Advertisements
Chapter 2 Reading MUWADDAT by Aysha A Bagudo BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

MUWADDAT by Aysha A Bagudo

Author :  Aysha A Bagudo Category :  Complete Novels

Chapter   2 / 53

3K to 6K   out of 157.9K words

mallakesa arayuwarta, tunda ta kammala karatunta na diploma ,ta cire rai da wani karatu,
"kin ci gidanku dole kiyi karatu mai zurfi domin shine burin mu iyayenki, na asali da iyayen goyonki ,guda nawa kike yanzu da zakice baki da muradin karatu idan bakiyi karatu a halin yanzu ba uwar me zakiyi?
aranta tace "aure mana daddy ...... +

" yanzu ne daidai ki natsu ki tsaya kiyi karatu amatsayinki na yarinya yar shekara ashirin da haihuwa "daddy ni dai banason karatun nan yanxu kabarni kawai iya dilomar ma dana ta isheni .. "

"haba muwaddat ni fa nafi son kiyi karatu mai zurfi Allah yasani, "to da kika nace baki son karatu,aure kike so ko me ?

muwaddat ta d'an noke kai ala'mun jin kunyar mgnrsa tana dry "kinga nifa Allah yayoni da mugun son karatun boko bansani ba kodan nasan dadin karatun ne?
"ki taimaki rayuwata dataki ki cigaba da karatu, kafin muwaddat tace wani abu hjy hajara tashigo parlour'n wanda tun kafin ta k'arasa shigowa parlour'n take jin yadda alhj yake jaddawa muwaddat zance karatu mai zurfi yake son tayi.

da sallama tashigo parlour'n tana "cewa ka rabu da wannan yarinya mara wayo kawai ,in da kai ya waye da karatu nan ,shine ita take cewa bazatayi ba, tasamu guri ta zauna tunda bataso "idan bakiyi karatu ba uwar mezakiyi uhmmmmm?

"ki duba kiga yadda mata suka samu cigaba a dalilin karatu mai zurfi, ita kanta ummin taki tafison kiyi karatu mai zurfi kafin aure,amman shine dan iya shege kike cewa baki son karatu?
"baki son karatu sai me?

muwaddat tayi shiru tana jin kmr fito ta sanarwa da iyayenta burin zuciyarta, amman kunya tattare da fargaba ya hanata "ki dai gaya mata gsky karatu na da mutukar mahimmanci agurinta bari ummintata takaraso muji mai zatace, alhj muhamud
na gama fad'ar hk ya mike tsaye ya sa kai ya fice yana takaicin rashin son karatun da muwaddat take yi...

a harabar gidan yaci karo da motar dataje d'auko kanwarta da suke ciki daya, direban gidan na k'ok'arin daidaita tsayuwar motar yana ganinta ya fad'ad'a faraarsa sannan yaja ya tsaya yana jiran fitowarta, hjy mukarama ta fito a natse tana sanye cikin shiga ta alfarma doguwar riga ce har kasa sanye ajikinta da madaidaicin hijab, amman kallo daya zaka mata kasan cewar akwai gidan rana da tsantsar gogewa irinta 'yan boko atattare daita.

ta k'araso ahankali inda d'an'uwanta yaja ya tsaya yana jiran k'arasowarta "kar dai fita zakayi Yaya ?
"eh fita zan yi wai kafin ki karaso,dama wacan 'yar taki ta nemi 'bata min lokaci da tuni na bar gidan "

"me kuma baby muwaddat tayi ?
"da ita kullun bata wuce laifi agurinku shiyasa sam bata son zuwanta garin nan amman nake matsa mata "

"ai duk ke kike d'aure mata gindi amman nasan yanxu idan kika ji abinda tayi sai ranki yafi namu 'baci yadda nasan kike da kulafucin son tayi karatu.. "au akan karatu ne?

"akan shine mana wai yanxu nake mata maganar sai cewa tayi ita bata da muradin cigaba da karatu"

hajiya mukarama tayi murmushi tace "manta da wannn shirmen nata karatu d'an ada tayi sa, dan ma inaji tsoron gur'bacewar da rayuwa tayi yanxu ,ai da tare aka had'asu da bunayya "

"nima abinda naso kenan amman naga kamar ita bada raayin ma yin karatu, ni dai zan fita idan kin shiga kinsan yadda zakiyi daita "

"ai tafiya ma zamuyi zaman shirun ya isheni ni kad'ai a gidan daman itace abokiyar hirar tawa sukayi sallama yayi hanyar waje ita kuma ta k'arasa cikin gidan

*********
alhaji mahamud shine asalin mahaifin muwaddat, sai dai ba a hannunsa ta taso ba, ta girma ne a hannun k'anwanrsa da suke uwa daya uba daya , wato hjy mukarama da mijinta alhj ishaq , hjy mukarama da mijinta suna mugun son muwaddat ,babu irin kulawar da gatan da basu nuna mata ba , ko d'an cikinsu albarka .

su biyu kawai iyayensu suka haifa suka mutu suka bari a duniya, mahaifinsu tun mukarama na k'arama ya rasu ,suka cigaba da rayuwarsu da mahaifiyarsu, sun sha gwagwamaryar rayuwa kafin daga baya mahamud ya isa munzali mutun, d'an ma mahaifiyarsu jaruma mace ce ,ta iya sana'oi iri iri ,da hk ta raini ya'yanta , sai dai shi mahammud bai samu damar karatun boko mai zurfi ba asanadin matsananciyar rayuwa da suka riski kansu a wancan lokaci ,iyakarsa secondary school kawai ya tsaya wanda yayi a karamar hukumar koko ,
domin alokacin primary school kad'ai ce a kauyen nasu babu secondary, sai dai akai mutun wani gari, sai dai hkn bai hanashi jajircewa na ganin kanwarsa tasamu karatun ta kowani bangare ba. +

bayan mahammud ya gama makarantar gaba da primary, ahankali ahankali yake sanarsa ta kwadago ta hanyar kasuwanci,da farko dai gyaran agogo yake har Allah yasanya masa albarka ya bunkasa arzikinsa ya zamo wani abu ..
adalilin wannan sana'ar tasa yasa yayi suna ciki da wajen kauyen har ake kiransa da muhamud mai gyaran agogo, wanda duk inda zaka shiga a fad'in kauyen nemansa, matukar baka sanya lakaninsa ba ,sai dai ka gama karad'e kauyen babu mai ce maka yasanshi.

bayan wani lokaci sai mahaifiyarsu ta kamu da ciwo ajali ta sha jinya sosai ,suka rasa yadda zasuyi, gashi ciki da wajen kauyensu babu asibiti sai anjen wani gari mai kuruna dake makwabta taka da kauyensu ,idan akace za'a kai mutun asibin ma zai iya yiwuwa ya rayu domin kafin akarasa mararrabar garin mutun zai iya mutuwa , nawa nawa akayi akan idanunsu suka gani ,dan haka addua suke kullun Allah ya kawo musu d'auki daga gwanati mai ci alokacin data tallafi rayukansu ta gina musu asibiti da makarantar gaba da primary .
tunda mahaifiyarsu ta fara ciwon take barwa d'anta wasiyya a kullun bakinta baya shiru da mgnr diyarta mukarama ta kance "mahamud ko na mutu dan Allah ka kular min da 'yar'uwarka kaga bata da kowa sai kai," kai ne uwarta kaine ubanta domin zan tafi na barta acikin lisafi na kurciya Muhammad ka rike zumunci ,mukarama amana ce a hannunka ina son ka kaunaceta fiyye da komai ka kula da maraicinta da rayuwarta karka bari ta zubda hawayenta akan damuwa kowace iri ce ..

duk sanda mahaifiyarsu ta tasa shi gaba tana bar masa wasiyya ya kan share hawaye yace "ki daina furta wannan kalmar inna cuta ba mutuwa ba,sannan ba'a san inda rai yake ba, babu wanda yasan gawar fari ban da Allah, baki sani ba ko mune zamu rigaki mutuwa.

"kayya d'an nan dayake hk take kiransa kasancewarsa d'an fari , "wannan ciwon bana tashi bane, ni kaina ban sa ran zan warke ba har in tashi ba, domin wannan ciwon bai kamani da wasa ba, ni dai fatana ko na tafi na barku ka rike 'yar'uwarka da daraja kada ka auri macen da zata shiga tsakaninku, duk abinda, zata maka kayi hakuri kamata uziri, ku had'e kanku ka aurar daita ga mutumin da kasan zai riketa da daraja sannan ka inganta rayuwarta da karatun addini dana boko tak'arasa mgnr tana janyo numfashi da kyar wasu zafafan hawayen tausayin ya'yanta yashiga gangarowa bisa kuncinta. +

haka ma duk sanda mukarama ta kunsantota mgnrta kenan "mukarama ki rike d'anuwanki, ki rufa masa asiri a duk sanda hkn takasance, ki d'auke shi matsayin uba, domin hausawa sunce babban wa uba ne, ku rike zumunci atsakaninku, duk abinda kika samu nashi ne hk shima, ku zamo tsintsiya mad'aurinku daya Allah yayi muku albarka.

tunda inna ta kwanta ciwo bakinta baya shr da barwa mahmamud da mukarama wasiyya da amanar junansu ,su rike junansu , ciwon dai na ajali ne rana daya zazzabin ya tashi zanga zanga suka nufi asibiti Daita ,akan hanya kmr ko wani lokaci Allah ya amshi rayuwarta batare dataga auren ya'yanta ba.
bayan rasuwar mahaifiyarsu sun shiga damuwa kwarai da gaske kar ma dai mahamud yaji labari musamman idan yaga mukarama tana yawon kukan mutuwar innarsu ,duk sai tausayinta ya kamashi domin yasan dole kewar inna ta dameta, wani lokacin da kansa yake bata umarnin tashiga gidan mukotansu gurin hajara . +

hajara kawar mukarama ce tare suka taso tun innarsu tana da rai, basa rabuwa tare suke al'amurasu tare sukayi makarantar boko haka islamiyya ,idan bakaga mukarama ba tana gurin hajara akwai sabo da shakuwa mai tsananin atsakaninsu dama kuma can iyayensu aminan juna ne, byn rasuwar mahaifinyarsu, mahaifin
hajara na d'aya daga cikin wanda ya taimakawa rayuwarsu dan haka shima mahamud lokacin daya samu rufin asiri bai manta dasu ba hatta karatu hajara shi yake biya musu kudi tare da kanwarsa ,komai ya tashi yiwa mukarama ya kan had'a da hajara yayi musu tare irin karar dayake musu , yasa iyayen hajara suke matukar jin dadi sosai, kullun cikin yabonsa suke.

wata rana mahamud na gida yana wanke mashin dinsa sai kuwa hajara tashigo gidan da gudu tana huci ,sauran kiris tayi karo da machine dinsa, ganin mahamad tsaye yana kallonta sai tayi saurin komawa da wani gudun a kunyace ,ya kwalla mata Kira ta dawo da baya yace "zo nan sai kin gaya min dalilin gudun naki, bana hanaku irin wannan guge gujen ba, hajara tasa hannuwanta duka ta rufe fuskarta dashi tana dariya shima diriyar yayi kana yace "wai hajara in tambayeki shin me yasa kike jin kunyata ne?
tayi shiru kanta a sunkuye yace "ko nayi miki kama da surukinki ne?
nan ma shr tayi yace "ni na lura duk sanda kika shigo gidan nan bakya sakewa ko kuma tsorona kike ji.?
hajara ta girgiza kai yace "to me yasa bakya iya kar'bar abu agurina sai dai mukarama ta kar'ba muku?
nan ma shiru tayi mukarama ce ta fito daga cikin d'akin tana dry,mahamud ya kalli mukarama, sannan yace"wai me ya sa kawarki take jin kunyata?

mukarama tace "inajin kodan taji goggo tace.... ya d'an dubeta da sauri yace "me goggon tace ?
mukarama tayi shr tana kallon hajara tana dry kuma taki k'arasawa, dayake yasan halin shirmensu kurun sai ya rabu dasu yace "ku wuce kubani guri Allah yasa na sake ganin kuna irin wannan guje gujen sai kace wasu kanan nan yara.

ranar wata litinin da safe mahamud yashiga gidansu hajara domin ya gaida su, hajara najin muryarsa taki fitowa daga cikin d'akin, byn sun gama gaisawa da mutanen gidan baban hajara yace"wai shin mahamud kai har yanzu baka fara tunanin aure ba ne?
tunda Allah ya amshi ran mahaifiyarku ,ai sai ka d'aure ka nemi abokiyar zama kodan ka ragewa 'yaruwarka kewar innarku data rasa.

yace "wallahi baba nima nayi wannan tunanin to sai dai ina kan dudubawa in samo wacce ta mallaki kanta, baba yace "naso ace ina da 'ya babba da zan kulla zumunta atsakaninmu amman tunda banida ita ga hajara nan na baka, sai a wanketa akai maka.

abin yabawa mahamud mamaki ya danyi driya kana yace "lallai baba kanason ka had'a rigima kasan kuwa yadda hajara take tsananin jin tsorona ?
bama haka ba baba yaushe za'a ce za'a yiwa hajara aure yarinyar da sai ma yanzu zasu kare primary, nima kuma dakake ganina karatu zan koma.

mahaifin hajara yayi dry sannan yace" duk wannan bawani abu bane in dai kana sonta tunda kana son bokon itama sai ka barta tayi karatu agidanka.
mahamud ya sake yin dry"amman baba baka ganin irin shirmen da zasu ta min acikin gida.

"duk babu komai sai ka jure har zuwa lokacin da zasu yi hankali mahamud ya d'an dubi babar hajara yace "kin dai ji goggo ,baba yana neman ya had'ani da rigima.
cikin murmushi tace "to idan haka ne ai nice na fara furtawa kai dai tunda ance anbaka ba sai kayi fatan alkhairi Allah ya tayaka riko ba, babu yadda mahamud ya iya dan haka yace shikenan goggo na karba Allah ya rika min .
a daidai wannan lokacin mahamud yasamu gurbin karatu a jamiar d'an fodio dake jahar sokoto inda zai karanci kasuwanci.

zance aurensa kuwa da hajara abu kmr wasa, abu ya kankama yana da shekara biyu a jimi'a aka soma shirye shiryen aure cikin kankanin lokaci aka saka hajara lalle agama biki aka kaiwa mahamud amaryarsa .
ba k'aramin raino mahamud yayi ba ,kafin hajara ta zama cikakkiyar mace ba, ya dai sha shirmensu ita da mukarama, haka nan ya dage da kyautata musu kullun yana tsaye akansu komai suke bukata zai siyo ya kawo musu da yake yara ne masu hankali da natsuwa sukayi zamansu lafiya su fad'i tare su tashi tare suna harkarsu su duka suna jin dadi zama da junansu ahankali ahankali rayuwarsu ta cigaba da gudana cikin jin dadi har sanda mukarama tasamu karatu a makaranta kwana dake aleiro government girl's comprehensive secondary school aleiro, yayinda hajara kuma ya samammata makaranta anan cikin garinsu, dan Allah ya tallafisu ya amshi rokonsu yasa aka bud'e musu jeka ka dawo. 1

kullun zata makaranta idan ta tashi ta dawo gidan mijinta, tayi girki da sauransu hidimomi gida, rayuwarsu dai gwanin sha'awa in kaga yadda mahamud yake tattalin hajara sai ka rantse wata shararriya soyayya sukayi kafin aurensu.

shi dai mahamud mutun ne mai son mace taji dadi gashi da busha sha, ga sakin fuska da saukin kai ,hajara dai ta samu soyayya da kulawa agurin mijinta, kullun babanta na saka masa albakar saboda ya rike amanar da'aka bashi kuma gashi da zumunci domin mahamud ya maida iyayen hajara tamkar nasa komai zaiyi ya kan nemi shawararsu haka suka cigaba da rayuwa ganin sha'awa .
ta bangarensa karatunsa ma bashi da wata matsala komai na tafiyar masa yadda yakamata idan ya dawo hutu kuwa zai kama kasuwancinsa na siye da siyar, sannan ya bud'e k'aramin shago a kofar gidansu wanda yake gyara agogo.

******
lokaci zuwa lokaci idan mukarama tazo hutu hk samari ke yi mata caaaa amman sam mahamud ya kekashe kasa yace "bai san da wannan zance ba, karatu zatayi duk wanda yaji zai iya jiranta to ya jira ,wanda ba zai iya ba, ya k'ara gaba ya nemi matarsa, cikin haka ya kammala da karatunsa
,kasuwancinsa ya k'ara bukasa, komai yana gara masa domin zuwa yanzu ya fantsana cikin duniya neman arziki, dan har sun bar kauyensu zuwa cikin birnin ilorin state .

byn wani kankanin lokaci sai gashi ya zama matashi attajiri dake da mallakin gidaje, ya sayi motaci baya ga yaran kauyensu daya Diba suke karkashinsa.
zuwa lokacin yana da yaro daya mai sunan Ibrahim ,suna kiransa da akram da yake sunan mahaifinsa garesa ..

mukarama ta tagama karatunta na gaba da primary, ta zama cikakkiyar budurwa sosai gata da kyau da gogewa da iya tsara kwalliya ,cikin wannan lokacin ishaq abokin Muhammad wanda ya kasance abokin kasuwancinsa ne ya dawo daga kasar maleshia akan harkan kasuwanci da karatunsa .

ishaq hadadden matashi saurayi ne tsayaye mai zati da haiba uwa uba naira ta zauna ajikinsa asalinsa dan Kano ne amman babu inda baya shiga adalilin kasuwanci.

wata rana ya kawowa Muhammad ziyara,inda Muhammad yace "mukarama ta kawowa abokinsa abun motsa baki,tashigo parlour'n cike da natsuwa da kamewa uwa uba kunya, ai kuwa ishaq yana d'aura idanunsa akanta yarasa tsukuni amman dayayi wani tunani sai yayi saurin kawar da abinda yaji akanta, ta ajiye tire ishaq yace "ga leda nan ta wuce dashi tsarabarsu ce aciki, sam mukarama taki d'auka, ya d'auka ya mika mata nan ma taki amsa yace" haba kanwarmu ina ganinki mai kalar wayyayu, a wannan zamanin yaushe ake kunya hk?
mukarama ta juya akunyace zata fice daga parlour'n, 'yar drya Muhammad yayi yace "to in kin shiga ki turomin hajara kawai ,tana fita ishaq yace "amman wannan wani irin kunya ce hk sai kace ba yar zamani ba?
alhj Muhammad yace" ina ruwan mukarama haka Allah yayita komai nata sai ta had'a da kunya yarinya ce mai tsananin kawaici babu ruwanta.
yace "da kyau hk nake son naga mace nada kawaici da alkunya a dukkanin al'amuranta da ganin kanwar tamu mijinta ya dace kwarai ya fad'i hk saboda tunaninsa ko tana da aure.

alhj Muhammad yace"kuma ka gani bata da miji har yanzu bata tsaida miji ba karatu take domin ina da burin akanta,ina son na ingata rayuwarta da karatu boko domin a dama wannan duniyar daita, shiyasa duk masu kawo hari nake katse masu hanzari har sai ta gama, yanzu haka tana matakin diploma .

ishaq ya d'an dubesa a razane domin yasan asaninsa mutane karkara haka ,basu fiyye barin yaransu su jima hk batare da yin aure ba ....
"gsky abokina kayi nmj k'ok'arin gurin ingata rayuwarta ,yanzu dai kace babu kowa akasa masu neman aurenta?

"babu kowa ina suka ga fuska, ai sai sunga fuska tukun zasu zo, ni dai burina tayi karatu mai zurfi ta yadda zata taimaki al'umma da ita kanta, nan dai suka bar zance suka shiga hirar kasuwanci dayake daman harkar kasuwamci ne ta had'asu har suka zama abokai, acikinsu duk wanda wata harka tashigo hannunsa daya san za'a samu alheri y kan janyo dan'uwansa ciki, su samu alkhairi tare kasancewar dukansu ba masu kyashi ko bakinciki bane ,kowa yana k'aruwa da kowa suna harkar arziki tare gwanin sha'awa.

tunda ishaq yakoma gida sai ya kasa samun sukunin zuciya duk yadda ya runtse idanunsa mukarama yake gani tana yi masa gizo ,haka nan abin mamaki jiyayi gbdy ya tsinci kanshi da matsanancin kaunar mukarama ,ganin dayayi mata ya gigita kwalkwaluwarsa ,sosai yarinyar ta rikitashi ,ya rikice akanta har tunaninta na neman hanashi sukuni yin barci, shi kansa sai juya al'amarin yake aransa yadda farat daya ya gigice akanta gashi dan'uwanta na da buri akanta, dan hk ya danne abun aransa yacigaba da hakuri ,haka soyayar mukarama yayita cinsa arai har sai da aka samu wasu yan watani.
************
ran nan dai ishaq ya kasa hakuri adalilin soyayyar mukarama da kullun take sake huda kahon zuciyarsa, dan hk a zaunen da yake agaban mahamud yasoma maganar yadda yake son mukarama.
mahamud yayi shr yana sauraron abokinsa har yagama zayyana masa irin kaunar dayake yiwa mukarama,Muhammad yace "naji dadi kwarai kuma ina matukar farinciki da wannan bayani naka ,sanin kanka ne kafi karfin komai agurina ,zai yi wuya ka nemi

2 / 53