Bauchi. Mahaifiyar sa AISHATU wacce aka fi sani da Iya sunyi auren zumunci ne da

Baban sa Mallam Musa wanda ake ira da Baffi.

"Tunda suka yi auren nan Allah bai basu haihuwa ba har suka share shekaru goma sha biyu cikakku, hakan ne ya tada hankalin Iya saboda dangi sun yi caaa akanta suna faWin juya ce,"

Musa ya ara aure.

"Wannan tashin hankali yayi wa Iya illa sosai, don kuwa haukacewa ne kawai bata yi ba, ana"

cikin wannan yanayin ne wani al'amari ya faru wanda shine mafarin komai cikin rayuwar wannan ahali na Malam Musa.

"Wata guda da fara wannan hatsaniya Iya ta samu ciki, kada ku so ku ga murna wurin Baffi don kuwa a ranar sai da ya raba buhun gero fiye da ashirin saboda farin ciki. Dangi murna kowa yake yi da wannan cikin yayin da kowa ya wallafa ranshi akan yaron da masu so da kuma"

marasa so.

Haka Iya ta raini cikin nan tare da taimakon Baffi da kuma Mahaifiyar sa Baba Maunde. Baffi da Baba Maunde sun matuar bawa cikin Iya kulawa ta musamman har ta kai watanni tara ta haifi

"Wan ta namiji, kyakkyawa son kowa."

Bayan sati guda da haihuwar yaro Baffi yayi masa laabi da Umaru. A ranar Iya ta samu goma

"sha tara na arzii daga kowanne fanni, dangin ta da kuma dangin Baffi."

"Haka dai yaro ya ci gaba da girma har ya kai shekarun fara zuwa Waukar karatu, da yake Allah yayi mishi baiwa ta musamman yana da shekaru goma sha shida ya kammala haddar sa ta Alqur'ani. Bayan ya dawo Baffi yasa aka shiryawa Umaru ar wata warya-kwarya yadda aka ci"

aka oshi.

"Tun bayan dawowarsa Baffi ya ke zuwa da shi gona har ya kai shekarun Aure. A lokacin ne kuma fitina ta Sarke, Iya ta kawo zaSi Baffi ya kawo zaSi. Da yar aka samu Baffi ya janye nashi zaSin akan sharaWin bayan shekara da auren Umaru zai auri Zaliha Wiyar Abokin sa wacce ita"

tace tana son Umaru.

"Sannu sannu babu wuya inji hausawa, haka aka sanya ranar auren Umaru da Barira ar yar Iya."

Barira mutum ce ba mai aunar tashin hankali ba hakan yasa suka yi zaman su lafiya da mijin ta Umaru wanda shima lokaci guda yaji ba zai iya ara auren wata matar ba bayan Barira.

Shekara guda da auren Allah ya albarkace su da samun aruwar a mace sai dai yarinyar tazo da

salo na musamman. Ranar suna yarinya taci suna Aishatu...an yiwa Iya takwara kenan.

"Tun daga wannan lokaci Zaliha ta fara oarin shiga gidan Mallam Umaru tare da udurruka masu Wumbin yawan gaske, da farko ta fara ne da salon ta na a mace ganin ba zata ci riba yasa ta fara biye-biyen an duba wanda suka tabbatar mata da cewa in dai Barira na raye to"

gidan Umaru bata da matsuguni.

Wannan abu shi ya ara tunzura Zaliha saboda haka ta nemi Aminiyar ta Larai suka nufi gurin boka don cimma manufar su ko ta yaya ne. Abu mafi muni bayan boka ya maimaita mata irin abun da an duba suka faWa mata sannan yace matsawar tana son auren nan to sai an kashe

"Barira, Ba tare da ta damu ba kuwa ta sanar da BOKA shawarar da ta yanke."

Bayan Boka ya sallame su suka nufi gida zuciyar su cike da Wumbin farin ciki.

"Sati guda da faruwar wannan al'amari kwatsam Barira ta fara jinya, lokaci anani jinya tayi tsanani bata iya gane komai sai dai a tayar a kwantar, ana cikin wannan yanayi kuma Mallam Umaru yazo da al'amarin son auren Zaliha. Kowa abun ya bashi mamaki sai dai babu yadda"

suka iya saboda haka kowa ya kawar da kanshi ya zubawa sarautar Ubangiji ido.

"Iya tayi matuar bain ciki da hakan, saboda irin halin ko in kula da Mallam Umaru ke nunawa"

akan jinyar Barira yasa Iya Wauke ta ita da Wiyar ta ta kawo su gaban ta tana jinyarta.

"Rayuwa kenan, kullu nafsin za'iatul maut...wata rana Allah ya karSi ran Barira. Iya tayi kuka"

kamar ba gobe haka dangi sun ji mutuwar ta kasancewar ta mace mai sanyin hali da aunar jama'a.

Sati guda cif da rasuwar Barira Mallam Umaru ya auro Zahiha wacce yake jin ta kamar

sarauniya a birnin zuciyarsa. Daga nan komai ya fara sauyawa.

angaren Aishatu Wiyar Barira Allah ya raya ta sai dai tun lokacin da ta fara zama ta soma addabar iya da Sarna. Idan zanin shimfiWa aka shimfiWa a gado to in Sha Allah sai ta yaga shi

fata-fata da hannun ta.

"Basu Wauki abun da muhimmanci ba kawai sun Wauke shi ne matsayin iriniya, ana haka yarinya ta fara rarrafe sai abu yaci gaba, idan girki aka Waura to zata je ta tunkuWar da shi ba tare da jin wahalar hakan ba, babban abun mamaki kuwa shine yadda wuta bata kama yarinyar duk irin"

wasan da zata yi da ita.

A wasu lokuta kuwa ta kan rarrafa jikin buhuhunan hatsi da aka tanada don ci ta Sula asan su ba jimawa buhun zai yoye haka sai anyi sabo. Wannan abu ba aramin mamaki yake bawa Baffi da Iya ba saboda Sarnar ta wuce hankali da tunani amma basu taSa sanar da wani na

waje ba.

"Kwanci tashi babu wuya a wurin Allah, Aishatu ta fara tafiya, tunda ta fara takawa kuma zaman gida ya zama ba nata ba, Sangaren Sarna kuwa sai abun da yayi gaba ammah tafi so ta fita gidan maota sam bata son zaman gida. Hakan kuma na da alaa da Baffi saboda bata iya yi"

mishi musu in yace abu.

"Idan Aishatu ta fita mawabta babu abun da take sai Sarna, tun suna shiru har abun ya fara isar su suka fara kai arar ta. Iya da a lokacin ke daure mata gindi sai tace sharri akayi wa Wiyar ta , hakan ne yasa jama'ar gari suka kafa ahon zua kan ar Iya bayan tattarawar sirri da suka yi."

Sun riga sun yanke hukuncin hukunta ar Iya a duk lokacin da ta musu ba dai-dai ba sai dai

abun da basu sani ba tafi arfin su baki Waya.

"Wata rana lokacin ar Iya bata wuce shekaru shida ba a haife, ta fita yawon ta da ta saba ne"

kwatsam ta bi ta layin wani marowacin mutumi. Dai-dai zuwan ta ofar gidan mutumin ya fito da

"langar sa cike da waina. Tunda taga wainar nan kuwa hankalin ta ya tashi, hakan yasa tabi bayan mutumin ko Waya ya bata."

"Bayan ya zauna a shimfiWar tabarma irin ta kaba Win nan ta iso, ido ta zuba mishi amma abun ka da marowaci bai gane ba. Ganin bashi da niyyar bata yasa ta faki idon sa ta jawo langar ai"

kuwa ta arta a na kare yayin da take cin Masar shi kuma mutumin bai daina bin ta ba.

"Sai da ta cinye tsaf ta daina wanda mutumin gashi abun tausayi ya jigata, ganin hakan yasa ta"

wulla masa langar ai kuwa rasss sai a kanshi. Tuni ya fashe jini sai zuba yake.

"Da yar aka tsayar da jinin a chemist tukunna ya dawo. Wannan dalilin ne yasa mutumin harzua har ya yanke hukuncin kai ara fadar ArWo. Bayan ya faWawa ArWo abun da ya faru ne sai ArWo ya aika a ira masa Baffi. Kamar ta sani kuwa lokacin suna zaune a tabarma ta tasa tukunyar Wumamen safe a gaba sai ci take kamar jaka, ana sallama kuwa ta fita akace tace ana"

sallama da mai gidan a fada....

"Tana isarwa Baffi sao ta shiga bukkar Iya, bata jima ba ta fito still hannun ta kwaSe da Sakar"

miyar kuka da ta shafe ko ina na jikin hannun.

"Baffi na fita bai tsaya ko ina ba sai a fada, mutanen da ya gani mail a fadar ne yasa ya shiga"

"tashin hankali na wani lokaci, lokaci guda da ya tuna da jikar sa ar Iya nan ya gano hala ta"

aikata wani laifin ne.

Bayan gaisuwa irin ta mutunci da suka yi da Mai martaba kamar kullum. Mai martaba yayi gyaran murya yace:

 Toh Mallam Musa tunda Allah yayi ka iso da wuri kai tsaye zamu fara abun da ya tara mu Cikin sanyin jiki Baffi ya kaWa kai.

" Toh Malam Musa, kamar yadda kaga na aika a ira ka ba wani abu bane ya faru sai wannan abun da JIKAR ka ta wajen Iya ta aikata "

Yana kai nan ya tsaya tare da yiwa dogarai alamar su shigo da mutumin nan. Baki buWe Baffi ke kallon sa don kuwa abokin sa ne Ishiyaku. Ganin kansa Waure da bandage da kuma plaster

yasa Baffi maida hankali don jin me ArWo zai ce.

" Toh Mallam Musa, kamar yadda kaga Mallam Ishiyaku kansa naWe da kayan ciwo, ba komai ne ya faru da shi ba sai karon da suka yi da jikar ka wacce ta kusa hallaka shi bayan sace masa waina a daro da tayi "

"Kasa magana ma Baffi yayi yayinda kunya tabi ta lulluSe shi, tuni ya sunkuyar da kan sa asa. Mai martaba ya ara gyaran murya yace  Mallam"

"Musa muna sauraron ka, kayi shiru "

Cikin arfin hali da takaici Baffi yace

" Don Allah Mai martaba ayi wa ar Iya hauri in Sha Allah in na koma gida Zan hukunta ta, yaran yanzu ne ka haifa baka haifi halin su ba, don Allah ayi mata afuwa."

Tuni mutanen wurin suka kaure da hayaniya wani yana faWin

" Wallahi ba zata saSu ba, ko dai a Wauko yarinyar nan a hukunta ta ko kuma wallahi mu bi har gida mu nakasa ta. yayin da wasu ke ganin hakan ba dai-dai bane."

Wani Matashi Wan azagwai ne ya mie yace:

" Wallahi ko yanzu a zo a hukunta ta ko mu mu hukunta ta, yarinya arama duk ta addabi jama'a, Aradu ArWo in ba'a hukunta taba toh mu zamu bi mu hukunta ta "

Tsawa ArWo ya buga nan da nan aka yi shiru ana sauraron sa.

" Toh mun ji orafi daga wurin mahaifin mai laifi, Mallam Ishiyaku ya kake ganin za'a yi? Ka"

haura ko kuma sai an Wauko yarinyar?

Na gefen shi ne ya zuga shi hakan yasa yace sai dai a ira yarinyar.

ArWo yace  Shikenan ammah miye hukuncin yarinyar?

Hayaniya ta kacame wasu na faWin a biya kuWin raunin da tayi kuma a bata aikin noma da yiwa matan ArWo aike sannan kullum ayi mata bulala uku da safe. Wasu masu tausayin kuma cewa suke ayi mata hauri yarinya ce...cikin zafafan mutanen ne wani ya kalli mai cewa ayi hauri yarinya ce yace

" Kutumar uba, toh wallahi yarinyar nan tafi mahaukacin kare haWari "

Ganin ba zasu yi shiru ba kuma sun tayar da rigima ne ArWo ya daka tsawa kafin yai gyaran murya.

 Ya isa haka ya faWa yana mayar da kallon sa kan Baffi.

" Toh Mallam Musa, kai yanzu me kake ganin za'a yi? "

Bai kai ga bada amsa ba suka ji Muryar yarinya arama wacce bakin ta ma bai gama fita ba tace

 Toh ai ba shi yayi laifin ba nice

"Shiru ne ya wanzu yayin da kowa kallon sa ya koma kan ar Iya da ta tsaya a gaban su yam ko tsoro babu a tattare da ita, nan da nan wasu suka sha jinin jikin su yayin da wasu kuma suke"

miewa tare da yunurin kamo ta....

Mu haWu gobe don jin cigaban yarintar ar Iya!

"Ko kuna tunanin zata bari su hukunta ta kamar yadda suke ikirarin hakan? Duk AMSOSHIN ku na jiran ku, sai mun haWu."

Ku yi sharing sannan kuyi comments.

*DIAMOND BHATOOL ce!*

"[4/27, 5:57 PM] Diamond Bhatool :"

NAZARI WRITER'S ASSOCIATION

[Marubuta masu aiki da zallar fasahar zamani tare da bin a'idojin rubutun Hausa cike da

kyakkyawan nazari don

2 / 15