Advertisements
Chapter 16 Reading Kida A Ruwa Book 2 Complete Hausa Novel Hausa Novels
Advertisements

Kida A Ruwa Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Billyn Abdul Category :  Action Novels

Chapter   16 / 24

45K to 48K   out of 71K words

   Zasu fara magiya ya ce, “Okay nace Mammah tai zamanta kada ta dawo goben kenan?”.

      Ai tuni suka saki batun dawowa gidan suka fara murna jin Mammah zata dawo. Abin zai birgeka har su Auntys ɗin farin ciki suke yi. Shi dai Imran yay ma Baby addu'a sosai ya ɗan zauna suka taɓa hira sannan ya miƙe zai tafi. Dole Aunty Hafsat ta miƙe suka wuce tare. Su kuwa sai anyi sallar magriba sannan koma isha'i....

>>>><<<<★★>>>><<<<

          ★DUBAI★

  Cikin zafin rai take magana kuma da harshen turanci. Shi ko yayi sabale yana kallonta dan komai tayi birgeshi take. Shi kaɗai yasan irin wutar masifar sha'awarta da yake ji tsahon shekaru. Ya kuma kasa binta ta ƙarfi batare da yasan dalili ba. Bayan kuma hakan abu ne mai sauƙi a garesa duk da kuwa yasan tana da aure. Yasan inda wata ce ba ita ba yanda yake narkama uwarta kuɗi duk da hakan ba komai bane a garesa da tuni ya mata fata-fata ta yanda ko rayuwarta sai ya ce ga yanda zatayi sannan zata gudanar da ita.

      Yanzu haka yana ƙasar Garmany ne harka business ɗinsa Hajiya Hasiba ta tura masa saƙon kudirin Nabeeha, yana gani hankalinsa ya tashi, a take ya kira duk wani Companyn sauka da tashin jirage yasa aka rufe damar Nabeeha na barin ƙasar. Amma duk da haka hankalinsa yaƙi kwanciya a daren ya baro ya dawo dubai ɗin. Kai tsaye gidan nasu yayo, cikin sa'a kuma ya sami Nabeeha a falo zaune ta haɗa kai da gwiwa tana kuka. Zama yay kusa da ita da kai hannu zai taɓata ta zabura, shine take zazzaga masa ruwan masifa data sakashi zuba mata ido kawai yana kallonta...

        Su Ismat dake laɓe farin ciki ya kamata, dan itama wlhy ta tsani guy ɗin nan, dan bata da wani burin daya wuce Nabeeha ta koma ɗakin aurenta. Ta haka ne kawai itama zata samu cikar nata burin na mallakar Ja'afar. Cike da munafunci Amima ta dannama Hajiya Hasiba kira da mahaifiyarsu data shigo gari tun cikin satin daya gabata. Aiko cikin mintinan ƙalilan suka iso dan duk suna kusa da gida ne dama. Wata tsawa Hajiya Hasiba ta dakama Nabeeha. Cikin zafin rai ta ɗaga hannu zata mareta caraf Adeel ya riƙe hannun.

       Cike da gadara ya ce, “Karma ki fara dan ina ganin mutuncinki na haihuwarta da kikayi, amma da a maimakon riƙe hannun nan naki sai dai ki jisa a ƙasa yana lilo”.

    Maimakon jin zafin abinda yay mata murmushi Hajiya Hasiba tayi daga ita har ƙanwarta Mamawo. Cike da girmamawa suka shiga faɗin, “ALLAH ya huci zuciyar babba ɗan manya jinin alkairi. Nayi kuskure ayi haƙuri raina ne ya ɓaci. Taya zata zauna tana gaya maka irin wannan shirmen..”

       “Karki damu ta isa ne ai, girmanta ne. Ni zan koma kawai, amma zan dawo anjima anan zanyi dinner”.

    “An gama ranka ya daɗe”.

Hajiya Hasiba ta faɗa cike da girmamawa. Yayinda Mamawo ke wani shegen murmushi tana binsa da wani kallo zuciyarta cike da abubuwa. Amma a zahiri baka isa karantar abinda ke ranta ba dan cikakkiyar ƴar bariki ce data iya takunta. Yana ficewa suka koma yima Nabeeha faɗa da nuna mata karfa ta dawo tana dana sani da wannan damar da ALLAH ya bata. Wai miye akai akayi wani Haysam can da bata da tabbacin yana ma raye ko an jima da kashe shi ne.

      Kuka ta saka musu cike da bori da rashin kunya tabar wajen. Dole sukai shiru bayan duk sun ja tsaki. Bayanta itama Ismat tabi zuciyarta na zafi. Koda ta shiga ɗakin taga Nabeeha ta kwanta tana kuka zaman lallashinta tayi, ganin taƙi yin shiru ta ɗauka wayarta a karo na farko ta danna kiran Jiddah, abinda sai ta jima batayi ba saboda duk haushinta suke ji akan gaskiya da take gaya musu.

     Batai zaton zata ɗaga mata ba ma, amma sai gashi ta ɗaga cikin tsaftatacciyar sallama. Da ɗan rawar murya Ismat ta amsa mata, sai kuma ta fara gaisheta. Ɗan jimmm Jiddah tayi kafin ta amsa tana kallon Abban su dan taje barka gidan Aunty Mimi ne shine ta biyo gidan gaishe su. Kukan da Ismat ɗin ta fashe da shi ne ya saka Jiddah faɗin, “Ismat lafiya kuwa? Ko wani ne ya rasu?”.

       “Aunty babu wanda ya rasu, kawai abubuwa ne suka mana yawa. Mom ta takura dole sai Aunty Nabeeha ta kashe aurenta ta auri wannan mayen mutumin. Jiya mukai shirin gudowa kawai ta sace passport ɗinmu ta ɓoye. Yau kuma sai gashi yazo. Aunty ki taimakemu ki sanar da Abba yazo ya tafi damu. Wlhy gida muke son dawowa, aunty Nabeeha na son komawa gidan mijinta”.

      Jiddah dake jin jikinta ma na rawa ta ɗan saci kallon Abbansu. Ai ko yayi kicin-kicin da fuska yama maida hankalinsa a television inda ake hira da ɗan takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin jam'iyar SGP, wato tsohon janar ɗin soja kuma ɗan majalisan tarayya mai ci Janar Yusuf Shu'aibu Tafida. Yawu masu kauri ta haɗe, cikin damuwa ta maida kallonta ga Hajiya Zuwaira da suke kira Ummu a gidan. Idan ka cire Nabeeha da Ismat da har yanzu basa ko gaisheta. Kai Ummu ɗin ta girgiza mata alamar ta kwantar da hankalinta, dan taji komai itama kasancewar hansfree ta saka wayar.

     Cikin dauriya Jiddah ta ce, “Wannan shi nake nuna muku tun farko amma kuka kasa ganewa Ismat daga ke har Aunty Nabeeha. Yanzu dan ALLAH yaushe rabonku da kiran wani a cikinmu har Abban, aƙalla shekara uku kenan fa. Ni kuma kun saka ni a black list kona nemeku bata shiga harta WhatsApp. Ni yanzu a wannan gaɓar mizan iya yi, wane tabbaci ne dani akan baku biye ma Momy ɗin ba akan ƙudirinta.....”

        “Wlhy aunty bamu taɓa aikata wani abu saɓanin abinda kike tunani ba mu kammu balle Aunty Nabeeha”.

    Duk da Jiddah bata da tabbaci sai da ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi, duk da tasan wacece mahaifiyarsu akan son duniya babu abinda bazata aikata ba. Itafa ko uwarmi zasuyi suyi ba ruwanta tunma suna ƙananunsu indai kuɗi zai shigo fine. Hawayen da suka cika mata ido ta haɗiye, ta ce. “Shike nan Ismat ki bani zuwa gobe, yanzu haka ma bana gida naje barkar Aunty Mimi ne data haihu. Amma zan yi magana da Abban”.

          “To aunty dan ALLAH ki taimaka mana, ke kaɗai ce hope ɗinmu a yanzu wlhy”.

     “Karki damu in sha ALLAH duk yanda muke zan taɓoki, ni dai fatana ku cigaba da riƙe mutuncinku kada ku biyema Mom”.

    “In sha ALLAHU Aunty ki mana addu'a”.

       “Ita nake muku kullum”.

Daga haka ta sauke wayar. Tun kafin ma tai magana Uncle Nasiru ya dakatar da ita da faɗin, “Tashi ki wuce gida dare yayi? ALLAH ya bamu alheri”.

     Yanzu kam sosai idonta ya tara hawayen, ta waiwaya tana kallon Ummu. Kai ta jinjina mata alamar taje, tabar komai a hannunta kawai. Sai kawai ta miƙe tai musu sallama ta fita. Dama ita ta tuƙo kanta. Aiko tana shiga motar ta kife kanta a sitiyari kawai ya fashe da kuka. Ta jima tana kuka har sai da maigadi yazo yana mata knocking glass sannan ta haƙura ta share hawayenta taima motar key......

<%>°<%>°<%>

      PRISON

      

     Wani zuba masa kaifafan idanunsa yay a hankali, tare da sakin wani murmushi mai zafi da izza, mai tabbatar da cikakken izgili da raini fiye da nashi. Dan a ƙarshe da wani salo irin na maida mutum banza sakarai Dada ya taɓe baki. Sannan cikin son tunzurawa ya ɗan karkatar da kansa, fuskar sa ta cika da izza mai nutsuwa. Like yana magana da wani shasha can ya furta,

       “Tofa! kaga fa kana ƙoƙarin bani mamaki.” Ya yi murmushi mai ɗan kaifi, ba na farin ciki ba, na jarumin da ya saba da iya riƙe nauyin abu a zuciya da ƙwaƙwalwa batare daya bari abokin gaba ya fahimci lagonsa ba. Cikin halin ko in kula ya cigaba da da ɗin, “Ka zo nan kana min barazana da dorinar ƙarya, ka ce ku ne ƙasa, ku ne haske, ku ne gwamnati. Amma duk da wannan ƙarfin ikon naku kuma kuka zaɓi ɓoye fuska kamar masu tsoron haske a gaban ZAKIN dake ɓoye cikin keji?. Gaskiya ban yarda da wannan ƙarfin ikon naku mai kama dana ƴan wasan kwaikwayo ba, ya kamata ku koma ku canja shiri.”

      Ya ɗan sake matsawa gaban tebirin sosai yana sassauta murya kamar mai son yin raɗa idanunsa na sake shiga cikin na baƙon, sai dai  muryar tasa ta cika da nauyin, da ƙarfi irin na masu izzar ƙarfin zuciya da jarumtar ƙwarai dake jinsu ko a ɗaure su ba masu risinawa wawaye bane.

      “Ɗan aike!. Ka manta da abu ɗaya.”

     Shiru ya mamaye ɗakin. Baƙon ya tsaya tamkar an dasa shi a wajen yana kallon Zak-Shadow da jin ƙaguwar son barin wajen dan wani irin firgitashi al'amarinsa keyi, dauriya kawai yake da dannewa saboda sanin akwai camara a jikinsa dake ɗaukar komai. Kai tsaye kuma duk abinda suke tattaunawa ƴan ƙungiya ma na kallonsu........✍️

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*

*_+227 98 94 12 81_*

*_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*

*_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899*

*_Moniepoint MFB_*

*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_*

*_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_*

*_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_*

*_Chapters & Audio_*

@BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276*

*_Access Bank_*

*_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_*

*_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_*

*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_*

*+234 805 568 7449*

*_Telegram Number👇_*

*+234 903 234 5899*

*_Maza ku matso MASOYAN Bilyn Abdull da IDANU suka hana karatun novels...._*

*_Tofa Bilyn ku ta samo muku hanya mai sauƙi da kina aiki, ko kina kwance kina hutawa, ko kina inda baki son yawan surutu earpiece ɗinki kawai zaki maƙala a kunne ko Bluetooth kisha sauraren littafin KIƊA A RUWA.... Cikin sauƙi.... 💃_*

*_Kar dai na cika ku da zance. Zamu fara saida littafin KIƊA A RUWA.... Na saurare (Audio) kenan akan farashi mai sauƙi da rahusa._*

*_Akwai VVIP AREWAPEN kenan 💃_*

*_Akwai VIP Telegram 💃_*

*_(Ƴan WhatsApp ku haƙura kawai ƴan ta'addar bati sunfi yawa a cikinku gaskiya tsoron rashin m ɗinku nake 😂🤣)_*

*_Telegram Audio 2k ne kacal ba tsada 💃. Sai kusaka ta wannan account ɗin👇_*



_(2k)_

*9032345899*

*_Moniepoint MFB_*

*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (2k)_*

*_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_*

*_Telegram Number 09032345899_*

*_Ƴan NIGER🇳🇪 kuma bazamu barku a baya ba in sha ALLAHU zaku biya (Telegram vip 1,500 CFA) domin littafin KIƊA A RUWA..... na ji Audio-vocal. Sai ki biya tanan👇_*.

_(1,500 CFA)_

*_+227 98 94 12 81_*

*_My NITA_*

*Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 1,500 CFA vip telegram*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*

*_+227 98 94 12 81_*

*_AREWAPEN (Vvip)_*

*_Chapters & Audio_*

@BilynAbdull

*_Ƴan WhatsApp kuzo muyi shawara idan zaku iya amana ayi harkar nan daku 😂, dan bana son a barku a baya duk da dai bakwa ji, ba raga min zakuyi ba na sani duk da ƙaunar da nake muku 🤣😂._*

*_Typing📲_*

*_💦KIƊA A RUWA...!!💦_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*

_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_GENERAL FICTION_*

_Wannan labari ƙirƙirarre ne. Sunaye, wurare, da abubuwan da suka faru duk ƙirƙira ne, ba su da alaƙa da gaskiya ko wani, koda Bilyn Abdull ce 😂._

*_BOOK 2_*

_Chapter 21_

__________________

*_HUMMM! Anzo dai-dai wajen fa. Nace anzo inda kuke jiran fa. Darrrr ne masoya 💃💃💃💃💃_*

*_KIDA A RUWA... AUDIO AREWAPEN & AREWABOOKS 💃💃_*

*Na Bilyn Abdull*

*_Anata hayya-hayya babu ku ina zan barku da ji a labari. Masu iya magana fa kance (A SA A BAKA YAFI A RATAYA). Ni daku akwai amana fa, dole nake nemo muku mafita kuma ku SHOSHALE 💃_*

_Alhamdulallahi MASOYA masu matsalar IDO matsalar ku ta ƙare kuma, ya fara sauka da ZAFINSA fa 💃._

*Ina magana akan masu jiran AUDIO ne. Maza ku garzaya AREWAPEN ko AREWABOOKS domin sauraren naku kuma faka-faka.*

_Hajjaju kina aiki kina sauraren kayan ki, ƴan gayu babu ruwan ku da kallon screen 😘. Sai da ku NA-WAJENA. 😀😘💃._

*_Ina gaya muku faka-faka zan zube muku su, ku zo gaɓar da ake kuma mu cigaba da tafiya tare. To mi yafi ranku ALLAH na tuba._*

*_Ku na Bilyn Abdull ne. Bilyn Abdull ɗin ma fa taku ce, dan dole Oga ya raba daku walle. Yo irin wannan ji daku da nake haka😂😘😘😀😀😀._*

__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

........Tunaninsa ya katse sakamakon cigaban kalaman Zak-Shadow masu zafi da sanya zuciya raɗaɗi.

         “Idan kaje ka sanar da iyayen gidanka saƙo daga ni Haysam Abdul-rasheed Shehu. Ku na mallakar gwamnati, amma ba kwa mallakar ƘASA. Ku na mallakar masu muƙami, amma ba kwa mallakar mutanen da suke amsa sunan KASAR. Ka sanar musu. Idan suna tunanin zasu sarrafa ni kamar karnukan su… to su sake tunani tun kafin lokaci ya ƙure musu. Ka faɗa musu. Wannan ba ƙarshen wasan ba bane, farkon rugujewar su ne, domin kuwa yanzu ne za'a FARA WASA na GASKIYA. Ka faɗa musu. Wanda yake da cikakken iko ba ya zuwa ya gaya wa wanda yake tsoro barazana. Domin wannan zuwan naku tabbatar min yay da kun MATSORATA ne, kuma ni abin tsoronku ne. Na ji ƙamshin wannan tsoron naku tun shigowarka nan. Ka faɗa musu. Idan kun kasance da ikon da kuke ikirari… ku kasheni kawai zai fi muku sauƙi da samun cikar burin ku cikin salama” ya ɗan yi dariyar da ta sake tsokano zuciyar bako. Batare da bashi damar cewa komai ba ya cigaba da faɗin,

     “Ka faɗa musu. In har kukai sakacin ƙin kasheni da ɗaukar zantukana cika baki, to ku shirya… ku shirya wasan da muka fara ba lissafin saƙar zaren ginin gidan GIZO-GIZO ba. Ka faɗa musu. Shi wannan filin da suke cika bakin samarwa domin ƙwallon ƙafa, da jinin da zasu jiƙa ƙasar domin ta tausasa. Ni ne zan samar da filin WASAN, sannan na jiƙa ƙasar da jinin jikinku. A maimakon buga wasan ƙwallo na ɗaura muku sarƙar mata a ƙafafuwa ku zagaye filin da takun RAWAR ƘOROSO. Ka faɗa musu. Ni nake tsara gangar da masu kiɗanta, kuma tabbas in sha ALLAHU sune zasu taka wannan rawar fa. Ka tafi ka faɗa musu. Na gane kun TSORATA. Sannan wannan SAƘON daka kawo zai zama kuskurenku na farko. Na biyun zai biyo bayan fitowata daga nan. Ka faɗa musu. Idan har iyayensu sun haifesu da alfaharin igiyar aure, kamar yanda ni Haysam Abdul-rasheed Shehu Kobi A'isha da Abdul-rasheed suka haifeni da wannan alfaharin ku rubuta kalamaina ku ajiye da yaƙini a saman dutse. Sannan ku shirya.”

     Ya turo kujerar ya tashi a hankali yana sakin murmurshin ƙasaita tamkar sarki ya miƙe daga gadon mulkinsa. Ya zubama agogon hannunsa idanu na sakanni tare da sake sakin murmushi mai ma'anoni da yawa sannan ya fara takun dake nuna alamar barin wajen. Da sauri shima baƙon ya kalla agogon nashi mai ɗauke da camara saboda kallon da Zak-Shadow yay ma agogon ya tabbatar ɗayan biyu ne, ko dai ya fahimci camara ɗin ce ko ya tsargu....

     Dada da yay takun da bai gaza biyar ba ya tsaya cak, tare da juyowa a hankali, idanunsa suka sauka a kan mutumin. Fuska ta bogi, amma mugunta ta gaskiya.... Murmushi ya sake saki da ɗan taɓe baki. Cikin salon isar da saƙon ƙarshe a inda yake da tabbacin masu aiken na kallonsa yanda ya dace domin idanunsa kam a kan agogon mutumin ya furta,

      “Ni bana kare gwamnati. Bana kare hukumar soji. Bana kare kujerun ƴan mulkin mallaka. Amma ku sani. Na kare ƙasa. Na kare mutanen ƙasa. Na kare gaskiya duk da ƙarfin ikon UBANGIJI mai IZZA da cikar mulki na gaskiya. Wannan kuma… Shine abinda kuke tsoro. Zan ƙara tabbar muku, idan har kuka bar Haysam Abdul-rasheed Shehu a raye, zai cigaba da tabbatar muku wannan tsoron a cikin ZUKATA. Bance zan iya komai ba, amma bazan taɓa raina kaina a gaban ALADU irin ku ba”. Ya ɗan yi shiru yana murmurshi mai ciwo, dan kowace kalma yana fitar da ita ne daga zuciyarsa kamar takobi mai kaifin gayawa jini ya wuce.

     Baƙo da zuciyarsa ke dukan uku-uku cike da ƙarfin hali ya ɗan taɓe baki, numfashinsa dake fita da rawa ya fisgo da ƙyar dan neman ƙwace masa yake. A karo na farko ya ji wani abu ya motsa masa a ƙirji, ba tsoro bane kawai, ba kuma bakin ciki bane kawai. Bayyanan nen rauni ne dake tuna masa, shima fa ɗan ƙasa ne tamkar Zak-Shadow, yana da dangi a ciki ba iyalai kawai ba, yana da ƙarfin ikon kiranta tushe ba son tara dukiya da ƙarfin ikon son mulki kawai ba....

       Dada daya gama fahimtar raunin nasa dake son bayyana ya juya zai fita abinsa yana murmurshi, sai kuma ya sake tsayawa tare da juyowa a lokaci guda. Da tabbatar wa ya ce, “Ya kamata na sake jaddada muku domin fita hakki. Kar ku barni a nan domin in gani daga shirin shirin ku. Idan kukai wannan

16 / 24