Author : Billyn Abdul Category : Action Novels
ya daɗe kada ai haka. Mudai bari a zauna dasu aji miya haɗasu, duk da nasan Naja'atu da Ruƙayya fitinannun yara ne amma basa faɗa sai da dalili...”
“Oh yanzu na fahimta, to kodai kaine ka sakasu su aikata ma saboda kana nemansu? Dan ba abin mamaki bane idan muka dubi yanda malamai suka koma fasiƙanci da ɗalibansu a makarantu”.
“Innalillahi wa'ina ilaihiraji'un, Hajiya wane irin magana ce wannan? Dan na faɗi abinda yake gaskiya kuma sai ki aibantani da yaran da suke tamkar ƴaƴanki. Amma dai.....”
“Teacher Khalil ya isa haka. Ka fahimta kawai ranta ne ya ɓaci. Yanzu dai ka kira gidan su yaran sannan azo min da su nan yanzu nan”.
Sosai ran wanda aka kira da Teacher Khalil yake a ɓace da zancen matar, sai dai bai sake cewa komai ba ransa na ƙuna ya shiga neman layin wanda yasan Yaya ne gasu Ruƙayya, amma fin kira goma bai shiga ba. Ganin ba samu zaiba principal yace ya sake kiran wata number mana, canja kiran yay zuwa ɗayar number da yake da ita, cikin sa'a kuwa ta shiga. Koda aka ɗaga cikin nutsuwarsa yay bayanin daya dace, a ƙarshe ya sanar da ana buƙatar ganin wani nasu babba daga haka ya ajiye wayar ya fita a office ɗin....
Mintina kaɗan Teacher Khalil ya dawo, sai da ya shigo sosai matasan ƴammata biyu suka bayyana. Ta gaba fara ce tas kuma ƙyaƙyawa, siririya daga ganin fuskata kasan zatai rashin ji. Wadda ke biye da ita ma da zasu iya zama kai ɗaya black beauty ce masha ALLAH, itama dai daga ganin fuskar nan kasan zatai tsiwa. Su duka sanye suke da uniform skirt peach color da farar riga long sleeve shirt, sunyi zanzaro da skirt ɗin, sai ɗan ƙaramin baby hijjaf fari shima da iyakarsa matashin ƙirjinsu da ake kiran kamar su da suna ƙwailoli. Daga ƙasa safa ce doguwa data zo har gwiwar ƙafa saboda skirt ɗin nasu kaɗan ya zartar gwiwar sai takalman sandal baƙaƙe na ƴan makarnta. Ga shi dai uniform ne ana saka shi badan ado ba, amma yayi musu matuƙar ƙyau da zaunawa a madaidaicin jikinsu ɗas kamar ka lashesu. Ga wani ƙamshin turare mai sanyin daɗi na fita a jikin nasu da gogaggun uniform ɗin su da suka sha karin guga kamar batun safe suka sakasu ba.
A makarantar ba'a dukan ɗalibai sam, dan makaranta ce ta kuɗi kuma ta ƴaƴan manyan ƙasa. Duk wanda aka gani a school ɗin lallai ubansa yaci ya ƙoshi ne. Shiyyasa daga ƴaƴan masu mulki saina jami'an gwamnati dana manyan ƴan kasuwa. Dan makarantar ma ta baƙin haure ce ƴan ƙasar waje ba ƴan ƙasa ba. Rabi da kwatar malaman cikinta duk masu jajayen kunne ne, sauran tsiraru irinsu Teacher Khalil ne kawai ƴan ƙasa baƙaƙen fata, sai kuma shi kansa principal ɗin shima dai ɗan ƙasa ne.
Da farko idanu principal ya zuba ƙyawawan ƴammatan biyu, yayinda matar nan ke zuba musu uwar harara kamar idannunta zasu zubo. Hakama ƴarta dake lafe a jikinta tun shigowar yammatan dake sa'ointa ta sake mannema uwarta tana harararsu. Suko sun wani tamke fuskoki suna cika suna batsewa. Haɗa ido baƙar tayi da yarinyar, tako watsa mata uwar harara da nunata da yatsu biyu alamar saita tsokale idon...
Wani irin takaici ya sake mamaye zuciyar uwar, dan ta kasa gane ita zata tsokalewa ido ko ƴar tata tunda itama hararar take. Baki ta buɗe zatai magana principal ya katseta sakamakon ambaton sunan yaran da yayi.
“Ruƙayya Imran Abbas”.
A cinkushe farar tace, “Yes Sir!”.
Ya sake maida idonsa ga baƙar ya ce, “Naja'atu Muhammad”.
Itama cikin tura baki tace, “Yes Sir”.
“Ku miyasa bakwa jin magana ne, yara kamar ibilis ne malamin ku kullum cikin kawo ƙararku ake. Yanzu ku duba yanda kuka fasa mata kai, inda abin yazo da ƙaddara fa...?”
“Sir sai kun haɗa da addu'a fa a lamarin nan, dan lokuta da dama aljanun mu ne ke wannan aika-aikar bamu bane ba ko my Trouble Buddy?”. Ta ƙare maganar da juyawa tana kallon Ruƙayya.
Caraf Ruƙayya ta amsata da “Hakane wlhy My Trouble Queen, Sir wani lokacin bayin kammu bane ba. Amma zamu faɗa a gida su ƙara dagewa da addu'a da neman magani ko zamu nutsu. Wani lokacin kuma yaran ne tarbiyyarsu bata cika ba shine muke ɗan daidaita musu sahu.”
Kallon kallo aka koma tsakanin Principal da Hajiya mai ƴa, yayinda Teacher Khalil daya san halin kayansa ya kauda kai yana murmurshi kawai. Yarinyar kuwa kuka ta fashe da shi, “Wlhy Momy ƙarya suke, babu wani aljanu da suke da shi. Haka suke yi sai sun gama rashin mutuncinsu sai suce aljanun su ne suka tashi.”
“Barsu Baby zan nuna musu su ƙananun ƴan iska ne, badai sun ce su basa ji ba.” tai maganar tana ɗaukar wayar ta. Ƙoƙarin dakatar da ita principal keyi amma taƙi saurarensa. Abinda zai baka mamaki ko'a kwalar rigar Ruky da Nimrah. Tsabar sun shahara ma chocolate Nimrah ta ciro a aljihun gaban rigarta ta shiga barewa, koda ta gutsira sai ta miƙawa Ruky ma ta gutsira hankalinsu kwance suke ci kuma. Takaici kamar ya shaƙe principal, bai iya sake magana ba kawai ya zuba musu ido.....
★★★
Da steps uku-uku yake tsallako stairscase ɗin ƙayatacen falon dake fidda ƙamshi mai ɗan karen daɗi. Waya ce manne a kunnensa, sai da yazo gab da direwa ya cire wayar yana cusata a aljihun jallabiyar jikinsa. Ko kaɗan bai dubi sashen kujerun falon ba balle ya san akwai mutane ma. Fuuu ya wuce kai tsaye ga ƙofar fita abinsa...
“Wai saurin mi kake haka kamar zaka tashi sama ko ganin mutane bakayi?”.
Juyowa Ammar yayi dai-dai yana gab da fita a ƙofar falon gaba ɗaya, cikin ɗan dafe kai da furzar da iska ya dawo cikin da baya dan shi sam baima lura da su ba saboda tsabar hankalinsa baya a jikinsa. “Sorry Yaya wlhy ni ban ganku ba ma. Daga makarantar su Ninah aka kirani wai ita da Ruƙayya sun fasama wata yarinya kai da duka har iyayenta sunje school ɗin da ƴan sanda, shine principal ɗin ya kirani saboda yanata neman layin Yaya Bilal bai shiga ba, shine nace masa baya ƙasar ne, da akace su bada number wani suka bada tawa”.
“Ya rabbi, anya wataran waɗan nan autocin na Mammah bazasu saka a tattare kaf jama'ar gidan nan zuwa station ba. Ni kam ba jiya Ja'afar yaje wata shari'ar tasu Tahafiz ɗinsu ba?”.
“Jiya ne wlhy Yaya Ma'aruff, dan bama a gama case ɗin ba yau sai Yaya J ɗin ya sake komawa suka ce.”
Kiran daya sake shigowa wayar Ammar ce ta hana Yaya Ma'aruff magana, shima bai ɗaga ba, sai kallon Yaya Ma'aruff ɗin da yayi. “Yaya bari naje sune suke sake kira fa. Da alama abin fa serious ne”.
“Nima ai banga ta zama ba muje kawai dama zanje wani wajene na biyo gidan amsar takardu wajen Mammah. Amma yau inaga sai na zane Ninah da Ruky a gidan nan, yara sai baƙin fitina saboda sunga Mammah na hana a duke su.”
Ƴar dariya Yaya Ammar yayi a karo na farko, dai-dai yana kama handle ɗin ƙofar ɗakin ya ce, “Ashe Mammah zatai ma kowa baki yabi titi a gidan nan, taɓa mata kafi autoci ai yaƙi ne mai zaman kansa. Yaya kaima nasan ka faɗa ne kawai ba iya dukansu zakai ba”.
“Ai ko yau zan baka mamaki”.
Yaya Ma'aruff ya bashi amsa dai-dai suna kaiwa ga mota....
✯✯>><<✯✯>><<✯✯
★DUBAI★
“Yanzu ke dai Nabeeha ina nuna miki abinda zai fisheki amma kullum kina runtse ido ko? Shekara fin takwas idan na taroki nan sai ki zille nan kamar nice zanji daɗin rayuwar bake ba”.
Sake tsuke fuska Nabeeha dake kwance a gado tana sarrafa laptop ta sake yi. Shiru kamar bazata tanka ma Momyn nata ba sai kuma ta ɗago tana kallonta. Rai ɓace ta ce, “Momy wai mi kike so nayi ne? Aure kan aure ko bin mazan waje da aure na?. Kinfi kowa sanin fa Haysam ba saki na yayi ba, da auren kenan zan kula mutumin da ranki ke so dan kawai yana da kuɗi yana kuma baki?”.
Zaune Momy takai kusa da ita, cikin kwantar da murya ta ce, “Ni ba haka nake nufi ba Nabeeha, taya zan so ƴar cikina tabi maza ne. Kawai dai ina son ki farka daga wannan nannauyan barcin naki. Yaron nan shekara ɗai-ɗai har ashirin da biyar aka yanke masa a gidan yari, a hakan ma baki da tabbacin zai fito. Ki duba yanzu shekarunsa takwas kenan, Imran da yake ubansa mai kuɗi ne shekara uku ya fito, shi ko ubanwa ya sani ko ya sanshi, manyan nasa ma duk ya bisu ya zage da rashin mutuncinsa da girman kai. Kina ganin da ƙuruciyarki da ƙyawunki zan bari ki ƙare rayuwarki a jiransa ne. Ganinsa ma ya gagareki kwata-kwata. Amma ki duba mutumin nan yanda yake mutuwar son ki, hotonki kawai ya gani a waya ya haukace tsahon shekaru kuma bai taɓa fushi ba. Ƙyaƙyƙyawan Balarabe jinin mulki ga kuɗi tamkar sune ƙasar takawar sa, ƙyawawan mata nawa ƴan uwansa larabawa ya watsar yace kece zaɓinsa. An kawo masa ƴaƴan sarakuna kala-kala a dauloli daban-daban na larabawa amma ko kallonsu bayayi. Ya nace sai ke, ke ɗin nan da kika taɓa aure tsahon shekaru a gidan miji, ƴar Africa, Africa ɗin ma a ƙasa irin tamu, a ƙasar tamu ma a yankin mu da tsiya ta mamaye. Haba Nabeeha kima kanki faɗa wlhy. Idan jirgi kikace kina so na kanki mutumin nan sai ya baki shi, kalla gidan nan da muke ciki fa ƙyauta ya ɗauka ya bani shi batare da yaji ko ɗar ba. Shi wancan matsiyacin da ya rufe idonki in ce ko mota bai taɓa siya miki ba, hasali ma gidan da kuke ciki da kuɗin ubanki aka gina shi. Saboda ya nuna miki shi tattacen ɗan iska ne gagararre ya auri ƴar cikinki. Idan zaki dawo hankalinki ki dawo tun kan lokaci ya ƙure miki. Idan ba hakaba zakiyi dana sani a lokacin da kika rasa Adeel shi kuma aka tabbatar miki ya mutu a gidan yarin shasha kawai”..
Ta miƙe fuuu zata bar ɗakin cike da takaici da baƙin ciki. Dan gaba ɗaya ta fahimci baƙin cikin cigaba ƴar tata take mata.........✍️
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number👇_*
*+234 903 234 5899*
*_ASSALAMU ALAIKUM MUTANE NA MASU ALBARKA_*
*_Maza ku matso MASOYAN Bilyn Abdull da IDANU suka hana karatun novels...._*
*_Tofa Bilyn ku ta samo muku hanya mai sauƙi da kina aiki, ko kina kwance kina hutawa, ko kina inda baki son yawan surutu earpiece ɗinki kawai zaki maƙala a kunne ko Bluetooth kisha sauraren littafin KIƊA A RUWA.... Cikin sauƙi.... 💃_*
*_Kar dai na cika ku da zance. Zamu fara saida littafin KIƊA A RUWA.... Na saurare (Audio) kenan akan farashi mai sauƙi da rahusa._*
*_Akwai VVIP AREWAPEN kenan 💃_*
*_Akwai VIP Telegram 💃_*
*_(Ƴan WhatsApp ku haƙura kawai ƴan ta'addar bati sunfi yawa a cikinku gaskiya tsoron rashin m ɗinku nake 😂🤣)_*
*_Telegram Audio 2k ne kacal ba tsada 💃. Sai kusaka ta wannan account ɗin👇_*
_(2k)_
*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (2k)_*
*_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*
*_Ƴan NIGER🇳🇪 kuma bazamu barku a baya ba in sha ALLAHU zaku biya (Telegram vip 1,500 CFA) domin littafin KIƊA A RUWA..... na ji Audio-vocal. Sai ki biya tanan👇_*.
_(1,500 CFA)_
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*
*Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 1,500 CFA vip telegram
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_AREWAPEN (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull
*_Ƴan WhatsApp kuzo muyi shawara idan zaku iya amana ayi harkar nan daku 😂, dan bana son a barku a baya duk da dai bakwa ji, ba raga min zakuyi ba na sani duk da ƙaunar da nake muku 🤣😂._*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💦KIƊA A RUWA...!!💦_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_GENERAL FICTION_*
_Wannan labari ƙirƙirarre ne. Sunaye, wurare, da abubuwan da suka faru duk ƙirƙira ne, ba su da alaƙa da gaskiya ko wani, koda Bilyn Abdull ce 😂._
*_BOOK 2_*
_Chapter 8_
__________________
_A KANO KI KE…? Kina neman inda zaki siyi abinci mai daɗi? Kina ƙiyar yin girki gashi zaki yi baƙi?, kina neman inda zaki yi order abinci mai daɗi wanda zaki fita kunya?. Masu abinci suna suka tara, akwai abinci mai daɗi akwai a lallaɓa. Kina son ki siyi abincin da zaki ɗauka a saudia ki ke? Kuna son ku siyi abincin da in kuna ci zaku dinga murmushi saboda daɗi da khamshi?. LEEMARS_DELICIOUS itace kat a wannan ɓangare, tazo muku da nau’in abinci kala-kala na gargajiya da na ƙasar waje. Tana siyar da MANDI RICE, GRILL CHICKEN, CHICKEN BIRYANI, FUNKASO, ALELEN GWANGWANI, BREAD POCKET da sauran su. Fannin abin sha akwai natural ZOƁO mai zaƙi, wanda aka yi shi da ingantattun kayan marmari masu ƙara lafiya, akwai wanda bashi da zaƙi domin masu ciwon sugar da masu gudun ƙiba._
_me ku ke jira? Maza ku garzaya shafin ta na instagram ko TikTok domin ku ganewa idanun ku, ku danna wannan link din domin yin magana da ita kai tsaye. Ko ku neme ta a number wayar ta da take ƙasan rubutun nan._
INSTAGRAM
👇🏻👇🏻👇🏻
https://www.instagram.com/leemars_delicious?igsh=MWRzZWtnYXM4ZHB2dw%3D%3D&utm_source=qr
CALL/WHATSAPP
👇🏻👇🏻
wa.me/2349030398006
TIKTOK
👇🏻
https://www.tiktok.com/@leemars_delicious?_t=ZS-90ZQJ2mNJKc&_r=1
Kar ku sake a baku labari, siyan na gari mai da kuɗi gida.❤️❤️🫶🏻
__________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________
.......Adeel ibn Ubaidullah Qureshy. Cikakken balarabe ne ɗan asali gaba da baya. Jinin sarauta dan kuwa daula babba suke da ita a yankin larabawa. Sannan zuri'arsu zuri'a ce mai ɗunbin dukiya da kaso huɗu na arziƙin Dubai yana da alaƙa da shi. Adeel irin gagararrun yaran nan ne da giyar mulki data kuɗi ke ɗawainiya da su. Dan kuwa iya shegen da yake zubawa a cikin Dubai ba'a magana.
Harkar business ce ta haɗashi da Hajiya Hasiba, a dalilin First Lady da suke aminta. Sunyi wani zaman meeting Hajiya Hasiba ta kasance kujerarta kusa data Adeel a meeting room ɗin, irin ta ajiye wayarta a table sai aka irin kirata ɗin nan, bata ɗaga ba kasancewar suna a halin meeting har kiran ya tsinke, dai-dai screen ɗin wayar na komawa yanda yake ƙyaƙyƙyawan hoton Nabeeha dake a fuskar wayar Hajiya Hasiba ya bayyana. Sai ko karaf a idon sa. Cak ya tsaya da bayanin da yake ya zubama wayar ido, abokan meeting ɗin nasa sukaji shiru duk sai suka ɗago suna kallonsa, cike da basarwa ya ɗauke idanunsa ya cigaba da jawabinsa, amma bini-bini idonsa nakan screen ɗin wayar Hajiya Hasiba har aka tashi.
Hajiya Hasiba ta lura da kallon da Adeel kema wayarta, amma sai bata kawo komai a ranta ba har suka wuce. Mizai faru da daddare kawai sai ga Firt lady ta kirata wai Adeel nason magana da ita, idan ba damuwa kuma so yake su haɗu. Mamaki ya kama Hajiya Hasiba, ta tambayi ko lafiya? First Lady ta bata amsa da cewar wai akan wani hoto ne da ya gani a fuskar wayarta sanda suke meeting. Sosai Hajiya Hasiba ta zaro idanu tana dafe baki, kafin ta ce, “Kai ranki ya daɗe ɗiyarki ce fa Nabeeha, kin san dai tana da aure kin kuma san waye mijinta da fitinarsa”.
Cikin nuna rashin damuwa First Lady tai murmurshi da faɗin, “Yo ALLAH na tuba sai me Hajiya Hasiba, aure nawa ne a wannan zamanin da shi gara babu. Ke dai kawai ai sha'ani. Mijinta kuwa girman kansa na banza ba ko sisi, kin san waye kuwa Adeel? Hummm na baki dama daga nan zuwa minti talatin ki bincika sai ki yanke hukunci. Ni dai na isar da saƙo yace zai turo mota a ɗaukeki a kaiki inda yake ”. Daga haka ta yanke wayarta.
Shiru Hajiya Hasiba tai na tsawon lokaci, dan babu abinda ke zuwa mata a zuciya da brain sai fuskar Zak-Shadow. Amma dai ta daure ta fara binciken waye Adeel kamar yanda First Lady ta bata shawara. Tun a ambaton farko kanta ya nema bugawa, jin nasabar gidansu kawai, jin ɗan waye daga zuri'ar daya fito. Data bincika arziƙin zuri'ar tashi kawai bama shi wadda ya mallaka ba bata san ta rikito a kujera ba tsabar rawar jiki. Har lokacin da za'a ɗauketa yayi bata iya ta dawo a hayyacinta ba saboda matsanancin mamaki. Ai babu ɓata lokaci ta shirya