Advertisements
Chapter 11 Reading Kanwar Matatah Book 1 Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Kanwar Matatah Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Takori Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   11 / 60

30K to 33K   out of 178.7K words

ta dakawa _Khalil_ wani irin tsawa tare da fad'in, "Wallahi _Ibrahim_ ka kuma yarda iyayenka suka fad'a ka fad'a zan mugu-mugun sab'a maka. Kuma umarni na baka yanzu-yanzun nan ka tura masu kud'in nan. Ko miliyan d'ari suka ce ka basu, ka tura yanzu nan." Tsaki uncle Ridwan yayi tare da fad'in, "Don kin ga idanun mu shine zaki rik'a acting kamar ta kirki? To ba million d'ari muka buk'ata ba, miliyan hamsin da bakwai muke buk'ata. Kuma dole ne a tura, don kud'in d'an uwanmu ne ake handama da babakere a kai." Hajiya dariya ma maganar ya bata, don a bayyane yake suke handama da babakere akan dukiyar marayu. Kuma wuta suke ciwa kansu. Don bada dukiyar gado suka dogaro ita da Y'ay'anta ba, gaba d'aya Y'ay'anta babu wanda bashi da na kansa. _Khalil_ kuwa a take ya fiddo wayarsa yayi transfer d'in kud'in zuwa account d'in uncle Shamsu tare da sauke Madhuu dake jikinsa don ransa yayi mugun b'aci ya wuce d'akinsa. Da kallo dukansu suka bisa dashi tare da fad'in, "Shege mai halin yahudawa. Ji yanda yake taunar cingam kamar wani karuwa. Shiyasa fa tura y'ay'a k'asashen waje sam bai yi ba, don a nan ne y'ay'a suke koyo mummunar d'abi'u da taurin kai. Don su komai sai kaji ana fad'in human right. A can fa ko uwa ce ta daki d'anta, d'an yana da damar kai ta kotu domin a naima masa hak'k'i! Kai Allah wadaran naka ya lalace." Fad'in uncle Ameeru. Uffan Hajiya bata k'are cewa ba har suka k'are fitinarsu suka fice daga gidan. _Khalil_ yana shiga d'aki ya cire rigar jikinsa ya wurgar a k'asa tare da saka k'afa tattaka kamun yayi ball da ita sannan ya saka hannu ya chakud'a gashin kansa kamar zai yi hauka. K'ugu ya rik'e yana wani irin huci. K'arar k'ofar d'akinsa ne ya dawo dashi tunaninsa tare da k'arisawa ya bud'e k'ofar. Kaucewa yayi ya bata hanya ta shigo sannan ya kulle k'ofar tare da danna wani madanni glass ya zuge. Wani irin mahaukatan kayan saka suka bayyana a jikin hanga, wasu kuma a ninke a cikin loka. Hannu ya kai ya zaro wata shirt mai botura sannan ya danna madannin glass d'in ya zuge. Saka shirt d'in yayi sannan yayi buttoning tare da zauna a k'asa dai-dai k'afafunta Hajiya tare da d'aura kansa a kan k'afarta sannan ya soma magana, "Hajiya bak........!" D'aura hannunta tayi a kan leb'ansa tare da fad'in, "Ba komai ake magana akai ba _Khalilullah_, wani abun kana gani k'iri-k'iri ana cutarka, amma sai ka kau da kai kamar Allah ya amsar maka hak'k'inka. _Khalilullah_ wad'annan mutanan y'an uwan mahaifinka ne. Idan har ka raina su kamar mahaifinka ka raina. Don Allah ka rik'a kiyaye abunda zaka jawo min magana. Baka ganin d'an uwanka Abdul-Hakeem, ko ni ta kansu bai yi, sabgar gabansa kawai ya saka a gaba. Kai ma da zaka daure ka cire idanu a kansu, da ka taimaka min." Kamar ba zai ce komai ba, sai kuma ya d'ago tare da fad'in, "Hajiya kin fi kowa sanin su Uncle sunfi saka min idanu akan Yaya Abdul-Hakeem. Kina jin fa abunda suke cewa sai kace a kansu nake, wai wata guda suka bani in nemo matar aure ko kuma su aura min Nina, wallahi da na auri yarinyar nan, gwara na mutu babu aure. Lokacin da Papa yake da rai, wani abune basu yi mana ba, shi kansa papa ba kyalesa suka yi ba. Ko shishshige masan da suke yi suna had'a mu fad'a dashi, au duk sabida dukiya ne. To yanzu dai gashi ya mutu ya bar masu duniya, but still they're after his money. Ni wallahi Hajiya ban dogara da kud'in Papa ba ke kin sani, kud'in da na tara a yanzu haka, ko da babu ko sisi daga cikin kud'in Papa, zan iya rik'e gidan nan kaf har dasu kansu Uncles d'in, ba tare da na girgiza ba. Kuma wallahi Hajiya duk kud'in da nake bawa su Uncles, a cikin dukiyata nake cirewa sabida ba zan iya tab'a kud'in marayu ba. Idan har su basu da wannan imanin da tsoran Allah, to ni ina da shi. Kud'in nan ba nawa bane ni d'aya. Ko yaya Musaddiq da yake cewa ya yafe, ai wallahi bai yafu ba, don hakkinsa ne." Ajiyar zuciya Hajiya ta sauke tare da fad'in, "Yanzu _Khalilullah_ ashe kud'i gare ka haka? Kana nufin duk mak'udan kud'ad'en nan da kake fitarwa kana turawa iyayenka, a cikin guminka ne?" Murmushi _Khalil_ yayi tare da fad'in, "Hajiya ai kece baki bani damar yi maki bayani akan dukiya ta. Da na fara maki magana kike dakatar dani. Kar ki manta asibitoci na bakwai a nan Nigera, akwai _Khalilullah Specialist hospital_ anan Kaduna har guda uku, akwai biyu a Abuja, d'aya a Jos, sannan akwai d'aya a Kano. Kuma ina da hannun jari a *_WAZIRI GOLD STUCK COMPANY LIMITED_*, kuma bayan CEO d'in nine mai babban share a ciki. Sannan ga 400houses da na gina a millennium city. Kin ga kuwa ai d'an naki matashin multibillionaire. *_THE YOUNG BILLIONAIRE_*" Ya k'arisa maganar yana dariya. "Duk nasan dasu, amma ban tab'a d'auka kana samun mahaukatan kud'i haka ba. Allah ya cigaba da saka maka albarka a kasuwancinka. Dukanku gaba d'aya." Da "Ameen" _Khalil_ ya amsa. Kallonsa ta kuma yi with very serious face tare da fad'in, " _Khalilullah_ dagaske nake yi, wannan karan akan maganar aure ina bayan iyayenka, gaskiya nima na gaji da ganinka haka babu matar aure. Maganar da babanka yayi d'azu bai min dad'i ba ko kad'an. Ni nasan tarbiyan da na bawa y'ay'ana. Babu yanda za'ayi d'ana ya ajiye dadiro a wani wajen. Kullum cikin addu'a nake masu akan Allah ya kare ku daga sharri Zina, da duk wani aikin alfasha. Dan Allah _Khalil_ kayi k'ok'arin ka fitar da matar aure kamun wa'adin da suka baka ya cika." Hannunta ya kama tare da fad'in, "Hajiya ki kwantar da hankalinki, surukarki na zuwa nan kusa, na riga na fitar da matar aure, lokaci kawai nake jira. Ki taya ni da addu'a Hajiya. Amma dan alfarmar ubangiji ina so Hajiya, duk abunda za kiji, ko kuma zaki gani nan gaba a kaina, kar kiyi fushi dani, domin fushinki a gare ni masifa ce. Wallahi ban tab'a yar da tarbiyan da kika d'ora ni a kai ba. Ki ajiye batun wa'adin da Uncles suka bani, ki dai taya ni da addu'a kawai. Ai ba a kansu nake ba, kuma babu wanda ya biya kud'in makaranta a cikinsu balle ya naimo min aikin yi. Babu wanda ya isa yayi min auren dole." Mik'ewa Hajiya tayi tare da fad'in, "Naji _Khalilullah_, amma ko ba dan su ba, kayi danni don ina son ganin y'ay'anka kamun rai yayi halinsa. Allah yayi maka albarka." Har k'ofa ya rakata yana fad'in, "Ameen Hajiyata. Ina son ki." Hajiya na ficewa ya rufe k'ofar tare da zama dab'as a kan gadon yana tunanin kurar dake gabansa. Shi sam ba ta Uncles d'insa yake yi ba, abunda ya sani shine babu uban da ya isa yayi masa auren dole. Wayarsa da ya fara ringing ya kalla, ganin wacce ke kira sai da ya waro idanu kamun ya mik'a hannu ya d'auki wayar, kallon screen d'in ya dunga yi har kiran ya tsinke sannan yabi kiran, ringing uku ta d'aga tare da fad'in, "Assalamu alaikum!" Sai da ya lumshe idanu jin sautin muryanta a dodon kunnansa. Kwanciya yayi flat yana kallon sama ba tare da yace komai ba. "Hello! Hello!! Ba'a ji nane? Yi magana mana. Naga miss call ne d'azu wajajen k'arfe sha d'aya na safe. Hello!" Yana jin ta amma yak'i yin magana. "Ina ga network ne." Ta fad'i tare da yanke wayar. Cire wayar yayi daga kunnansa ya tsurawa screen d'in idanu kamar Saran yake gani ta ciki. Wani murmushi mai sauti ya kuma saki tare da fad'in, "Wato sai yanzu ta d'auko wayar taga miss calls d'insa kenan. Na tabbata da ta san nine, baza ta kira ba." Ya fad'i hakane tare da ajiye wayar a gefe jin ana kwad'a kiran sallar la'asar a masallacin dake cikin gidan. Bayi ya fad'a tare da d'auro alwala sannan ya fito daga d'akin, a parlor ya taras da Saude sai bala'i takewa magensa, "Shegiyar kuliya kin san dai ban k'aunar ki rab'o jikina, amma sabida naiman jidali da masifa sai ki rik'a rab'ata kina sunsunani. Kai wannan mage da muni kike. Ni tafi can dan Allah." Ta fad'i hakan tare da yin amfani da sandar hannunta ta tura magen baya. "Ke! Ke!! Ke!!! Kul kika kuma tab'a min mage. Madhubala wutar kyau d'in ce kike cewa mummuna? To ya take dake kenan da uban kachakoren hak'ora a gaba? Kin fi kowa sanin takanas na hau jirgi har Paris na taho da Madhu. Ke ko a idanu ai bata yi maki kama da ordinary maguna ba. To Allah Saude ki kiyayi kanki dani a cikin gidan nan. Kin san Allah, saboda Madhu ina iyawa Hajiya pampo ta mayar dake k'auye ko kuma billahi in cire wad'annan shegun hakoran da suka fito suke hana bakinki rufuwa. "Wallahi halittar Allah. Yanzu kai yaya _Khalif_ kana iya halittar ko k'umba ne da kake kushe halittata. Maza hau sama ka gyarawa rana tsayuwarta. Kuma bari in fad'a maka kagi, baza ka tab'a samun kyakkwar mace irina ba." Dafe k'irji _Khalil_ yayi tare da fad'in, "In mutu maza su kai ni ba mata ba. Yanzu ace an kawo min mata mai irin muninki, ai nasan wabillahi ba k'aramin zunubi na aikata ba. Ni bari ma na wuce masallaci gashi can za'a tada salla kar in rasa Jam'i wajen sauraron shirmen ki." Yana gama fad'in haka ya fice da sauri don sallar za'a tada. Laure kuwa isa gaban wani madubi dake jikin bango ma shape d'in heart tayi tare da kallonta kanta tana jujjuyawa, "Wallahi kyakkyawa nike, dube ni fa! Na tsani kyau wallahi. Abun d'aya ne yayi mani cikas, wad'annan hakwaran da suka turo." Ta fad'i tana mai bud'e baki tare da fiddo hakwaran waje. "Miyauuuuuoou!" Magen tace tare da mimmikewa kamar dai irin ta firgita d'in nan. "Kuga min shegiya. Ba dai hak'oran nau bane suka tsorata ki!" "Ai ko ni na tsorata Laure!" Aunty Maryam ta fad'i tana mai k'arisa shigowa d'akin. "Kai aunty Maryama, menene abun tsoron a jikina." Kallon mopan hannunta tayi tare da fad'in, "Yi abunda ke gabanki Laure. Ke kullum idan aka saka ki aiki, sai kin tsaya shirme. Aiko tabbas zamu had'a kai ni da _Khalil_ cikin gidan nan a mai da ki k'auye tunda ba aikin kike son yi ba, gwara a kawo wacce za tayi." Turo baki Laure tayi tare da fad'in, "Allah kana gani kuma kana ji, ka shiga tsakanin nagari da mugu. Ni da Hajiya in Sha maka Allahu mutuwa ce zata raba mu!" Waro idanu aunty Maryam tayi tare da fad'in, "Har gidan mijin tare za kuje? Ko kuma da Sadi mai gadi za'a had'a ku aure sai ku tare a wancen d'akin nasa na bakin gate, kin ga kenan mutuwar ce zata raba ku da Hajiyar." Sai da Laure ta saki mopa ya fad'i sannan ta shiga fad'in, "Tuf-tuf-tuf! Allah kar ya biye bakinki aunty Maryam. Yanda nake kyakkyawar nan, ai sai kyakkyawa iri na. Kin ganni nan, idan ba irin samarin nan da ake nunawa a bullihud (Bollywood) ba na k'asar indiya, to bafa zan auri kowa ba. Ni da cewa nayi Sulamankan (Salman Khan) zan aura, amma sai na samu labari ashe bala'in zuciya ne dashi, kuma duk shekarun nan nasa bai tab'a aure ba. Kuma yanzu yayi man tsufa, sharakan kuwa, Hajiya shaida ce, har lambata aka basa domin ya shawo kai na, amma na nuna sam ni ban amince ba, don ni ba zan tab'a auren mai mata ba." Ta k'arisa maganar tare da kai hannu ta d'auki mopa, aunty Maryam kuwa dariya ta kwashe dashi tare da fad'in, "Shi sharakan (Sharukh khan) d'in ne ya samo lambar taki yake ta bibiyarki akan ki taimaka masa?" Sai da Laure ta juya idanu sannan tace, "Kwarai kuwa!" Dariya aunty Maryam ta kwashe dashi kamun tabi corridor d'in da zai sadata da d'akin Hajiya. Khalil kuwa yana fitowa daga masallaci, ya dawo cikin gida ya wuce d'akinsa kai tsaye don lokacin abokiyar fad'an nasa ta gama mopping d'in ta bar parlourn. Wanka ya sake yi ya shirya cikin shadda gezna kalar emerald green. Kallon kansa yayi a madubi ya saki murmushi ganin yanda kayan suka yi masa matuk'ar kyau. Links ya d'auko a cikin wani madaidaicin glass box ya saka a hannun nasa sannan ya d'au cumb ya taje sumansa da yake shek'i. Don _Khalil_ d'an gayu ne na bugawa a jarida. Turarensa ya d'auko _Imperial Majesty_ ya fesa kad'an sannan ya mayar ya d'auko oud shima kad'an ya saka ya mayar, ya kuma d'auko _Boadicea The Victorious_ ya kuma fesawa. Sai gaba d'aya turaren uku suka bada wani irin fitinannan k'amshi mai sanyaya zuciya. Half cover shoe na _Roberto Cavalli_ ya d'auko na kalar emerald green ya saka sannan ya d'auki key d'in motarsa da waya ya fito. Gaba d'aya ya same su su hud'u a parlor, Hajiya, aunty Maryam da y'arta Maimoon sai abokiyar fad'arsa Laure. Tun kamun ya k'ariso parlourn k'amshin turarensa ya sanar da zuwansa. Laure ce ta soma magana, "Dan Allah yaya _Khalif_ ka taimaka min ko a d'an kwalbar fiya-fiya ka d'an d'iga min turaren nan naka mai saka mutum cikin nishad'i yayin da ya shak'i k'amshinsa." Harararta yayi tare da fad'in, "Sai dai ki mutu, mayya kawai!" Aunty Maryam kuwa cewa tayi, "Uhm, wannan irin kwalliya haka? Ko dai nayi k'anwa ne?" Dariya _Khalil_ yayi tare da fad'in, "Very soon aunty. Moon har an dawo daga school d'in?" Ya k'arisa maganar yana kallon d'iyar aunty Maryam. "Uncle na dawo tun d'azu. Ai yau Thursday babu Islamiyya." Hannu ya saka cikin aljihu tare da fiddo _MASTIKA GUM_ ya mik'a mata d'aya shima ya b'are d'aya ya saka a baki. Da harara Hajiya ta bishi tana mai sakin tsaki tare da fad'in, "Ita ma kana so ka koya mata d'abi'ar banzan ko? Ka kiyaye ni _Khalilullah!_ Tom." Dariya yayi tare da fad'in, "Allah huci zuciyar Ummi ne. Daga yau ba zan rasa k'ara bata ba, nayi alk'awarin." Remote ta jehosa dashi yayi saurin kaucewa yana dariya. Laure kuwa cewa tayi, "To ya _Khalif_ tunda ban samu turaren ba, nima a bani dank'on in tauna?" Da sauri ya kalleta tare da fad'in, "Da wasu hak'oran?" Murgud'a baki tayi tare da fad'in, "Wallahi halittar Allah. Hajiya kina dai jinsa ko?" Harararta Hajiyar tayi tare da fad'in, "Allah ubangiji ya k'ara. Ai kina jin ina maganar banso ana cin dank'on amma saboda kin raina ni shine kike tambaya a baki. Wato idan mutuwa zanyi in mutu. Allah ya k'ara." Dariya aunty Maryam da _Khalil_ suke yi har da Maimoon. Ita kuwa Laure sosai ta shak'a tare da turo baki gaba. "Hajiya sai na dawo!" Fad'in _Khalil_. "A dawo lafiya." Ta fad'i. "Uncle a taho min da tsaraba." Moon ta fad'i tana mai d'ago masa hannu, shima hannun ya d'aga mata tare da fad'in, "In sha Allah" sannan ya fice ya nufi parking lot ya danna key wata had'ad'd'iyar mota k'irar *_Mercedes-Benz GLB-Class_* fara k'al tayi k'ara. Bud'e murfin motar yayi tare da yin reverse dama tuni driver ya bud'e masa gate ya fice daga gidan. Yana hawa titi ya fiddo wayarsa yayi connecting da redion motar ya kunna wak'a ya shiga bin wak'ar,
Oh oh oh oh oh oh oh oh oh oh, oh oh oh oh oh.
Oh oh oh oh oh oh oh oh oh oh, oh oh oh oh oh.
Give me freedom,
Give me fire,
Give me reason,
Take me higher.
See the champions
Take the field now.
Unify us,
Make us feel proud.
In the streets our
Heads are liftin'
As we lose our
Inhibition.
Celebration.
It surrounds us.
Every nation.
All around us.
Staying forever young,
Singin' songs underneath the sun.
Let's rejoice in the beautiful game.
And together at the end of the day,
We all say,
When I get older,
I will be stronger,
They'll call me "Freedom",
Just like a wavin' flag.
When I get older,
I will be stronger,
They'll call me "Freedom",
Just like a wavin' flag.
So, wave your flag.
Now, wave your flag.
Now, wave your flag. Dai-dai wani dank'areran supermarket ya tsaya tare da shiga ciki yayi parking motar sannan ya fito, yana shiga ciki ya nufi wajen foodstuff. Tashin farko buhun shinkafa biyar ya nuna, k'aton d'in superghetti, macaroni, couscous, mangyd'a, manja, golden morn, cornflakes, babban gwangwani madarar gari, milo, Suger cube carton, carton d'in kifin gwangwani sardine har uku, semovita, doya, da Irish kasancewar duk akwai anan supermarket d'in. Create d'in kwai goma, 5alive irin manya-manyan goran nan carton uku, exotic, chocolate kala-kala. Frozen chicken, beef da sauransu duk ya saya masu uban yawa sannan ya bada ATMcard d'insa aka cire kud'in sannan gaba d'aya aka kwashi kayan aka kai masa boat. Yawan kayan ya saka har a back seat sai da aka saka kaya wasu ma har front seat. Kai tsaye daga nan ya wuce Jos road gidansu Sarah...............







*=?m?GARKUWAR MATA*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa =???muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA=?m? ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci

11 / 60