Advertisements
Chapter 3 Reading MUWADDAT by Aysha A Bagudo BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

MUWADDAT by Aysha A Bagudo

Author :  Aysha A Bagudo Category :  Complete Novels

Chapter   3 / 53

6K to 9K   out of 157.9K words

wani abu a wurina na hanaka, musamman ma irin wannan alfarma ta aure, to amman akwai wani hanzari ba gudu ba kmr yadda kasani, bazan aurawa mukarama mijin da bazai barta tacigaba da karatunta ba, matsawar ka amince zata cigaba da karatunta agidanka shikenan na amince kaje ka nemi yardarta matukar ta amince da kai zan aura maka ita.

ishaq ya sauke naunauyen ajiyar zuciya kana yace "wannan ba wata matsala bace ni kaina har yanzu akan karatu nake kasan da haka ,domin lamarin kasuwancinmu na bukatar ilimi mai zurfi,bugu da kari ilimin mace nada matukar mahimmanci arayuwa.

"haka ne kam Allah yasa mu dace kana iya turo magabatanka idan ta amince , ishaq yace "ameen had'e dayiwa abokinsa godiya " domin sosai yaji dadin lafazinsa mahamud na gama fadar hk ya bari parlour'n.

ishaq ya nemi ganawa da mukarama ,byn tashigo parlour'n suka dan yi shru kad'an sannan yakira sunanta "ko kinsan zuwan nawa na yau dominki ne sabanin sauran lokuta?
ta d'an kalleshi cikin natsuwa, yayinda ta zuba masa idanu tana kallonsa da sauraren abinda zaice dan gabad'aya zuciyarta ta matsu da son jin abinda ke cin ransa akanta, domin itama tana jin wani abu a game dashi .
yacigaba "hakika mukarama dazaki min alfamar dana dan gutsara miki abinda ke cin raina a game dake, Allah yasamin tsananin kaunarki tun ranar farko dana d'aura idanuna akanki dayake nasan ba aure yayanki zai miki a wannan lokacin ba sai nayi kokarin danne sonki cikin zuciyata har sai yanxu ,a yanzu dai ina gabatar miki da kaina amatsayin wanda yake son aurenki amman menene ra'ayinki akaina ?
mukarama dai tayi shiru saboda batasan amsar dazata bashi ba, domin mutumin yana yi mata kwarjini ganin bata da niyyar bashi amsa yace "haba mukarama ya kikayi shr ai gara kiyi magana shi sha'anin aure ai ba'a yinsa da wasa zan so jin ta bakinki koda bakya sona barema bana fatan haka nafi son kiyi min alfarma bisa soyayya kar ma ki tsaya duba alaka don ba itace tasani sonki ba.

" kyawawan halaiyenki da dabi'unki na kirki ne suka janyo zazzafar kaunarki ,ki taimawa rayuwar wannan tsohon tuxuron ki aureshi domin idan kika ki aurensa ina tabbatar miki hk zai k'arasa sauran rayuwarsa batare daya ajiye iyali ba.

mukarama ta cigaba da yin shiru sai dai wannan karon kanta na sunkuye ,murmushi yayi saboda sanin halinta na kunya "haba zuciyar ishaq ki dan yi min magana ko naji dadi "tayi dariya amman batace komai ba yace"kenan dai ana son ishaq ya hakura," mai yiwuwa ina da wani abun da baza a soni dominsa ba? +

sai a lokacin ta girgiza kanta, yace "ni kam muddin ba magana ki kai ba, gani nake ban canci asoni ba ,shi yasa kika barni da kokon barana a hannu, ai sauran maneman ba hk ake musu ba, ko kuma ko dan anga ni babban yaya ne kike ganin nayi miki tsufa?

maganarsa ta bata dariya har ta sa ta d'ago kanta da sauri suka dubi juna sannan tace "ko kad'an ba haka bane, ni dai aguna baka da wani aibu da kowace irin mace zata kika ,sai dai abunda nake son kagane ban taba yankewa kaina hukunci ba sai dai yayana ya yanke min.

"idan ta wannan bangare ne mugama magana da yayanki har ya amince har ma da sharadinsa nason ki cigaba da karatunki byn aurenmu, na kuma ji na gani na amince da hakan ,saboda ina matsanamcin sonki "duk da haka ni dai nayiwa kaina alkwarin komai zanyi sai da amincewarsa.
"da kyau kinga wannan biyayyar taki tana daga cikin abubuwan dayasa na kamu da sonki tunda kin tabbatar zabin d'anuwanki shine zabinki, a she dai naci babu hamayya kenan, domin na tabbatar d'anuwanki ba zai iya zaba miki wani fiyye dani ba.
"amman duk da hk xan baki lokaci kije kuyi shawara da matar yayanki tunda itace ta hannun damarki, dan ta abokina shi bana jin komai domin shine yace in nemi soyayya agurinki domin yana son baki cikakkiyar yanci shiyasa nake ganin yanzu shawara ta rage keda hajara babu ruwan aminina ,dan ko yau muka daidaita gobe ma yana iya d'aura mana aure.
ta dan fad'ad'a murmushinta "shikenan Allah yayi mana zabi mafi alkhari "yauwa masoyayyita abinda nake son ji kenan daga gareki, domin zabin Allah shine mafi alkhairi a gurinmu, gbdy dai ishaq ya gama kashewa mukarama jiki da salon soyayyarsa wanda sukayi tasiri a zuciyarta. +

sosai yasamu matsugunni agurinta ,byn sunyi sallama tare da yi mata alkwarin zai dawo wani sati domin jin shawarar data yanke, kafin su rabu sai da yayi mata alkhairi mai yawa wanda kunya ta hanata kar'ba ,sai daya takurata sosai sannan ta amsa game da yi masa godiya tashige ciki, tana shiga Kai tsaye d'akin hajara tashiga domin ta fesa mata labari da bata ganta cikin parlour'n ba sai ta bita uwar daka ta isketa kwance ita da akram akan lafiyayyen gadonta suna ta sharar bacci cikin nishadi ta dan ja ta tsaya tana jan tsaki .

"ke kam aunty hajara kin cika so baccin tsiya ta fad'i hkn a fii yayinda tasa hannu tana girgizata, ta d'an motsa kadan tare da rungume d'anta ajikinta batare da ta bud'e idanunta ba ta sake komawa bacci abinta .
a hanzarce mukarama ta maka mata duka, hajara a firgice ta d'an bud'e idanunta ganin mukaramaa tsaye akansu tace "kai d'an Allah mukarama in banda d'aukar haki ki barmu muyi baccinmu .
mukarama cikin zolaya tace "mijinki yace na taimaka na tasheki sai nayi laifi?

hajara da sauri ta watseke tare da tashi, zaune har da d'an murmushinta, mukarama ta kwashe da dry "uhm yar dadi miji daga jin zance miji kin wani wartsetake to karya ne bashine yake nemanki ba ni nake son mgn dake hajara ta d'an kai mata duka "kyaji da karyarki ke daman babu damar kiga mutun yayi bacci sai kin tasheshi .
mukarama tace "ai ina ganin akan shegen baccin nan naki sai nayi miki kishiya in tura amarya d'akin yayana kina nan kina shirgar bacci.

"haba dan Allah kin isa ai dagani babu kari ai ni nafi karfin amarya.
"kiyi cika bakinki kigama zanyi maganinki .
suka fashe da drya .
kiyi driyarki ahankali karki tasar min da yaro inji cewar mukarama.

"ai kuwa babu mai hanani magana, kiyi shru albishir nazo miki kinsamu dankareren suruki idan bakiyi shiru ba wallahi na fasa "hajara tazaro ido "da gaske koda wasa "da gaske mana "to waye surukin nawa?
"abokin yaya.

hajara tayi dry har da shewa "gsky in dai shine yayi min, mukarama ta zauna ta zayyene mata yada sukayi sai data gama jin komai tayi murmushi tace "haba ai daman nasan za'a rina shiyasa kika ga ko mamaki banyi ba kinsa ance inkaga kare yana shinshina takalmi d'auka yake son yi ,Allah dai ya tabbatar da alkhari gsky kinyi sa'a more miji d'an gayu d'an boko attajiri kyakkwawa...
"kinga ba surutu nace ki min ba shawara nazo kibani "hajara tace kawai ki auri abunki tunda mu duk muna sonshi ba wata matsala kuma bashi da wani aibu dan ko mutumin kirki ne gashi attajiri in kika aureshi zakiji dadi mukarama tace"ki ture zance kudi kinsan ni kudi basu dameni ba, ni kawai kwanciyar hankali nake nema atare da namiji. +

"karki damu in dai kina sonshi kurum ki aureshi ni dai ina baki goyon baya karma ki tsaya wani hasashe kiyi aurenki kawai da zuciya daya ki shiga gidansa da kyakkyawar niyya Allah ne mai bada zaman lfy bare ma nasan mutumin Nada kirki, zai rikeki amana.

mukarama tace" shikenan Allah ya tabbatar da alkhairi in yaya yashigo ki gaya masa na amince hajara tayi dry shikenan ishaq zai d'auke mana ke ,zamuyi kewarki in kin tafi dawa zamuyi hira?
sai ki dinga yi da mijinki, ni meye zai dameni tunda nasamu nawa abokin hirar.

hajara tace "dadin abun dai baki da baki balle nasa ran zaki yi hira da miji "ki kwantar da hankalinki wannan karon zaki sha mamaki yadda bakina zai bud'e bari dai ayi auren ,ni nasan irin soyayyar da zan nunawa ishaq ,ke ko fita sai naga dama zan barshi suka kyalkyale da dry gabad'aya hajaa tace "kmr gaske "a ture maganar wasa zan dinga tarairayarsa domim karya hango wata.
hajarra tace "ai shi nmj bakomai bane idan yashiga hannun mace mai wayo, komai girmansa ya kan dawo tmkr yaro in har ya had'u da macen da ta iya kissa sannan ladabi da biyayya ma wani ginshiki ne a cikin zaman aure, amman mu mata hausawa duk bama d'aukar wad'an nan abubuwan da mahimmanci .

mukarama tace "ai kuwa duk kina yi babu laifi kina k'ok'arin kamantawa gashi nan kullun sai k'ara rikita min yayana kike abun bako tausayi "kema ba gashi nan kina shirin zuwa ki rikita yayan wasu ba "
amman ai kinsa ni nafiki kunya bazan dinga irin abinda kike yiwa yayana ba.

"zauna nan garin jin kunya a je ayi bake, gara ma in zaki cire kunya tun wuri ki cire domin mazan zamani nan basu wani so kunyar nan, ki zage ki tarairayi mijinki, "yanxu ina karuwai suke a gari?

"babu su domin karuwai na d'akin mazajensu, wallahi wata idan kikaga iskancin datake zubawa mijinta domin gamsar dashi sai kinyi mamaki ,yanzu karuwai babu market kowace takama gabanta..
suka fashe da drya a daidai lokacin da Muhammad yashigo ya daga labule d'akin "to gwana kingama mata hudubar?

kunya duk takama mukarama a zuciyarta tace" Allah dai yasa ba duka hirarsu yaji ba hajara kuwa ta dake tace "kai kace daman la'be kake mana ,ka dai san la'be babu kyau.

cikin driya yace "ina ruwana da hirar shirmenku, ke din ma yaushe kikayi baki har da zaki koyawa wata yadda zata rikita miji ya zauna a tafin hannuta?
mukarama tayi saurin cewa "kai yaya bafa hk tace min ba, zancemu ne kurun mukeyi ,"idan haka yaji sai me kissa nake koya miki don abokinsa yazamo a tafin hannunki Muhammad ya dube yana yar dariya "ke din me kika iya balle har ki koyawa wata? +

ta d'an hararesa "haka din da kake rainawa dai ina yi ma ,ina laifi ma da kasamu hk wasu mazan nacan basu samu irin kulawar da nake maka ba. ganin mukarama na gurin yasa yayi saurin wayancewa "karki sake yarda da hudubar wannan kawartaki mallake nmj a tafin hannunki bashine ba ladabi da biyayya shine gaba da komai ,halaiyar kirki ake neman ga mace.

hajara tace "da kuma me ?
yace "da iya girki ta sake cewa byn nan fa?
tana kallonsa tana dry "ke mukarama ina ganin , in dai abokina yayi miki shikenan sai ayi magana aure kin dai san ba gurin da za'a tsaya 'bata lokacin bane , in kuma ba kya sonsa gara tun wuri ki gaya min in sanar dashi domin babu wata yaudara atsakaninmu dashi, ko ban fad'a miki ba Kinsa matsayinsa agurina, in kina sonsa komai cikin gaugawa za'a yi agama ba tsayawa za'a yi ana ja masa rai ba ,kinsa ni ban iya kwalo kwalo ba ya fad'a yana kallon mukarama wace tace "yaya ai magana tana hanunka sai abinda kace, ni duk abinda ka yanke daidai ne.

girgiza kai yayi "haba mukarama ki dai ki fad'i son zuciyarki idan kina so nima ina so, idan kuwa baki so nima banaso "ai ni matsawar kana da rai bazan iya yankewa kaina hukunci ba, sai abinda ka yanke min,.
ya d'an yi shiru hajara tace "tunda hk ne shikenan aje mun zabi abokinka sai kace ya fito ya d'an washe baki yana murmushin jin dadi "lallai kun kyauta min kuma mukarama ta fiddani kunya in ta aureshi zan fi kowa farinciki saboda abokina mutumin kirki ne nasan bazaki ta'ba nadamar aurensa ba, nagode Allah yayi miki albarka bisa biyayyar da kike min..

mmn sudais ce
💗💗💗💗💗💗
MUWADDAT
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
+

~NA~

*AYSHA A BAGUDO*

~DEDICATED TO~
_AUNTY SALAMATU AYYUBA_
_(UMMIN KADUNA )_

WARNING!!!

FOR THE FIRST TIME !!!! I WILL LIKE TO SAY," DON'TS READ THIS NOVEL ,IF YOU KNOW YOU ARE NOT MARRIED... ❌❌❌COZ THIS BOOK CONTAINS ONLY FOR MATURE PEOPLE , IF YOU READ IT, IS FOR YOUR OWN RISK ......

WATTPAD @HAUESH

BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM

Page 3

......Tun da alhj Mahamud yasoma sanyawa mukarama albarka ,murmushi yaki 'bacewa a fuskarta ,hajara ta du'beta a sukwane tace "kai duniya mukarama ko kunya baki ji ,ana zance aurenki kina guri , sai wani nishad'i da annashuwa kikeyi ..

Wani sabon murmushi mukarama ta sake yi "bil hakki da gaske mugun son ishaq ya kamata sosai tun kwanaki ma na lura da rawar kafar da takeyi akansa ,kalli ma yanzu kaga rawar jikin da take ,barin in taji yazo gidan ta dinga 'bare 'bare kenan tana hanzari zuwa gaidashi ,wata sabuwar kunya ta kama mukarama ta tashi da sauri zata fice daga d'akin tana dariya ,alhj Mahmoud ya dakatar daita "kinga dawo kiyi zamanki in dai tsiyar hajara ce kin saba daita ,tunda tayi baki neman take ta bud'e bakin kowa ta karfi da yaji.

Mukarama tace 'kai ma yaya kayi mata kishiya kawai mu huta da halinta hajara ta kwashe da dariya ahayyeeeeee yau zan ga had'in kai acikin gidan nan, to Dan kince yayi min amarya sai me ?

Ince ba'a kaina aka fara ba sannan kuma ba akaina zata zauna ba ita shegiyar kishiyar, tazo Dan ubanta ...

"Duk dadin baki yayanki yake miki Dan yaga zaki yi auri abokinsa yanzu da wani ne da watakilla ya rungumi transformer Amman shi Da kansa yasan mijin mace daya ne ..

Alhj Mahmoud yace " yarinya karki cika baki in kika zugani gobe gobe sai ,naje na biya sadakin wata yarinya da take mutuwar sona in ga tsiya"

Mukarama ta kwashe da dariya, har da yiwa hajara gwalo, hajara tace" lallai mukarama wai ni kike kwayewa baya agaban yayanki bari ?

"La yaya kalli kaga daga jin zancen kishiya har idanun hajara ya raina fata ..sukayi Dariya gabadayansu har hajara wace cikin dariya tace "zan miki mummunar addu'a kema kina shiga gidan ahmed da wata biyu ya gano wata ,tunda dai zuga shi kike yi ayi min kishiya ,wace Sam sunanta ma bai da dadin fad'a .

Byn Sati biyu ishaq ya sake zuwa gurin mukarama byn sun gaisa suka zarce da hira, wannan karon yaji dadi sosai da yadda ta sake dashi har suka tautauna sosai da kanshi yace "na ji dadin irin kar'buwar Dana samu duk da dai har yanzu baki furta min cewar kina sona ba ,Amman dai na gamsu dari bisa dari sannan na gamsu da bayyani da yayanki yayi min kuma hausawa sunce labarin zuciya a tambayi fuska ,ina ga tun da mun rigada mun amincewa juna ai ba sai an d'auki dogon lokaci ba ,abin nan tuwona maina ne zan so ace mun yanke lokaci kinga tun daga yanzu mu fara shirye shirye Dan tun Dana sheidawa hjyta batunki ta kasa zaune ta kasa tsaye, domin burinta arayuwa bai wuce taga na ajiye iyali ba Amman me kika gani? +

Ta D'an dubeshi cikin murmushi tace "ina ganin wannan maganar zaifi kyau kuyita tsakaninka da yayana "eh na San da haka ,Amman shi Mahmood ya sheida min, in dai ina bukatar aurenki ko gobe ma zai iya d'aura mana aure ,shi yasa nake ganin nida ke yakamata mu zauna mu tsara lokacin da muke bukata .

Ta janyo ajiyar zuciya da kyar ta fesar saboda yadda maganarsa ke shiga jikinta kana tace " to kai kmr wani lokaci kake ganin ya dace ?

"Yauwa zuciyar ishaq ni dai idan kin amince zuwa karshen shekarar nan yayi min ,nan da wata biyu kenan sai ayi komai cikin gaugawa a d'aura aure tare da biki, ta D'an fad'ad'a murmushinta tana kallonshi tmkr yau ce rana ta farko data soma sanyashi acikin idanunta .

ahankali muryata ta fito still kwayar idanunta na cikin nashi tace "haba dai nan da wata biyu ina ma laifin wata uku .

Yayi saurin ware mata matsakaitan idanunsa ,"wani irin wata uku idan dai baso kike labarin mutuwata ta riskeki ba ,ko na dibo kayana na dawo gidanku da zama ba,ki San ko irin yadda nake jinki a zuciyata?

"In aka kai watanin uku ba'a shafa fatiha ba,ai sai na fara sanbatu ,mgnr yabasu dariya gabadaya

"in dai ba wani babban uzuri gareki ba ,gaskiya bana son a dau lokacin domin ina son muje aikin haji tare InshaAllahu,dan alkwari nayiwa kaina bazanje aikin hajji ba sai da matata saboda zanfi jin dadin tafiya tare da iyalina, Amman ban sani ba watani uku da kika ambata ko akwai wani tanadi na musamman da za'a yi domina ?

"sai in hakura har zuwa wani lokaci kinsa ku mata bakwai rabo da daburu da hikimomi.
"Ta sunkuyar da kanta kasa "babu wani shiri da zanyi daman gani nake kafin lokacin mun Dan dada fahimtar juna "ai babu wata fahimtar data wuce kaunar da take cikin zukatanmu kin Riga kin San ina sonki ,kema ko baki fad'a ba nasan kina sona batun yau ba na gane akwai kaunata a zuciyarki .
A kunyace ta rufe fuskarta tana dry "kinga kuwa fahimtar juna bazata yi wahala ba ,yanzu dai kin amince min karshen watan nan nake son na turo kayan aurena kuma in kin tashi tarewa banason yayanki yayi wahalar siyan komai domin babu abinda ban zuba acikin sabon gidana ba ,komai akwai ke kawai suke jira . +

Cikin murmushi tace "bakasan yadda yaya ya fika d'aukin wannan auren ba ,domin tunda yaji ka furta maganar auren yayi oder a kamfan, hatta kayan kitchen ya gama siya ..

Ishaq yayi D'an murmushi "ina ruwan mutumina ai naga alamar yafi kowa doki auren nan, to tun da yake ya rigada ya siya miki kayan d'aki babu komai asasu a extara room's.

kanta a sunkuye tace "shikenan Allah ya nuna mana ya kara budi Amman ni dai Dan Allah karkace zakayi wata hidima kayan aure komai na yafe, ya D'an dubeta cike da fara'a a zahiri gsky yaji

3 / 53