Advertisements
Chapter 13 Reading Kida A Ruwa Book 2 Complete Hausa Novel Hausa Novels
Advertisements

Kida A Ruwa Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Billyn Abdul Category :  Action Novels

Chapter   13 / 24

36K to 39K   out of 71K words

yana jan Ammar a jikinsa......

%><%><%><%><%>

         Kwance take a madaidaicin gadon ɗakin daya kasance guda biyu iri ɗaya hannunta da waya tanata faman zabga murmushi, kai da gani kasan wani abu dake ƙayatar da ita take kallo. Dai-dai nan Ruky ta buɗe ƙofar bayinsu ta fito, ɗaure take da towel alamar wanka tayo, ganin yanda Nimrah ke zabga uban murmurshi bakinta har kunne yasa ta matsawa kusa da ita ta yarfa mata raɓar ruwankan dake ta bin farar fatarta.

       Ɗagowa Nimrahn tai da sauri irin na firgita, dan haka Ruky ta ƙyalƙyale da dariya. Cikin harara ta kai hannu ya goge ruwan data yarfo mata ɗin ta ce, “Ƴar wulaƙanci miye na yarfa min ruwa?”.

     Ruky na ƴar dariyarta har yanzu ta ce, “Gani nai kinata faman washe baki kamar ƴar tallar makilin, wai har yanzu hoton jaririyar kike faman kallo?”.

        “Humm bazaki gane ba Ruky ALLAH jarirai nada ƙyan kallo, ina son jariri sosai, shiyyasa kike ganin duk sanda su Ammie suka haihu nake tarewa a sashensu. Ke nifa ko aure nayi duk shekara zan dinga hauhuwa”.

      “Kambu, Ninah amma baki da hankali, duk shekara fa?”.

    “Eh wlhy, ke ni ƴan bibbiyu ma”.

  Zama kusa da ita Ruky tai da mai a hannu ta ce, “To ALLAH ya baki. Ni sai da kikai maganar haihuwa ma kika tuna min da sayyadi Kamal. Hummm bawan ALLAHn nan fa da gaske kamar yanda ƴan ajinmu ke gulma ya mutu a kanki Ninah, idan yana karatu hankalinsa duk a kanki. Ga kuma Teacher Khalil, yanda ya wani dage yana karemu randa muka suburbuɗi Hibba Abubakar na sake tabbatar da zancen Maimoon Qasim fa”.

     Baki Nimrah ta taɓe tana gyara zama. “Ruky rabani da wannan shashancin kinji, ni wlhy duk basu min ba.”

       “Kai Ninah kiji tsoron ALLAH, wlhy duk ɗinsu sun haɗu, dama dai kawai kice ba yanzu ba ne sai na yarda, dan mukace mun kawo samari yanzu ai ƙaniyarmu Uncle's zasu ci, musamman Uncle Bilal da akoda yaushe yake mana gargaɗin nan. Amma ALLAH nidai ina son soyayya, kinga idan naga Seniors ɗin mu na lobewar nan da boyfriends ɗinsu, ko mazan da ƴan mate ɗin mu sai naji kamar na bama Anwar ko Uncle Haneef ɗin gidan Mamy dama”.

         “Lallai Ruky baki da hankali, yo ALLAH na tuba ko soyayya zanyi mi zan wani yi da ƴan tamatsitsin yaran school ɗin mu. Yo yaushe suma aka gama aikarsu kiran yayunsu gida. To ALLAH bari kiji, ko dariya naga kimma wannan Anwar ɗin sai na ci masa mutunci. Karki maida mu marasa aji mana, ƴan yara da su inama laifin kamar Yaya Ammar haka. Amma kosu Teacher Khalil nawa suke”.

       “Hhhh shegiya Ninah, wato marasa aji? To yaushe ma muka gama tafasar balle mu ƙone har kike batun wani aji. Shekara sha biyar fa muke. Ga aunty Biebah nan harta kammala master ɗinta bata ma zancen aure, ta dage sai Dada ya dawo gida zatai aure. Hakama Aunty Ma'u dake ƙoƙarin kammala Secondary ita da Aunty Halimatu, balle azo kammu haihuwar jiya inji Yaya Mu'azz. Da kike kiran su Teacher Khalil yara kuma, ai bana jin Yaya Ammar zai girmesa. In baki so kamarsu ba tsoho kike so kamar su Daddy ko mi?”.

       “Ƴar wulaƙanci, kamar su Daddy kuma? Kamar shekarun Uncle Ammar dai, amma kamar su Daddy ai da kunya ƴar soyayyar nan bazaka samu ka bajeta ba, kin san kuma nifa ina son harkar nan ta love ba wasa” tai maganar tana kashema Ruky ido ɗaya, bata jira cewar ta ba ta cigaba da faɗin, “Ya Mu'azz kam bar ɗan rainin hankali, shima sai kace ba haihuwar jiyan ba. Ya gama mana rashin m ɗinsa dai sai mun riga shi aure. Dan mu yanzu idan Daddy yace rana ɗaya za'a haɗa auren da Small Mom da su Aunty Ma'u mune next. Shifa, sai ya jira Uncle Bilal, Uncle Ammar da Yaya Khalifa ma ƙila, to ko Yaya Imam ya girmesa.

      “A'a wlhy kar ki masa baki, duka shekara nawa Yaya Khalifa ɗin ya bashi, sai dai ayi musu tare, gara Yaya Imam to, kuma shima tare suke tafi a school ai”.

    Cike da dariyar mugunta Nimrah ta ce, “Oho dai, ko haka ɗin mun more masa. Ke muyi gulma mana. Dan ALLAH baki ga wai kamar Uncle Bilal da Aunty Ma'u akwai wata a ƙasa bane?”.

      “Humm wlhy na gani, ranar graduation ɗin su Small Mom sai wani kallon ƙasan ido yake mata.” dariya suka kwashe da ita harda tafawa.

Nimrah ta ce, “Wlhy soyayya tayi Besty, idan ban samu ɗan soyayya ba na rako mata duniya”.

Cikin dariya Ruky tace, “Muna son soyayya zaki ce, ai duk wanda yazo sai mun tantance shi walle karki damu, love ai duniya ce”.

“A wlhy love duniya ce, shiyyasa nake son maƙalewa a sashen su Mamy, dan in ana bajakoli su da su Uncle's nasha kallona”.

“Muguwa, wlhy Ninah kiji tsoron ALLAH, tun baki tafasa ba zaki ƙone. ALLAH yasa su ganoki suci ƙaniyarki, kinga sai ai miki auren ai”.

“Shegiya ni da ke ai duk sammakal ne, zatace ta tadda muje mu”.

Dariya suka sake fashewa da ita suna tafawa.....

    Buɗe ƙofar ɗakin nasu ya saka su yin shiru, sai kuma duk suka rufe bakunan nasu da hannu. Biebah ta hararesu.

       “Anya kuna duba agogo kuwa? Kuke mana irin wannan ihun dariyar haka kamar sabbin kammu”.

      “Kai Mom ALLAH hira ce kawai tai daɗi”.

     “Kuma da ihu haka? Na sake jin wannan dariyar kamar ba mata ba sai na ɓata muku rai. Dalla ku bani wayata kuyi shirin barci ku kwanta” tana gama faɗa ta amshi wayar tata da Nimrah ke kallon hoton baby, Dan su basu da waya Uncles nasu sunce ba yanzu ba. Juyawa tai ta fita tana mai rufe musu ƙofar. Gwalo sukai ma bayanta a tare, kafin Nimrah ta miƙe zuwa bayin itama dan yin wanka. Bata wani jima ba ta fito, lokacin har Ruky ta gama nata shirin barcin ta haye gadonta, dan kowa da nashi. Ƙasa-ƙasa suka cigaba da hirar a haka kuma duk ta sanari har Nimrah ta shirya itama ta haye nata gadon.

       WASHE GARI da wuri suka ta shi, babban burinsu tafiya gidan Aunty Mimi ganin baby musamman ma Nimrah da jiya ba'aje da ita ba. Dan tana barci su Aunty Shariffa suka wuce da Ruky, sai yau Biebah tace zasu je tare tunda itama bataje ba taje Tahafiz, amma tace mata yau ma sai sunje sun dawo daga Tahafiz suma sannan. Rashin sabon barcin safe saboda makaranta yasa suna kammala salla sukai bitar karatun Alkur'ani dan sun san yau sayyadinsu zai amshi hadda sukai azkar kowa ya miƙe. Ruky ta fara gyara ɗakinsu ita kuma Ninah ta wuce gyaran ɗakin Biebah. Koda ta shiga ɗakin Biebah harta sauka ƙasa taya masu aiki haɗa breakfast ita kuma. Sun kammala gyara ɗakuna har bedroom ɗin Mammah duk da bata nan basa gajiya da gyarawa sannan suka shiga wanka. Dama bedrooms suke gyarawa da sama ɗakin su Yaya Ammar, sauran wajaje kuma masu aiki. Shirin sukai cikin uniform ɗin islamiyya su ash color na wando da hijjab har ƙasa tsahon hijjab ɗin yasa da yawansu basa yin rigar suke saka t-shirt a ciki. Fitowarsu dai-dai da fitowar Biebah daga nata ɗakin tana wani kalar sassanyan ƙamshin turare. Su duka kasa haƙuri sukai sai da suka tanka.

      “Woow Small Mom kin sayi sabon turare ne? Wlhy wani ƙamshin bala'i mai kassara jiki”.

      Murmushi tayi tana ɗan girgiza kanta. “Yan biyun Mammah kenan iyayen iyayi ƴammatan gobe. To wannan ƙamshin da kuke ji ba turaren kanti bane, haɗaɗen turaren gida ne dan khumra ce ma kawai na ɗan shafa sai kabasa da nayi a kaya na, nima a sashen Aunty Lailah na samoshi. Tace sun saya ne itama wajen Maman Abdull ita da Aunty Shariffa mai kamfanin SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387. Ni kaina ba ƙaramin rikitani ƙamshin sukai ba, yau ina dawowa zan kirata harna amshi number ɗinta zan saya”.

         “Kai Mom dan ALLAH ki haɗa damu, wlhy ƙamshin yayi sosai. Haba ALLAH jiya naje amso abu wajen Ammie ina shiga naji Uncle Ma'aruff na santin turaren data saka na wuta, ashe ita da Mamy ne”.

     “Eh tare suka saya, sunce Aunty Hafsat ta haɗasu da ita, kun san Mamanku bata wasa da ƙamshi shiyyasa ta riƙe Yaya Imran gam. Akwai Turare wuta, khumra kaloli har uku. black humra, white humra, brown humra. Akwai kuma oil perfume da kullacham da genine da Turare kabasa kaloli uku shima, white, black, and brown, har gyaran jiki duk tana yi”.

       “Wayyo Aunty zaki na suma, ALLAH kin san a gidan nan nice na gado Ammy son ƙamshi. Dan ALLAH ki haɗa damu”.

    Cikin dariya Biebah ta ce, “Uhmmm Ninah son bati kenan. Shike nan zan haɗa daku, amma ku bari sai na tambayi su Yaya sun ƙara mana kuɗi, dan nima kuɗin nawa baida yawa”.

     Cike da farin ciki suke godiya. Nimrah ta sake faɗin, “Ai muna dawowa islamiyya zan zarce gidan Ammy, in mun dawo gida ma harda sashen su Mamy”.

     Hararta Ruky tai da faɗin, “Mudai wuce, an gaya miki ke kaɗai zaki, nima ai kin koya min jarabar son ƙamshin. Irin wannan turarurrukan ai baka wucesu ALLAH”........✍️

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*

*_+227 98 94 12 81_*

*_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*

*_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899*

*_Moniepoint MFB_*

*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_*

*_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_*

*_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_*

*_Chapters & Audio_*

@BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276*

*_Access Bank_*

*_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_*

*_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_*

*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_*

*+234 805 568 7449*

*_Telegram Number👇_*

*+234 903 234 5899*

*_Maza ku matso MASOYAN Bilyn Abdull da IDANU suka hana karatun novels...._*

*_Tofa Bilyn ku ta samo muku hanya mai sauƙi da kina aiki, ko kina kwance kina hutawa, ko kina inda baki son yawan surutu earpiece ɗinki kawai zaki maƙala a kunne ko Bluetooth kisha sauraren littafin KIƊA A RUWA.... Cikin sauƙi.... 💃_*

*_Kar dai na cika ku da zance. Zamu fara saida littafin KIƊA A RUWA.... Na saurare (Audio) kenan akan farashi mai sauƙi da rahusa._*

*_Akwai VVIP AREWAPEN kenan 💃_*

*_Akwai VIP Telegram 💃_*

*_(Ƴan WhatsApp ku haƙura kawai ƴan ta'addar bati sunfi yawa a cikinku gaskiya tsoron rashin m ɗinku nake 😂🤣)_*

*_Telegram Audio 2k ne kacal ba tsada 💃. Sai kusaka ta wannan account ɗin👇_*



_(2k)_

*9032345899*

*_Moniepoint MFB_*

*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (2k)_*

*_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_*

*_Telegram Number 09032345899_*

*_Ƴan NIGER🇳🇪 kuma bazamu barku a baya ba in sha ALLAHU zaku biya (Telegram vip 1,500 CFA) domin littafin KIƊA A RUWA..... na ji Audio-vocal. Sai ki biya tanan👇_*.

_(1,500 CFA)_

*_+227 98 94 12 81_*

*_My NITA_*

*Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 1,500 CFA vip telegram*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*

*_+227 98 94 12 81_*

*_AREWAPEN (Vvip)_*

*_Chapters & Audio_*

@BilynAbdull

*_Ƴan WhatsApp kuzo muyi shawara idan zaku iya amana ayi harkar nan daku 😂, dan bana son a barku a baya duk da dai bakwa ji, ba raga min zakuyi ba na sani duk da ƙaunar da nake muku 🤣😂._*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💦KIƊA A RUWA...!!💦_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*

_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_GENERAL FICTION_*

_Wannan labari ƙirƙirarre ne. Sunaye, wurare, da abubuwan da suka faru duk ƙirƙira ne, ba su da alaƙa da gaskiya ko wani, koda Bilyn Abdull ce 😂._

*_BOOK 2_*

_Chapter 17_

__________________

https://chat.whatsapp.com/HKCgesG0ua47qN8hwnCNAo

Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu

Muna muku marhabun lale da shigowa wannan group din mai albarka

Muna saida turaruka na arebiyan perfumes da kuma designer's perfumes dana gida dana motar dana office dana labile da turaren kujeru da kuma by oils masu na mata dana maza masu sanyaya zukatan ma'abota san kamshi ,munada kayan kitchen masu kyau cikin sauki sai kunzo

https://chat.whatsapp.com/HKCgesG0ua47qN8hwnCNAo

https://telegram.org/dl

https://www.tiktok.com/@yusufjummai?_r=1&_t=ZS-91wLXnmiIIa

https://www.instagram.com/jummai342?igsh=dTQ0bnZobTRwN3Vm

07061352952 or 08034528104

__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

.......Gaba Biebah tayi tana musu dariya, dan in dai halayen Twins ɗin gidan nasu ne tafi kowa sabawa. Suna sakkowa dining suka nufa, Mu'azz ne kawai zaune yana kari shima sanye da uniform ɗin islamiyyar. Cike da neman magana Ruky ta ce, “Su Yaya yau kuma da yunwa aka tashi?”.

     Harara ya wulla mata, batare daya tanka ba ya cigaba da danna doyarsa a baki. Nimrah tai dariya tana zama a kujerar kusa da shi. “Kaga rabu da ita Yayana. Kasan ita Ruky wani lokacin uwar gulma ce. Ina kwana”.

      “Ai ke da ita duk sammakal. Wannan saurin gaisuwar bana ALLAH bane faɗa min nawa kike so?”.

     Dariya Biebah da Ruky suka sanya. Cikin ɓata fuska da tura baki Nimrah ta ce, “Kai Yaya sai kace wata mayyar kuɗi, kai shike nan bazamuyi shirin arziƙi ba sai ina son kuɗi”.

          “A to nasan halinki ne ai Ninah”.

    Tashi tai a kusa da shi ta canja kujera, ya ce, “Oho dai”.

Bata kula shi ba, dan dai-dai nan ma su Abees suka shigo da gudu suma sanye da irin uniform ɗinsu. Tuni Nimrah ta miƙe tana faɗin, “Oyoyo my Afry”.

     Ai ko da gudu Afrah tai kanta, ta ɗagata sama tana juyi da ita suna dariya dan ƴar gidanta ce. Su Aheel kuwa wajen Ruky da Biebah da Mu'azz sukayi suma. Nan fa surutun falon ya ƙaru, dan bayan yaran sun gaishesu suma duk zama sukai Ruky ta saka ma kowa abinci a gabansa. Sai da Biebah ta tsawatar ma surutun basu sannan sukai shiru kowa ya maida hankali ga abincinsa. Shaf-shaf suka kammala suka fito karsu makara.

      Yau sabon driver ɗin su ne zai kaisu. Wanda suna haɗa ido da shi yau ma gaban Nimrah ya faɗi, dan haka ta kauda kanta gefe tana gaishe shi kamar yanda su Biebah ke gaishe shi. Dan ba yaro bane. Gaba Mu'azz ya shiga shi da Abees da Aheel. Su kuma ita da Ruky da Biebah suka shiga baya, sai Afrah da Ayyan tare da su. Mu'azz ne ya dinga nuna masa hanya har suka iso. Islamiyyar su babba ce sosai, dan harda securitys. A inda ya dace yay parking duk suka fita. Karaf suka haɗa ido da Nimrah, yanda tsigar jikinta ta wani tashi sai da ta ambaci hasbunalahu wani'imal wakil a zuciyarta. Da sauri ta kama hannun Afrah suka bar wajen. Shima kansa ya kauda yana maida idanunsa kan Mu'azz.

      “Ɗana zan tafi ne ko zan jira ku anan har ku fito?”.

    “A'a Baba zaka koma gida, sai ƙarfe ɗaya kuma in sha ALLAHU sannan an tashi su Ayyan kazo ka ɗaukesu mu kuma ka taho mana da abinci, sai anyi la'asar kuma ka dawo ka ɗauke mu.”

          “To to ba damuwa ALLAH ya nuna mana”.

    “Amin ya rabbi, zadai ka gane hanya ko?”.

     “Sosai kuwa, karka damu zan gane. Ai na taɓa aiki tanan wajen sosai dan nayi taxi”.

     “Oh ALLAH sarki, shike nan sai an jima ɗin to baba”. Daga haka shima Mu'azz ɗin yabi bayan su Nimrah da tuni sun shige.....

    }}}{{{{}}}}{{{{

          “Alhamdulillah Sir! Yanzu kam komai ya kammala kenan, sai jiran umarnin fara campaign”.

     “Haka ne Imran, amma ni duk ma jikina yayi sanyi. Badan al'amarin Haysam ba banga abinda zai kai ni shiga siyasa ba. Dan siyasar ƙasar nan sirrikan cikinta basu da daɗin tonawa. ALLAH dai ya rufa mana asiri ya ƙara kare mana imaninmu”.

       “Amin ya rabbi Sir. Amma abubuwan dama ko ba'ace komai ba duk mai hankali yasan akwai ɗunbin kwamacala a ciki kam. ALLAH dai ya kare mana ku, ya azurtamu da shugabanni na gari.”

    “Iyakarta kenan kam. Mu dai ku cigaba da mana addu'a, ku dinga saka yara na mana.”

        “In sha ALLAHU Sir za'a ƙara dagewa, dama anayi a koda yaushe. Sir nace yanzu bazaka sake sama mana damar ganawa da Haysam ba. Wlhy ina cikin matsanancin matsin zuciya na kewarsa matuƙa. Shekara biyar ba kwana biyar ba”.

     Sosai tausayin Imran ya sake cika zuciyar Janar, dan har idanun Imran ɗin sun cika da ruwan hawaye. Cikin kwantar da murya ya ce, “Kayi haƙuri Imran, na san kai da zuri'ar Haysam da iyalinsa dole ne ku kasance cikin bege da kewarsa. Kuma hatta muma muna cikin wannan yanayin. Amma ina sha ALLAHU aski ne yazo gaban goshi, kasan kuma masu iya magana sunce daman yafi zafi. Dole ne mu cigaba da daurema zukatanmu, dan wannan gaɓar da muke da babban shiri a kansa tafi kowace gaɓa nauyi da haɗari, idan mutanen nan suka fahimci muna da wani shiri wlhy zasu iya kashe Haysam ta

13 / 24