Advertisements
Chapter 45 Reading Kanwar Matatah Book 1 Complete Hausa Novel Hausa Novels
Advertisements

Kanwar Matatah Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Takori Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   45 / 60

132K to 135K   out of 178.7K words

tace akan ?a?asa, nan da nan ya Waure fuska tamau. "Kayi abunda na umarce ka dashi ko kuwa???" FaWin Hajiya tana watsawa Khalil harara. Ko kamun yayi wani yun?urin yin magana tuni Aunty Falmata mai bin Aunty Yagana tace, "Ba magana ake yi maka ba don ubanka? Ko sai na taso ba na sha?i wuyarka!" Ta ?arisa da ?arfi har sai da Khalil ya razana, "Hajiya wallahi, tallahi daga gidan nake, su kansu iyayenta basu san bata gidana ba, ashe dana koreta ba gida tayi ba, can dangin babanta ta nufa." Ya ?arisa maganar a tausaye. "Dubi yanda yake wani rausayar da kai kamar maraya, to ubanka zaka ci, kuma dole ka rabu da yarinyar nan tun da ba tare aka haife ku ba. Yaro duk kabi ka zama wawa a kan mace!" FaWin Aunty Yagana. "Uhm! Baku ji wata maganar banza da yake yi ba, wai ta tafi dangin mahaifinta. Ina ce nan Marmari yayi bincike lokacin auren naku, kowa cewa yake bai san asalin mahaifinta ba, su dai kawai tarewarsu suka gani a unguwar, kuma babu wanda ya taSa ganin wani ko wata daga cikin ?an uwansu yazo gidan, kaii Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'una, wannan fitina haka!" Hajiya ta faWi har da buga cinya. Tun da suka fara magana ko tari ya Abdullahi bai yi ba yanzu da yayi gyaran murya tare da faWin, "Hajiya, tun farko irin haka na guda shiyasa na?i auren don zuciyata bai kwanta da ahalin ba, amma Hajiya kece ki kai ta tausata akan inyi ha?uri ayi auren tunda dai mutane huWu sun bata shaida a kan ita matar Khalil Win, sannan kika ?ara da faWin, laifin wani bai shafan wani. To Hajiya yanzu hakan ma ha?uri za kiyi tunda dai an riga an haWa zuri'ar nan kuma laifi bana matar Khalil bane, na ?anwar matarsa ce, kuma laifin ?anwar matarsa babu yanda za ayi ya shafi matarsa, tunda ke shaida ce hatta ita kanta matar tasa ba barinta tayi ba. A bar abunda ya wuce ya wuce, sai a tari gaba kawai." Tsabar zuciyar Hajiya na tu?u?i, ta buWe baki za tayi magana ta sha?e da miyau, take ta hau wani irin mugun tari, idanunta na zubar da hawaye. Da sauri Laure ta nufi kitchen ta Wauko bottle wata ta buWe tare da kawowa Hajiyar, da sauri Hajiya ta karSa ta kafa kai, sai da tasha rabi sannan ta ajiye goran tana mai da numfashin. Babu abunda kake ji a Wakin sai "Sannu Hajiya!" Sai da ta lafa sosai sannan ta shiga faWin, "Marmari idan har ka san ba zuwa kayi ka taimaka min muyi wannan ya?in tare ba, to ka tashi ka koma tun yamma bata yi maka ba, don ka san wallahi, ba zan taSa yarda Saratu ta kuma zama da Khalil ba in har nice na haifesa, idan kuma zai yi mani musu da gardama, sai in sallawa duniya shi!" "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un, Hajiya!" Khalil ya faWi da ?arfi har da dafe ?irji yana zaro idanu. "Haba Ya Bilki, ai wannan furucin bai kamata ya fito daga bakinki ba matsayinki na uwa, idan ki kai haka ai sun ci riba. Hakan ma ba zata faru ba, Khalil ai me biyayya ne, ko ba haka ba Ibrahim, mai sunan Wan gatan Allah!" FaWin Aunty Yagana har da dariya. Sunkuyar da kai yayi tare da gyaWa kan alamar eh. Aunty Falmata kuwa cewa tayi, "Yauwa Khalil, ko kai fa! Yanzu abunda za ayi, dubawa za kayi cikin dangi na nan ko na can Maiduguri, a kwai ?an mata tsala-tsala, na san dai ba zai wuce kyal-kyal banzar matar nan taka bace kake ganin baza ka samu sama da ita ba kasancewar jajur kuma kyakkyawa, to akwai waWanda suka fita komai a cikin dangin ubaka dana uwarka. Dangin ubanka akwai irin su, Ajaja, Gona, Am'an, yaba, yakaruu duk kyawawane duk da kuwa ba?a?e ne, idan kuma basu yi maka ba, sai ka tafi dangin uwarka, ka san dai Shuwa ba baya ba wajen kyau, gasu Hindatu, Rakiya, Raliya dasu Aysha da Ameena, kai nayi tuya na mance da albasa, ga wannan ?a ?ar wajen Mariya, _Habbooba_! Kai ita ma na zaSa maka, Yarinya kamar India, yanda kasan ita tayi kanta tsabar kyau, ga gashi don san yana Waya daga cikin abubuwan dake tsole maku idanu ku maza." Caraf Hajiya tace, "Wallahi ni Habbooban ma tafi kwanciya min a rai, kawai ayi magana da iyayenta, idan sun amince sai ayi magana. So nake ayi komai cikin gaggawa, kuma ni wallahi na ha?ura da zamansa a nan Nigeria kuma dama ni na matsa a kan ya dawo nan Win, to yanzu na ha?ura, ana Waura auren sai ya tattara matarsa su koma cen _Las Vegas_ Winsa da zama." Da gefen idanu Ya Abdullahi ya kalli Hajiya tare da Wan yin murmushin gefen baki tare da mi?ewa yace, "Muje can side Win naka naga yarinyar!" Yana gama faWin haka ya fice, da sauri gaba Waya mutanen Wakin suka mi?e suka fito don suma duk abunda ake yin basu ga Aina'u ba. Jiki a sanyaye Khalil ya mi?e yabi bayan ya Abdullah zuwa side Winsa, shi ya saka key ya buWe sannan ya shiga, ya Abdullahi yabi bayansa, su Hajiya kuma suka bi bayan ya Abdallah. "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Kuna jin warin da nake ji kuwa a cikin Wakin nan kamar gawa ta ruSe?" FaWin Nafeesa tana mai toshi hancinta. Gaba Waya sauran ma toshe hancinsu suka yi, "Allah yasa ba wannan shaiWaniyar bace ta mutu a cikin gidan mu!" Hajiya ta faWi. Cikin sauri Khalil ya nufi sama yana tsallake step bibbiyu. ?afa ya saka ya daki ?ofar ta bulle da ?arfi, da wani uban sauri ya koma baya yana toshe hanci tare da zaro idanu, "Wa'innahu Sulaimanu!" FaWin Aunty Yagana da aunty Falmata. "Ibrahim menene wannan ka ajiye a Wakin ka." ?agowa Aina'u tayi cikin wa.i irin mugun azaba tare da faWin, "Ku taimaka min, ku taimakeni Aina'u ce!" Kuka Hajiya ta fashe dashi tare da faWin, "Wallahi tallahi jama'a mu kiyaye ALLAH! Mu kiyaye ALLAH jama'a!! Yanzu wannan yarinya Aina'u ce ta koma haka?" Kallonta Nafeesa take tayi cikin tsoro, ganin da tayi mata na ?arshe shine ranar da tazo washa garin auren su Khalil. Yanzu kam ta lalace, tsirara take a cikin Wakin, ma?ogwaronta a waje, idanunta ya zazzago, ko ina a jikinta babu inda babu rami zu?u?u, duk inda tsokar ta yanko ta faWo, tsutsotsi ke cunkusuwa a wajen suna cin sauran naman dake wajen. Gaba Waya Aina'u ta fice daga hayyacinta, gashin kanta duk ta gama fuzgar shi, ha?oranta duk jini ta gama tattaune leSenta. Sai wani irin mi?ewa take yi tana zabura sannan sai ta fasa ihu tare da kai hannu gabanta ta kwakwulo kunamu ta watsar a tsakar Wakin sannan ta hau burgima tana buga kanta da bango. "Hajiya a fitar da yarinyar daga gidan nan, ta koma can gidan iyayenta dan Allah!" Fadin Nafeesa jikinta na wani irin rawar tashin hankalin ganin halin da Aina'u take ciki. Ya Abdallah kuwa girgiza kai yayi tare da saurin barin waje yana mai faWin, "Hajiya yanzu yarinyar nan zata bar gidan nan, ku fito mu fita." Gaba Waya suka bi bayansa, Khalil kuwa sai da ya kalli Aina'u sannan yace, "Ban taSa jin Wigon tausayinki ba Aina'u, domin kuwa kin cutar dani matu?a, Kuma idan har Hajiya tayi nasarar rabani da matata, hmmm!" Yana gama faWin haka ya fice daga Wakin da sauri hawaye na zubar masa. Cikin ?an?anin lokaci ya Abdallah ya kirawo wani mai akori kura ya bashi 50k ya toshe hanci tare da saka glove, bayan lulluSe jikin Aina'u ya kinkimeta ya saka a bayan akori kuran ya tada mota ya nufi jama'a road can gidansu Lami. Lokacin da aka shigo da Aina'u gidan, ihu Lami ta ri?a yi tana tuma a ?asa, su Na'ima kuwa tsoron Allah ne ya ?ara huda zukatansu, duk da halin Aina'u sai da ta Wan basu tausayi. Saboda tsananin warin da take yi, Waki Waya da akai masu ?atoto saboda kiwo suka share sannan suka ajiye ta a ciki, babu abunda take yi sai tone-tonen abubuwan da tayi. Lami na jin sunan _Hell Ofulafu_ gabanta ya buga da ?arfi ta fito daga Wakin tana faWin, "Rose Merry! Rose Merry ce kawai zata iya kai Aina'u wajen Hell! Yesu Almasihu ka kawo ?arshe Rose a wannan rana mai albarka ta Sunday." FaWin Lami tare da fizgar zanin dake kan igiya ta fita fuuuuuuuu. Saboda tsabar tashin hankali Lami ko abun hawa bai hau bata hau ba, haka tayi ta tafiya a ?afa har ta isa gidan Rose Merry. Knocking ta hau yi a ?ofar gidan kamar zata ?arya duk da kuwa akwai kwaWo dake nuna alamun mutanan gidan basa nan, don anty Rose Merry idan ta tafi church duk Sunday bata dawowa sai bayan la'asar ko kuma gab la'asar. "Madam ai gidan a kulle yake, kalli padlock Win mana." FaWin wata bayarabiyar mata mai Wauke da ?aton bawon gorunan magani a kai, sai a sannan ta kalli kwaWon tare da kai hannu ta taSa, zamewa tayi ta zauna akan dakalin gidan, don ji take ba zata iya taSa tafiya ba tare da tayi ido huWu da Rose Merry ba. Ta kusan awa Waya a wajen kamun Aunty Rose Merry ta ?ariso wajen cikin shigar farar atamfa mai ratsin sky blue, sai farar rigar less da kuma sky blue Win gwaggwaro. Tana ganin Lami ta washe baki tare da faWin, "Elizabeth Akanchewa Uchendo, ?awata, my childhood friend." "Stop that nonesense Rose Merry David Anthony! I came here to ask of what you did to my daughter! You've poisoned my daughter's heart Merry, Yesu Almasihu ya tsine maki, ?awancena dake babu alheri a ciki, ke guba ce, ke shaiWaniya ce, kin kai min ?ata wajen azzalumin nan _Hell Ofulafu_, tun ranar farko da kika fara kai ni Abia na san wannan mugun mutum ne mara imani, duk tsafin da ake yi a gidanmu, baza su iya rashin imanin da Hell yake yi ba, yanzu na ?ara tabbatar da cewa kece kika kashe min Wana Lukman, kuma ki sani, na rantse da tsafin Babana, You will pay for what you did!" Lami na gama faWin haka ta juya zata bar wajen, da hannu Waya Aunty Rose ta jawo kafaWanta tana wani irin murmushin mugunta, sai da ta juyo da Lami gaba Waya sannan ta kyasta babban yatsarta da kuma manuniya tare da faWin, "Hey Elizabeth, do you think I came all the way from Nassarawa state to Kaduna, just because of our friendship? You're a fool, a big fool Elizabeth! Nazo Kaduna ne domin mijinki, don mijinki Elizabeth! Tun ranar da na fara ganin Nuhu, naji ina matu?ar ?aunarsa, amma kuma sai kika min shigar sauri, sannan kuma kin tuna abunda Akanchewa Uchendo ina nufin mahaifinki yayi wa Babana, yayi masa asiri ya raba shi da mamana, ya raba shi da duka arzikinsa sannan ya mayar dashi makaho, Ni kuma gani har yanzu ban taSa aure ba. Kina tunanin sai ni kuma in zuba maki idanu ki auri Wan gidan malaman can, sannan kuma in barku kuyi zaman lafiya?" Sai ta girgiza kai tare da Waukar ?afa Waya a kan dakali sannan tace, "Bari na faWa maki abunda baki sani ba Elizabeth, nice sanadin lalacewar duka ?a?anki, Ni na kai sunanki wajen Hell, nayi amfani da kwaWayin duniyarki, na saka Hell ya sakaki kika kai ?a?anki ga halaka, sannan Wan ki tilo namiji na saka masa cutar sata da kuma shaye-shaye, ?a Waya ce ta gagare ni, ita ce Saratu, Ni na saka Hell ya saka maki tsanar mijinki da jin haushinsa da kuma rashin ganin ?imarsa, sannan Ni nasanwa mijinki karayar arziki bayan na nakasta ?afarki, ?arki kuma Aina'u, banyi mata komai ba, jinin mahaifinki ne ke yawo a jikinta, don ita ce tayo gadon ubanki gaba Waya har ta damesa ta shanye. Kuma Lami yanzu aka fara wasan a tsakanin mu. Ban san mai Aina'u tayi ba, amma tun da tace min tana so in haWata da Hell na tabbatar Aina'u Wiyarki ce, domin bata yada halinki dana mahaifinki ba. Mu zuba ni da ke Elizabeth!" Tana gama faWin haka tayi wani murmushi tare da kaucewa ta nufi wajen ?ofa ta buWe tare da shiga ta bugo ?ofa. Lami ta jima a tsaye tana jujjuya maganganun Rose Merry kamun taja jiki a sanyaye ta nufi gida. "Ai da zafi-zafi akan daki ?arfe Hajiya Mariya, Ni dai idan har ba'a tsayarwa Habbooba miji ba, nayi wa Khalil kamu!" FaWin Hajiya tana murmushi..............


_Kar ku damu, zamu haWu gobe in Sha Allah. Na san nayi laifi kam_ =?,?


*=?m?GARKUWAR MATA*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa =???muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA=?m? ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci *GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi=???
Nono=???
Sanyi=???
Karin kiba=???
girmar hips=???
Ni'ima=???
Sabulai=???
Humra=???
Turarukan wuta=???
Matsi=???
Miski=???
Dilka=???
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai=?? ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA=?m? Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari
DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
*08089965176*
*07084653262*


*_K'ANWAR MATATA ISN'T FREE, PAY #500 VIA THIS ACCOUNT NUMBER 0592412800 ZULFAU SAID GTBANK AND SEND YOUR EVIDENCE OF PAYMENT THROUGH THIS NUMBER 08128755583_*

_MATAR SAYYADEE_
[29/10, 12:57 PM] Rahamanatu: Cike da farin ciki Hajiya Mariya tace, "Hajiya Bilki wanene zai ?i son haWa jini dake? Ai wallahi ko an tsayarwa Habbooba miji, ha?uri za'a bashi, gida bai ?oshi ba ba'a baiwa na dawa ba, balle kuma Habbooba bata da wani tsayayye miji. Ba'a jima da kammala degree Winta ba. Yanzu ne ta Wan soma kula samarin ma." Wani ajiyar zuciyar farin ciki Hajiya ta sauke tare da faWin, "Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Shikenan tuwona maina, yanzu abunda za'a yi, ki Wan fara Kwankwasawa Alhj Mutallab da maganar kamun daga nan su Marmari su zo tambayar aure, don so nake kawai da sun zo, har lokacin biki a tsayar. Allah yasa dai kar Habbooba ta bamu matsala!" "Hajiya baki da matsala, Habbooba kuma babu matsala daga wajenta in Sha Allah." Layla dake gefen Hajiya Mariya sai jan gyalen lifayan data naWe jikinta take yi tana faWin, "Umm! Umm!!" Ita kuma haj Mariya sai kai mata duka take yi tana bige hannunta, sai da ta gama wayar sannan ta kalleta a fusace tare da soma magana cikin yaren Shuwa, "Mai yasa baki da hankali ne Layla? Kin san da wacce nake magana amma sai takura ni kike yi, baki bari in gama wayar tukun sannan kiyi min duk maganar da zaki yi min!" Turo baki kyakkyawar farar yarinyar tayi tare da faWin, "Haba Umm, why always Habbooba? Komai Habbooba, duk abunda kika samu, Habbooba, idan kyauta za kiyi, Habbooba is the first person to received before everyone, haba Umm!" Layla ta ?arisa maganar cikin Wacin zuciya. "To yanzu kuma me nayi Layla?" FaWin Hajiya Mariya tana mai zama kusa da Laylan. "Naji lokacin da kuke magana da Aunty Yagana a parlour, shine kika yi sauri kika dawo bedroom Winki, and then yanzu kuma kina magana da aunty Bilkin Kaduna, kuma i heard anything you were saying, it all about uniting Habbooba and that son of her's!" Janyota jikinta tayi tare da faWin, "Haba Layla, ba wai nafi son Habbooba bane a kanki, kin ga you're just 18years, amma ita she's 27years, kin ga dole ita zan so na fara kawaswa a nan gidan tafi gidan nata mijin kamun ke. Be petient, in Sha Allah kema mijinki na nan zuwa soon!" Shuru Layla tayi bata ?ara cewa komai ba. Tayi haj Mariya tayi tare da fita daga bedroom Winta ta nufi na Habbooba, tun daga corridor Win da zai sadata da Wakinta take jiyo sautin wakar _Allela Belela_ kamar zai fasa dodon kunnenta, sai data toshe kunnen sannan ta iya ?arisawa har cikin Wakin Habbooban sannan ta kai hannu ta zare socket Win radion ta jefar. Wata fara tass Win budurwa ce kwance a kan gado daga ita sai wani Short kalar baby pink wanda ya tsaya mata iya cinya, sai rigar short Win ta kamfanin Armani da ya kawo dai-dai inda short Win ya tsaya mata, gashinta ba?i siWik mai uban tsayi daya barbazu akan gagon, rubutu take yi a kan wani jotter kuma a lokaci guda tana kallon screen Win iPhone X Winta, jin wa?ar da take sauraro ya tsaya cak sai tayi saurin juyowa da sauri, kyakkyawa ce ta bugawa a jarida, gashinta ya watsu baya, wasu kuma suka rufe gefen fuskanta, hannu ta saka ta mayar da gashin baya tare da turo baki ganin mahaifiyarta ce da wannan aikin. "Habbooba." Mahaifiyar ta kira sunanta a hankali tare da zama a bakin gadon, cikin sauri

45 / 60