Advertisements
Chapter 17 Reading Kida A Ruwa Book 2 Complete Hausa Novel Hausa Novels
Advertisements

Kida A Ruwa Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Billyn Abdul Category :  Action Novels

Chapter   17 / 24

48K to 51K   out of 71K words

sakacin zan zauna in rubuta yadda zan rushe ku daga cikin ɗakin nan da wawancin ku ke sakaku kallonsa keji”. Ya kammala da murya mai sanyi, amma mai ɗauke da tabbataccen iƙirari.

       “Kuna da duhu. Ni kuma ina da hasken da yake huda duhun nan naku. Saƙo na ƙarshe, duk wanda ya sake zuwa inda nake da saƙon ku, zan bashi amsar da zai maido muku. Sai dai GAWARSA ce zata dawo da amsar da gangar jikinsa ba BABU RUHI....”

       Ya saki murmushi tare da salute da yatsa ɗaya kacal sannan ya juya abinsa cikin takun nan nasa da wanda basu fahimcesa ba ke kallon na izgili da izza. Ƙofar ya buɗe ya fita ba tare da ko waiwaye ba yabar baƙo da rawar zuciya da jiƙewar gumi, ga shi ya gagara koda motsi a wajen tamkar wanda gangar jikinsa ta mutu ta barshi da fitar numfashi kawai........

<%><%><%><%>

         Cike da nutsuwa take haɗa masa abincin karin a gabansa, duk da kuwa tana daga tsaye ne shi a zaune kan ɗaya daga kujerun daning ɗin. Ya zuba mata idanunsa na girma fuskarsa da murmurshi. Sai da ta kammala zata matsa ya riƙo hannunta. Kallonsa tayi itama a karo na farko, sai dai fuskarta ita sam babu walwala alamar akwai abinda ke damunta ko ranta a ɓace yake.

      “Juwairiyya mike damunki ne wai?”.

     Yanda yay maganar cikin taushin murya yana sake tsatstsareta da idanu ya sata sunkiyar da kanta. Sai dai batace komai ba. Numfashi ya ja ya fesar tare da sake matsa hannunta cikin nashi, ya buɗe baki zai magana kenan takun fitowar wani daga cikin yaran ya sashi yin shiru yana sakar mata hannun. Itama matsawa tai kaɗan dan mai fitowar har ya bayyana. Ba kowa bane face Abdul-rasheed da suke kira Imam saboda sunan aboki, amini kuma mahaifi gasu Dada da yaci. Imam shine babban ɗanta a gidan, sa'anni suke shi da Mu'azz koma muce ya girmesa da kusan 2years. Yarone nutsatstse yana tsananin kama da Uncle Nasiru, akwai mai bi masa Halimatus'sa'adiyya. Sai Bintu sa'ar su Nimrah, itama dai ƙawarsu ce dan ƙiriniyarsu ɗaya da ita, idan suka haɗu sam basa jin bari musamman idan an samu hutun makaranta sukan haɗu anan ko gidan Mammah ko gidan Daddy Imran. Adam da Sadiq sune ƙananu a gidan, dan Hajiya Zuwairah ta haifesu ne ma kusa-da-kusa sakamakon gwanne data samu, ta haifi Adam da wata uku ta sake samun cikin Sadiq, hakan yasa tsiransu nasu ba yawa.

 

     “Abba ina kwana? Ummu Ina kwana?”.

    Imam ya faɗa yana mai kaiwa duƙe. Hannu Uncle Nasiru ya miƙa masa alamar suyi musabaha yana murmurshi, yayinda Hajiya Zuwairah ta amsa masa da kulawa. Fuskar Imam da murmurshi ya bama Abban hannu kamar yanda yake masa kullum. Dai-dai lokacin Sadiyya da Bintu ke fitowa suma dan ɗakinsu ɗaya.

       Abba ya ce, “Abdul-Rasheed kaifa abokina ne ba suruki ba”. Murmurshi Imam yayi kamar yanda ya saba a duk sanda Abban nasu ya faɗi haka. Hakama Hajiya Zuwairah na tayashi. Imam na kaiwa zaune a kujera shima su Bintu suka ƙaraso dining ɗin, cikin girmamawa suka gaida Abban sannan Ummu da Yaya Imam. Duk sun amsa musu da kulawa, Ummu ta kalli Sadiyya tana faɗin, “Halimatu taso min su Adam suzo suyi kari, dan yanzu haka ma basu tashi ba balle batun tafiya Tahafiz, ni narasa miyasa kukafi ɗaukar tafiya boko da muhimmanci a rayuwarku fiye da islamiyya”.

      Sadiyya data zama budurwa sosai tai ƴar dariya da faɗin, “Ummu itama islamiyya muna so ALLAH, baga Yaya Imam nan ba har jami'a fannin Islamic ya zaɓa”.

       “To ai shi dama yana son karatun addini ba irinku ba. Dan magajin mai sunan nashi ne da Haysam.”

    Hajiya Zuwairah ta bata amsa. Murmurshi Uncle Nasiru yayi, zuciyarsa na tuno masa amininsa kuma ɗan uwa Abdul-rasheed, tare da jin raunin zuciya na gagara taka kowacce irin rawa akan al'amarin babban ɗa na ƙwarai irin Haysam. Wannan raunin nada matuƙar tasiri a zuciyarsa, dan a shekarun nan da Dada ke a rufe kusan shine ya sake assasa ciwon Uncle Nasiru ɗin matuƙa fiye da shekarun baya...

Bintu ce ta katse tunaninsa da faɗin, “Abba dan ALLAH ya maganar maidani makarantar su Nimrah ɗin? ALLAH ina son na koma can zanfi yin ƙoƙari da himma, dan ALLAH kuma har islamiyyarsu nake so”.

     “Zaki ƙara ƙoƙari da himma ko zaki ƙara shiririta da rashin ji. Kune zaku haɗu a waje guda kowa bai shiga tamanin ba. A yanzu ma ita da Ruƙayya ya aka ƙare dasu balle kin ƙaru. Abba kada ka wani maidata can idan bazata zauna a inda take ba ta barshi. Dan suna haɗuwa su ukun nan kowa yaga boni”.

         Tamkar Bintu zatai kuka ta ce, “Kai Yaya Imam, maimakon ka tayani sai ka zuga Abban kuma. ALLAH bazamuyi ba. Ai ko su basa wasa da karatu kaima ka sani fa. Ummu dan ALLAH ki saka baki”. Sai hawaye sharr. Dariya suka sanya mata. Uncle Nasiru ya shafa kanta da faɗin, “Haba Mamana harda kuka. Nima fa ba naƙi bane, ina duba ta Imam ne kawai. Dan nasan kuka haɗu a school ɗaya ke da Nimrah da Ruƙayya sai dai ta ALLAH kawai, wai Gwari ta sai maye. Yanzu ma yaya aka ƙare da su su biyun, kwanaki fa a lokaci guda aka basu suspension boko da islamiyya. Ɗiyar ɗan majalisa guda suka fasama kai tsabar rashin tsoro da ƙiriniya, to idan kuka haɗi ai nasan wataran ƴar shugaban ƙasa zaku bazar a ƙasa ko minista”.

     Dariya Imam da Ummu keyi, Sadiyya dake isowa wajen su Sadiq biye da ita ta ce,........✍️

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*

*_+227 98 94 12 81_*

*_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*

*_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899*

*_Moniepoint MFB_*

*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_*

*_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_*

*_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_*

*_Chapters & Audio_*

@BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276*

*_Access Bank_*

*_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_*

*_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_*

*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_*

*+234 805 568 7449*

*_Telegram Number👇_*

*+234 903 234 5899*

*_Maza ku matso MASOYAN Bilyn Abdull da IDANU suka hana karatun novels...._*

*_Tofa Bilyn ku ta samo muku hanya mai sauƙi da kina aiki, ko kina kwance kina hutawa, ko kina inda baki son yawan surutu earpiece ɗinki kawai zaki maƙala a kunne ko Bluetooth kisha sauraren littafin KIƊA A RUWA.... Cikin sauƙi.... 💃_*

*_Kar dai na cika ku da zance. Zamu fara saida littafin KIƊA A RUWA.... Na saurare (Audio) kenan akan farashi mai sauƙi da rahusa._*

*_Akwai VVIP AREWAPEN kenan 💃_*

*_Akwai VIP Telegram 💃_*

*_(Ƴan WhatsApp ku haƙura kawai ƴan ta'addar bati sunfi yawa a cikinku gaskiya tsoron rashin m ɗinku nake 😂🤣)_*

*_Telegram Audio 2k ne kacal ba tsada 💃. Sai kusaka ta wannan account ɗin👇_*



_(2k)_

*9032345899*

*_Moniepoint MFB_*

*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (2k)_*

*_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_*

*_Telegram Number 09032345899_*

*_Ƴan NIGER🇳🇪 kuma bazamu barku a baya ba in sha ALLAHU zaku biya (Telegram vip 1,500 CFA) domin littafin KIƊA A RUWA..... na ji Audio-vocal. Sai ki biya tanan👇_*.

_(1,500 CFA)_

*_+227 98 94 12 81_*

*_My NITA_*

*Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 1,500 CFA vip telegram*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*

*_+227 98 94 12 81_*

*_AREWAPEN (Vvip)_*

*_Chapters & Audio_*

@BilynAbdull

*_Ƴan WhatsApp kuzo muyi shawara idan zaku iya amana ayi harkar nan daku 😂, dan bana son a barku a baya duk da dai bakwa ji, ba raga min zakuyi ba na sani duk da ƙaunar da nake muku 🤣😂._*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💦KIƊA A RUWA...!!💦_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*

_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_Faka-faka KIDA A RUWA....AUDIO a AREWAPEN masu fama da idanu💃💃_*

*_GENERAL FICTION_*

_Wannan labari ƙirƙirarre ne. Sunaye, wurare, da abubuwan da suka faru duk ƙirƙira ne, ba su da alaƙa da gaskiya ko wani, koda Bilyn Abdull ce 😂._

*_BOOK 2_*

_Chapter 22_

__________________

https://chat.whatsapp.com/HKCgesG0ua47qN8hwnCNAo

Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu

Muna muku marhabun lale da shigowa wannan group din mai albarka

Muna saida turaruka na arebiyan perfumes da kuma designer's perfumes dana gida dana motar dana office dana labile da turaren kujeru da kuma by oils masu na mata dana maza masu sanyaya zukatan ma'abota san kamshi ,munada kayan kitchen masu kyau cikin sauki sai kunzo

https://chat.whatsapp.com/HKCgesG0ua47qN8hwnCNAo

https://telegram.org/dl

https://www.tiktok.com/@yusufjummai?_r=1&_t=ZS-91wLXnmiIIa

https://www.instagram.com/jummai342?igsh=dTQ0bnZobTRwN3Vm

07061352952 or 08034528104

__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

.........“Wlhy Abba zasu aika kada ka amince da daɗin bakinta. Idan ba haka ba nima sai dai a maida ni makarantar su Asma'u ai ƙawaye basu ƙawaye ba”.

     Caraf Adam yace, “Muma haka Abba”.

     Dariya kowa ya sanya. Abba ya shafa kan Adam da Sadiq. “Kenan dai na gane a gidan nan kowa yana jealous da Mamana kawai”.

        “A da alama kam”.

  Cewar Ummu tana murmushi. Itako Bintu tayi kicin-kicin da fuska alamar jin haushi. Sai da Ummu ta lallasheta sannan ta yarda ta zuba abinci. Daga haka suka nutsu suka fara karyawa babu mai magana. Sai da suka kammala kowa ya miƙe dan zuwa yay shirin Tahafiz har Imam. A lokacin ne Uncle Nasiru ya sake kallon Hajiya Zuwairah dake gyara gurin duk da su Bintu duk sun kwashe kwanikan sun kai kitchen.

      “Zamu iya magana yanzu?”.

Kallonsa ta ɗanyi, sai kuma ta tura baki kama ƴar yarinya. Dariya yayi yana haɗe hannayensa da faɗin, “To ni dai duk ma laifin da nayi ayi haƙuri ai min afuwa. Amma dan ALLAH a sanar min damuwa kada zuciyata ta sake kumbura.”

          Kanta ta sunkuyar kawai batare da tayi murmushi data saba yi ba a duk sanda yay irin wannan maganar, sai kuma ta ɗan sauke numfashi cike da nutsuwa ta ce, “Abban Jiddah akan maganar jiya da kaƙi sauraren Jiddah akai ne. Bayan kuma ni da kai duk munji abinda Ismat ta faɗa fa. Yanzu dan ALLAH sai ka bari ɓacin rai ya rinjayeka barin yaran nan a cikin tarkon musiba? Kana jin fa abinda ke faruwa; a tunaninka watarana mahaifiyarsu bazata ci galaba akansu ba musamman ma Nabeeha dake ɗauke da igiyoyin aure a kanta! Nasan Nabeeha mai laifi ce a gareka, dan babu izninka babu na mijinta ta koma wata ƙasa da zama bayan ana cikin damuwa da halin da mijinta ke ciki, amma abinda zamu kalla ko tana da laifi wani kaso ne a ciki Hajiya Hasiba nada wani, saboda tana da tasiri ƙwarai da gaske akan al'amarin yarannan idan ka cire Jiddah da ALLAH yay saurin fargarwa...”

        Cikin ɗacin murya da sauyawar idanun da ɓacewar murmushin kan fuskarsa ya ce, “Ya kike so nayi Juwairiyya? Shin basu ne suka zaɓi irin rayuwar ba shiyyasa suke ciki? Ai su duka ba yara bane har Ismat ɗin da ake ganin batai aure ba, amma suke biyewa gafalar uwarsu da son duniya ta rufema idanu ko”.

       “Hakane, amma abinda zamu duba har yanzu su yara ne akanmu. Sannan mata ne. Mufa mata a kowace sigar rayuwa a karkacen nan muke tamkar haƙarƙari. Shekaru basa saka mu canja ko ilimi. Sai wanda UBANGIJI yaso ya gane kawai daga cikinmu. Mu godema ALLAH da yarannan basu tasirantu da huɗubarta ba ma har suka fahimta illar al'amarin. Dan wlhy UBANGIJI ne kawai ke riƙe da igiyoyin auren Nabeeha saboda Haysam mutumin kirki ne, in sha ALLAHU ALLAH bazai haɗa masa zafi biyu a lokaci guda ba. Dan ALLAH kayi wani abu kodan Haysam, saboda koba komai da saka hannunka ya auri Nabeeha, sannan yana sonta”.

       “Hummm Juwairiyya....”

    “Dan ALLAH karka ce A'a Abban Jiddah”. Tai maganar cikin katse masa hanzari. Ajiyar zuciya ya ɗan sauke kawai. Tare da faɗin, “Shike nan zan duba. Amma ki sani Adeel yaro ne mai dauɗar duniya a hannu, sannan ya fito daga babbar zuri'ar da yake da ƙarfin aji ako ina a duniya musamman ma ƙasashenmu na Afirika. Barowarsu ƙasar nan zai zama babban al'amari. Amma zan gwada wata hanya idan za'a dace.”

        “ALLAH yasa a dace, dan duk ƙarfinsa bai kai na UBANGIJI ba ai. Darajar auren dake kan Nabeeha ALLAH zai hanashi dukkan nasara. Itama ALLAH ya shiryar da ita ta gane halakar da take neman jefa yarannan da kanta.”

     “HUmmm”.

Kawai Uncle Nasiru yace, itama sai ta saki zancen ta ɗakko na batun zuwa sake duba Aunty Mimi mai haihuwa duk da kuwa randa ta haihu taje. Amma a matsayinta na kamar uwa koda Mammah na nan dama ita ya kamata ta yi abinda uwa zatayin, saboda ita da Mammah suna jin kansu kamar ya da ƙanwa uwa ɗaya uba ɗaya. Kamar yanda Uncle Nasiru ke ɗaukar Mammah ƙanwarsa uwa ɗaya uba ɗayan. Bai hanata ba, shima ya miƙe yana faɗin zai shirya dan yau yana da ganawa da sanata Yusuf Shu'aibu Tafida tsohon janar. Addu'a tai masa dan tasan dai ganawarsa da Janar ɗin baya wuce akan batun fitar Haysam da suke ta fafutuka da kai-kawo tsahon shekaru.....

===============

       Koda su Oga Jush suka gama sauraren Dagger sai ya saki wani murmushin da akan jima ba'a gani akan fuskarsa ba. Kafin kowa yay magana shiya fara faɗin, “Yarinyar takai shekara nawa yanzu?”.

          “15years ne Sir, harda kusan watanni biyar”.

     “Zamu iya ganin hoton ta?”.

  “Har ma videos akwai Sir, dan tunda aka sanar mana tana raye tare da shi Molen a kuma gidan su Zak-Shadow shekara huɗu kenan na saka ana bibiyar al'amarinta batare da ko shi kansa Mole ya sani ba.”

       “Shiyyasa kake birgeni, dan kasan aikin ka sosai”.

    Oga Jush ya faɗa yana ma Dagger murmurshi. Suma sauran dai sun nuna alamun jin daɗin abinda Dagger ɗin yazo da shi. Dan su biyar ne kacal a meeting ɗin iya su manya. Oga Jush, Black Spider, Mr Specter, Viper sai shi Dagger ɗin dake matsayin yaro. Babu wani ɓata lokaci Viper ya amsa wayar Dagger akai connecting da ƙaton television ɗin dake meeting room ɗin.  A take hotunan kyakkyawa Nimrah suka fara bayyana a mabanbanta wajaje. Makarantar Islamiyya da boko, wasu wajajen ma a super market ne sunje shopping, wasu taron Birthday party ne na ƙawayensu kona cikin family. Babu dai wanda suke a titi kasancewar babu inda ake bari suna zuwa da kansu a abin hawa na kasuwa. Kusan a waje uku akwai Ruƙayya a ciki, ɗaya da Mu'azz da Biebah. Sai da suka kammala kallo har ƙarshe da videos ɗin ma kafin Mr Specter yay tambayar sauran wanda suka gani tare da ita.

     Kai tsaye Dagger ya fara musu bayani yana dawo da duk inda take ba ita kaɗai ba baya. “Wannan ɗiyar abokin nan nashi ce Imran, koda yaushe suna a tare, da alama itama yarinyar ta koma gidan su Zak-Shadow ɗin da zama ne. Duk wani rashin ji tare suke yinsa sunanta Ruƙayya. Wannan kuma namijin sunansa Mu'azz, ɗan ƙanwar Zak-Shadow ɗin ne, ubansa kuma yayan Imran ne wanda in baku manta ba farkon aikinmu muka nema bayanan Zak-Shadow a wajensa yaƙi bayarwa aka saka Zinga ya kashe shi. Sai babbar autar su Zak-Shadow ɗin ce wadda ubanta da ban a cikinsu.”

       “Lallai yara sun ƙosa”.

    Cewar Black Spider yana dariyar ƙeta. Suma sauran dariyar suka ɗanyi. Kafin Mr Specter ya sake faɗin, “Miye labari akan yarinyar?”.

         “Bata jin magana ƙwarai da gaske oga. Dan a duka makarantun da tayi babu inda sunanta bai zama fitacce ba ita da wannan ɗiyar Imran ɗin. Fitinannun yara ne na bugawa a jarida. Bata san wani abu tsoro ba, balle kurari. Ga kauɗi da jarumta”.

       “Wannan kam kayanmu ce. Za kuma a amfana da ita kwarai da gaske. Kamar yanda uban nata ke burin ta dawo hannunsa zamuyi amfani da hakan zakuma mu dawo masa da ita. Ko muce zata dawo garemu.”

      “Sir ai ba dawowar ce matsala ba, shima fa uban kansa ta manta waye shi. Mutanen gidan kawai takema kallon ahalinta.”

     “Zamu goge mata duk wannan tunanin. Dole tasan ainahin ubanta a yanzu. Ta hanyar sanin makashin uwarta da zuri'arta”.

        Duk kallonsa suke alamar basu fahimta ba. Dan haka kai tsaye ya ce, “Zamuyi amfani da edited video ɗin nan. A nuna mata shi, shi ne kawai zai sata fara bincike da neman hanyar sanin ainahin maruƙan nata, da sanadin zuwanta gidan. Mu kuma sai muyi amfani da damar binciken nata mu jawota jikinmu muna bata dukkan information ɗin da take nema da buƙata. A ƙarshe mu sakata yi mana aikin da muke buƙata akan family ɗinsa, sai dai zamu ƙarfafata ne akan itace zata ɗauki fansa”.

     Cike da gamsuwar bayanin ogan nasu suka shiga tafi farin ciki na bayyana akan fuskar su. Shi kansa Dagger bakinsa yaƙi rufuwa dan daɗi, a ƙasan ransa kam ayyana wa yake masoyiyarsa ta kusa zama tashi dai kenan. Dan tun sanda aka fara kawo masa hoton Nimrah da videos yarinyar taima zuciyarsa shigar sauri. Ya kuma yi ma kasan alƙawarin mallakarta matsayin mata. Yanda ya gama zama tuzurun nan shekara da shekaru babu aure sai a

17 / 24