Author : Aysha A Bagudo Category : Complete Novels
shi kuwa bunayya da sauri ya bi bayan d'aya daga cikin likitocin yana tambayarsa ,yanayin jikin umminsa ,suna tafiya doctor na yi Masa bayani ,har suka shiga cikin office dinsa, ya dan juyo yana dafa kafadar bunayya "ka kwantar da hankalinka inshallahu zata samu sauki, ka dinga had'awa da addua zamuyi mata allurar yanzu dan ta samu relief, bunayya yayi jugun hawaye na kwarara akan kuncinsa , da kyar yayi karfin halin juyawa batare da ya cewa likitan komai ba, ya bar office din kai tsaye d'akin d'a'a kwantar da ummi ya nufa ,yana shiga ta bud'e idanunta tana ganin shine, ta d'auke kanta zuwa wani bangare tare da cewa "kace masa kar ya k'araso gareni banason ganinsa ,ya bar d'akin nan bana son ganina acikin idanuna , karaf maganarta ta shiga cikin kunnuwanshi .
tun kafin Wanda aka bawa sakon ya fad'a masa , ya tsaya daga inda yake yana duban ummi da har lokacin kuka take ..
"Ummi ....
Ba..bana son jin komai daga bakinka ta k'arasa maganar tana sauke numfashi da kyar "
Hannu abi ya d'aga masa al'amun ya tafi kawa ..
Ahankali ya juya jikinsa a matukar sanyaye ya fice ya nufi harabar hospital din yana jin wani irin kuna acikin zuciyarsa , kai tsaye bayan mota ya bud'e ya shiga ya zauna yana jin wani irin bakinciki ,batare da bata lokacin ba direba ya yiwa motar key ,suka bar hospital, zaune kawai yake a bayan motar amman shi kad'ai yasan abinda yake ji ,shi kad'ai zai iya misalta halin tashin hankali da yake ciki.
da fari baiyi tunani zai damu a dalilin cikin jikin muwaddat ba domin ganinsa haka shine sakamakon masu hali irin na iyayensa ,sai yanzu ya fahimci abun ba haka bane, suna shigowa gidan ,ya nufi part din umm domin ganin halin da muwaddah take ciki ,can karshen gadon ummi ya iske kwance tana jujjuya Kai had'e da rike kasan mararta ,ya k'arasa gareta da sauri yana k'ok'arin kamota jikinsa ta goce "karka ta 'bani ... kana ta yunkura ta mike tsaye ta soma tafiya.
Da kyar take takawa ta fito tana layi hakan yasa ya biyo bayanta da sauri yana Kiran sunanta "muwaddat Ina zaki cikin wannan hali ?
Ta juya ahankali domin fad'a Masa bakar magana jiri ya kwasheta tayi kasa zata fad'i cikin rud'ewa ya kamota jikinsa ya d'auke cak dan ganin jini a bin kafafunta , part dinsa yayi daita , da kyar ya samu jinin daya soma bin cinyoyinta ya tsaya amman ya Sha wuya sosai, yanzu wani irin son cikin ne ya dawo masa sabo fil ....
Allurar bacci yayi mata domin tasamu natsuwar zuciya, amman ta burkice masa tana zuba masa ruwan bala'i ..
Duk yadda yayi k'ok'arin ya shawo kanta ta fahimceshi amman abin yafi karfinsa, sai faman had'ashi da Allah take ya rabata da ciki ,gabad'aya ya sake shiga rudu ..
yana kallonta ta fice daga bangarensa shima ya biyo bayanta anan suka ci karo da idanun baba mai gadi kallo daya yayi masu ya kawar da kansa yana Allah wadai da masu hali irin su "da al'amun uwarsu bata da lafiya, amman hakan bai saka sun hakura da juna ba, wannan wace irin maseefa ce haka?
yayi maganar a kasan ransa " ko yake zuwa yanzu ya daina ganin laifin su sakacin iyayensu ne ..
Binta bunayya ya shiga yi har ya karaso inda take bai tsaya wata wata ba ya d'auketa ya sabata a kafad'arsa yayi d'akinta daita ,ya kwantar yana mata sannu , sannan ya koma cikin part dinsa, har kusan magariba yana d'akinsa kwance bai tashi ba tunani Kashi da Kashi ke dawainiyya dashi, jifa jifa ya kan Kiran abi ya tambayi yanayin jikin ummi ,sannan haka ya dinga zariya tsakanin part dinsa zuwa na ummi domin duba lafiyar muwaddat..
Karfe biyun dare muwaddat ta farka daga baccin daya d'auke ta ,yana zaune akusa daita ya zuba mata ido, hannushi cikin nata jin motsin datayi ne yasa ya gane ta farka da sauri ya mike yana Kiran sunanta muwaddat, sai ma ta rufe idanunta wasu zafafa hawaye na zubo Mata babu irin maganar da bai mata ba amman ta shareshi band'aki ya shiga ya had'a mata ruwan mai d'an dumi zuwa yayi zai d'auketa duk da Jikinta babu kwari sai data fixge tana zabga masa uwar harara "bana son jin hannunka ajikina na tsaneka ka rabu dani ..
Kuka ne yaci karfinta, jin kukan nan yake har cikin zuciyarsa ya kasa ce mata komai "
Can kusan minti goma yace "plz muwaddat kina bukatar kulawa da taimakona a daidai wannan lokacin ..
"Banason ko wani iri taimako ne daga gareka ka barni na mutu na huta da wannan bakinci ," komawa tayi tayi kwanciyarta, har kusan asuba yana fama daita tana jin Fitarsa matsalaci ....
Koda ya dawo ma kusa daita ya tsaya ,ban da hawaye babu abinda idanuwanta ke zubarwa cikin sanyayyiyar muryarsa yace "Dan Allah muwaddat na rokeki ki bar kukan nan haka kada yayi miki illa "
"Yaya kuke son nayi, gaki tashin hankali gurinki ,ga matsalar ummi ,Ina bukatar kowane daga ciknku arayuwata ,bana son ba rasaki "kiyi hakuri muwaddat ki d'auka kaddararmu ce tazo haka ...
Gefe ta juyar da kanta "ka rabani cikin Nan ni banaso .......
Shiru yayi kawai had'e da kafeta da tsumammun idanunsa ,yau tazo Masa da abubuwa dayawa tashin hankali da rudani , gabad'aya duniya ta cakud'e mashi waje d'aya ba ta bangarenta ba, bata bangaren umminsa ba ,bai ta'ba sanin haka tashin hankali irin wannan daya ke ciki yake da ciwo ba , "ya zai yi da kaddara data afka masa?
" d'an da zai fara samu a duniya shine yazo ta wannan hanyar ...."
Cike da muryar kuka tace "dan Allah ka rabani da cikin tun kafin ummi ta dawo ,na had'aka da Allah ka ci ....
"Dan Allah dan annabi malama ya isheki "
"enough muwadda "
" Wai ma me kika d'auke ni ne ?
"Mahaukaci ko me ?
"Nasan na aikata zina dake na tsawon lokaci har ga sakamakon nan ajikinki ,amman wallahil azim bazan iya zubar da wannan ciki ba ....
"Bazan iya d'aukar wannan zunubin ba ...
"bazan iya kashe kiyashi ba ,bare gudan jini ...... I can't muwaddat Yana gama fad'ar haka ya juya fuuuuuuuuuu cikin tashin hankali...
Mmn sudais
MUWADDAT PAGE 39
page 39
dan baka hanzarta zubar min da cikin
nan ba ,zan gudu, dan kuwa zaku nemi
gabad'aya ku rasa, bai tsaya ba, yace"ki fi
ruwa gudu, idan kin tashi gudun ki tafi
lahira karewarta kenan, ciki ne dai ni
muhammed auwal bazan zubar ba,ba
kuma zan saka hanunana ba,na dai d'auki
zunubin aikata zina ,amman batu na
zubda ciki
bai k'arasa maganarsa ba ya k'arasa
ficewa daga d'akin, aiko ta sake rushewa
da kuka..
Kai tsaye bakin get ya nufa inda yana
zuwa ya tsaya ,a kan baba mai gadi ,yana
bashi umarni "baba ka tsaya kan aikinka
sosai ,acikin gidan akwai muwaddat kamar
yadda kasani ,duk lokacin dana nemeta na
rasa abakacin Aikinka, kuma wallahi tallahi
kaji na rantse kotu ce zata rabumu .. .
yana gama fad'ar haka ya juya ya nufi inda
motar ummi take parke
Bakin baba mai gadi na rawa yace " Ina ai
bama za'a yi i haka ba ,ai tunda ka fad'i
haka, an gama.
aranshi kuwa cewa yayi tsinanun ya'ya
kawai Allah yasa karku kashe iyayenku da
fitinarku, yana nan tsaye har sanda
bunayya ya tadda mota,shi kuma ya bud'e
mashi get ya fita, sannan ya samu guri ya
zauna akan farar kunerarsa ya kunna radio
ya soma sauraron labarai ..
Ahankali yake tuki yana zance zuci ,har
sanda ya kawo hospital inda mutanen da
suka san shi d'an madam ne suka shiga yi
masa, ya mai jiki,shi kuma yana basu
amsa da alhamdullahi, adaidai bakin
Coridon da zai Kai ka dakin da ummi take,
suka had'u da abi wanda ya dawowarsa
kenan daga massalaci .gaishe shi yayi
had'e da tambayarsa jikin ummi ?
Alhamdullahi ka godewa Allah jikin
umminka yayi sauki sosai ,zuwa anjima
nan zamu dawo gida yaya muwaddat din
take, hope babu wani Abu da ya sameta
jiya?
"Lafiyar nan dai da sauki abi ,tare suka
k'arasa cikin d'akin abi nayi masa nasiha
koda suka isa d'akin ,sun iske ummi ta
idar da sallah tana k'ok'arin mikewa da
kyar ,sai dai har lokacin kallo d'aya zaka
mata kasan tana cikin tashin hankali da
damuwa mara misaltuwa ,kallo d'aya tayi
masa ta d'auke kanta daga garesa ta
koma kan gado ta zauna ya k'araso gareta
yana kok'arin yi mata sannu cikin
sanyayyiyar muryarsa ,amman Sam taki
amsa masa illa ma sake
tamkar wace aka aikowa da sakon
mutuwa ,abi ne ma ya d'an bashi kulawa,
amman shi ba wannan kulawar yake so ba
shi yafi son ummi ta amsa masa, bazai
iya jurar fushin umminsa ba ... haka ya
cigaba da tsayauwa agurin yana bata
hakuri har karfe takwas ta bugu ganin ta
mike tayi kwanciyarta akan gadon marasa
lafiya ya juya ya tafi .
had'e rai datayi
Har yaje asibitin ya dawo damuwa ce cike
da zuciyarsa ,duk wanda ya gansa yasan
yana cikin matsanancin 'bacin rai bai sake
neman inda muwaddat take ba yayi
zamansa a bangarensa ,baba mai gadi
kuwa ya kasa ya tsare abakin get.
Bayan sallar azahar yaji hon din shigowar
mota, haka nan jikinsa ya bashi abi ne
suka dawo ,dan haka ya tashi ahankali ya
isa jikin window tare da yaye labule yana
lekewa, tabbas shi din ne ya hango har da
umminsa gabansa ne yayi wani irin mugun
fad'uwa da karfin gaske.
ya dawo ya canza kaya zuwa jallabiyar
brown colour sa'banin d'azu da yake sanye
da vest da boxer, ya fito yana taku cike da
sanyin jiki ,koda ya fito har sun shiga cikin
gidan shima yasanya Kai ,inda ya iske
binta mai aiki sai faman jerawa ummi
sannu take tana amsawa da kyar shima
sannun yashiga yi mata ..
Ganin binta tsaye ne yasa ummi taki korar
bunayya,da binta zata tafi ummi tace "ina
muwaddat?
"Ina ganin tana d'akinta"
"Je ki kice mata tazo yanzu"binta tace
"tam had'e juyawa ta bar parlour'n.
binta na barin bangaren ummi tashiga
Zuwa bunayya ruwan bala'i ta inda take
shiga bata Nan take fita ba abun har yaso
bawa abi mamaki dan shi tunda yake bai
taba sanin mukaramarsa na da irin
wannan halin ba sai wannan lokaci
"ishaq ka fad'awa d'anka...ka fad'a masa
banason ganinsa arayuwata da duk inda
nake ,har ya gama iya rayuwarsu kar ya
kusanto inda nake bani bashi ..
"Wallahi matukar baka bukatar nayi wani
mummunar furuci akansa ya fad'a masa
kiyayi zuwa inda nake ,ta k'arasa maganar
tana hakki sama sama...
Alama abi yayiwa bunayya ,daya bin
umarninta yasan duk wannan abun datake
na wani lokaci,da kuma bacin rai ,bacin
rai kuwa babu abinda baya sawa
Bunayya wanda idanunsa suka rikid'e
sukayi ja tsabar tashin hankali da yake ciki,
ya juya da kyar yake daga kafafunsa ya
fice daga parlour'n.
Yana fita ummi ta fashewa da wani sabon
kuka.
Jiki a matukar sanyaye muwaddat ta shigo
parlour'n tamkar gazar da kwai ya fashewa aciki ,kanta sunkuye a kasa ,dan
bazata iya duban idanun ummi, ba haka
ma abi ,ummi ta d'ago ta dubeta cike da
tsantsar 'bacin rai da nadamar rikonta
datayi arayuwa ,datasani kam tayi shi
babu adadi ,data san haka zata zamo
mata arayuwa wallahi da batayi ganganci
d'aukota ba, ta barta tare da iyayenta
ganinta yanzu yasa kukanta ya tsananta
saboda wannan tashin hankali yasa tayi
wata irin katuwar rama wanda yasa kallo
d'aya zaka mata kasan tana d'auke da ciki
,muryar ummi a sarke tace "yanzu
saboda Allah da annabi kun kyauta min
kenan, barin ke muwaddat da kika biye
masa, ke fa macece.. ?
"da girmanki da hankalinki da tunaninki
kika biye kaninki suka aikata zina..
Abi yayi saurin runtse idanunsa kana ya
bud'e su yana nunawa muwaddat gurin
zama saboda ganin yadda jikinta ya soma
"mai yasa kika biyewa kaninki kuka aikata
mana haka muwaddat?
"mai yasa muwaddat?
"ko kin manta matsayinki ahalin yanzu kin
tsaida mijin aure ,har ma da sa ranarsa
akanki?
"wai a ina ma kuka yi wannan cikin na
tsawon wata biyar bamu sani ba?
ummi ta mike tayo kanta gadan gadan abi
ya tsaidaita ta hanyar rikota ..
"ka barni nayiwa wannan shegiyar
yarinya dukan mutuwa ,da girmanki
muwaddat da hankalinki da tunaninki idan
bunayya yaro ne ke yarinya ce ?
"'shekara ashirin da biyar zuwa da shida
amman kika biye masa kika ruguza
tarbiyar dana baki na tsawon shekaru,
"yanxu me kike son duniya tace akaina?
ta k'arasa mgnr tana kuka tana nunata da
yatsan hannuta "hakika kun cuceni kun
cuceni.. kunci amanata ,kun yaudareni
yanzu ni na cancaci wannan tozarci
muwaddat, na amince dake, na baki
dukkanin yardata, ban taba tunanin zakiyi
min haka ba "why muwaddat?
why why why!!!
kika biye wa son zuciyar auwal?
"wayyo Allah ni mukarama, yau ni tawa ta
sameni mai zancewa d'anuwana ya
fahimceni..?
abi ya kamota ya zaunar daita agefenshi
"kiyi hkr mukarama ,kinsa Baki da lafiya
zuciyarki na bukatar natsuwa ki d'auka
haka tamu kaddaro tazo, babu yadda
zamuyi bamu isa mu gujewa kaddararmu
ba lahaula wala kuuwata illa billah, babu
tsimi babu dabara duk abinda Allah ya
tsarawa bawa to babu tantama sai abun ya
sane shi ki yawaita furta kalmar inna lillahi
wa inna ilaihi rajiun acikin zuciyarki...
muwaddat ta taso daga inda take zaune
jikinta na rawa, ahankali take d'aga
kafafunta har ta K'araso ta durkushe
agabansu' abi dan girman Allah ka bar
ummi ta zarta da duk wani hukunci data
gadama akaina,na cancaci fiyye da duka
agurin ummi akan abinda nayi, tayi min
duk abinda zatayi koda kuwa ta kama ta
kasheni ne, ka barta matsawar zata huce
takaicin abinda nayi mata.
ta juya ta fuskanci ummi idanunta taf da
ruwan hawaye suna zuba akan kuncinta
umminah kiyi hkr dan girman allah ki yafe
mana,duk da ba ke ce kika kawoni duniya
ba amman idan kika tsine min sai
tsunuwarki tayi tasiri akaina, dan Allah
ummi ki taimaka ki taimaki rayuwata ki
rabani da wannan ciki koda kuwa mutuwa
zanyi na gwan
wannan cikin shegen dake jikina...
haka akan dai na haifi
daga ummi har abi saurin runtse
idanuwansu sukayi da saboda d'acin
kalmar data fad'a, "first jikan da zasu samu
a duniya shine yazo mata ta wannan
hanyar da bata dace ba, ita kuwa wani irin
kuskure ta tafka arayuwrta?
"ummi wallahi nayi danasani arayuwata.
abi dan Allah kabawa ummina hakuri kace
ta yafe min wallahi sharrin sheidan dana
zuciya, wallahi bazan sake ba na tuba abi
ta k'arasa maganr cikin kuka tana had'e
hannunwanta duka ..
shiru ne ya biyo baya sai sheshekan kukan
ummi da nata dake tashi ahankali "baza'a
zubar da cikin jikinki ba muwaddat ,za dai
musan abinyi tashi ki shiga d'akinki abi ya
fadi hkn yana kallonta...
ta yunkura da kyar ta tashi tashiga jan
kafafunta da suka mata nauyi ta nufi
d'akinta tana kuka, tana shiga ta ta fad'a
kan gadon tana sake fashewa da wani
kukan "na cutar da kaina,na cuci
rayuwarta yau nice d'auke da cikin shege"
wayyo Allah ni muwaddat ina zan kai
wannan kayan abun kunyar.. .
..?
zumbur ummi ta mike tashiga zagaye
parlour'n tana zance zuci" dan dole tasan
abunyi kafin kunnuwan mutane gari dana
danuwanta suji wannan abun kunyar da
aka aikata acikin gidanta ,dan dole ta
nemawa kanta mafuta, "to mai zanyi ?
'mai zanyi akan wannan cikin..? Ta
tambayi kanta.
"dole na samo mafurtar abinyi, shiru tayi
sannan ta nufi d'akin cikin sauri abi yabi
bayanta shima atare suka Shiga d'akin
"mukarama yanzu Yaya zamuyi?
ta tako ta fad'a kirjinsa tana wani irin kuka
mai ban tausayi •ban sani ba ishaq.
bansan abinda zamuyi ba. amman nafi
tunanin mu zubar da cikin nan kawai shine
kwanciyar hankalinmu.
"wannan ba shine mafuta ba mukarama ,
illa zunubi da zamu d'aukarwa kanmu,
muyi hakuri mu rungumi kaddararmu data
samemu wannan abun daya faru duk
laifinmu ne,kuskurenmu ne mukarama,
tunda yaron nan tun farko ya nuna mana
aure yake so, ya bini ya biki yayi iyakacib
kokarinsa amman muka kekashe kasa
muka ki yarda •mu kace karatu 'yanzu
ga illar abinda son zuciyarmu ya jawo
Mana, da'ace mun barsa tun farko yayi
aurensa da duk haka bata faru damu bae
kalu bali ga iyaye masu hali irin namu
,mukarama ni dake muka tsunduma
yaranmu cikin wannan mummunar
rayuwar _
•wa man kaddarallahu haqqa kadarihi*
ki yarda da wannan kaddarar data
samemu mikaram daman duk muslimi
dole ne yayi imani da kaddara mai kyau ko
akasinta, ni dai na yarda da kaddara data
fada mana kuma na amsheta da hannu
biyu biyu wannan shine sakamakon iyaye
irinmu masu biye son zuciyarsu
zare jikinta tayi a jikinsa ta koma ta
kwanta akan katifa, numfashi take
saukewa ahankali ahankali kana ta runtse
idanunta gam ta dinga jin wannan bakon
aliamarin dake faruwa daita tamkar a
almara ko wani shirin film, itace zatayi jika
ta wannan hanyar?
"anya zata iya wannan hakuri ta bar cikin
nah kuwa?
"kai dole tasan abunyi, Cire cikin zatayi
alabashi daga baya ,sai a yi musu aure ,
Udata bar wannan abun kunyar azo ana
zaginta a gari wallahi gara ta Cire mata
. koda a boye ne batare da sanin daci da radadi tana jin bazata iya jure
wannan abun kunyar data aikata da
kaninta ba, tana jin tamkar tattara inata
inata tabi uwa duniya. ko ta kashe kanta
"karki kashe kanki ki mutu kafira ga zunubi
zinar da kika aikata ga na kisan kai, gara ki
Shiga uwa duniya
take ta amince da wannan shawarar da
zuciyarta ta bata"cikin sauri ta karasa inda
jerin akwananta suke ta dauko karamar
ciki ta isa gaban wardrobe dinta tashiga
dibar kayanta da abubuwan amfaninta
tana zubawa aciki..
can bangaren ummi dake kwance akan
gadonta tana faman joyi daga karshe ta
yunkura ta mike jikinta tmkr ba nata ba, ta
zauna tana sake goge hawayen daya
gagara tsayawa a idanunta Ita isa bakin
bayi da niyyar Shiga ta dauro alwala .cak ta
tsaya kirjinta na wani irin harbawa can
kuma tasoma jiyo motsin haka nan
zuciyarta lace ta leke taga me ke faruwa .
cikin sanda ta fito ahankali tana taka step.
gabanta yayi wani irin mahaukaci bugawa
da karfln gaske sakamakon abinda
idanunta yacin karo dashi , muwaddat ce
ke kiciniyar bude kofar babban parlour'n
da niyyar fita.
Wata uwar razananniyar Kara ta Saki
hade da jero sallati ,wanda janyo hankalin
abi ya fito daga d'akinsa a firgice Yana
dubansu muwddat kuwa wani irin tsalle
tayi hade da jifa da akwatin hannuta
,jikinta ya kama rawa take kuma dan
cikinta yasoma motsi sosai abinda bata
ta'ba ji ba kenan a tun samuwarsa..
•me nake shirin gani yau ni mukarama?
"me kike Shirin aikatawa muwaddat
"ina zaki da akwati?
muwaddat ta rushe da kuka jikinta na rawa
. •tambayarki nake nace ina zaki ?
"Kar dai guduwa zakiyi muwaddat ki barni
cikin wannan tashin hankalin? tasoma taka
step biyu biyu ko ganin gabanta batayi har
ta k'araso gabanta tace •guduwa zakiyi ki
barni ko me?
jin tayi shiru taki amsa mata tambayoyunta
yasa tashiga yaryarfa mata mari •guduwa
fa kike shirun yi muwaddat?
"yanzu daman zaki iya barin?
"zaki iya guduwa ki barni cikin damuwa ?
" idan kin gudu ina zaki eye?
Ki fada mun ina zaki tana tambayar ta tana yarfa
Mata wasu marurukan daga karshe ta rufe ta da duka
"Gara na kashe ki da hannu na binne gangar jikin ki
akan ki gudu ki Shiga k'
wannan shine kare na farkO da ta
SMaya hannunta aiikin a tun
,duka tayi mata har
sai da abi ya tsaidaita tukLJnM1
kasa tana kuka •guduwa take Son yi ta
barni ishaq Cikin tashin hankali "
miki daga
• kike k Ok'arin kinsa
jurar rashinki ba, tasorna
gindi Z•JWa inda di take
durkushe gwiwaWinta tana ta
ajikinta •karki barni