Advertisements
Chapter 8 Reading Kida A Ruwa Book 2 Complete Hausa Novel Hausa Novels
Advertisements

Kida A Ruwa Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Billyn Abdul Category :  Action Novels

Chapter   8 / 24

21K to 24K   out of 71K words

harda suspension na 1week”.

       “What! Ya rabbi”.

   Hararar Mu'azz Mammah tayi, zatai magana Imran ya ce, “Shi miye laifinsa, ga waɗanda zaki harara nan Mammah, ki haɗa musu da duka ma. Wai sai yaushe zamu huta da halin Ruƙayya da Nimrah a gidan nan ne?. Ku kuma kun zauna kuna kallonsu, mai makon tun a school ɗin ku naɗa musu bugun kawo gishiri suji a jikinsu kamar yanda sukama ƴar mutane”.

        “A'a wannan muguwar shawara ce Imran. Ya zakace su dakar min yara. Naji sunyi kuskure, amma kowa dai da irin ƙuruciyarsa, sai ku musu addu'a. Nan da lokaci kaɗan duk zasu bari, sannan wannan faɗan akan gaskiyarsu ne”.

       “Mammah idan jikinsu ya gaya musu ko. Shike nan nasan maganinsu, Boarding school zasu koma bari su kammala tarm ɗin nan.”

    Kuka Nimrah da Ruƙayya suka ɓarke da shi, dan a duniya sun tsani Boarding school. Tuni sun zube a ƙasa sunyi gurfane suna roƙon Daddy Imran da tuni ya zauna. Karo na farko Aunty Shariffa da Aunty Lailah suka gaida Imran ɗin da fara bashi haƙuri suma akan a bar batun Boarding ɗin nan dan ALLAH.

      “Ina ku barsu ai gara suje muma mu huta. Kuma wannan zaman suspension ɗin zaku gane kuran ku da shi. Masu aikin gidan nan duk su shirya suje gida su huta. Kune zaku koma gyaran gida, har sashen Auntys ɗin ku, kuma kune zakuna abincin gidan duka da wanke-wanke safe, rana, dare”.

      “Wlhy Daddy indai baza'a je Boarding school ɗin ba mun yarda zamuyi ko Sisy?”

    Nimrah tai maganar tana kallon Ruƙayya, da sauri Ruky ta ɗaga mata kai da faɗin, “Eh wlhy Daddy mun amince. Uncles dan ALLAH kusa baki, Mammah mun tuba, Aunty please ku bashi haƙuri”.

        Ganin yanda su Yaya Ja'afar duk suka kalleshi suma fuskarsu na sauyawa alamar zasu fara roƙon nashi ya hararesu, kafin ya juya yana nunama su Nimrah hanyar upstairs yace, “Ku tashi ku bama mutane waje”.

     Ai da gudu-gudu suka miƙe sukai sama. Ko gama hayewa basuyi ba Ja'afar yace, “Yaya Please hukuncin yayi tsauri da yaw.....”

    Bai ƙarasa ba Imran ya hararesa. “Eh ai dama duk kune ke shagwaɓasu. To bazan bar gidan nan ba ma sai masu aikin sun tafi, duk wanda ya tayasu kuma shima sai na bashi nashi horon”.

     Tsit sukai kowa yana tura baki gaba. Dan kuwa umarnin Imran dai-dai yake dana Dada a wajensu. A yanzu ma da babu Dada shine ya maye musu gurbin komai nasa a gidan. Daga ƙarshe dai ɗaya bayan ɗaya suka fara zare jikinsu a falon, su a dole an taɓa musu kafi auta. Cikin gatse Imran ya ce, “In kunji haushi ku ɗaukesu ku bar ƙasar inga tason ƴaƴa”.

       Dariya Mammah tayi, sai da suka gama fita itama ta bama Imran ɗin haƙuri da faɗin, “Aikin ya musu yawa ayi haƙuri, koda girkin gidanan aka barsu na safe kawai ya ishesu hukunci”.

       “Mammah ALLAH yaran nan basa ji da yawa, ki yi haƙuri kona kwana huɗu suyi ƙila su dawo hankalinsu. Ɗazun nan fa Asma'u ke sanar da ni jiya an basu suspension a islamiyya har sai da Ja'afar ma yaje, yara suna abu kamar wasu maza”.

       “To ya za'ai kowa da irin ƙuruciyarsa sai haƙuri. Watarana sai kunga kamar ba'ayi ba in sha ALLAH”.

     “ALLAH yasa muna da rabon kaiwa wannan lokacin. Dama nazo ne akan batun ganin likitan ki, komai ya kammala sai ku fara shiri ke da Ammar ɗin ko”.

          “To ALLAH yay muku albarka. Yanda kuke ƙyautata mana kuma ALLAH ya baku tsahon rayuwar da ƴaƴanku zasu ƙyautata muku su jiyar daku daɗi nan”.

      “Amin Mammah, ALLAH ya ƙara muku lafiya da tsohon rayuwa kuma. Sai batun Haysam, a cigaba da tayamu addu'a in sha ALLAHU muna ganin nasara a wannan karon. Dan yanzu haka ma daga wajen Janar nake, kin san yau sunyi primary election na party ɗinsu Alhamdullah kuma shine yaci matsayin candidate”.

     Wani irin yalwataccen farin ciki ne ya bayyana akan fuskar Mammah, ta haɗiye hawayen da suka cika mata ido tare da faɗin, “Alhamdullahi ya rabbi, UBANGIJI Ya tabbatar mana da alkairinsa. Yasa iyakar jarabawarce tazo”.

         “Amin Mammah, in sha ALLAHU iyakance tazo. Dan in har Janar ya haye kujerar nan ina mai tabbatar da ko sati bazaiyi a gidan gwamnati ba Haysam zai fito.”

    “Idan shi alkairi ne ga ƙasa gaba ɗaya, ALLAH ya bashi nasara, bazan so saboda nasarar fitowar nawa jinin wasu su ƙuntata ba, dan haka zamu cigaba da addu'ar zaɓin alkairi in sha ALLAHU”.

        “Haka ne Mammah, ALLAH ya zaɓa mana abinda yafi alkairin”.

    Sun ɗan ƙara tattauna abinda ya dace kafin yay mata sallama ya wuce..........✍️

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*

*_+227 98 94 12 81_*

*_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*

*_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899*

*_Moniepoint MFB_*

*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_*

*_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_*

*_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_*

*_Chapters & Audio_*

@BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276*

*_Access Bank_*

*_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_*

*_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_*

*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_*

*+234 805 568 7449*

*_Telegram Number👇_*

*+234 903 234 5899*

*_ASSALAMU ALAIKUM MUTANE NA MASU ALBARKA_*

*_Maza ku matso MASOYAN Bilyn Abdull da IDANU suka hana karatun novels...._*

*_Tofa Bilyn ku ta samo muku hanya mai sauƙi da kina aiki, ko kina kwance kina hutawa, ko kina inda baki son yawan surutu earpiece ɗinki kawai zaki maƙala a kunne ko Bluetooth kisha sauraren littafin KIƊA A RUWA.... Cikin sauƙi.... 💃_*

*_Kar dai na cika ku da zance. Zamu fara saida littafin KIƊA A RUWA.... Na saurare (Audio) kenan akan farashi mai sauƙi da rahusa._*

*_Akwai VVIP AREWAPEN kenan 💃_*

*_Akwai VIP Telegram 💃_*

*_(Ƴan WhatsApp ku haƙura kawai ƴan ta'addar bati sunfi yawa a cikinku gaskiya tsoron rashin m ɗinku nake 😂🤣)_*

*_Telegram Audio 2k ne kacal ba tsada 💃. Sai kusaka ta wannan account ɗin👇_*



_(2k)_

*9032345899*

*_Moniepoint MFB_*

*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (2k)_*

*_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_*

*_Telegram Number 09032345899_*

*_Ƴan NIGER🇳🇪 kuma bazamu barku a baya ba in sha ALLAHU zaku biya (Telegram vip 1,500 CFA) domin littafin KIƊA A RUWA..... na ji Audio-vocal. Sai ki biya tanan👇_*.

_(1,500 CFA)_

*_+227 98 94 12 81_*

*_My NITA_*

*Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 1,500 CFA vip telegram

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*

*_+227 98 94 12 81_*

*_AREWAPEN (Vvip)_*

*_Chapters & Audio_*

@BilynAbdull

*_Ƴan WhatsApp kuzo muyi shawara idan zaku iya amana ayi harkar nan daku 😂, dan bana son a barku a baya duk da dai bakwa ji, ba raga min zakuyi ba na sani duk da ƙaunar da nake muku 🤣😂._*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💦KIƊA A RUWA...!!💦_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*

_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_GENERAL FICTION_*

_Wannan labari ƙirƙirarre ne. Sunaye, wurare, da abubuwan da suka faru duk ƙirƙira ne, ba su da alaƙa da gaskiya ko wani, koda Bilyn Abdull ce 😂._

*_BOOK 2_*

_Chapter 10_

__________________

_A KANO KI KE…? Kina neman inda zaki siyi abinci mai daɗi? Kina ƙiyar yin girki gashi zaki yi baƙi?, kina neman inda zaki yi order abinci mai daɗi wanda zaki fita kunya?. Masu abinci suna suka tara, akwai abinci mai daɗi akwai a lallaɓa. Kina son ki siyi abincin da zaki ɗauka a saudia ki ke? Kuna son ku siyi abincin da in kuna ci zaku dinga murmushi saboda daɗi da khamshi?. LEEMARS_DELICIOUS itace kat a wannan ɓangare, tazo muku da nau’in abinci kala-kala na gargajiya da na ƙasar waje. Tana siyar da MANDI RICE, GRILL CHICKEN, CHICKEN BIRYANI, FUNKASO, ALELEN GWANGWANI, BREAD POCKET da sauran su. Fannin abin sha akwai natural ZOƁO mai zaƙi, wanda aka yi shi da ingantattun kayan marmari masu ƙara lafiya, akwai wanda bashi da zaƙi domin masu ciwon sugar da masu gudun ƙiba._

_me ku ke jira? Maza ku garzaya shafin ta na instagram ko TikTok domin ku ganewa idanun ku, ku danna wannan link din domin yin magana da ita kai tsaye. Ko ku neme ta a number wayar ta da take ƙasan rubutun nan._

INSTAGRAM

👇🏻👇🏻👇🏻

https://www.instagram.com/leemars_delicious?igsh=MWRzZWtnYXM4ZHB2dw%3D%3D&utm_source=qr

CALL/WHATSAPP

👇🏻👇🏻

wa.me/2349030398006

TIKTOK

👇🏻

https://www.tiktok.com/@leemars_delicious?_t=ZS-90ZQJ2mNJKc&_r=1

Kar ku sake a baku labari, siyan na gari mai da kuɗi gida.❤️❤️🫶🏻

__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

........Su Nimrah dake laɓe da tunanin za'a sake maganar makarantarsu jin shiru su Mammah ma sun ɗauki wani zancen daban suka bar wajen. Suna shiga ɗaki Nimrah ta ce, “Trouble Buddy! Kin san mi zamuyi?”.

     “A'a sai kin faɗa”.

  “ALLAH in dai Daddy ya dage sai ya kaimu Boarding ɗin nan randa aka kaimu samun wata Senior ɗin zamuyi mu lakaɗa mata dukan da a washe gari za'a kirashi ace an koremu gaba ɗaya. Idan mun dawo gida mu dage masa kan bamu san munyi ba aljanu ne damu da gaske.”

      Sai da Ruky tai dariya sosai sannan ta ce, “Sai da ke Hot Pepper! Amma fa ni kin san wani lokacin ina da ɗan tsoro, kada muje wajen ƙaryar aljanu a samo wani ustazu ya daki banza da sunan Rukya, ko'a ƙara na kwanaki yace zai aurama su maigadi mu.”

         “Ai ke banza ce. To bari kiji ALLAH bazasu bari a dake mu ba. Balle ma in har za'a Boarding ɗin nan dole muyi sanadin da za'a haɗa harda Fiddo da Bintu”.

     “Muguwa naga mu kaɗai mukai laifin? ALLAH ki dinga jin tsoron ALLAH Ninah”.

     Itama dariya tayi yanzun kam, ta wani juya idanunta manya cike da iyayi, “Yo da tsoronki nake ji Ruky. Bazaki gane ba idan muka haɗu mu duka sai Boarding ɗin ma tafi daɗi idan ta zama ƙaddarar mu. Mu haɗu mu dinga darje bakin ƴan iska da duk suka nuna mana yatsa.”

      Tafawa sukai suna dariya....

Nace ALLAH dai ya shirya waɗan nan yara🏃🏼‍♀️. Daddy Imran ka rufa mana asiri ka barsu a Day school ɗinsu, kada wataran suja maka ka sake komawa inda Dada yake.🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️😂.

____________★

         Aiki gida dai ya tabbata akan ƴan caskalen gidan Mammah, dan kuwa a bazata washe gari tunda safe sai ga Imran a gidan, suna tsaka da barcinsu ya saka Aunty Biebah taso masa su. Da farko sai faman layi suke suna ma Biebah kukan shagwaɓar ta barsu su barci suke ji, amma suna cin karo da Daddy suka watsakke, a tare suka zube suna gaishe shi. A taƙaice ya amsa musu tare da faɗin, “Oh barci ma kuke yi har zuwa yanzu? Batun breakfast, shirya ƙannenku zuwa school duk wa zai yi?”.

      “Daddy kayi haƙuri, ALLAH bamu san barci ya sake ɗaukar mu ba”.

    “Na baku mintuna goma ku wuce ku shiryo su Abees”.

     Kafin ma ya gama rufe baki sun fice a sashen. Kai tsaye sashen su Yaya Ja'afar suka nufa kamar zasuyi kuka, dan suyi sauri sai suka rabu. Nimrah ta shiga sashen Yaya Ma'aruff ita kuma Ruky na Yaya Ja'afar. Shigowar Nimrah dai-dai da fitowar Aunty Lailah daga ɗakin su Aheel, fuskata da murmushi ta ce, “A'a Ninah miya faru ba'ai shirin makaranta ba?”.

     Kamar Nimrah zata saki kuka ta ce, “Ammie kin manta muna suspension? Zan shirya su Aheel kije ki kwanta kawai”.

       “Oh na manta, amma Ninah aikin zai muku yawa, ga haɗa breakfast ɗin gida gaba ɗaya, ga gyaran sashen ku. Kije kawai bari na shirya su kinji”.

      “Ammie Dady fa na nan”.

Cikin ɗan waro idanu Aunty Lailah ta ce, “Gidan Yayan yazo da sassafen nan?”.

     Kai ta jinjina mata. Dai-dai da fitowar Yaya Ma'aruff ya ce, “Wayo yazo da sassafe?”.

      “Wai ya Imran”.

  Murmurshi kawai Yaya Ma'aruff yayi yana girgiza kansa da faɗin, “ALLAH yanzu gaba ɗaya Yaya Imran ya canja zuwa Dada, da dai babu ruwan shi da faɗa amma yanzu ya gaje halin twiny sa. Ninah zo nan”.

       Sum-sum Nimrah ta iso inda yake, zama tai a ƙasan lallausan carpet ɗin tace, “Uncle good morning”.

      “Morning sarakin ƙiriniya, ke dai ke da Ruky ku saka mutane surutu shine jin daɗin ku ko. ALLAH idan baku canja ba duk randa Dada ya dawo gidan nan sai kun gane Yaya Imran bai iya komai ba”.

       Caraf Nimrah ta ce, “Uncle kenan Dada shi mugu ne?”.

      Dariya yanda tai ɗin yaso saka Ma'aruff, amma sai ya danne ya murmusa kawai. “Dada ba mugu bane, amma baya son rashin ji, ku tambayi Ammar zai baku labari dan shi ma da rashin ji ya fara Dada ya saita shi da horon sojoji. To kuma idan baku nutsu ba duk randa ya dawo jiki magayi”.

           “In sha ALLAHU zamu ma bari, amma dan ALLAH Uncle wai shi Dadan yana wace ƙasa ne? Yaushe kuma zai dawo? ALLAH ina son na ganshi, kaga sai a hoto muka taɓa ganinsa shima sau ɗaya ne Mammah tasa aka tattare hotunan aka ɓoye”.

      Sai da Yaya Ma'aruff ya haɗiyi yawu mai ɗaci sannan yay ma Nimrah murmurshi kaɗan. Bayan su masu hankali har yanzu daga Mu'azz har su Nimrah basu san Dada na prison bane, kawai ance musu yana wata ƙasa ne yin wani aiki mai muhimmanci. Dan ko Biebah ba komai ta sani ba sai kaɗan-kaɗan daga cikin lamarin shima dan ya watsu a media ne lokacin...

      “Ninah in sha ALLAHU Dada zai dawo, ina ji a jikina nan kusa ma kuwa zai dawo gare mu. Ku dai ku cigaba da addu'a kawai. Dan zuwansa garemu zai iya zama tamkar haɓo ne kinji”.

        “ALLAH yasa Uncle, kuma in sha ALLAHU kullum zamu dinga zama mu da su Abees muna addu'ar”.

    To ALLAH yay muku albarka. Ina Sisin taki?”.

    “Mun raba aiki ne tana can zata shirya su Abees”.

        “To kinga tunda ga Ammien ku na shirya su Aheel anan tashi muje, ni zan janye Yaya Imran ɗin sai kuyi sauri ku haɗa breakfast kawai”.

    Sosai farin ciki ya kama Nimrah, koda suka fito suka leƙa sashen Yaya Ja'afar sai suka sami Rukyn ma ba aikin take ba, tana gyarama Afrah gashi ne dan har an musu shirin makarantar ma. Sai kawai ta kamota suka fito zuwa sashen Mammah, ta ƙofar baya ta kitchen Yaya Ma'aruff yace su shiga, shi kuma ya zagaya riƙe da hannun Afrah dake zuba masa surutu, dan itama dai akwai baki ta gado su Nimrah ɗin.....

Tun a haɗa breakfast Nimrah da Ruƙayya suka san ALLAH ɗaya ne. Masu aiki kuwa na ƙoƙari kwarai-ƙwarai da gaske. Suna wayyo-wayyo Uncles ɗin nasu da Auntys na dariya suka jera a babban family dining table ɗin makeken falon Mammah. Dan dama haka suke cin abincinsu a tare tun daga na safe har na rana ga wanda suke a gida. Na dare kuwa dama kowa yana nan. Kowa na ƙoƙarin kammalawa ya wuce aiki suko suna haƙilon gyaran kitchen, ga Mu'azz ya saka rayuwarsu gaba. Daya motsa sai ya ƙwala musu kira.

       “Ninah bani kaza, Ruky baku ajiye abu kaza ba”.

     Suko takaici ya ƙulesu sai su ɗakko a hasale su dangwarar masa. Dariya kamar ta kashe su Aunty Shariffa. Aunty Biebah ce ma suka bata tausayi bayan tafiyar Daddy Imran tace su gyara falo kawai bari ta tayasu gyara bedrooms tunda dai can ai babu camara balle Yaya Imran ɗin ya gani. Dan koda zai wuce sai da ya sake jaddada musu idan ma basuyi ba zai gani ta cctv Camaras dake zagaye da gidan tako ina. Wannan ya sake sasu tsorata suka dage. Duk da taya sun da Aunty Biebah tayi basu kammala komai ba sai 12 da wani abu, a wahale sukai wanka sukazo falo inda su Aunty Shariffa ke hira dan su basa zuwa aiki, shiyyasa koda yaushe suna sashen Mammah suna ɗebe mata kewa. Balle yanzu hirar na armashi Mu'azz yana gida zaune kafin ya wuce University. Yau kuma anyi sa'a Aunty Biebah ma dake gab da kammala master nata bazataje school ba. A ƙasan lallausan carpet ɗin falon suka zube kowa na maida numfashi.

     Mu'azz ya kwashe da dariya cike da mugunta. “Oh ALLAH yau ga mata sunyi aikin gida. Ku a haka za'ai muku aure kuje kunayi, dan ALLAH ji Ninah kamar an tsamo mage a ruwan zafi, gara-gara ma Ruky”.

        Kamar Nimrah zatai kuka ta ce, “Mammah kin jisa ko, wai nice mage a ruwan zafi”.

      “Shi kuma muzuru ko?”.

Cewar Biebah na jifansa da filo. Cafewa yay yana dariya da faɗin, “Kai small Mom muzuru kuma. Dan ALLAH kar ki saka yaran nan su raina ni mana. In ba haka ba ALLAH zan zuga Daddy a kaisu boarding school ɗin nan mu huta. Su Ayyan sun ishe mu”.

       “Idan su basu tafi Boarding school ba

8 / 24