Author : Billyn Abdul Category : Action Novels
Tsahon kwanaki sun cika cir, awanni 48 ya rage a fara jefa kuri'a, dan haka batun campaign komai ya lafa a koma jiran ranar jefa kuri'a da gwamnati ta riga ta fitar kuma kwanaki 2 ne kacal, dan yau alhamis....
★_______________________★
★RANA BATA ƘARYA
Yau safiyar asabar. Safiyar zaɓen shugaban ƙasa. Duk wani masoyi na yan takara a kowane ɓangare jikinsa na'a farce ne. Ba yan takara kaɗai ba da zuri'ar su yan kasa kansu kowa hankalinsa nakan fata ga wanda yake so. Dan haka kasar ta wayi gari a yanayin sai addu'a kawai. Wasu cike da fata, wasu cike da tsoro duk da tako ina jami'an tsaro na aikinsu ne.
A ka'ida daga shekara sha takwas ne za'a iya saɓe zuwa sama. Dan haka su Nimrah basa cikin masu jefa ƙuri'a. Amma ganin su Mu'azz zasu suka maƙale zasu je. Mammah kam Daddy Imran da kansa yazo ya ɗauketa ita da Hajjo ya kaisu suka jefa kuri'arsu da wuri sosai tare da Janar Yusuf Shu'aibu Tafida da iyalansa. Duk da dai ba kai tsaye Daddy Imran ya fito a tawagar janar din ba saboda bada ƙafa. Amma janar na jefawa da iyalansa suna a rukuni na biyu da suka jefa suma. Daga can Mammah tabi Hajjo suka wuce can gidan dan suma su Gwaggo Khadijah zasuje gaida Abba, amma su basuje jefa kuri'a ba daga gida za'a kaisu can tunda Mammah ce ta riƙesu tace sai an gama zaɓe zasu koma gida, kuma acan suke da mazaɓa.........✍️
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number👇_*
*+234 903 234 5899*
*_Maza ku matso MASOYAN Bilyn Abdull da IDANU suka hana karatun novels...._*
*_Tofa Bilyn ku ta samo muku hanya mai sauƙi da kina aiki, ko kina kwance kina hutawa, ko kina inda baki son yawan surutu earpiece ɗinki kawai zaki maƙala a kunne ko Bluetooth kisha sauraren littafin KIƊA A RUWA.... Cikin sauƙi.... 💃_*
*_Kar dai na cika ku da zance. Zamu fara saida littafin KIƊA A RUWA.... Na saurare (Audio) kenan akan farashi mai sauƙi da rahusa._*
*_Akwai VVIP AREWAPEN kenan 💃_*
*_Akwai VIP Telegram 💃_*
*_(Ƴan WhatsApp ku haƙura kawai ƴan ta'addar bati sunfi yawa a cikinku gaskiya tsoron rashin m ɗinku nake 😂🤣)_*
*_Telegram Audio 2k ne kacal ba tsada 💃. Sai kusaka ta wannan account ɗin👇_*
_(2k)_
*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (2k)_*
*_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*
*_Ƴan NIGER🇳🇪 kuma bazamu barku a baya ba in sha ALLAHU zaku biya (Telegram vip 1,500 CFA) domin littafin KIƊA A RUWA..... na ji Audio-vocal. Sai ki biya tanan👇_*.
_(1,500 CFA)_
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*
*Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 1,500 CFA vip telegram*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_AREWAPEN (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull
*_Ƴan WhatsApp kuzo muyi shawara idan zaku iya amana ayi harkar nan daku 😂, dan bana son a barku a baya duk da dai bakwa ji, ba raga min zakuyi ba na sani duk da ƙaunar da nake muku 🤣😂._*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💦KIƊA A RUWA...!!💦_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_Masu fama da matsalar idanu kuma naku ya fara sauka a AREWAPEN faka-faka AUDIO da zafinsa. Book 1 zaku sameshi a cikin book 1. Book 2 na tare da book 2 shima. 💃💃😘😘😀_*
*_GENERAL FICTION_*
_Wannan labari ƙirƙirarre ne. Sunaye, wurare, da abubuwan da suka faru duk ƙirƙira ne, ba su da alaƙa da gaskiya ko wani, koda Bilyn Abdull ce 😂._
*_BOOK 2_*
_Chapter 28_
__________________
https://chat.whatsapp.com/HKCgesG0ua47qN8hwnCNAo
Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu
Muna muku marhabun lale da shigowa wannan group din mai albarka
Muna saida turaruka na arebiyan perfumes da kuma designer's perfumes dana gida dana motar dana office dana labile da turaren kujeru da kuma by oils masu na mata dana maza masu sanyaya zukatan ma'abota san kamshi ,munada kayan kitchen masu kyau cikin sauki sai kunzo
https://chat.whatsapp.com/HKCgesG0ua47qN8hwnCNAo
https://telegram.org/dl
https://www.tiktok.com/@yusufjummai?_r=1&_t=ZS-91wLXnmiIIa
https://www.instagram.com/jummai342?igsh=dTQ0bnZobTRwN3Vm
07061352952 or 08034528104
__________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________
..........A ƙafa zuri'ar Mammah suka fita domin zuwa jefa kuri'a dan anan cikin street ɗinsu ne mazaɓar tasu take, dan babu wanda aka bari a gidan har su Afrah. Kasancewar anguwa ce ta ƴan gayu babu hayaniyar mutane, wasu ma duk sun koma state ɗinsu jefa kuri'a a can yasa anan ɗin babu yawan jama'a babu hayaniya balle damuwa. A nutse su Uncle Ma'aruff da su Aunty Shariffa suka jefa har zuwa kan Mu'azz karamin gidan. Kuma alhamdullahi dukansu Janar Yusuf suka dangwalawa. Suna kammalawa suka juya zuwa gida abinsu. Nimrah da Ruky ne a gaba, suna tafiya da baya-baya Mu'azz na musu video dan Nimrah harda Teddy ɗinta ta fito. Dan haka su Abees keta binta dan suna son taɓa teddyn magen. a jikinsu, su duka sun musu ƙyau, tare da fidda tsayinsu masha ALLAH...
★WASHE GARI aka tashi da batun sakamakon zaɓe. Hankalin su Nimrah ba'anan yake ba. Bama kuma su fahimci miye damuwar ƴan gidan da batun sakamakon zaɓen ba da suketa bibiya tun jiya. Dan kamar wasa ranar ma a gaban television suka yini. Har kuma akai sallar magriba babu wani bayani, sai da aka dawo sallar isha'i suna cikin cin abinci aka sanar.....
A wannan daren ba gidan Mammah kawai ba ake jiran jin sakamakon zaɓen shugaban ƙasa ba, kusan ƙasar gaba ɗaya a kowanne gida hakan take, dan yau Daddy Imran salla kawai ke sakashi matsawa a gaban television amma ko abinci sai Anmie ta matsa masa ma yake cinsa, shima laumomi ne kawai. Ga Asma'u da Khalifa nane da shi suma. Zuciyarsa kam cike take da tsoro da fargaba.
A wasu gidajen kuwa irin namu na talakawa an kunna fitilu ƴan uwa da abokai sun taru a gaban rediyoyi suna jiran murya ɗaya tak ta shugaban zaɓe, murya ce da zata faɗa musu ko tarihin ƙasar za’a sake rubutawa ko zai sake maimaita kansa ne da wanda ba zaɓinsu ba.
★★★
Ko'a gidan tsohon Janar Yusuf Tafida ya ɗauki wani irin shiru mai nauyi. Yana zaune a kan kujerarsa mai laushi, hannunsa riƙe da remote, television ɗin a kunne amma zuciyarsa na bugawa da ƙarfi. Matarshi, Hajiya Zainab, tana zaune a gefensa, hakama kaf yaransa har mazan dake da mata na a falon zaune zagaye dasu kowa zuciya na rawa da addu’a, dan sun san yanda mahaifinsu ya ƙwallafa rai akan shugabancin nan yana buƙatar sanda za'a sanar da wa ya samu ace suna kusa da shi. Hakan zai bashi ƙarfin gwiwar amsa daga abinda ƙaddara zatazo da shi.
Tunda shugaban zaɓe ya fara magana kusan a lokaci guda numfashin biliyoyin al'ammar ƙasar ya tsaya cak.
_“A bisa sakamakon da aka tattara, ɗan takarar AGS Party, Honourable Yusuf Shu’aibu Tafida… ya lashe zaɓen shugaban ƙasa.”_
“Ya arrahim!”.
Hajiya Zainab ta faɗa tana mai fashewa da kukan farin ciki tare da miƙewa ta rungume Janar da ke kusa da ita kamar yayi sumar zaune. Sai da ta sake furta, “Alhamdulillah Daddyn Deen! Alhamdullahi!. ALLAH ya baka, ALLAH ya cika maka burinka, ALLAH ya baka wannan ne don ka gyara gaskiya!”.
A hankali Janar ɗin ya lumshe ido, zuciyarsa cike da wani nauyi mai girman gaske, nauyin da yake jin tamkar ya ɗauka daga yanzu nan har zuwa shekaru da yawa. Lokacin da ya buɗe ido sai kawai ya zame yay sujida, ganin haka itama ta bishi, hakama yaran da gaba ɗaya suka kacame da ambaton Alhmdllh duk sai suka bisu....
★★★
A gidan Mammah ma lokaci guda falon yay wani irin shiru na sakan, kafin su Yaya Ma'aruff su kacame da ambaton kalmar Alhamdullah. Sai da suka ga Mammah ta tafi sujida sannan suma duk suka bita har su Ruky. Mammah ta jima bata ɗago ba saboda hawayen da suke zubar mata. Koba komai tana ji a ranta nesa tazo kusa in sha ALLAHU. Sai da ta goge hawayen tas sannan ta ɗago tana murmurshi. Su dai su Yaya Ja'afar na mamakin yanda Mammah ke son janar ya samu kujerar nan, amma basu taɓa tambaya ba, yanzu ma kuma basu tambayar ba. Kawai suna ganin da Yaya Imran na son shi ne dai. Kuma Dada ma sanda yana nan yana girmama al'amarinsa matsayin ogansa......
<<%>><★><<%>>
Shima dai a ɓangaren Daddy Imran tamkar Janar ana sanarwa yi yay tamkar ha suma a zaune. Duk ihun da Khalifa da Asma'u keyi baima jisu ba sai da Ammie data zuba masa ido tana murmushi ta kama hannunsa ta matsa a cikin nata. Wani nannauyan numfashi ya kawo hawaye na cika masa ido. Ya kalli Ammie dake lallonsa cikin ido tana murmushi, dan duk da bai taɓa fitowa ya sanar mata shirinsa tsakaninsa da Janar ba tana tsintar wasu abubuwan nasu ta waya idan suna yi. Yau kam ko kunyar yara baiji ba ya jawota jikinsa ya rungumeta, a haka cikin dabara ya share hawayen da suka cika masa ido. Kafin ya saketa ya tafi sujida shima. Sai suma duk suka bishi, yana ɗagowa yayma su Asma'u alamar suzo gareshi, suma su biyun ya haɗasu ya rungume dan auta barci yake.
Sai da ya sake su suna masa congratulations yana gyaɗa musu kai da ɗaukar waya dan bakinsa ma ji yay ya masa nauyi. Kai tsaye layin janar ya kira duk da baida tabbacin samu, dan yasan a yanzu duk wani masoyinsa abinda yake ƙoƙarin yi kenan...
Tabbas hasashen Daddy Imran akan Janar haka ne, dan wayoyine keta rige-rigen shigowa wayar sa a dai-dai wannan lokacin, sai dai ta yayansa kawai ya ɗaga sai ga ta Imran ma. Sunan da ya gani yasa zuciyarsa ta tsaya na ɗan daƙiƙai. (Imran....) Sai yaga sunan na koma masa bibbiyu tamkar haɗe da sunan Haysam. Sai da ya lumshe idanu ya sake buɗewa sannan ya ɗaga yana kaiwa kunnensa. Daga sallama abu na biyu da Daddy Imran ya furta shine,
“Sir… mun yi nasara Alhamdullah. Subahanal-lah. Allahu-akbar. ALLAH ya tabbatar da alkairi, mulki jarabawa ce mai girma, ina roƙon UBANGIJI ya dubi tsarkin zuciyarka, da ƙyaƙyƙyawan fatanmu da ƙyaƙyƙyawan zaton da muke maka yay riƙo da hannayenka wajen baka damar sauke nauyin al'ummar wannan ƙasa gwargwadon iko. Duk wanda zai kasance da kai a cikin wannan sha'anin mulkin in har bazarana ne shi ga sauke hakkokin mutane koda wanene ALLAH ya tauyeshi ta inda zai rasa ƙarfin iya yin komai. UBANGIJI ya zama gatanka, bangon jinginarka, mafakarka, damu baki ɗaya. Once again, Congratulations, Sir.”
“Thanks you Imran. Amin ya rabbi Jazakallahu khairan. Imran ka san wannan nasara ba tawa ba ce. Tawa da taka ce. Ta Haysam ce. Ta gaskiya ce.”
Hawaye ne suka cika idanun Daddy Imran daga can, muryarsa na rawa ya ce, “Na gode, Sir… na gode da bama wannan YAƘIN daraja da kake yi.”
“Yaƙin Haysam yaƙinmu ne ƙasa gaba ɗaya, wanda bai sani bane ko bai fahimta bane kawai keja da baya. Ka shirya, dan tun gobe idan ALLAH ya kaimu nake so ka fara haɗa min duk bayanan shari’ar Haysam tun daga farkon ranar da aka fara har ƙarshe. Ba zan shiga gidan gwamnati ba tare da na duba gaskiya ba. Lokaci ya yi da za mu dawo masa da mutuncinsa tare da namu muma Imran. Dan haka kwana ɗaya kawai zanyi da shiga gidan gwamnati Haysam ya fito in sha ALLAHU”.
Daddy Imran ya gyaɗa kai, hawayen da yake ta riƙewa tun ɗazun na sauka masa. Muryarsa ta shaƙe a cikin maƙoshinsa dake kai-kawo da nauyin shekaru takwas na zafi ya furta, “Sir! Sai nake jin kamar ina mafarki ne irin wanda na sabayi. Dan ALLAH idan barci nake kada ku tada ni”.
“Ba barci kake ba Imrana. Gaskiya bata da lokacin jira. Dole tun a yau mu tunawa kammu akwai wani mutum da ba zamu bari ya cigaba da kwana cikin duhu ba bayan ALLAH ya bamu wannan AMANAR, maza kaje, jeka ka fara shirin fitowar gwarzon haziƙin jarumin soja mai gaskiya da kwatanta gaskiya akan kowace gaskiya duk ƙarfinta.”
“Thanks you Sir! Thanks yo...”
Daddy Imran ya kasa ƙarasawa saboda yanayin da yake ciki misaltashi sai UBANGIJI. Ji yake tamkar zai faɗi sai da ma Ammie ta riƙeshi suka zauna ta miƙa mashi ruwa. Dama ta kora su Asma'u suje suci abincin dan kaf ɗinsu yau babu wani abincin kirki a cikinsu saboda uban gayya bai ci ba hankalinsa nakan television yini guda.
Tambayar da Ammie ta jefa masa a karo na farko game da al'amarin yasa Daddy Imran kallonta cikin ido. Wani sassanyan murmushi ya sakar mata, batare da ya buɗe mata ba a dunƙule ya furta, “Akwai wani mutum guda dake bina bashi Hafsat, bashin adalci, bashin ƙauna, bashin zuminci. Kuma lokaci ya yi da zan biyashi koda da kwatantawa ne.”
“ALLAH ya cika maka wannan buri Daddyn Khalifa”.
“UBANGIJINA ya cika min sai dai tabbatarwa”. Ya faɗa cikin salon raɗa da rungumeta a jikinsa.....
=============
★PRISON★
A kwanakin farko na kawo television ɗin ɗakinsa bai maida hankali akan zaman kallonta ba, dan lissafinsa nakan haɗa kalaman vistor ɗinsa da musu fashin baƙi a farashin mutane masu hangen nesa da basu raina bincike irinsa. Abu uku kawai da aka turke tvn da ita ne ya fara tasirin jan hankalinsa gareta dole. Sun saka mata security ta yanda bata kasuwa, bai iya rage volum, bai canja tasha daga ukun nan kacal duk da kuwa akwai remote. Duk da basu sakata da ƙara mai takura ba kasancewar sa mutum mara san damuwa da hayaniya sai da ta fakurashi a kwanakin farkon. Sai daga baya daya fahimci an kawota ne garesa dan tai masa irin wannan takurar ai sai ya dake ya ajiye komai gefe har a kwana na huɗu ya maida hankali a kallon fashin baƙin masana akan taron campaign ɗin da aka rufe, a bazata yaci karo da na Janar Yusuf Shu'aibu Tafida ne a gaba. Duk da bawai akan Janar ɗin masu fashin baƙin ke tattaunawar ba, suna tattaunawa ne akan mabiyan ɗan takara, inda daga ƙarshe suke faɗin alƙaluma na sake nuna tsohon Janar dake gaba wajen tara masoya a duk jahar da yaje. Wannan shine karo na farko daya fara bama tvn hankalinsa, daga ranar kuma ya cigaba da bibiyar komai daki-daki, har hakan ya bashi damar fara tantance kowace fuska dake tare da Janar Yusuf dama sauran ƴan takara tun daga na shugaban ƙasa har zuwa shugabannin jihohi. A haka aka gangaro har ranar zaɓe, duk yanda abubuwan ke gudana nan ma yana biye, sai ta kai har ƙirga ƙuri'u ya bibiya. Sai dai a yau da aka tashi da jiran faɗar sakamako ya yini da ciwon kai saboda matsawa kansa da ayyukan ƙwaƙwalwa da yay a cikin satin nan gaba ɗaya. Dan haka bai wani maida hankali ba sosai ga television ɗin, bayan ma ya idar da sallar isha'i yay zaman fara karatun Alkur'ani ne, kasancewar tvn ba kasuwa take ba, ba rage ƙara take ba a bazata bayanin shigaban hukumar zaɓe ya shiga cikin kunnensa.
Cak harshensa ya tsaya dai-dai da bugun zuciya na sakanni, kafin ya iya ɗago manyan idanunsa zuwa kan tvn ya saukesu akan fuskar ɗan jaridar dake maimaita kalmar.........✍️
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number👇_*
*+234 903 234 5899*
*_Maza ku matso MASOYAN Bilyn Abdull da IDANU suka hana karatun novels...._*
*_Tofa Bilyn ku ta samo muku hanya mai sauƙi da kina aiki, ko kina kwance kina hutawa, ko kina inda baki son yawan surutu earpiece ɗinki kawai zaki maƙala a kunne ko Bluetooth kisha sauraren littafin KIƊA A RUWA.... Cikin sauƙi.... 💃_*
*_Kar dai na cika ku da zance. Zamu fara saida littafin KIƊA A RUWA.... Na saurare (Audio) kenan akan farashi mai sauƙi da rahusa._*
*_Akwai VVIP AREWAPEN kenan 💃_*
*_Akwai VIP Telegram 💃_*
*_(Ƴan WhatsApp ku haƙura kawai ƴan ta'addar bati sunfi yawa a cikinku gaskiya tsoron rashin m ɗinku nake 😂🤣)_*
*_Telegram Audio 2k ne kacal ba tsada 💃. Sai