Author : Aysha A Bagudo Category : Complete Novels
da kaskantar da kanshi da muryarsa yace
"Shi...shikenan babu komai ni ..ni.zan barta ummi kamar yadda kika nema bazan sake sa'bawa umarninki ba, sai dai ummi bazan ta'ba yin aure arayuwata ba, saboda muwadda ta rigada ta tafi da duk wasu abubuwana masu mahimmanci arayuwa.
sai abu na gaba cikina ina son abuna koda duk duniya zasu tsine min, koda zan rasa komai da kowa ku bani abuna da zara ta haifa ,kar akai min d'a gidan marayu gsky ..
Ganin yadda ya nuna son cikinsa a sarari yasa ummi ta zarce da yi Masa nasiha dan ta tsorota matuka da yanayinsa ,wasu abubuwa yake tamkar wani hamshakin magidanci , duk abinda take fad'a sam baya jin abinda take cewa saboda ya tafi duniyar tunanin, tausayin kansa ne kawai ya dira masa da kuma son muwadda da yake azabtar dashi ...
Kansa na sunkunye a kasa haka zalika muryarsa na rawa yace" ummi ki ya fe min maganar da nayi Miki a yanzu , shine abinda nake son naji daga bakinki a halin yanzu ,da kyar ummi ta bud'e baki tace "bunayya na yafe maka tun a baya dana gane kuskurena sannan a yanzu ma na yafe maka ....
wani irin sanyi dadi ne ya ziyarci zuciya da ma gangar jikinsa, duk da yana cikin damuwa da tashin hankali amman hkn bai hanashi jin farinciki ba "na gode ummi na gode daman nasan umminah mai yafiya ce ,ya d'aura kansa bisa cinyoyinta, ahankali ta Kai hannunta saman kanshi "Allah yayi maka albarka , sai dai bani da kwarin gwiwar fuskantar d'anuwana ta rushe da kuka "karki damu ummi inshallahu zai fahimceki....
"Allah yasa nima ka yafe min ,nashiga hakinka nashiga rayuwarka domin nice silar komai daya faru , zance nafi son al'ameen da Kai wannan ba haka bane an ridaga an gama magana da iyayensa yanzu idan muka hanashi me kake tunanin mutanen kalgo zasu fad'a akanmu ?
"Ni dai ummi karki Kai min d'a gidan marayu ...."to yaya kake son nayi nifa banason kowa yasan da wanna batun ...
Bunayya bai samu sukuni ba tun daga ranar da abun ya faru ,sai da yayi kusan kwana goma bai nemi inda muwadda take ba, itama bata nemi shi ba ,daman kuma yasan ba neman nasa zatayi ba, ya damu sosai har sai daya kira yaya akram ya fad'a masa abinda ummi ta zarta ,yaya akram yace "abinda nake so da kai kasamu natsuwa ,sannan ka kwantar da hankalinka har zuwa sanda zata haihu din, ni kuma muddin ina raye zan tsaya maka har sai ka mallake muwadda amatsayin mata.. ..maganar yaya akram ta kwantar masa da hankali har yaji natsuwa kad'an a jikinsa..
*********
bangaren muwaddat kuwa babu laifi ta d'an saki ranta ta yarda ta amincewa kaddarar data fad'a mata, sai dai duk sanda ta tuna tana d'auke da ciki ,ranta idan yayi dubu sai ya 'baci, tana kitchen tana had'a xuma da madara wanda ya zame mata kaida idan bata sha ba babu zaman lafiya .
taji bakincikinta na karuwa a halin da take ciki ,babu abinda yake ta'ba zuciyarta da wuce buris din da bunayya yayi daita , haka tacigaba da aikin gabanta da kula da abubuwan da suke gabanta ,ahankali tasoma k'ok'arin fitowa daga cikin kitchen hannuta rike cup tana juya zuma da madarar data had'a ,gabad'aya hankalin na kan zumar har miyonta na tsinkewa .
sam bata ji tsayuwarsa abakin kofar kitchen din ba, tacigaba da takowa shi kuma yashiga binta da kallo yana kare mata kallo duk da bai ga fuskarta ba hakan bai hanashi ganin kyawun da ta k'ara ba, ta murje tayi fresh ta sake yin haske na ban mamaki,kirjinta yayi wani irin cikowa kmr ana hura su, take komai yasoma kwance masa ,daidai da rana daya tunda abun ya faru bai sake samun ishashen bacci a natse ba , alokacin kallo daya zaka mata kasan tana d'auke da juna biyu, dan kamar kar ayi maganar cikin ,cikin yasoma bayyana cikin wani irin shaukinta yacigaba da kallonta har taxo daf da zata fito taji nauyin mutun akanta tare da jin sanyayyen kamshin turarensa mai tsayawa arai, ta d'ago da sauri suka had'a ido dashi ,tsurawa juna ido sukayi suna kallon junansu batare da kowanensu yayi magana ba, "yaushe rabon da suga juna tun washegarin ranar da abun ya faru, ta d'auke kanta akansa ta bi gefensa zata wuce.
ya riko laulausar tafin hannuta "ina zaki wuce ki barni byn kinsa gurinki nazo naji lafiyar baby nah ,a fusace ta d'ago suka sake had'a ido dashi ya kashe mata idonsa d'aya yana sake tsareta da tsumammun idanunsa.
muryarta na craking tace"sakar min hannu and don't ever touch me again in......
"shiiiiiii ya d'aura hannunsa akan lip's dinta "meye abun tada jijiyar wuya muwadda ?
"wani dare ne jemage bai gani ba?
"karewar ta'ba miki hannu ince har cikina kike d'auke dashi ajikinki, jinina na rolling acikin jikinki ni dake mun rigada mun zama abu d'aya...zaki haifa min d'a ko 'ya su kirani da baba..
ta fixge hannunta cikin 'bacin rai tasoma tafiya cikin sauri kad'an ya rage bata tuntsira ba, ya biyota da sauri cikin d'aga murya "wallahi idan kikayi ganganci da wani abu yasamu cikina sai na d'aureki bayan na d'auki mummunar mataki a kanki......
*******
duk kun biya kun biyar ummi haka tasanyawa jikinta jarumata ita da abi har da muwaddah suka bi jirgi zuwa ilori, tunda ta isa gidan kowa yasan babu lafiya saboda yadda jikinta yake a matukar sanyaye kamar sauran lokuta ba hankalin momy da dady ya tashi kwarai saboda basu ta'ba ganinta haka ba, cike da tashin hankali suka shiga rigerigen tambayarta abinda ya faru sai ko ta fashen musu da kuka itama muwadda ta fashe da kuka, take mumy itama ta kama kuka "dan girman allah mukarama ki fad'a mana damuwarki "me ya faru waye ya rasu ko wani abu ne yasamu auwal ?
dan batasan bunayya yana gidan ba saboda tun da suka zo yana part din yaya akram.. parlour'n dady ya d'auki shiru ,yayinda da dady yayi shiru ya cigaba da kallon yar'uwarsa kamar yayi kuka, gabad'aya ta kasa fitowa tayi bayanin abinda ya kawosu,yadda tayi shiru haka shima abi yayi ya zubawa sarautar Allah ido , sai akram ne yayi karfin halin bayanawa su dady komai , kmr saukar aradu haka sukaji saukar maganar mumy da dady suka shiga kallon abi da ummi har ma da muwaddah, ummi tayi saurin sunkuyar da kanta kasa tana kuka dan tana jin kunyar had'a ido da dan'uwanta,muryarta a hankali ta fito tana rokonsa "kayi hakuri yaya ban rike amanar da'aka bani ,ka yafe min yaya dan girman allah karka juya min baya nasan nayi kuskure... ta karasa mgnr tana kuka.
bayan wasu mintuna dady ya numfasa sannan yasoma "magana cikin karfin zuciya "mukarama ki daina kuka, kukan ya isa hk kinsan idan akwai abinda na tsana a duniya bai wuce kukanki ba, mu biyu kad'ai iyayenmu suka haifa suka mutu suka bari, banida kmrki, hk kema baki da kamata "muwadda kuma yarki ce halak malak.......
abinda ya faru kuma ba zina yaran suka aikata ba ..... ...
Mmn sudais
MUWADDAT
page 41
...Dif numfashi da zuciyoyin rayuka had'u suka tsaya na wuncin gadi ,sakamakon jin saukar maganar dady da suka ji tamkar saukar aradu acikin kunnuwansu .
gabad'aya a firgice sannan a gigice suke bin junansu da kallo mai cike da tsantsar mamaki, kana suka sake maida idanunsu akan dady dake tsaye a gabansu fuskarshi babu yabo babu fallasa .
kallonsa suka cigaba da yi domin neman k'arin bayani yadda hakan ta kasance ,barin ummi wacce gabad'aya ilahirin jikinta ya d'auki rawa ....
Kusan ta fi kowa farinciki da murnar wannan a'lamarin .....
Sautin muryar dady ne ya sake karad'e parlour'n
" Tabbas gaskiya ne abinda kunnuwanku suka jiyo muku daga bakina ,a gidan nan Kuma acikin wannan parlour'n nawa na d'aura auren muwaddah da Muhammud auwal ,bisa yardata da yarda wakilin auwal wato umar kanin mahaifinsa da Kuma shi kansa mahaifin auwal din wanda ya kasance amini gareni .......
"a lokacin da aka d'aura auren abokina alhaji safyan na nan ,sai baba mai gadina gashi can da ransa bai mutu ba akirasa, sai umar da shi kansa alhji ishaq din, dan haka yara ba zina suka aikata ba sunan suka aikata ...
"Kamar umar yasan abinda zai faru gaba kenan , yazo min da zance ,alokacin naso naki amincewa bisa wani uziri nawa a she umar ya hango abinda mu muka kasa hangowa ......
"Dan haka sai mu
godewa Allah, da Allah yasa da au.......
"Babu wani aure anan dady....... yaya akram ya furta hakan kansa a sunkuye zuciyarsa na farfasa had'e da bugawa .....
"A zahirin gaskiya dady kuskure ne irin wannan auren , yanzu da ba dan ina nan ba, da an tafi akan kuskure wanda mafi yawa daga cikin mutane suke aikata shi da siga aure ,alhalin ya haramta ....
"yanzu misali wakilin auwal ne yazo tambayar auren muwaddah a gurin waliyin muwaddat, suka taru suka amince, har suka had'a aure hakan ya hallata , Tabbas wannan tabbataccen aure ne da muslinci ya yarda dashi ,amman irin aurensu auwal da muwaddat sam bai hallasta ba, kuskure ne mai girma a muslince , domin bazasu kusanci junansu ba har sai sun san cewar su din ma'aurata ne ,saboda an d'aura auren batare da sanin su ba ,saboda yakamata ne kafin su fara saduwa da junansu su kasance sun san cewar su din ma'aurata ne ,idan har basu San cewar su din ma'aurata bane niyyar su ,niyya zina ce babu aure.
Numfashi da ajiyar zuciya ya sauke alokaci d'aya ,kana ya cigaba da cewa "tabbas wannan zina suka aikata kuma laifin yana komawa ne kan waliyansu bisa kuskuren su na rashin sheida musu cewar su din ma'aurata ne .........
Tun da yaya akram ya soma zayyano magana daki daki babu wanda ya sake bud'e baki yace dashi "uffan "
gabad'aya parlour'n da mutanen dake zaune acikin parlour'n suka sake d'aukar shiru na wani lokaci ...
gabad'aya cikin ahlin babu wanda zuciyarsa bata buga ba tsabar tashin hankali da firgicin bayanin yaya akram, sannan sai alokacin hankalin dady abi har ma da sauran mutane dake parlour k'ara tashi dukkaninsu tsuma suke , tabbas abinda akram ya zayyene a halin yanzu tabbass haka yake a cikin addini , to yanzu me ye abun yi ?
"Meye mafuta acikin wanna lamarin ?
tambayar da dady ya soma aikawa 'kwal'kwaluwarsa kennan gumi na keto masa ...
Alokacin da umar yazo masa da zance har sanda suka yi komai suka gama atsakaninsu, bai yi tunanin kuskuren haka ba ,Kuma umar yaso kwarai a sanarmawa yaran shine mutun na farko daya yaki ba da goyon bayan aikata hakan, ya hana sheidawa yaran bisa wani tsautsauran ra'ayinsa, a tunaninsa ai baza su ta'ba kusantar junansu ba har sai lokacin da suka kammala karatunsu, sannan a sheida musu cewar su din ma'aurata ne " a she babban kuskure suka tafka arayuwarsu without knowing....
"Wannan shine ga koshi ga kwana yunwa "
"Tun da yaya akram ya dasa aya ya kasa d'ago kyawawan idanunsa dake cike da ruwan hawaye ,zuciyarsa ce ke wani irin beting da sauri sauri, ahankali ya Kai hannunsa daidai saitin zuciyarsa dake bugawa da karfin gaske ,yana janyo numfashi da kyar yana fitarwa domin dai yasan iyayensa sunyi kuskure arayuwarsu , kuskure kuma wanda har abada bazasu daina dasun sani ba ....
Ba za ma su san, sun tafka babban kuskure arayuwarsu ba ,sai lokacin da nashi sirrin ya fito fili ...
"Sai dai kafin zuwan lokacin zai so Allah ya d'auki rayuwarsar ya huta da ganin tashin hankali da zasu riski kansu ciki , don idan akwai abinda ya tsana a halin yanzu bai wuce iyayensa su san ya aikata zina arayuwarsa har ma yana da ya'ya a wata uwa duniya .."
"yafi jin tausayinsu akansa, baya son tashin hankalinsu ,bayan son ganinsu cikin damuwa ...
"su amince masa sun yarda dashi ,sun bashi dukkanin yarda da amanarsu, shi kuwa me zai ce musu idan hakan ta kasance ?
"Ya Allah ka d'auki rayuwata kafin zuwan wannan ranar," Allah Allah ka d'auki rayuwata ....."
Haka ya dinga maimaita kalmar acikin zuciyarsa can kuma tari ya tsarke shi saboda kukan dake yunkuro fito masa ....
A daidai wannan lokaci sai ga uncle umar shi da bunayya, cikin hanzari bunayya ke bin bayan uncle umar, sai dai kallo d'aya zaka masa ka fahimci cewar a tsorace yake, bai ta'ba tsintar kanshi cikin jin tsoro da shiga tashin hankali irin na ranar ba, domin bai san abinda zuwan nasu zai haifar ba, rugujewar zumunci ko sa'banin haka "
Koda suka shiga parlour'n suka iske duk mutanen dake zaune a parlour'n sunyi jugun jugun, masu tagumi sunyi ,masu zubar da hawaye nayi ,haka ma muwaddah kuka take so tana d'aura dukkanin laifi bisa kanta ....
Yanayin fuskokinsu yasa jikin uncle umar yin sanyi ,ya k'arasa ga abi ya mika masa hannun kana ya Isa ga alhaj Mahmud wanda kansa yayi mugun d'aurewa ,da kyar dady ya mika masa hannu suka gaisa kana ya samu guri ya zauna kusa da dan'uwansa yana tambayarsa batare da 'bata lokaci ba abi ya shiga zayyene masa komai ...
Zaro idanuwa bunayya yayi waje, yana duban abi da gaske "muwaddat matarsa ce ?
"Kenan ba zina suka aikata ba ?
"Cikin jikinta ba d'an zina bane ?
"Kai Kai wannan wace irin rana ce garesa ?
So yayi ya isa ga masoyiyarsa ya rungumo jikinsa ya rarrasheta akan kukan da take , sai dai yana jin tsoro aikata hakan ,ba zai iya sake d'aukar fushin umminsa ba ,ta azabtu matuka da abinda yayi mata ,shi kansa yana tausaya mata daga ita har muwaddat din...
Dammmmmm kmr saukar aradu yaji zuciyarsa tayi wani irin mahaukaci buguwa da karfin gaske ,har sai daya dafe daidai saitin zuciyarsa , take bugun zuciyarsa ya tsaya sakamakon jin dagon sharhin da abi ke wa uncle umar ,kusan second biyu numfashinsa ya dawo gangar jikinsa ,zuciyarsa tashiga bugawa da sauri ,nan da nan gumi ya shiga keto masa a dukkanin ilahirin jikinsa .
"ko ina na jikin shi kad'uwa yake kamar mazari "dan Allah abi karka ce haka, ina matukar bukatar muwaddah arayuwata "Kai ne fa kace min nan gaba zanji dadi har ma nayi farinciki da abinda zai faru , sai yanzu na fahimci manufar maganarka ,dan Allah ,dan girman Allah abi idan wani laifi nayi yasa zaka kawo wannan dagon sharhin ,ka yiwa Allah kayi hakuri, karka haramta mana aurenmu daya inganta , sambatun yake har sanda ya k'araso gurin da muwaddat ke zaune sunkuye da kanta tana zubar da ruwan hawaye , while zuciyarta na bugawa.
"abi ni dai koma meye ina sonta haka, idan da aure ko babu ina sonta, kuma zan rayu daita muddin rai, cikin sa'a ya cafki tafin hannunta cikin nasa yana massaging dinsu hankalinsa a matukar tashe ..
wani k'ara ta saki da karfi ta fixge hannunta cikin nasa ,wani irin duba yayi mata yana jin tamkar ya rufeta da dukan abinda tayi ..
muryarsa a harzuke yace " ke malama ki fito ki fad'a musu kema kina Sona mana , kamar yadda nake sonki, kuma zamu sake sabon aure da zarar kin ... kin ..
saurin katse harshensa yayi saboda ganin irin kallon da ummi ke jifansa dashi ....
Ita kuwa muwaddah hawaye ne ya gangaro daga idanunta yayinda bakinta ya kasa furta komai sai kallonsa data cigaba da yi ..
jikinta a sanyaye ta yunkura zata tashi da niyyar barin gurin dan bata jin zata iya cigaba da zama agurin ..
Saurin riko laulausar tafin hannunta yayi sannan yace "where the hell are you going?
Bai jira mai zata ce ba ya maida ita mazaunin da take k'ok'arin tashi "you are not going anywhere sai kin fad'a musu ni dake duk muna son juna kuma... .
wata uwar razananniyar tsawa abi ya buga masa had'e da furta "live her alone ,ko kana hauka ne ?
Bunayya ya marairaice fuska yana girgizawa abi kai "maza tashi ka koma can "plz abi karka min haka ......
Allah sarki ita kam ummi zuba masa ido tayi kawai ta kasa ce masa komai , tana jin wani irin zallar 'bacin rai na ratsata ,gefe d'aya Kuma hawaye na bin kuncinta ,ji take a duniya bunayya ya gama tozarta ta ,ya gama wulakantata ,ya bada damar da duniya zatayi Allah wadai daita.
"shin ita din uwa ce kuwa ,ko kuwa iyaye mata ta rako duniya ?
"Shin ta cancaci ta zama cikakkiyar uwa kuwa acikin alumma?
"Wace irin tarbiyya ta bawa d'anta?
" ta sani bai taso a gabanta ba, amman dukkanin rayuwarsa tana hannun Allah da ita, da Allah ya damkawa lamuransa ,ko da yake bai kamata ta ga laifinsa ba ,dukkanin laifi yana kanta da mahaifinsa ne .....
Uncle umar dake zaune a gefen abi ya kallesu daya bayan d'aya yaga duk sun shiga rud'anin da tashin hankali , ya d'an yi murmushi wanda ya bayyana zatin fuskarsa kana yace "kamar yadda akram yace "zina suka aikata ,haka din ne zina ce sai dai ta wani bangaren ba zina suka aikata ba bisa tawa hujjar da zan zayyano a yanzu .....
Bari nayi muku bayani dalla dalla , wato ba kowace aya bane ake samun ayar datayi magana akan irin wannan auren ,ita aya tana zuwa tayi magana a dunkule kun ga ne ?
" Kamar yanzu misali duk cikin alqur'an babu inda Allah yace wannan auren ya haramta , hadith's annabi s.a.w ne da akin annabi suka zo suka bayyana hakan ,akwai abubuwan da suke zuwa a