Advertisements
Chapter 14 Reading Kanwar Matatah Book 1 Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Kanwar Matatah Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Takori Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   14 / 60

39K to 42K   out of 178.7K words

gama Hajiya tunda kin kusa samun jika daga gidan idan ma abunda da aka fad'an da gaske ne." Fad'in ya Barrister. Yaya Abdullah kuwa cewa yayi, "Ina bayan Hajiya, domin baza mu d'aukowa kanmu abunda zai je ya dame mu ba. Idan har bincike ya nuna ba gidan mutunci bane, to fa za muyi masu duk abunda ya kamata, idan yarinya ta haihu mu karb'i d'an ko y'ar, amma kuma maganar kawo uwar cikin zuri'ar mu, an soke ki. Hajiya duk ku shirya, _Khalil_ d'in ya tashi yayi mana jagora zuwa gidansu yarinyar. Ni kuma daga nan, zan yi bincike sosai akan ita yarinyar, idan babu wani nak'asu, to _Khalil_ zai aureta, idan kuma akwai, to fa sai dai ya hak'ura." Tun da aka fara maganar sai yanzu Abdul-Hakeem yayi magana, "Amma yaya Abdullah, idan iyayen suka ce basu yarda ba fa? Misali suke sai sun kai abun ga hukuma. Bakwa ganin hakan zai tab'a k'imar Papa da ake ganin mutuncinsa duk da baya da rai, kuma mutuncin gidan da da mu gaba d'aya sai ya tab'u. Musamman kai da babban mutum da aka sansa da kuma ya Barrister da yayi fice sabida sunan papa da yake bearing." Wani mugun numfashi Hajiya taja tare da fad'in, "Nima wallahi tunanin da nake ta yi kenan cikin zuciyata. A gaskiya _Mu'azzam_ baka kyauta mana ba sam. Ka shafawa gidanmu bak'in fenti." Mik'ewa tsaye yaya Abdullah yayi jin kiran sallar azahar tare da fad'in, "Babu abunda zai faru in Sha Allah! Ku tashi muje muyi sallah." Gaba d'aya suka tashi suka fita. Hajiya kuma cike da mamaki ta yanda ake samun ciki ba tare da d'a namiji ya kusance mace ba ta koma d'akinta. A nan ta taras da Nafeesa da Aysha ko wacce ta d'auro alwala. Aysha ma hannunta rik'e da darduma tana k'ok'arin shimfid'awar Hajiya ta shigo. "Hajiya har kun gama meeting d'in?" "Uhm, idar da sallah Aysha kizo ki fitar dani cikin duhu, dama Barista yace min kece zaki fitar dani." Hijjab Aysha ta saka tare da fad'in, "To bari na idar da sallar." Kasancewar juya masu dardumar tayi, gaba d'aya suka tada sallar, ita kuma Hajiya ta mik'e ta shiga bayi tare da d'auro alwala ta fito. Sai da suka idar da sallar har Hajiya sannan Hajiya ta kalli Aysha tare da fad'in, "Yi min bayanin nan Aysha. Ta yaya za ayi mace ta samu ciki ba tare da d'a namiji ya kusance ta ba." Kallon juna Aysha da Nafeesa suka yi kamun Aysha tace, "Eh to, akwai hanyoyi biyu da mace ka iya samun ciki ba tare da namiji ya shiga jikinta ba. Hanya ta farko, akwai wani abu da turawa suke cewa Invitro fertilization ko kuma artificial insemination. Ma'aura sun fi yin wannan idan matar ta kasa samun ciki sai suje ayi masu wannan. Ruwan miniyy namijin zai bada, sai a saka ita macen, idan kuma macen baza ta iya d'aukar cikin ba, sai a sawa wata macen a mahaifarta domin ta raini cikin ta haifesa. Hanya ta biyu kuma, akwai mazan da suke wasa da y'an matansu ba tare da sun shiga ainahin jikinsu ba, sai su rik'a goga al'aurarsu a jikin y'an matan na su, kuma idan har namiji sai gamsu, ma'ana ya kawo a jikin ita budurwa, to akwai yuwuwar ta samu ciki a wannan lokacin don Y'ay'an halittun dake jikin d'a namiji kamar iska haka suke wajen sauri. Amma Hajiya mai yasa kika yi min wannan tambayar." Wani ajiyar zuciya Hajiya ta saki tare da fad'in, "Abunda d'an uwanku ya aikatawa wata yarinya da k'arfin tsiya kenan. Kuma sai Allah ya kama shi yarinyar ta samu ciki." Gaba d'aya suka kaure da salati. "Amma ya _Khalil_ bai kyauta ba wallahi." "Uhm! Ai ni na jijjiga da na samu labarin jiya, wallahi har sai da na kwanta ciwo. Kuma yanzu haka da za'a gwada jinina sai anga ya hau. _Mu'azzam_ ai ya b'ata wayansa. Ku fita muci abinci a parlour don gidansu yarinyar zamu je yanzu haka. Don ina tunanin Marmari yau zai koma Habujan." Mik'ewa suka yi suna jimamin labarin da Hajiya ta basu tare da fita daga d'akin lokacin tuni su Ya Abdullah sun dawo. Aunty Maryam da Laure kuwa Sai kaiwa da komowa suke yi wajen dinning suna jera abinci. Sai da suka gama tsaf sannan gaba d'aya suka nufi dinning d'in. Aunty Maryam ce tayi serving kowa sannan ta koma ta zauna tayi serving kanta. _Khalil_ kuwa ko ta kan abincin bai yi ba don ko cokali bai tab'a ba. Gaba d'aya tunanin sun tafi wani wajen sabida furucin da ya Abdullah yayi akan idan har bincike ya nuna gidansu Sarah ba gidan mutunci bane, to babu aure tsakaninsu. Gashi kaf unguwar duk wanda za'a tambaya to ba zai tab'a bada shaidar arziki a kan gidan nan ba. Saukar cokali da yaji a goshinsa ya saka ya dawo cikin hayyacinsa da sauri yana kallon saitin da yaya Abdullah yake tare da susa goshin don ya same sa sosai. "Tunanin mai kake yi da bazaka ci abinci ba." Fad'in ya Abdullah fuska a d'aure. Hannu ya saka a abincin ya soma jujjuyawa cokalin kamun ya kai loma d'aya baki. Gaba d'aya ji yayi abincin ma d'aci yayi masa. Da kyar ya iya had'iye wanda ya kai baki. Gudu b'acin ran yaya Abdullah haka ya dunga tura abincin a bakinsa duk da kuwa ba dad'i yake yi masa ba. Yaya Abdullah ne ya soma mik'ewa bayan ya goge bakinsa da tissue ya koma kan kujera ya zauna. Yana tashi _Khalil_ ya ajiye cokalinsa tare da jingina da kujera ya lumshe idanu. Harara Hajiya ta watsa masa cikin zuciyarta tace, "Mai ka gani ma! Ai yanzu ka fara shiga tashin hankali." Kwafar da tayi ne ya saka ya bud'e idanu ya kalleta ita kuma ta yi kamar bata gansa ba ta cigaba da cin abincinta. Sai da suka kammala gaba d'aya sannan suka shiga shirin zuwa gidansu Sarah. Su shidda ne kawai za suje, Ya Abdullah, ya Barrister, ya Abdullah-Hakeem, Hajiya da shi _Khalil_ d'in. Mota d'aya suka shiga su uku, kuma Khalil ke jan motar, yayin da convoy d'in motar sojoji suke biye dasu, motar ya Abdullah a tsakiya wanda Hajiya kad'ai ke ciki. Gaban _Khalil_ babu abunda yake yi sai fad'uwa har yayi parking a dai-dai k'ofar gidansu. Gaba d'aya layin ya kaure da siren d'in motocin soldiers d'in nan. Gaba d'aya layin sai ya rud'e, mutane sai fitowa suke suna lek'e musamman da sauke inda motocin suka yi parking kuma gaba sojojin sun fito sun k'ame a k'ofar gidan da kuma ko wani lungu da sak'on na layin. Daga sama har k'asa sojojine kai kace yak'i za ayi. Wani soldier ne ya bud'e murfin motar da ya Abdullah yake ciki tare da sara masa sannan ya matsa ya k'ame k'am. Lami da Y'ay'anta dake cikin gida kuwa, tsurewa suka yi kowa na neman wajen b'oyo. Hankalinsu bai gama tashi bai sai da suka ga soldiers kusan goma sun shigo gidan ko wannensu ya samu position ya k'ame sabida shigowar Hajiya cikin gida. Kuulululuuuu cikin Lami ya bada wannan sautin. Baba NUHU kuma da kyar ya mik'e tare da dogaro sandarsa ya fito yana fatan Allah yasa ba wani magana su Lamin suka kuma jawo masa ba. Ganin sojoji cike a gidansa bai san sanda ya k'ame k'am ba yana salati cikin zuciyarsa har ta kai ga fitowa fili. Hajiya kuwa ganin yanda duk gidan suka tsorace don hatta Y'ay'ansu Na'ima kuka suka sa, sai ta saki murmushi tare da fad'in, "Kuyi hak'uri mun shigo ba tare da izini ba kuma mun tsorata ku." Tana gama fad'in haka sai ta juya baya tare da fad'in, " _Khalil_ kana ina, shigo mana kayi masu bayani." A wanda kwai ya fashewa a ciki _Khalil_ ya k'ariso tare da d'an d'ukawa yace, "Barka da rana, ina wuni Baba? Tare muke da mahaifinta da y'an uwana sun zo wajenka ne." Lami na jin haka ta saki wani k'aramin ajiyar zuciya tare da jinjina kud'i da k'arfin iko irin nasu. Amma kuma duk da hakan a tsorace take. Don kamar an cire mata haukar kanta ita da sauran y'ay'anta. Aina'u kuwa sai bin su take yi da idanu gabanta na fad'uwa. "Ku shigo daka ciki mana. Marabanku. Sannunku da zuwa. Ku k'ariso ciki." Fad'in Baba yana mai dogara sandarsa tare da basu hanya. Allah yaso yau da safe Sarah ta biya Aina'u dubu biyar ta gyara d'akin Baba tsaf duk da kuwa babu komai a ciki sai yaloluwar katifarsa, don ko ledar tsakar d'aki babu sai siminti kawai. Na'ima taho ki shimfid'a masu tabarmar." Fad'in Baba. Babu musu da sauri Na'ima ta nufi d'akin Baba tare da shimfid'a k'atuwar wankakkiyar tabarmar baban tare da saurin fita. Su Hajiya da su ya Abdullah suka shige cikin d'akin Baba tare da zama a kan tabarmar ba tare da nuna kyama ba. Na'ima kuwa da sauri ta fad'a d'akinsu tare da soma d'akawa Sarah duka don ita bata ma san mai ke faruwa ba don tun k'arfe goma take bacci bayan ta gama kelaya amai mai kashe jikin d'an Adam. "Dan ubanki ki tashi ga dangin saurayinki sun zo." Da sauri Sarah ta tashi jin abunda Na'ima tace. "K'anwata wallahi kin tako arziki. Kin san su wanene suka zo gidan nan kuwa. Bud'e window ki fara lek'a waje tukun." Fad'in Na'ima. Da sauri Sarah ta tashi ta nufi window kasancewar ta waje yake tare da bud'ewa. Da sauri ta jawo ta rufe tana kallon Na'ima tare da fad'in, "Na'ima sojoji na gani a layin? Wa aka kashe. Ba dai _Lucky boy_ bane ya d'auko mana magana. Yanzu hakan wayar wani sojan ya sato. Mun shiga uku mu kan yau." Fad'in Sarah tana neman fashewa da kuka. "Banza kawai! Nace maki dangin saurayinki ne yazo. Ina ga fa babansu baban Soja ne. Don yanzu haka har da mahaifinsa da y'an uwansa suna d'aki wajen Baba." Waro idanu Sarah tayi tare da fad'in, "What! Mai suka zo yi to?" Hannu Na'ima ta watsa gefe tare da fad'in, "To to wa ya sani. Watak'ila dai sha tara na arziki suka zo baki. Ke dai wallahi kin tako! Bari na fita na bawa idanuna abinci." Na'ima na fad'in haka tayi waje. A can d'akin Baba kuwa, bayan gaishe-gaishe da suka yi a tsakaninsu, sai Hajiya tayi nuni ga yaya Abdullah tace, "Wannan shine babban d'ana, soja, lutanan genaral ne, sai wannan, shi kuma barista ne, wannan kuma d'an sandan farin kaya. Na san ka san wannan ko? (Tayi nuni ga Khalil) tare da cigaba da fad'in Shi kuma dakta ne. A jiya na samu labarin b'arnar da ya aikatawa 'yarka, kuma mun tsaresa ni da y'an uwansa sai da ya fad'a mana gaskiya na cewar fyad'e yayi mata" dai-dai nan Lami ta shigo d'akin ita dasu Nuratu hannunta d'auke da farantin wanda aka sanya ruwan gora mai sanyi da kuma kwalin exotic d'in da _Khalil_ ya kawo ta ajiye tare da rab'ewa tace, "Sannunku da zuwa. Ina wunin ku?" Hajiya da yaa Abdullah suka amsa yayin da Barrister da ya Abdul-Hakeem suka gaisheta. Don a girme ya Abdullah ya girmi Lami sai dai suyi sa'a da Baba Nuhu. "Ita ce mahaifiyar yarinyar." Baba ya fad'i yana mai nuni da Lami wacce ta sunkuyar da kai kamar mutuniyarki. Baba da _Khalil_ kuwa mamaki ne ya kashe su ganin yanda Lami ta natsu. Kuma natsuwarta nada nasaba da kwarjinin da ya Abdullah yayi mata da kuma tsoron uban sojojin da ta gani a waje. Hatta su Nuratu wani irin natsuwa suka yafo suka daurawa kansu. Cike da ladabi suka gaishe da su Hajiya sannan suka fita. Hajiya ta cigaba da fad'in, "Dan girman Allah muna neman yafiyarku duk da kuwa mun san an cuce ku, domin duk wanda ya b'ata maka y'a yayi maka cuta mafi muni don ya b'ata mata record. Amma fa baza mu tilasta ku ba, ga d'ana nan Muhammad Kabir, a shirye yake da ya tsaya maku idan har kuna neman adalci a kotu. Wallahi d'ari bisa d'ari na bashi goyon baya da ya tsaya maku tsayin daka har sai alk'ali ya yanke hukunci bisa adalci." Murmushi Baba yayi yana mamakin karamcin irin na Hajiya tare da fad'in, "Duk bata kai haka ba Hajiya. Kuskure dai an riga anyi, sai dai a tari gaba kawai. Allah dai ya yafe maka kura-kuran mu gaba d'aya ya kuma kiyaye na gaba. Amma maganar zuwa kotu duk bata taso ba. Kuma har gida kamun zuwan ku, shi Ibrahim ya shigo har nan d'aki ya bani hak'uri kuma ya shaida min kuskure ne da sharrin shaid'an. Tun a wancan lokacin ni na yafe masa wallahi. Kuma ina mai tabbatar maku itama Saratun ta yafe masa." Kallon Lami Hajiya tayi tare da fad'in, "Baiwar Allah nasan sai kin fi kowa jin zafin wannan abu, kiyi hak'uri ki gafarci d'ana. Nasan zafin da kike ji matsayinki na uwa." Da sauri Lami tace, "Wallahi babu komai ai ya wuce. Ibrahim ya wanke laifinsa ai." Lami ta fad'i tana washe baki. Baba da _Khalil_ kuwa addu'a suke ta yi cikin zuciyar Allah yasa kar Lami ta nuna halinta. "Ina ita yarinyar take?" Fad'in Hajiya. Da sauri Lami ta mik'e tare da fad'in, "Bari a kira ta." Tana fad'in haka ta fice. Kai tsaye d'akinsu Sarah ta nufa. Tsaye ta same ta duk tayi jugum-jugum. "Ki fito mahaifiyar uban cikin nason ganinki." A rud'e Sarah tace, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Wayyo Allah mai zan yi mata." A zafafe Lamin tace, "Zaki fito ko sai naci ubanki. Shegiya y'ar bak'in ciki. To kyauta za tayi maki." Sarah bata k'ara cewa komai ba sai d'aukar dogon hijjab d'inta har k'asa da tayi ta saka tare da fitowa ta nufi d'akin Baba gabanta na fad'uwa. Sallama tayi sannan ta shiga tare da rab'ewa waje d'aya. Tun da ta shigo _Khalil_ ke binta da idanu. Kuma a kallon farko da yayi mata ya gane halin da take ciki na tsoro. "Ina wunin ku?" Sarah ta fad'i muryanta na cracking. "Taho nan d'iyata. Zo nan kin ji." Fad'in Hajiya tana mai mik'a mata hannu. A hankali Sarah ta mik'e ta nufi inda hajiyar take tare da zama kusa fa ita kanta a k'asa. "Kiyi hak'uri d'iyata. Sannun kin ji. An cuce ki tabbatas. K'aramar yarinya dake." Ita dai Sarah bata ce komai sai zuciyarta dake bugawa da sauri da sauri. Ga wannan k'amshin turaren _Khalil_ wanda ya riga ya kama jikinsa da yake kashe mata jiki. Gyaran murya yaya Abdullah yayi tare da fad'in, "Baba mun yanke hukunci a kan _Ibrahim_ shi zai auri Saratu idan har ka amince." Baba ya d'ago ya kalli ya Abdullah tare da fad'in, " _Ibrahim_ yazo min da wannan maganar na kuma amince masa a wancen lokacin amma kuma nace masa sai da amincewarku, kuma shi yasan dalilin da yasa nace hakan." Yaya Abdullah yace, "Yarinyar nada wani matsala ne wanda ya kamata mu sani?" Girgiza kai Baba yayi tare da fad'in, "Yarinya bata da wani matsalar komai. Sai dai yayyinta basa jin magana wanda hakan yasa ake masu kud'in goro har da ita Saratun. Amma Saratu natsatstsiyar yarinya ce. Na fad'a maku hakane da baki na ba sai kunji a waje ba. Don na san dole ne kuji. Don karo ba bakwai kenan ana fasa aurenta. Wannan na k'arshen ma sabida abunda ke cikinta ne yasa aka fasa. Don kowa kallon mara kamun kai yake mata." Kamun ya Abdullah yace wani abu Hajiya tace, "Wannan ba matsala bane, don laifin wani baya tab'a shafar wani. Mu baza muyi maku butulci ba musamman ma da ya kasance har da sanadin abunda _Ibrahim_ yayi mata wajen rugujewar aurenta. In Sha Allah _Khalilullah_ shine mijin uwata Saratu. Da zarar Sarah ta haihu lafiya, satin suna shine zai zamo ranar d'aurin aurenta da _Khalil_, ko yanzu haka ma sabida ba zai yi ayi aure da ciki bane, da sai ince a d'aura auren kawai. Sai dai ina mai gargad'in ku da babban murya kar hakan ya saka ku zubda cikin nan dake jikin yarinyar nan don hakan zai zama zunubi biyu, kuma idan har da gangan aka yi hakan, to ina mai tabbatar maku _Khalil_ ba zai auri uwata Saratu ba." _Khalil_ ji yayi kamar ya tashi ya taka don dad'i. Bai tab'a d'auka abun zai zo da sauk'i har haka ba. "Nagode Allah ya saka da alkhairi Hajiya. Ya Abdullah Allah ya k'ara girma ya dad'a kareka daga sharrin mak'iya. Baba na gode da ka bani Saratu." Da ameen duka d'akin suka amsa. Lami kuwa ta gama cika faaam bisa hukuncin da Baba ya yanke. Don bata shirya aurar da y'arta ba. So kawai tayi su tatsi kud'i iya kud'i a jikin _Khalil_ amma kwarjini da tsoro sun hanata ko kwakkwarar tari. Aina'u dake labe jikin windon d'akin Baba, wasu irin mak'udan hawaye ke zubo mata, bata tab'a tunanin kiran Hajiya a waya zai haifar da wannan abu da ya faru ba. Ta d'auka Hajiya za ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????tayi fushi sosai ta kuma jawa _Khalil_ d'in kunne akan kar ya kuskura ya k'ara zuwa nan gidan sannan kuma ya k'aryata cewar cikin jikin Sarah nashi ne. Barin wajen window d'in tayi da sauri tana toshe bakinta tare da soma magana cikin zuciyarta, "Ba zai tab'a yuwuwa ba, ba zan tab'a bari Sarah tayi aure ba. Baza ta tab'a auren _Khalil_, sai na jawo mata bala'i da masifa a rayuwarta idan har ta matsa sai ta aure sa." Ya Abdullah kud'in da bai san adadinsu ba ya ajiyewa Baba a kan katifarsa tare da fad'in, "Mun gode Allah ya saka da alkhairi. Ni zan wuce. Jirgin k'arfe biyar zan bi." Hajiya ma mik'ewa tayi tare da fad'in, "Mun gode fa sosai. Allah ya bar zumunci. Y'ata, Allah yayi maki albarka." Ta fad'i hakan tare da kamo hannun Sarah ta saka mata wasu warwaro guda biyu na zinari. Barrister da Abdul-Hakeem dukkan su sai da suka ajiyewa Baba kud'i a kan katifarsa kamun su fice daga d'akin. Har wajen k'ofa Baba ya raka su Hajiya yana d'aga masu hannu. Mutanan unguwar

14 / 60