Author : Billyn Abdul Category : Action Novels
yaran nata. Ƙayataccen ɗakinta ta shiga, ta zauna a bakin makeken nata gadon hannunta dafe da kanta. Jitake kan nata na wani mugun sara mata, sai dai abinda ke mata kai-kawo na takaicin yaran nata na son danne ciwon. Lallai lokaci yayi da zata nunama su Nabeeha ita ba sankaran uwa bace sha-sha-sha kamar yanda suke tunani. Taya zata bari ma Nasiru yaci nasara a kanta, bayan ya rabata da Jiddah ya rabata da Nabeeha da Ismat da suka rage mata kuma. Ta jima da fahimtar soyayyar da Ismat kema Ja'afar, sai dai bata damu ba ganin yanda shi Ja'afar ɗin yaƙi kulawa, amma yanzu ta fahimci Ismat na zuga Nabeeha ne su koma gidan ubansu saboda son da take ma Ja'afar, kenan da sunje sun kwantar ma da ubansu kai itama sai ya aura mata shi, shekenan ita kuma A'isha ta haifama ƴaƴa ko? To kuwa zasuci ubansu.
Da wannan tunanin tai ƙwafa, tare da miƙewa zuwa gaban wadrobe ɗinta, ta ɗibo duk passport ɗinsu dake wurinta, cire na Nabeeha da Ismat tayi ta canja musu waje, daga haka ta hau shirin fita. Dan tana buƙatar ganawa da Adeel yanzu nan basai gobe ba.....
§§§§§§§§§§§§§§§§
★EGYPT ★
“Mammah muje ki huta yau kam kin gaji fiye da kullum. Ga su Yaya Ma'aruff nata kira nasan burunsu kawai suji yanda results ɗin suke ne. Aunty Ummi ma naga ta kira video call ta WhatsApp”.
Murmushi Mammah tayi, cikin sauke ajiyar zuciya ta ce, “Ammar yarana duk sunyi kewata ne, nima ina tsananin jin kewarsu. Dan haka ni kam ba sai sati biyun nan ya cika ba zuwa jibi tunda sunce babu wata damuwa suna bamu maganin nan kawai mu koma gida”.
“Duk yanda kike so haka za'ai Mammah”. Yay maganar yana ɗan rungumota ta gefe, dama kuma suna tafiyar ne hannunta riƙe a nashi. A yanda ya ɗan rungumetan yana dariya itama yana murmurshi da kai masa rankwashi a kai yasa basa kallon gabansu balle mai tahowa. Karaf kuwa sukaci karo da wani abun da ya saka Mammah faɗin, “Subahanallahi”. Shima sai Ammar ɗin ya sake ta yana waiwayawa da ambaton, “Ya salam”. A dai-dai lokacin shima wanda sukai karon ya ambaci, “Subahanallahi” ɗin yana kaiwa duƙe da son riƙo takardun hannunsa da suka tarwatse a ƙasa. Cikin sauri Ammar ya bishi shima yana ƙoƙarin taimaka masa da sake faɗin, “I'm sorry sir”.
Fuskar mutum da murmurshi ya ce, “Karka damu ɗana, nima harda nawa laifin hankalina nakan takardun ne shiyysa ban lura da tahowarku ba. Mama kiyi haƙuri kem......”
Ya kasa ƙarasawa saboda dai-dai ya ɗago ne zai kalla inda Mammah ɗin take sukai ido biyu. Dan itama ta miƙo masa takardar data ɗakko ne datai gefe zatai magana a lokacin, sai ta dakata cak tana kallonsa. Ko shekara dubu tayi bazata manta wannan fuskar ba a duniyarta, balle shekarun da basu wuce talatin ba. Jin sunyi shiru Ammar daya gama tattarowa shima ya juyo yana kallon su, Mammah ya fara kallo datai tsaye ƙyam baki buɗe tana kallon mutum, da sauri ya maida kallonsa kansa shima. Ai da sauri ya wani ja baya yana waro idanu waje da faɗin, “Ya rabbi! Mammah waye shi?”.
Mammah da gaba ɗaya kanta yay wani dimmm ta gagara cewa komai, sai hannunta dake ƴar rawa har sai da Ammar ya matso ya riƙota jikinsa, sai dai har lokacin idanun nasa akan mutumin da alamu ya nuna shima dai yayi sumar tsugunne ne......
>>✿<<>>✿<<>>✿<<
“Assalamu alaikum”.
Aka kwaɗa sallama daga bakin ƙofar falon bayan anyi knocking har sau biyu. Ƙaramin tsaki Mu'azz dake zaune shi kaɗai a falon yana cin abinci yaja, ya tsani tashi yana cin abinci, dan yana tashin shike nan abincin ya fita a kansa kuma. Hanyar kitchen ya kalla inda yake jiyo surutun Nimrah da dariyar Biebah. Sai kawai ya ɗaga murya ya ce, “Ninah!”.
Daga can ta ce, “Kai Yaya Mu'azz miye kuma dan ALLAH? Bana kawo maka harda ruwa ba”.
“To uwar son jiki, dalla fito kiga waye ana knocking ne”.
Baki a sama ta fito, tana sanye cikin shirt da riga na lass milk da furanni coffee. Tayi ƙyau sosai daka ganta kaga ƴammatan zamani masu shegen iyayi da rawar kai. Harta nufi ƙofa ya ce, “Haka zaki fita ba hijjab?”. Baki ta ƙara turawa gaba, ta dawo ta ɗauka hijjab da sukan ajiye a falon saboda irin haka, dan Mammah ta saba musu sakawa musamman idan akai baƙon ido ko suka saka ƙananun kaya, wani lokacin ma sai taga kamar anfi takura mata da sakawa fiye da Ruky da Aunty Biebah. Sai da ta saka ta zura hannayensa sannan ta nufi ƙofar da aka sake bugawar, sallamar maigadi ta amsa tana buɗe ƙofar. Ya ɗan ja baya yana gaisheta.
“Baba ni dai ka daina rissina min dan ALLAH. Ina wuni?”.
Murmurshi maigadin yayi da faɗin, “Ai girmanki ne Hajiya. Dama baƙone yazo yace kuma sabon driver ne Malam Buba tsohon Driver ya aikosa”.
Ɗan jimm tayi sai kuma ta ce, “Okay to bari na sanarma Yaya Mu'azz, dan su Uncle's duk basa nan. Ammie da Ummie ma sun tafi gidan Mom (Aunty Mimi suke kira Mom) data haihu ɗazun”.
Fuska ɗauke da murmushi ya ce, “ALLAH sarki ALLAH ya raya, ya albarkaci abinda aka samu”.
“Amin ya rabbi”.
Ta faɗa tana rufe ƙofar ta juya ciki.
“Yaya wai sabon driver ne, kuma Baba Driver ya turoshi”.
Ɗagowa Mu'azz yay yana kallonta, sai kuma ya maida kansa ga television yana faɗin, “Oh to sannunsa da zuwa. ALLAH ya iyakance min jigilarku kullum kuna damuna da surutun ku da fitina. Ki haɗa abinci ki kai masa dan abinci nake ci sai na kammala na fita mu gaisa”.
Sai da ta cika baki da iska cikin ƙunƙuni ta nufi kitchen tana faɗin, “Ni wlhy yau ƙafafuna duk ciwo suke, dan anga Mammah bata nan sai wahala ake bani, yau tunda muka dawo school ban huta ba komai ni....”
Fiiiffgg! Filon kukera da Mu'azz ya jiho ya sameta a baya. Tako dage ta ƙwalla ƙarar data saka Biebah fitowa daga kitchen da gudu tana tambayar lafiya da riƙo Nimrah ɗin. Kai Mu'azz ya girgiza cike da takaici yana nuna fillon daya jefeta da shi.
“Small Mom fillo fa kawai na jefa mata dan tana min ƙunƙuni shine take wannan ihun. Wlhy Ninah kiji tsoron ALLAH. Wai uwar wa ma ya hanaki bin su Ammie ne kamar yanda Ruƙayya tayi?”.
“ALLAH sai na gayaka da Uncle, kuma ai dai naji zafi. Tunda na dawo kaketa sani aiki, na maka gyaran ɗaki, kace na maka ɗan wake, duk baka gani ba sai da ka ci zalina”.
“Oh gori kike min saboda kin min gyaran ɗaki da ɗan wake? Lallai ma Ninah ni ko”.
Kai Biebah ta girgiza da jan ƙaramin tsaki ta koma ciki tana faɗin, “Kudai bazaku taɓa canjawa ba ALLAH ya shirye ku. Ba sai ku cinye kanku ba jarababbu. Wlhy na ƙagara Mammah ta dawo gidan dan kun isheni”..........✍️
*_Typing📲_*
*_💦KIƊA A RUWA...!!💦_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_GENERAL FICTION_*
_Wannan labari ƙirƙirarre ne. Sunaye, wurare, da abubuwan da suka faru duk ƙirƙira ne, ba su da alaƙa da gaskiya ko wani, koda Bilyn Abdull ce 😂._
*_BOOK 2_*
_Chapter 13_
__________________
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/H1G4LliRqxk3ndOn6BNUES Assalamu Alaikum my people dafatan kunanan cikin aminci sunana ummuh sayyeed yar mutan Chadian traditional medicine center Zaria dealer in all kinds of magungunan mata turarukan wuta sudaniss dilka skin care products Ina kuke uwar gida mai capacity da amarya shalelan miji kumatso tafiyar takuce Kai har zawarawa banbariba balle Kuma yanshila tooo kumatso kusa yar mutan Chadian tace bazata barku a gantalaba domin kuwa Ina mai farin ciki sanardaku garabasar danata nadarmuku my customer kasaitaccan promo dazan muku wa inda basusamu ba to o gadama takarasamuwa tundaga yau (__25__11__2025_) harzuwa end of this month dinnan
Ga PRODUCTS DINMU KAMAR HAKA
Maganin sanyi set
Madarar tabaje
Tsumin bom
Gumbar narkakken dabino
Gumbar Aya
Zumar goron tula syrup
Matsin bakar kaya set
Home secret
Mallakar kasa
Turaran tsuguno
Humra brown
Humra duffur
Body milk 24hr
Turaran rushi sandal
White kajiji
Black kajiji
Sandalfleks
__________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________
..........Da gudu Nimrah tabi bayanta saboda wani fillon da Mu'azz ya ɗauka alamar zai ƙara jifarta da shi. Nan ma Biebah ta girgiza kai kawai tana cigaba da aikinta. Ita kuma ta nufi babbar kular abincin gidan ta ɗauka plate mai ƙyau ta zuba abinci. Dan su babu wani banbancin kwanon cin abincin masu gida da masu aiki. Suna daraja su, suna basu girmansu na ƴan adam. Gorar ruwa da lemo ta ɗauka duk ta haɗa akan tray, har zata ɗauka Biebah tace, “Dama kin haɗa dana maigadi shima dan bana jin Hinde takai masa”.
“Small Mom wlhy zai mun nauyi, wannan ma fa da ƙyar zan kai”.
“Nauyi fa? Ninah anya bada tsallen tsalli watsanga ba ranar haihuwar ki? Ke dai son jiki kamar wata kasa.”
“Small Mom ni bama zanyi auren ba ai balle na haihun, babu inda zanje nabar Mammah ta da su Uncle's ɗina. Kema bana son kiyi aure, kawai muyita zamanmu a haka yafi daɗi”. Ta ƙare maganar tana kashewa Biebah ido ɗaya.
“Mara kunya kawai, ni wuce ki ban waje”. Biebah ta faɗa tana dariya. Acan ƙasan ranta kuwa babu abinda ke faɗo mata sai fuskar Dada a ranar da aka ɗaura aurensa da Ninah ɗin, auren da Mammah ta hana kowa sake tada batunsa a gidan tace idan lokacin a sani yayi ayi. Murmurshi ta sake saki dabin bayan Nimrah data fita itama tana murmushin cikin tafiyarta ta yanga kamar yanda kowa ke faɗa. Dan Nimrah da Ruky irin ƴammatan nan ne masu shegen iyayi da gwalangwaso tun basu tafasa ba suke neman ƙonewa. Shekara biyu da suka wuce sannan suna 12years js 1 ta kamasu suna shirin makaranta sun ɗura suwa a leda sun saka cikin bra ɗinta da suka sata bata sani ba suka saka, suna ganinta suka ɓoye, ta tsaresu akan sai sun nuna mata kota rubuta ta ajiye duk randa Dada ya dawo ta nuna masa. Duk da basuyi hankalin sanin Dada ba labarinsa da yanda idan sukai laifi ake tsoratar da su da sunansa yasa suna jin shakka da girman mai wannan suna fiye da kowa a gidan. A wasu lokutan Ruky tafi Nimrah tsoro, sai ta sanya kuka tana nuna mata hannun bra ɗin. Ta shiga salati da tafa hannaye, cikin mamaki ta ce, (“Yanzu ku ubanwa ya saka ku saka bra?”).
A lokacin bakin Nimrah a sama ta ce, (“Small Mom wasu shaggun yara ne su Zerah a ajinmu suyita tura ƙirji sama wai su masu abu, sai suyita mana iyayi da labarin period, idan munyi magana suna mana dariya wai mu yara ne ƙwailaye, shiyyasa muma mukace zamu nuna musu munfi ƙarfin ƙwailaye wlhy”) dariya sosai zancen ya bata a lokacin, sai ma ta kasa musu faɗan ta shiga tuntsurawa. Ta kuma kasa hanasu tama fita. Ba kuma su fasa sakawar ba har sai da suka fara ƙirgar dangin na gaske, abubuwan suka fito. Shiyyasa idan ta tuno ita kaɗai sai taita dariya. Dan ko a yanzu tana fahimtar wataran ciko suke yi a cikin bra ɗinsu dan ƙirjin ya cika fiye da nasu duk da kuwa su duka ALLAH ya basu ba laifi. Sai dai da yake ba'a gama cika ƴammatan ba suna nan dai-dai da ɗan jikin su.....
<<<★>>><<<<★>>>><<<★>>>
★SOUTH AFRICA ★
“Amma baka ganin zuwanka gidan zai iya zama haɗari? Musamman daya kasance akoda yaushe Imran ɗin nan yana zaryar shiga da fita a cikinsu. Kai komai ma na zartarwar gidan shine tamkar a madadin abokin nashi a yanzu. Akwai zuminci mai girma da faɗi a tsakaninsu da bashi da shamaki da su fa”.
“Na sani ɗan uwa, amma bani da wani zaɓi sai nayin hakan. Shiyyasa nace maka zan ɓadda kama ai, kai dai kawai ka sama min irin facemask ɗin nan mai ɓadda kamanni da muke gani a films, dan gaskiya ba zan sake iya sati a wannan ƙasar ba. Dole na koma a gaɓar da za'a sake sabon wasa da yafi na baya zafi da armashi. Lokacin ɗaukar fansa yayi. Lokacin da Zak-Shadow zai tabbatar da KAREN BANA SHIKE MAGANIN ZOMON BANA kenan.”
Ƴar dariya abokin nasa yayi da faɗin, “Ka san miyasa kake birgeni kuwa Dude?”.
“Sai ka faɗa”.
“Kai jarumi ne, tsayayyen mutum mai ra'ayin kansa da bai da tsoro. Na tabbatar zaka iya fiye da abinda ka faɗa. Ina bayanka kaje a dama da kai cikin wannan babbar ƙurar dan ɗaukar FANSA. Ni kuma na maka alƙawarin baka kowane irin taimako kake buƙata, kawai da kaji ƙyaras ka danna min kira”.
“An gama abokina, shiyyasa nake sonka”. Tafawa sukai suna dariya cike da farin ciki. Kafin abokin ya ce, “To yanzu a matsayin me zaka je musu?”.
“Ina kan tunani ban yanke ba. Amma a labari mai inganci na samu cewar driver ɗinsu yayi accident 4weeks ago, inaga zanje matsayin me neman aikin tuƙin”.
“Alright hakan yayi, amma dai kabi a hankali dan kasan shima Imran ɗin nan shegen kansa ne, tamkar Hussain ɗin Zak-Shadow yake”.
“Karka damu oh, nima fa yanzu hatsabibin kaina ne, zan iya da kowane kalar zafin kansa. Tunda ma ba shine Hassan ɗin ba ai da sauƙi”.
“A Hassanu kam na can a garƙame”.
Dariya sukayi a taƙaice, saboda yanda abokin nasa yay maganar yana wani yarfa hannu da tallabe haɓa kamar ɗan daudu....
~~~~~~~~~~~~~~
★Nimrah kam data fito da trayn abinci kai tsaye bakin gate ta nufa, sai da tunda ta fito daga kitchen taji wani mummunan faɗuwar gaba ta sameta. Ajiyar zuciya mai ƙarfi taja tare da furzar da numfashi ta maida ƙofar ta rufe. Dama ta baya tabi saboda Mu'azz abokin faɗanta da kullum ne sai sunyi da shi ita da Ruky sama da sau goma. Yanzu zasu cashe anjima kaɗan ka gansu suna hira kamar abin arziƙi, da wahala kuma akai ƙarshen hirar ba'ai sabuwar rigima ba. Shine suke kallo kamar sakon su, shima kuma hakan yake kallonsu shiyyasa suka koma kamar kajinaye. Mu'azz tsokana, Nimrah da Ruky tsiwa.
Kamar mara laka a jiki ta ƙaraso bakin gate ɗin, inda tunkan ta ƙaraso maigadi ya miƙe da sauri yana faɗin, “Autar Mammah da kanki? Ai da kin kirani na amsa ko?”.
Batace masa komai ba face ɗan murmushi, sai da ya amshi tray ɗin sannan ta furta, “Na baƙo ne, bara naje na kawo maka naka kaima, ko su Kulu sun kawo maka ne.”
“To to ƴar albarka sannu nagode. Basu kai ga kawowa ba kam inaga aiki ne yay musu yawa”.
Nan ma bata tanka ba ta juya ta koma, zuciyarta na ƙara ƙarfin rawa kamar zata faso ƙirjinta. Kai har cikin ƙafafunta take jin wani kalar sanyi na ratsata da kasalar jiki. Haka dai ta daure ta sake ɗebo wani abincin ta sake kawo musu. Dai dai baƙon mutumin na fitowa daga bayin maigadi da buta a hannu. Ido su ka haɗa, ƙirjinta yay wani mummunan motsawa, har ta kusa cin tintuɓe zata faɗi ALLAH ya taimaketa maigadi ya tare abincin data watsar da shi a wajen kam.
Sannu maigadi ke mata yana kallon ƙafarta, haka shima baƙon a karo na farko ya ce, “Yi a hankali, badai kiji ciwo ba ko?”.
Idanunta a kansa ta jinjina kanta, sai kuma cikin rawar murya ta ce, “Ina yini”.
“Lafiya Lau, mun sameku lafiya? Ya tsofaffin?”.
A taƙaice ta ce, “Alhamdullah”. Sai dai muryarsa sai wani irin kai kawo da mata maimaici take a cikin kunneta da zuciya da ƙwaƙwalwa. Sai kuma ta bar wajen da sauri. Tayi ɗan nisa ta waiwayo ta sake kallonsa illahirin jinin jikinta na gudu kamar mai shirin tsiyaye wa ta ƙofifin gashi, karaf kuwa suka haɗa ido alamar shima kallon nata yake. Sai kawai ta ƙara sauri. Koda taje bakin ƙofar ma ta sake juyowa nan ma suka haɗa ido. Wufff ta shige ciki har Biebah na tambayarta lafiya.
“Ba komai Mom”.
Ta samu kanta da bama Biebah amsa a taƙaice tana share zufar data jiƙe mata goshi. Dole ta kama hijjab ɗin jikinta ta cire ta ajiye ko zata samu iska ta ɗan ratsata. Dan jikin window ma ta koma tana ta sauke ajiyar zuciya tsahon mintuna kafin ta koma gaban fright ta ɗauka ruwa mai sanyi sosai ta sha har roba ɗaya. Daga haka ta ƙaraso kusa da Biebah ta ɗauki wainar fulawa ɗaya tasa a plate dan dama ita suke soyawa ko hakan zai sa ta samu sassaucin yanayin da take ciki kafin wani ya farga.
A can gate kuwa murmushi maigadi yayi da faɗin, “Ɗan uwa bismilah ga abinci ko. Karka damu in dai Auta ce zakaga fiye da haka a wajenta. Ba komai