Advertisements
Chapter 21 Reading Kida A Ruwa Book 2 Complete Hausa Novel Hausa Novels
Advertisements

Kida A Ruwa Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Billyn Abdul Category :  Action Novels

Chapter   21 / 24

60K to 63K   out of 71K words

Ja'afar ya ce, “Haba Gwaggo, kwa taho ku kaɗai duk babu yara? Bayan kun san ba ganin juna ake ba tsahon lokaci sai irin haka ta faru”.

        “Makaranta tasa haka Ja'afar, amma in sha ALLAHU idan anyi hutu sai su zo. Tunda kudai kun tattaramu kun watsar, yaushe rabonku da Bauchi balle Maiduguri?”.

     “Dama idan sunje Bauchin ba ganinsu muke ba Adda Khadijah, iyakarsu gidan Yaya Jamilu da Adda Alawiyya. Dan nidai sau biyu suka taɓa zuwa min lokacin rasuwar Inno surukata, da ciwon Ahmadi”.

           “Munyi laifi Gwaggo Nanah, amma kiyi haƙuri zamu gyara in sha ALLAHU. Wani lokacin abubuwan ne ke yawa. Mafi yawan lokuta kuma zuwa Bauchin kasuwa ke kaimu. Ki tambayi Aunty Badiyya sau da yawa shima Uncle Jamilu a kasuwa muke samunsa ba gida muke zuwa ba. Itama Gwaggo Alawiyya takan jima bata gammu ba. Maiduguri ne dai kam ma zamuce muna shiga dan ziyara kai tsaye”.

       “To na gamsu, amma dan ALLAH a gyara, mun san mu masu kuskurene a gareku, amma kuyi mana afuwa kunji, Yaya Abdul-rasheed mutum ne mai son zumunci da Adda A'isha da Adda Yakura, na tabbatar kuma akwai wanan jinin alkairin nasu a tare daku, kar ku biyema aikin son zuciyar wasunmu ku watsar damu gaba ɗaya. Suma lokaci zai yi da zasu yi nadamar abinda suka shuka. Dan har ma wasu sun fara, Yaya Babba a tsakanin nan babu abinda yake sai tafka asarori kala-kala, ga yara cike da gida, mata har huɗu. Yaya Haruna ne ma za'ace da ɗan sauran damshi-damshi. Shi ko Yaya Garzali ma yaje ya tare saudia aikatau ƙiri-ƙiri ko takan matan baya bi sai ya gadama.”

      Sosai zancen ya girgiza su. Sai dai basu ce komai ba face ALLAH ya ƙyauta. A haka Ammar ya shigo shima da Mu'azz. Nan fa falon ya sake lacamewa da farin ciki. Sai kuma gasu Nimrah na fitowa cikin kwalliya tsaff suna baza ƙamshin turaren da suka satarma Aunty Biebah na SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387. Cike da farin ciki suka rungume Gwaggo Alawiyya da Gwaggo Khadijah dan su suka sani sukam. Abin birgewa bazaka taɓa cewa ba jininsu bane su. Sun gaida su Gwaggo Nanah suma. Suka amsa musu da kulawa duk da basu san alaƙarsu da gidan ba. Garama Fiddo ƴar Aunty Mommy data kwana a gidan itama, tunda sun jajje Bauchin ita.

       Gwaggo Khadijah ta ce, “Oh ni Dije Maman Ma'aruff ƴan matan nawa duk sun miƙe. Kaga yara kamar wasa sun ƙosa. A wannan sai aure”.

        Caraf Mu'azz ya ce, “Tab ɗin wazai kwasa Granny? Wannan gayyar ciwon kan da basu iya komai ba sai dambe da neman masifa da ƴaƴan mutane”.

      Baki duk suka tura gaba. Gwaggo Khadijah ta ce, “Kunga ƙyaleshi ƴan uku Ko nace ƴan huɗu dan banbu Bintu ne. Ai ana yin auren duk zaku daina ko. Kuma dai ai kowa da ƙuruciyarsa, shima idan za'a faɗi abinda yayi ai sai kowa ya gudu”.

        Dariya suka shiga yima Mu'azz suna masa gwalo, shiko yana hararsu da musu alamar zai kama su. Su Yaya Ma'aruff dai na murmurshi ne, Yaya Ammar kam dining ya nufa yana faɗin shifa yunwa yake ji, mi aka dafa ne?. Miƙewa su Nimrah sukai suma suna faɗin yunwar suke ji. Daga haka suka koma kan dinning ɗin harda su Mu'azz aka bar su Yaya Ja'afar suna hira da su Gwaggo Khadijah.....

<<%>><<%>><<%>>

      Da yamma shagalin suna aka sha sosai a gidan Aunty Mimi, duk da kuwa haihuwa ce ta huɗu tayi. Babu ƙarya su Nimrah sun cashe da rawa iya iyawarsu. Kasancewar hall aka kama iyakar kuma mata ne kawai a wajen dan ko su Mu'azz basu shiga ba sai abin ya ƙayatar. Ƙarfe shida aka tashi saboda sallar magriba. Nan fa motoci suka fara ɗibar mutane zuwa gidajensu. Su Nimrah dai yau a gidan Aunty Mimi zasu kwana. Dan haka sukabi ƙanin mijinta da yazo kwasar yaranta dana family ɗin mijinta. Duk da dai da farko ca sukai su bazasu shiga cikin yaran ba, sai da Aunty Shariffa ta fara musu faɗa da tabbatar musu zako ta kaɗa kansu zuwa gida sannan suka nutsu saboda suna son zuwa can ɗin su ƙarasa weekend ɗin su. Ga Bintu kuma ta ƙaru sun zama su huɗu yanzu.

        Haneef dake matuƙar son Ruƙayya na sharewa yana faman murmushi yace su jira shi ya kai yaran ya dawo to. Feedo ce ta amsa masa da “To Uncle”. Su Ruky kam aka wani ɗauke kai gefe. Murmurshin shaƙiyanci Nimrah tayi, tare da ɗagama Bintu gira ɗaya cike da gulma. Aiko suka kwashe da dariya. Ruky da tasan da ita suke ta balla musu harara da jan tsaki zata bar wajen Nimrah ta riƙota........✍️

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*

*_+227 98 94 12 81_*

*_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*

*_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899*

*_Moniepoint MFB_*

*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_*

*_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_*

*_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_*

*_Chapters & Audio_*

@BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276*

*_Access Bank_*

*_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_*

*_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_*

*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_*

*+234 805 568 7449*

*_Telegram Number👇_*

*+234 903 234 5899*

*_Maza ku matso MASOYAN Bilyn Abdull da IDANU suka hana karatun novels...._*

*_Tofa Bilyn ku ta samo muku hanya mai sauƙi da kina aiki, ko kina kwance kina hutawa, ko kina inda baki son yawan surutu earpiece ɗinki kawai zaki maƙala a kunne ko Bluetooth kisha sauraren littafin KIƊA A RUWA.... Cikin sauƙi.... 💃_*

*_Kar dai na cika ku da zance. Zamu fara saida littafin KIƊA A RUWA.... Na saurare (Audio) kenan akan farashi mai sauƙi da rahusa._*

*_Akwai VVIP AREWAPEN kenan 💃_*

*_Akwai VIP Telegram 💃_*

*_(Ƴan WhatsApp ku haƙura kawai ƴan ta'addar bati sunfi yawa a cikinku gaskiya tsoron rashin m ɗinku nake 😂🤣)_*

*_Telegram Audio 2k ne kacal ba tsada 💃. Sai kusaka ta wannan account ɗin👇_*



_(2k)_

*9032345899*

*_Moniepoint MFB_*

*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (2k)_*

*_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_*

*_Telegram Number 09032345899_*

*_Ƴan NIGER🇳🇪 kuma bazamu barku a baya ba in sha ALLAHU zaku biya (Telegram vip 1,500 CFA) domin littafin KIƊA A RUWA..... na ji Audio-vocal. Sai ki biya tanan👇_*.

_(1,500 CFA)_

*_+227 98 94 12 81_*

*_My NITA_*

*Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 1,500 CFA vip telegram*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*

*_+227 98 94 12 81_*

*_AREWAPEN (Vvip)_*

*_Chapters & Audio_*

@BilynAbdull

*_Ƴan WhatsApp kuzo muyi shawara idan zaku iya amana ayi harkar nan daku 😂, dan bana son a barku a baya duk da dai bakwa ji, ba raga min zakuyi ba na sani duk da ƙaunar da nake muku 🤣😂._*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💦KIƊA A RUWA...!!💦_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*

_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_Masu fama da matsalar idanu kuma naku ya fara sauka a AREWAPEN faka-faka AUDIO da zafinsa. Book 1 zaku sameshi a cikin book 1. Book 2 na tare da book 2 shima. 💃💃😘😘😀_*

*_GENERAL FICTION_*

_Wannan labari ƙirƙirarre ne. Sunaye, wurare, da abubuwan da suka faru duk ƙirƙira ne, ba su da alaƙa da gaskiya ko wani, koda Bilyn Abdull ce 😂._

*_BOOK 2_*

_Chapter 27_

__________________

IMZEEDVENTURE

✨ Duniyar luxury kayan kitchen & kayan yara masu kyau, unique, kuma classy ✨

Wai har yanzu kina nan a GWAMMA ɗinki ba Hajiya Bilqees ba madam😱?.

Yo ba dole na kiraki gwamma ba kitchen kamar na zamanin kakaninmu ba gyara ba kayan ƙawa 💃.

Mufa matan zamani daga kitchen ake fara gane mun kai ƴan gayun zamani💃🏼🤸. Dan haka maza garzayo na nuna miki hanyar da kema za'a fara kiranki Hajiya Bilqees ba Bilki ba 😀.

IMZEED VENTURA shine kankant a wajen maida mata ƴan ƙwalisa da kayan ado na kitchen harma dana jiki. Ga na yara gana manya kai komai mun haɗa sai wanda ya gani 💃💃.

Kina neman kayan kitchen masu kayatarwa?

Ko kayan yara na yan gayu, masu kama da sabo?

✔️ Siyan nan take

✔️ Order kayan gonjo

✔️ Adashe GATA don kayan kitchen

Shiga group ɗinmu ki gani da idanunki 👀👇

👉

https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt

📩 DM: https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1

📞 Call/WhatsApp: 07077532253

🎵 TikTok: Imzeedventure https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1

Kada a yi babu ke 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 ki shigo yanzu. Muna aika kaya ko ina kike cikin salama da kwanciyar hankali.🥰

Mu da kayanmu duk naku ne. Maza kuzo ku tattaremu a saka muku a mota ko Jirgi😂💃💃.

__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

.........“Sorry Trouble Buddy na. ALLAH ke ɗin ce kin cika wulaƙanci, Uncle Haneef fa ya haɗu ALLAH. Amma kiyita wani shan ƙamshi. Dan ALLAH ko kaɗan ki dinga kulashi mana, ALLAH idan ya ganki zakiga duk bakinsa yaƙi rufuwa”.

      “Ai shiyyasa bazan kulashin ba. Ni fa bana son susun namiji haba. Mutum babu wani jan aji. Kuma ni an faɗa masa za'a min aure ne yanzu mtsoww!!”.

       Bintu dake dariya ta ce, “Baby ai kece zaki saita shi yanda kike so. Amma kina wani yayyarfashi, jifa da salla yanda ya mana siyayya”.

          “Mayya dama ke ai kwaɗayi ne zai kashe ki ke da Ninah”.

     “Ya kashe mu dai, tunda tare muke”. Cewar Nimrah tana hararta. Ramawa tai itama, sai dai dai-dai nan Haneef ke dawowa dan haka hirar tasu ta tsaya. Fitowa yay da kansa ya buɗema Ruky gaba, zata zille ta shiga baya inda su Nimrah ke shirin shiga suka turata suna ƙumshe dariya. Juyawa Haneef yay ya kallesu da musu jinjina yana murmurshi. Daga haka ya rufe mata ƙofar ya zagaya dan suma har sun rufe.

     Yana fara tafiya a titi ya ɗan kalla Ruky, cike da son birgeta ya ce, “Muje shan Ice-cream ne Baby?”.

     Kai ta girgiza masa alamar a'a. Sai ya ɗan marairaice fuska, tare da maida lallonsa kan su Nimrah dake baya ta mirror. “Yaran Uncle muje mu sha ice-cream ne?”.

         Cike da iyayi Feedo ta ce, “Yes Uncle”.

     Nimrah zatai magana Bintu ta rufe mata baki, dan sun san bakinta ɗaya da Ruky. Ganin zata fisge itama Feedo ta ɗaura nata hannun akan na Bintu suka haɗu suka danne Nimrah. Sai da ta sakar musu wasu shegun mintsini masu zafi suka saketa kowanne na sosa wajen. Badan Nimrah da Ruky sun so ba akaje wajen shan wannan ice-cream dai. Haka ya jasu har ciki kowacce ta zaɓi flavor ɗin da take so. Ya ƙara musu da snaks. Duk yanda suka so ya maida su gida ƙi yay, haka ya janye ra'ayinsu suka zauna a wajen. Sai dai rashin sabo ya sasu kasa sakin jiki su dukansu. Dan abu ne da su dukansu ba tarbiyyarsu bace. Shi ko yanata tsiyaya musu zance da ɗaukarsu hoto da wayarsa iPhone.

        Ganin fa an fara sallar isha'i hankalin Nimrah ya tashi. Dan in har ka gansu a waje irin wannan lokacin tabbas da wani a cikin Uncles nasu ne ko Ya Mu'azz ko Aunty Biebah ko kuma sun raka su Aunty Lailah anguwa ko Ammie. Amma basu kaɗai ba balle wannan da saurayi ma wai.

      “Nimrah ya naga kin miƙe?”.

  Haneef ya faɗa yana kallonta.

“Uncle Haneef kayi haƙuri ka maidamu gida. Wlhy idan Mammah taji zatai mana faɗa, balle Daddy ko su Uncle's”.

         “Haba-haba ai in sun san nine babu wani faɗa da zasuyi”.

    Miƙewa itama Ruky tayi, hakan yasa suma su Feedo duk suka miƙe. Kafin ma Nimrah ta bashi amsa Feedo ta ce, “Wlhy Uncle koni Abbana ya sani ubana zai ci. Muje ɗin kawai ma ƙarasa a gida”.

    Babu yanda ya iya dole ya miƙe, ya tayasu tattare kayan suka fito. Kamar ɗazu yanzu ma dole Ruky gaba ta shiga. Cikin ƙankanin lokaci ya iso gidan Aunty Mimi da su. Yay horn maigadi ya buɗe masa gate ya shige. Suna fitowa a motar maigadi ya iso inda suke. Kai tsaye gaban Nimrah ya isa yana miƙa mata ledar hannunsa da faɗin, “Hajiya gashi wani yace a baki. Yata jiran dawowar ku amma yaji shiru yanzu babu jimawa yabar wajen nan.”

      Ba ita ba hatta su Ruƙayya da mamaki suke kallonsa. Cikin kasa daurewa Nimrah tace, “Kuma ni Nimrah yace a bamawa?”.

       “Tabbas ke yace, yace sunansa Kamal malaminku na islamiyya”.

     Ruky ce ta amshi ledar tana faɗin, “Wato shima Sayyadi Kamal ɗin nan ɗan naci ne fa na lura”. Daga haka tabar wajen fuuu. Tsaff su Nimrah sun fahimci fushin Haneef tai amfani da shi akan Kamal. Dan haka suka wayance da masa godiya suka shige cikin gida.

     Sun sami sauran dangin mijin Aunty Mimi da basu kai ga wucewa ba. Suka gaishe su suka wuce ɗakin da suke sauka in har sunzo gidan. Dama can suka kai kayansu da daddare. Ƙaton gado ne da zai iya isarsu koda su shida ne a ɗakin, sai wadrobe da mirror, sai ƙofar bayi. Kayan hannunsu duk suka ajiye suna zubewa a gadon kowa na faɗin wash, dai-dai nan Ruky data rigasu shigowa ta fito daga bayin alamar har tayi alwala. Suma duk miƙewa sukai, dan rashin yin sallar akan lokaci na tsaye a ran kowannensu. Bintu ce kawai ke period dan haka taja ledar snaks ɗinsu ta fara ci tana faɗin, “Bari muga mi Sayyadin ya aiko mana da shi shi kuma”.

     Tsaki Nimrah tayi a karo na farko tana shigewa bayi abinta. Fiddo ta sanya dariya dan Ruky ma harta kabbara salla. Dariyar su Bintu data cika ɗakin ya saka Nimrah fitowa da sauri, itama Ruky dai-dai tana idar da sallar ta juyo tana kallonsu. Litattafai ne a ledar saƙon Sayyidi Kamal suka nuna musu. Feedo ta ce, “Wannan fa shine auren ustaz ɗin, kaga wata lukutar jaraba wai saƙon littafai. Ninah kina cikin yanayi gaskiya”.

        Nan ma dariya suka sanya harda Ruky yanzu kam. Dan haka Nimrah ta watsa musu harara ta kabbar sallarta itama. Koda ta idar sun gama mata shaƙiyancin nasu, dan haka bata sake tada zancen ba ta haye gadon ta kwanta wai kanta ke ciwo. Da ƙyar suka lallaɓata ta zauna suka ƙarasa shan Ice-cream ɗinsu da snaks ɗin bayan Feedo ta idar da salla itama. Dan haka koda Aunty Mimi tai kiransu suzo su ɗeba abinci sukace mata sun ƙoshi. Bata takurasu ba dan taga abinda suka shigo da shi, ta kuma san aikin Haneef ne......

<<<<<<(⁠✷⁠‿⁠✷⁠)>>>>>

     ★CAMPAIGN★

     Kwanaki 100 na campaign suna gab da cika, dan kuwa ana satin ƙarshe na kammala taron kowane kamfen. Dan haka amsa kuwwar cikar kwanakin tamburan siyasa na gab da cika, tako ina ƙasa ta kara hargitsewa dan kowa burinsa satin ƙarshen nan ya tumfayesa da zuciyar yan kasar. Baka iya jin komai sai sautinkan waƙoƙin da aka rairana ƴan siyasa. Yayinda hankalin matasa kacokan ya koma can. Wasu ma sun ajiye harkokinsu da sana'o'in su ne kacokam. Kamar dai yanda aka saba alƙawuran nasu guda huɗu ne ga al'ummar ƙasa a lokacin da suke kan munbarin campaign. Zamu gyara muku harkar karatun, zamu inganta wutar lantarki, zamu wadata ku da ruwa, zamu gyara asibitoci.

       Cikin rashin lissafi da auna abubuwa a yanda ya dace, da taro da kwabon da ake raba mana mu talakawan ƙasa da ɗan sabulai da zannuwan ɗaurawa mai hoton ƴan siyasar a jiki sai kaji mun sallama muna bada kai bori ya hau. Babu ruwanmu da tantance wane shugaban ya dace damu? Mi muke so a ƙasar da kawunanmu bayan waɗan can lissafin huɗu da ko a karatu sukazo ya kamata ace mun haddace su tsaff zuwa yanzu daga daɗin bakinsu mu nemo cigabansu. Amma ina babu batun tantancewa, a wasu wajajan ma siyasar ta haɗa rigima ne tsakanin ƴan uwan juna saboda ni ina son wannan wane ɗan uwana yana son wancan ba jam'iyyar mu ɗaya ba. Wasu har gaba zakaga ta ƙullu mai girma a tsakaninsu. Yayinda su ƴan siyasar da sukeyi domin su suna can tare suke shan shayi, tare suke ƙulla mai fishshesu musamman akan abinda zasu ribantu da shi game da kuɗaɗen da suka kashe wajen jawo ra'ayinku idan sun haye. Wanda ma bai haye ba akwai hanyoyin da za'a bi dan maida masa wahalarsa ta bayan fage kune a ruwa...

     Alhamdullahi duk da irin tasu tafiyar bata banbanta data Janar Yusuf ba a yau kasancewar a ƙarƙashin damarsu ya ke shima a siyasar kamar saura abinda shekarun baya suka zo da shi wajen campaign shima dai shine a yau yake zuwa da shi. Kuma Alhamdullah zamu ce akwai nasara a al'amarin dan yana da magoya baya sosai a cikin jam'iyya da al'ummar gari.

         Abinka da soja, a kwanakin kai-kawon duk da wahala da jigatar rashin barci dana hutu zuciyar maza a tsaye take da ƙyaƙyƙyawan fata. Tun ana farkon satin nan da sukai zama da Imran ya kuma gana da Uncle Nasiru basu sake haɗuwa ba. Dan a zahiri Imran baida alaƙa da siyasar Janar. Gara-gara ma Uncle Nasiru har campaign ya rakashi sau biyu. Duk wani abinda ya dace su tattauna sun kammala sun ajiye kundin shirinsu gefe har sai ta ALLAH ta kasance. Wato aci zaɓe ko a faɗi...

   

21 / 24