Advertisements
Chapter 3 Reading Kida A Ruwa Book 2 Complete Hausa Novel Hausa Novels
Advertisements

Kida A Ruwa Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Billyn Abdul Category :  Action Novels

Chapter   3 / 24

6K to 9K   out of 71K words

guards suna sintiri cikin takun da ke nuna horo mai tsauri a wajen.

      “Major Imran Abbas?” ɗaya daga cikin guards ɗin ya tambaya.

   “Eh, ni ne”. Muryarsa ta yi nauyi kamar anyi masa sarƙa a wuya saboda yanda yake jin kansa da zuciyarsa dake bugawa da sauri-sauri.

      “Follow me, sir.”

   Kansa kawai ya jinjina, a ƙasan zuciyarsa yana ambaton sunan ALLAH. Ya bi guards ɗin zuwa wani dogon corridor da yake a tsaftace alamar ana kula da wajen sosai fiye da kima. Daga can suka kai shi wani ɗaki da shima yake zagaye da camaras kamar tsiya.

     “Ka ajiye wallet, takardu, da belt. Za a bincika ka kafin a shiga.”

    Babu wani nuna damuwa Imran ya cire belt ɗinsa dan wannan yasan dokar soja ce. Bai taɓa tunanin zai zo wannan wuri saboda Haysam ba. Bai taɓa hango cewa watarana ƙaddara zata kwaso su zuwa wannan ramin mai tudu da kwazazzabo ba.

     Bayan an kammala bincike sa yanda ya dace suka fita a ɗakin, wani ƙaramin ɗakin ganawa suka kai shi, wanda ke da tebur biyu da gilashi tsakanin su. Amma shi an canja musu saboda matsayinsa daga shi har Zak-Shadow ɗin, dan haka aka basu ɗaki na musamman ba tare da gilashi tsakanin su ba.

      Wani irin duka zuciyar Imran take tamkar ƙarfen agogo dake bada sakanni na motsawa ne da ita. Minti biyar.. Minti goma.. shiru. Sai zuciyar Imran ta ƙara ƙarfin bugawa kamar bugun gangar yaƙi, dan adadin mintinan da aka saka zai iya fitowa sun cika..

      Dai dai nan kuwa aka buɗe ƙofa a hankali. Sojoji biyu suka shigo da Lt. Colonel Haysam Abdul-rasheed Shehu Kobi. Sai dai ba irin Zak-Shadow ɗin da duniya ta sani bane a baya. Wannan Zak-Shadow ɗin ya canja da canje-canje masu yawan gaske, musamman a suffa ta soja zuwa wani abu daban, gashinsa ya yi tsawo sosai sama da yadda yake da, fuskarsa ta ajiye saje saɓanin da da babu ko ɗigon gashi a fuskarsa saboda kasancewarsa soja, fuskar sa ta ɗan rame amma kwarijin da cikar kamalar da gizago zaratan MAZAJEN na nan shimfiɗe a kanta. Ga tambarin sallarsa ya sake fita baƙi sosai akan goshinsa saboda hasken zaman waje ɗaya da fatarsa ta sake yi, ainahin haskensa na da kafin wahalar soja ta dusar da shi ya sake bayyana. Idanun nan kam sun wani sake juyewa kamar na kumurcin maciji.

     Hannunsa na sanye da ƙananan cuffs saboda dokar prison. Shi dama can bamai ƙiba bane, amma jikinsa a buɗe yake da ginannen ƙarfi irin na masu kulawa da tattali, dan haka ko a yanzu bazakace ya rame na tashin hankali ba, dan daga ganinsa kasan bai daina motsa jikin ba, zaka tabbatar da haka saboda takunsa dai nasa ne na soja mai ji da kansa, ko a cikin jeji, ko a cikin duhu. Ko a cikin bainar jama'a wannan takun ƙasaitar da jarumta baya canjawa.

      Ya ɗan tsaya kafin ya zauna. Sai kuma ya kalli guards ɗin da juyayyun idanunsa ya kaɗa kai kaɗan. Su sun san nan ɗin ba wajen wargi bane, dan ko KURA TA RAME TAFI ƘARFIN WAWASON ƘANANUN NAMUN JEJI. Ga shi dai a tsare, amma takashi ko manyan KAYA sun gagara, shiyyasa a tsaren yake amma girmamawa babu abinda ya canja. Ai ko mahaukaci yasan kallon ZAKI sai daga nesa, a nesan ma daga bayan keji, dan ko hannu ya samu zai iya yin wawaso. Yafi ƙarfin kallon banza ma balle ace za'a dake shi. Fitar kuwa sukai da sauri suka barsu su kaɗai.

      Shiru ya cika ɗakin. Shiru mai nauyin da ko ƙarar bindiga da harbi bai zama lallai ta iya yankesa ba. Su duka biyun sun zubama juna ido ne kawai kamar masu kallo a cinema. Imran ya ji hawaye sun cika masa ƙwayar ido. Amma ya danne. Zuciyarsa na ƙaraji. Dole ya kauda nasa idanun da kansa gefe yana ƙoƙarin haɗiye hawayen.

Zak-Shadow ya ɗan girgiza kansa, tare da zama, a hankali ya jingina bayan sa da kujerar. Juyayyun idanunsa suka sauka a fuskar Imran daya sake juyowa kamar yana lissafa duk wani abu da bai faɗa masa ba shekaru uku da suka shuɗe.

       Ganin Imran bashi da niyyar yin magana shi ya motsa nashi lips ɗin da sukai jazur cikin dakakkiyar golden voice ɗinsa dake cike da izza da amo ya furta, “Major Imran Abbas.”

     Kalmomi uku ne kacal. Amma Imran ya jisu har cikin tsakiyar zuciyarsa da brain. Da ƙyar ya iya dauriyar amsa wa da.

      “Sir…”

   Muryarsa ta kasa fita gaba ɗaya saboda sabbin hawayen dake cika masa idanu.........✍️

    

😭😭😭😭😭😭🙏

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*

*_+227 98 94 12 81_*

*_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*

*_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899*

*_Moniepoint MFB_*

*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_*

*_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_*

*_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_*

*_Chapters & Audio_*

@BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276*

*_Access Bank_*

*_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_*

*_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_*

*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_*

*+234 805 568 7449*

*_Telegram Number👇_*

*+234 903 234 5899*

*_ASSALAMU ALAIKUM MUTANE NA MASU ALBARKA_*

*_Maza ku matso MASOYAN Bilyn Abdull da IDANU suka hana karatun novels...._*

*_Tofa Bilyn ku ta samo muku hanya mai sauƙi da kina aiki, ko kina kwance kina hutawa, ko kina inda baki son yawan surutu earpiece ɗinki kawai zaki maƙala a kunne ko Bluetooth kisha sauraren littafin KIƊA A RUWA.... Cikin sauƙi.... 💃_*

*_Kar dai na cika ku da zance. Zamu fara saida littafin KIƊA A RUWA.... Na saurare (Audio) kenan akan farashi mai sauƙi da rahusa._*

*_Akwai VVIP AREWAPEN kenan 💃_*

*_Akwai VIP Telegram 💃_*

*_(Ƴan WhatsApp ku haƙura kawai ƴan ta'addar bati sunfi yawa a cikinku gaskiya tsoron rashin m ɗinku nake 😂🤣)_*

*_Telegram Audio 2k ne kacal ba tsada 💃. Sai kusaka ta wannan account ɗin👇_*



_(2k)_

*9032345899*

*_Moniepoint MFB_*

*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (2k)_*

*_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_*

*_Telegram Number 09032345899_*

*_Ƴan NIGER🇳🇪 kuma bazamu barku a baya ba in sha ALLAHU zaku biya (Telegram vip 1,500 CFA) domin littafin KIƊA A RUWA..... na ji Audio-vocal. Sai ki biya tanan👇_*.

_(1,500 CFA)_

*_+227 98 94 12 81_*

*_My NITA_*

*Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 1,500 CFA vip telegram

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*

*_+227 98 94 12 81_*

*_AREWAPEN (Vvip)_*

*_Chapters & Audio_*

@BilynAbdull

*_Ƴan WhatsApp kuzo muyi shawara idan zaku iya amana ayi harkar nan daku 😂, dan bana son a barku a baya duk da dai bakwa ji, ba raga min zakuyi ba na sani duk da ƙaunar da nake muku 🤣😂._*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💦KIƊA A RUWA...!!💦_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*

_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_GENERAL FICTION_*

_Wannan labari ƙirƙirarre ne. Sunaye, wurare, da abubuwan da suka faru duk ƙirƙira ne, ba su da alaƙa da gaskiya ko wani, koda Bilyn Abdull ce 😂._

*_BOOK 2_*

_Chapter 4_

__________________

_A KANO KI KE…? Kina neman inda zaki siyi abinci mai daɗi? Kina ƙiyar yin girki gashi zaki yi baƙi?, kina neman inda zaki yi order abinci mai daɗi wanda zaki fita kunya?. Masu abinci suna suka tara, akwai abinci mai daɗi akwai a lallaɓa. Kina son ki siyi abincin da zaki ɗauka a saudia ki ke? Kuna son ku siyi abincin da in kuna ci zaku dinga murmushi saboda daɗi da khamshi?. LEEMARS_DELICIOUS itace kat a wannan ɓangare, tazo muku da nau’in abinci kala-kala na gargajiya da na ƙasar waje. Tana siyar da MANDI RICE, GRILL CHICKEN, CHICKEN BIRYANI, FUNKASO, ALELEN GWANGWANI, BREAD POCKET da sauran su. Fannin abin sha akwai natural ZOƁO mai zaƙi, wanda aka yi shi da ingantattun kayan marmari masu ƙara lafiya, akwai wanda bashi da zaƙi domin masu ciwon sugar da masu gudun ƙiba._

_me ku ke jira? Maza ku garzaya shafin ta na instagram ko TikTok domin ku ganewa idanun ku, ku danna wannan link din domin yin magana da ita kai tsaye. Ko ku neme ta a number wayar ta da take ƙasan rubutun nan._

INSTAGRAM

👇🏻👇🏻👇🏻

https://www.instagram.com/leemars_delicious?igsh=MWRzZWtnYXM4ZHB2dw%3D%3D&utm_source=qr

CALL/WHATSAPP

👇🏻👇🏻

wa.me/2349030398006

TIKTOK

👇🏻

https://www.tiktok.com/@leemars_delicious?_t=ZS-90ZQJ2mNJKc&_r=1

Kar ku sake a baku labari, siyan na gari mai da kuɗi gida.❤️❤️🫶🏻

__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

........Dada dake kallonsa kallo mai cike da ƙauna daga UBANGIJI ya ɗan ɗaga hannunsa yana masa Alamar ka tsaya ka nutsu. Sai kuma ya sake motsa lips ɗinsa kaɗan ya furta “You’re a soldier Imran… but seeing you like this is giving me a headache. What’s happening to you?why are you acting like a woman?”.

Shima ya ɗan kawar da kansa gefe saboda idanunsa na son suyi wani abu saboda hawayen da suka sakko a fuskar Imran sharrrr. Kuka ko ɓacin rai ne shi kansa bai ma san wannene yake ji da ganin hawayen Imran ɗin ba. Cikin dakewarsa, idanunsa na kallon gefe ya sake furta, “Bazan tambayeka yaya kowa yake ba? Dan hakan shine mafi girman abinda zai sosa min ZUCIYA. Na ganka, shi ne abinda yafi komai muhimmanci Imran.”

        Da ƙyar Imran ya tsaida hawayensa. Fuskarsa da murmurshin ƙarfin hali ya ɗan matsa gaba, hannayensa duk biyu ya ɗaura kan teburin. “Munyi ƙoƙari.. Munyi komai… amma suka zaɓi yimana wannan zaluncin Haysam…”

      Dada ya katse shi da murya mai sanyi amma mai ƙarfi da nutsuwa, “Ba zalunci bane. Siyasa ce. Dama kuma ita siyasa ai ba ta rabuwa da jini.”

     Kai Imran ya girgiza. Cikin son ƙarfafa kai ya ce, “Na fahimta, kenan sun kulle ka saboda sun tsorata. Sun tsorata da kai. Sun tsorata da gaskiya. Sun tsorata da abin da ka sani”.

       “Na sani.”

     Dada ya furta a hankali yana ɗan murmurshi. Shiru ya sake mamaye ɗakin kowa da abinda yake tunani, fin sakan goma ya maida kallonsa kan Imran kai tsaye, kallon da ya tattara shekara uku masu zurfi: jarunta, kewa, hikima, da raɗaɗin da ya gama zagaye zuciyar mutum daga mutum ta zama tamkar dutse.

        Imran ya katse shirun da faɗin, “Kurakuraina suka kawo ka nan Haysam, zan sadaukar da rayuwata domin ganin ka fita kuma” ya share hawayen da suka sake silalo masa, batare daya bari yayi magana ba ya cigaba da faɗin, “Bayan rufe mu sun sauke COAS shima, sai dai bai daina gwagwarmaya ba, dan yanzu haka da tsayawarsa nazo nan.”

       Idanu Dada ya lumshe a hankali, batare da kula zancen Imran na farko ba ya furta, “ALLAH ya saka masa da alkairi, dama nasan ba zasu barshi ba shi da duk masu goya mana baya. Imran… ka dawo min nan idan ka samu lokaci. Muna da magana mai tsawo. Kuma kada ka sake jin damuwa. Kai kaɗai ne wanda ban taɓa zargi ba.”

      Idanun Imran suka sake zubo hawaye saboda wannan kalmomi na ƙarshe. Cikin jinjina kai ya ce, “Zak… har abada damuwa bazata barni ba in har kana a wannan wajen. Dan haka bazan taɓa barin ka a nan ba har abada”.

       Dada ya yi murmushi. Ba mai annuri ko farin ciki ba. Murmushi ne kawai irin na jarumta da taurin zuciya. Shi yasan fitarsa a wannan wajen sai wani ikon ALLAH, amma ba abune mai sauƙi ba.

      “Karka damu Imran. Ina a nan ne. Amma ba zan tsaya nan ɗin ba kamar yanda ƙaramin tunaninsu ke basu”. Sai ya jingina da kujera yana ɗan lumshe ido. “Kamar yanda na gaya maka kai ƙoƙari ka dawo. Idan ba haka ba ka fara zargina da guduwa, dan babu gudu babu ja da baya sai na ƙarasa wannan aikin”.

       Tabbas Imran ya tabbatar da alwashinsa cikin idanunsa da suka sake rikicewa, ya kuma san wanene Zak-Shadow ɗinsa, kaɗan daga aikinsa ya aikata dukkan abinda ya ƙudurta. Zama ya gyara cikin sassauta murya dan baya son akai ga matakin da Haysam ke harin saboda komai zai sake jagulewa ne.

      “Dan ALLAH kar akai ga haka MAZAN FAMA. Ina sha ALLAHU zan dawo. Zan dawo duk rintsi, zan......”

       Motsin buɗe ƙofar da ake yi ya katse Imran. Sojojin ɗazun ne suka dawo, hakan ya sasu fahimtar lokaci ya cika. Dan haka kafin ma suyi magana Dada ya miƙe abinsa, sai kuma ya ɗan zubama Imran ido na sakan ɗaya, kafin cikin dakakkiyar muryarsa ya furta, “Imran…”

     Imran ya ɗago kai yana kallonsa fuskarsa cike da damuwa da kewa..

          Ƙaramin murmushi yay masa, tare da furta, “Ka tsare min kanka. Daga yanzu ka saka a ranka sabuwar ƙaddara ta fara motsi.” Daga haka ya juya abinsa yay gaba, ya bar Imran cikin shiru mai nauyin da bin bayansu da kallo, idanunsa cike da hawaye, dan a wannan ƙadamin yama manta da kansa a matsayin soja.......

      <<>><<>><<>><<>>

      Da ƙyar Imran ya iya jarumtar hana kansa sanarma su Mammah ganawa da Dada da yayi. Dan ya tabbatar zai saka musu sabuwar damuwa ne bayan sanyaya zukatansu da UBANGIJI yayi badan sun manta da damuwarsu ba tsahon shekara uku da wasu watanni. Amma kamar yanda Dada ya roƙesa kada yay masa zancen kowa saboda zai zama fami a zuciyarsa yasan suma a garesu haka ne. Sai kawai ya zaɓi yin shiru ko Aunty Hafsat matarsa bai gayama komai ba.

       Hatta Janar dake jiran jin ta bakinsa ya gagara ganawa da shi. Dan a wani irin cinkushe zuciyarsa take a gaba ɗaya satin. Cikin kwanaki uku kacal bayan ganawar ta su rayuwar Major Imran Abbas ta canza. Ba ci, ba barci, sai tunanin kalamomin Zak-Shadow da yadda suka tsaya masa a wuya kamar an daure zuciyarsa da igiya. Duk inda ya zauna shi ne kawai a gabansa. Hatta aikinsa ya samu rauni a kwanakin nan.

       Ranar alhamis karfe biyu na rana yake cikin ofishinsa shi kaɗai, ya na kallon rubutun bayanin da ya yi wa janar mai ritaya jiya. Dan ya yanke shawarar tunkararsa kawai a yau su tattauna yanda ya kamata. Kamar abin almara dai-dai lokacin wayarsa ta fara tsuwwa, sunan da yaga yana yawo a screen ɗin ya sashi kasa ɗagawa har sai da ta tsinke, sake kira na biyu ne ya maidoshi a hayyacinsa, ya sauke numfashi mai nauyi kafin ya ɗauki wayar yakai kunnensa. Cike da girmamawa yay sallama, tare da miƙa gaisuwa.

     Daga can General Yusuf ya amsa, cikin damuwa ya cigaba da faɗin, “Imran kana lafiya kuwa? Kwanaki uku kenan ina saka ran ganinka amma shiru?”.

       “Kayi haƙuri Sir kawai ina cikin ruɗani ne. Amma dama yau na shirya samunka a gida bayan na tashi aiki”.

     Cikin sauke ajiyar zuciya Janar ya ce, “Nasan hakan zata faru, amma yaya zamuyi sai haƙuri Imran. In sha ALLAH watarana sai labari, duk wuya da juyin juya halin da za'ai Haysam bazai wulaƙanta ba da iznin UBANGIJI. Kazo dan nima na matsu mu tattauna”.

        “In sha ALLAHU Sir zan zo”.

   Daga haka sukai sallama Imran ya ajiye wayar.

       ★Kamar yanda Imran yay alƙawari yana barin office gidan tsohon General Yusuf Shu'aibu Tafida ya nufa dake tsaftatacciyar anguwa. Sai dai sai da ya kira Aunty Hafsat ya sanar mata yau bazai shigo gida da wuri ba. Hayaniyar da yaji yake tambayarta “lafiya nake jin hayaniya haka?”.

     Ta ce, “Lafiya lau mutanenka ne. Kaima kasan idan Nimrah da Ruƙayya na nan bakin kowa baya shiru. Daga Islamiyya suka zarto nan wai sai ka dawo ka maidasu gida”.

         Murmushi yayi da girgiza kansa, zuciyarsa na ayyana masa ‘ai dama sai hali yazo ɗaya ake abota’ dan rashin jin da Nimrah da Ruƙayya ke zubawa abin har ba'a magana. Tuni sun koma masu gida biyu, basu gidan Mammah basu nan gidansa. A fili kam sai ya ce, “In dai banan zasu kwana ba ki kira Ammar ya ɗaukesu, dan nikam ba yanzu zan shigo ba. Kin san kuma Mammah bata ƙaunar suyi dare a waje”.

      Cikin girmamawa tace, “Bari na kira shi to dan sunce komawa zasuyi. ALLAH ya dawo dakai lafiya”.

     Da Amin ya amsa mata yana yanke wayar. Dai-dai kuma isowarsa babban gate ɗin gidan General Yusuf. Yay horn maigadi ya buɗe masa bayan ya leƙo yaga waye. Kasancewar ba yau ya fara zuwa ba, kuma maigidan ya sanar da zuwan nashi yasa aka buɗe masa gate ɗin kai tsaye. Yana gama parking ɗaya a cikin sojojin dake gidan yay masa rakkiya har babban falon General Yusuf kai tsaye, dan ba'a ajiye shi a falon baƙi ba ma.

     Tunda ya shigo Genaral ke murmushi, Imran ya kai zaune cikin kujera shima tashi fuskar da ƙaramin murmushi. Gaisuwa yay masa irin ta oga kuma uba. Dan Genaral ya girmesu sosai a ƙalla yakai shekara 69 a duniya. Suko yanzu ne ma suka haura arba'in ɗin da wani abu. General ya amsa masa da kulawa, dan har cikin zuciyarsa yake jin ƙaunar Haysam da Imran saboda kwazon su da sanin aiki da gaskiya.. 

      “Bismilah

3 / 24