Author : Billyn Abdul Category : Action Novels
guba da hanyoyi masu sauƙi dan a yanzu sun fimu kusanci da shi. Mu cigaba da masa addu'a kamar yanda muka saba, tunda muna samu labari mai daɗi akan kasancewar sa cikin koshin lafiya daga yaron nan Captain Ibrahim, na yarda da yaron bazai kawo mana zancen daba haka yake ba, muma shaida ne tunda ya kawo mana wasiƙa da muka tabbatar daga Haysam take. In sha ALLAH ko ban samu mulkin nan ba a wannan karon zan ƙara ƙaimi Imran”.
“Maganarka haka take Sir, kayi haƙuri nima kewa ce da damuwa harta sani faɗar hakan. ALLAH ya saka maka da alkairi ya bada ladan zuminci.”
“Karka damu Imran, wlhy har cikin zuciyata nake jinku kai da Haysam da Haydar, dan naji matuƙar daɗin aiki da ku fiye da yanda kuke tunani. Shiyyasa nake jinku tamkar ƙannena da muka fito uwa ɗaya uba ɗaya. Zan iya bada rayuwata akan ganin Haysam ya fita, dan ya yimin abubuwa da bazasu ƙirgu ba. Sau biyu Haysam na tarar harsashi a wajen bani garkuwa, kuma duka biyun a jikinsa suka ƙare har yay jiyya. Taya zan manta da irin wannan ƙanin a duniyata in dai ina numfashi.”
Hawaye Imran ya share yana ɗan murmurshi, ya ce, “Ka cancanci fiye da haka a wajenmu Sir. ALLAH dai ya ƙara lafiya da nisan kwana mai albarka, ya kuma cika burin alkairi”.
Sun cigaba da hira da duk ta shafi batun Dada da siyasa. Kafin Imran yay masa sallama ya fito. Da yake cikin ɓadda kama yake maimakon gida sai ya ɗauki hanyar kasuwa, dan jiya Mimi ke sanar masa haihuwar ta, yanzu haka ma ya bari Aunty Hafsat zata je can barka. Wani shago ya fara shiga, sai da ya tabbatar babu mai bin bayansa daga gidan Janar sannan ya fito ya nufi babban shagon su Ma'aruff da yafi kowane shago girma da cikar kaya a kasuwar. Dan kuwa ƙaton waje ne da zaka iya samu abubuwa da yawa da duk ya shafi kwalliyar jiki. Ɓangare-ɓangare ne, akwai atamfofi, abayas, lesuka, shadda, materials, kayan yara tun daga kan jarirai har zuwa samari. English wears na mata dana maza, mayafai. Kai duk wani abinda ya shafi sutura ta maza da mata, yara da manya akwai ta. Sai bangaren kayan kwalliya, akwatina, cosmetics komai har zinari suna sayarwa. Kai shagon nan dai sai Alhmdllh, dan ko yara masu aiki sunfi ashirin a ciki. Suko manyan gwasake na office abinsu. Ga camaras tako ina da suke kallon shiga da fitar kowa daga ofisoshin nasu...
A tare ma ya taddasu a office ɗin Ja'afar, dan sakatariyansu batama yi yunƙurin fara zuwa neman masa izinin shiga ba sanin wanene shi a wajensu. Sai ma gaisheshi data shiga yi cike da girmamawa. Ya amsa mata a taƙaice yana wucewarsa yay knocking direct, sannan yay sallama ya shiga. Cike da farin cikin ganinsa da girmamawa suke masa barka da zuwa. Ma'aruff ya ajiye kofin tea ɗin hannunsa da yake sha yana miƙewa ya gyara masa kujera, dan basuyi breakfast a gida ba saboda sun makara aka haɗa musu suka taho da shi.
“Cin abinci a office sai kace tuzurai?”. Imran ya faɗa cike da tsokana. Dariya sukayi a tare. Ja'afar ya ce, “Yaya makara mukayi wlhy, kasan kuma twiny da wutar ciki ya azalzalan dole muka taho da shi. A haɗo shayi ko coffee ko kunu?”.
“Haba sai kace wani ku, sai da Auntynku ta cika min ciki na fito nikam. Bani ruwa mara sanyi kawai it's okay”.
Ja'afar na dariya ya kawo masa ruwan, da kansa ya zuba masa a kofi sannan ya zauna suna gaishe shi a tare. Da kulawa ya amsa musu, da faɗin, “Gobe su Mammah zasu dawo ko?”.
“In sha ALLAHU Yaya, wlhy duk kewarta ta ishemu gidan ba daɗi. Autocinta ma duk sunyi sanyi ko ƙiriniyar basa yi da ƙyau kwana biyu”.
“Ai ni kaina kewar tata nake. Jiya da safe dana leƙa gidan duk sai yay min wani iri. Dan itama Ammah ta maƙale a ƙauye taƙi ta dawo Abbah nata ƙorafi”.
Cikin dariya har suna haɗa baki wajen faɗin, “Ai jiya da muka je da daddare yanata faɗa, wai yau tunda safe zai aika driver a ɗakkota, shi ya gaji su Mabruka nata bashi kwamacalar abinci, tuwon ma jiƙaƙƙe suke masa”.
Yanzu kam dariya suke harda Imran. Dan rikicin Abba sai Hajjo ke iya masa. Itama idan ya rikice mata wani lokacin sai ta haɗa shi da Mammah da yake ɗauka tamkar babbar ƴarsa ake samun lafiya. Sun cigaba da hirarsu har suka gangaro kan batun Bilal da shima dai watan gobe zai dawo gida in sha ALLAHU. Sai magana auren Biebah data dage ita bazatai aure ba sai Dada ya fito, in ba haka ba ita da aure har abada. Imran da yasan ga shirin da suke yace su barta kawai in sha ALLAHU komai zai warware. Bai bari shagon ba sai bayan sallar azhar. Ya haɗo shopping na kayan babys da turamen atamfa har akwati biyu aka kai masa mota. Gida ya wuce kai tsaye, zaije ya ɗan samu ya huta bayan la'asar sai ya leƙa gidan Mimi yaga baby dan dama siyayyar duka tata ce......✍️
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number👇_*
*+234 903 234 5899*
*_Maza ku matso MASOYAN Bilyn Abdull da IDANU suka hana karatun novels...._*
*_Tofa Bilyn ku ta samo muku hanya mai sauƙi da kina aiki, ko kina kwance kina hutawa, ko kina inda baki son yawan surutu earpiece ɗinki kawai zaki maƙala a kunne ko Bluetooth kisha sauraren littafin KIƊA A RUWA.... Cikin sauƙi.... 💃_*
*_Kar dai na cika ku da zance. Zamu fara saida littafin KIƊA A RUWA.... Na saurare (Audio) kenan akan farashi mai sauƙi da rahusa._*
*_Akwai VVIP AREWAPEN kenan 💃_*
*_Akwai VIP Telegram 💃_*
*_(Ƴan WhatsApp ku haƙura kawai ƴan ta'addar bati sunfi yawa a cikinku gaskiya tsoron rashin m ɗinku nake 😂🤣)_*
*_Telegram Audio 2k ne kacal ba tsada 💃. Sai kusaka ta wannan account ɗin👇_*
_(2k)_
*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (2k)_*
*_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*
*_Ƴan NIGER🇳🇪 kuma bazamu barku a baya ba in sha ALLAHU zaku biya (Telegram vip 1,500 CFA) domin littafin KIƊA A RUWA..... na ji Audio-vocal. Sai ki biya tanan👇_*.
_(1,500 CFA)_
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*
*Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 1,500 CFA vip telegram*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_AREWAPEN (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull
*_Ƴan WhatsApp kuzo muyi shawara idan zaku iya amana ayi harkar nan daku 😂, dan bana son a barku a baya duk da dai bakwa ji, ba raga min zakuyi ba na sani duk da ƙaunar da nake muku 🤣😂._*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💦KIƊA A RUWA...!!💦_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_GENERAL FICTION_*
_Wannan labari ƙirƙirarre ne. Sunaye, wurare, da abubuwan da suka faru duk ƙirƙira ne, ba su da alaƙa da gaskiya ko wani, koda Bilyn Abdull ce 😂._
*_BOOK 2_*
_Chapter 18_
__________________
Suivez ce lien pour rejoindre ma communauté WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/IwLLYr02Uh9LdJDodFj837
*TALLAH!*
🛍️ “Ko ba ki da niyyar siya ba, ki zo ki shiga ki kalla kayayyaki — wallahi sai kin bude ido! Ballantana kuma nasan za ki tashi da kaya saboda kyau da araha.” ✨
🌸✨ “Shigo duniyar da kyau da jin daɗi suka haɗu — daga kyawawan laces na alfarma, Atamfa , abaya masu salo, zuwa kayan ado masu kyalli, kayan girki na zamani da sauran ƙarin abubuwa. REEYAT Investissement maradi nijer❤️🎉
Zaku same mu a wannan number in sha ALLAHU.
99197982.
__________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________
.........Sai da sabon driver ya tabbatar su Nimrah sun gama shigewa sannan ya koma cikin mota. Wayarsa ya ciro daga aljihu ƙarama tecno, ya kashe ta ya cire murfin da batteryn ta. A mamakina rigarsa ya ɗan ɗaga ya zaro leda mara girma sosai, koda ya kwance ta tsumma ne fari ya fara bayyana da aka nannaɗe wani abu a ciki. Ya shiga warware tsumman sai ga ƙaramar bindiga ta bayyana, ƙaramar takardar dake tare da bindigar a nannaɗe itama ya ɗauka ya warware layukan waya da yawa suka bayyana. Ɗaya a ciki ya ɗauka ya saka a wayar ya maida batteryn ya kunnata.
Kira yayi tare da kaita kunensa yana gyara zama. Ba'a wani jima ba aka ɗaga daga can. Kasancewar speaker ɗin wayar a buɗe take sosai yasa ake iya jin abinda nacan ke faɗa. Gaisuwa suka fara kafin nacan ya cigaba da faɗin.
“Ai harna fara tunanin sakawa a bi bayanka Mole, naji har kwanaki uku babu wani bayani daga gareka. Ina fatan dai lafiya? Ka samu karɓuwar da muke so a gidan?”.
Iska mai ƙarfi ya furzar cikin damuwa da ɗacin da yake ji a cikin maƙoshinsa ya furta, “Oga na samu ƙarɓuwa kam, sai dai akwai matsala gaskiya.”
“Matsala kuma? Yarinyar bata tare da su ne?”.
“Tana nan a gidan. Ta girma sosai ta zama budurwa. Sai dai babu wata alamar dake nuna tasan tana da wasu iyaye bayan su. Da alama abinda Goje ya taɓa sanar mana na an mantar da ita iyayenta gaskiya ne.”
“Amma uwar nan tata muguwa ce gaskiya. Tabbas da ace tana raye har yanzu ba ƙaramin barazana zata zame mana ba ita da ubanta.”
“Ai ko yanzu ta zame mana, dan ban san ta inda zan fahimtar da Uwa wanene ni ba har tai mana abinda muke buƙatar daga ƙarshe ta dawo hannuna”.
“Karka damu dole mu tafi mataki na biyu ne kawai gaskiya. Amma ka bari zan yi magana da oga muji wace shawara ko shiri yake da shi akan hakan. Tunda dama ya kamata mu sanar da shi da kanka zakai aikin yanzu, dan kar a samu irin matsalar da Buba yaso bamu. Yanzu a gidan kake kwana?”.
“A'a haba kaima kasan bazan kwana a nan ba. Dan wannan Imran ɗin da kuka raina shima shegen kansa ne. Tunda ya ganni alamun tsarguwa suka bayyana akan fuskarsa. Dole sai nayi taka tsantsan da shi. Dan ni kasan bana raina abokin gaba”.
“Kamar ni kake, dama su Oga ne ke ɗaukar Imran mai sauƙi, sun kasa fahimtar irinsu sunfi illa fiye da shi wanda suka ɓoye ɗin da bai iya shanye abu. Amma ka barsu za'aje gaɓar da zasu gane shima ba abinda zasuyi wasa da shi bane. Kai kuma ka ƙara yin taka tsantsan”.
“Ba damuwa sai na jika”.
Daga haka sukai sallama ya sake kashe wayar ya cire layin ya maida shi inda yake tare da bindigar nan. Sannan ya tada motar yabar wajen.....
(Hummm wa kuke tunani wai?)
}}}}}}}}}{{{{{{{{{
★PRISON★
Bai san fuskar ba, bai taɓa ganinta ba. Dan haka ya zubama vistor ɗin nashi jirkitattun idanunsa masu bulale abokan gaba koda bai tanka ba har na tsayin minti ɗaya. Tabbas ALLAH ya bama Dada basira mai ƙarfi, nutsuwa, dattako da sirrin iya aiki matsayin jami'in tsaro. Zakai matuƙan shan mamaki idan akace maka a wannan kalon na minti ɗaya kacal ya fahimci fuskar bogi ce a tare da mutumin, hakan na nufin yayi amfani da facemask wajen ɓoye ainahin fuskarsa.
Wani murmushin da sam bai niyyasa bane ya suɓuce masa, murmushi daya saka vistor ɗin nashi murmusawa shima, duk da bai fahimci ma'anar murmurshin Dadan ɗin ba shi. Shiru ya sake biyo baya a cikin ɗakin batare da yunƙurin tankawar kowannensu ba na tsawon lokaci. Tamkar Dada na ƙirga lokutan zamansa a wajen ne, minti biyar na cika daga agogon ɗakin da suke ya miƙe tsam batare da yace komai ba ya juya zai bar wajen.
“Bai kamata ka ƙosa haka da wuri ba, domin mu mutuwa ne, ana rayuwa da mu ne dole, tun daga ranar haihuwa”.
Cak Dada ya tsaya a takunsa na uku, sai dai bai juyo ba bai kuma ce komai ba har tsahon minti guda cir. Kafin a hankali cike da ƙasaitarsa mai tafiya da nutsuwar masu izza ya juyo gaba ɗayansa. Idanun nan nasa masu kaifi da zafi ya zuba masa, kafin a bazata yay wani sakaran murmurshi mai cike da ma'anoni masu ƙarfi da ya nema tarwatsa zuciyar vistor ɗin a cikin ƙarjinsa. Ya lumshe idanu ya sake buɗewa a kansa. Sai kuma ya buɗe lips kaɗan, gira a sama ya amsa masa da.
“Ni kuwa kaga anan sai banga siffofin kamala irin na mutuwa mai cika umarnin UBANGIJINA ba. Siffofin akuyoyin dake gudun tsiran neman mafaka a yayin da ruwan sama ya sauka kawai na gani a gabana”.
Sosai fusata ta nuna a fuskarsa vistor ɗin, duk yanda yaso danne fusatarsa hakan na neman gagara. Idanunsa sun yi ja sosai har hannunsa na rawa sai da ya dunƙuleshi a cikin juna ya matse yatsun. Dada dake kallon hannun nasa ya kauda idanunsa yana murmurshi. Ai ko sai hakan ya sake hasalashi, a kausashe ya daki tebirin yana furta, “Mune akuyoyin kenan?”.
“Amsa mai ƙyau”.
Dada ya bashi amsa kai tsaye yana sake takowa ya dawo wajen. Duk da hannunsa akwai handcuffs cike da salon manya ya juya kujerar ya zauna ƙafa ɗaya kan ɗaya suna kallon juna ido cikin ido. Dai-dai lokacin masu tsaronsa suka shigo saboda bugun teburi da baƙo yayi.
“Sir! are you all right?”.
Kansa kawai ya jinjina musu batare da ya kallesu ba balle yin magana.
“Okay”.
Suka faɗa suna salute ɗinsa da ɗan kallon baƙon da ya gama kaiwa wuya suka fice. Sai kuma ga wasu sun sake shigowa niƙi-niƙi da kwalaye. Su kam gaisheshi sukai kawai tare da sanar masa oga ne ya aikosu da kayan zasuyi aiki a ɗakinsa. Kamar zai ce wani abu sai kuma yay shiru da basu dama da hannu suka wuce ɗakin nasa. Ya ɗan bi kwalayen da kallo. Har sai da baƙon nasa yay wata dariyar iskanci da izgili. A wulaƙance ya ce, “Karka ji ka damu fa, mun ƙara maka matsayi ne, dan bai ƙyautu ace lokacin da mutanenka ke ihu da kururuwa kai kunnenka baya ji ba, idanunka basa gani ba. Shiyyasa muka kawo maka gift ɗin da zai baka damar ji da gani kusa da kai gab...”
Tsahon sakanni bashi da niyyar tankawa daga kalamansa, sai hakan ya bama vistor damar taɓe baki da sake faɗin, “Kana jin tsoron rasa rayuwa ne? Ko faɗa ka bada amsa ne kake jima fargaba?”.
Da wani irin salon luuu Zak-Dada ya ɗago idanunsa yana kallonsa cike da izza da nutsuwarsa da ALLAH ya mallaka masa a kowane hali. Sai kuma ya ɗan matso kaɗan ya dafe duka hannayensa dake sanye da handcuffs a saman table ɗin, idanunsa ya sake ajiyewa kai tsaye cikin nasa tamkar zai soke ruhinsa da su. Da golden voice ɗin nan tasa mai razanasu ya furta, “Jarumin gaske sulƙen yaƙi da linzamin dokinsa ne kawai GUZIRINSA. Duk lokacin da kaji abokin faɗa ya zagaye kansa da MAKAMI ni Haysam Abdul-rasheed Shehu Kobi na faɗa maka tsoro ne ya saka shi”.
“Tsoro!?”.
Baƙo ya faɗa cike da son aro jarumta da ƙarfafa kai na dole. Sai kuma ya murmusa yana ɗan buga yatsunsa akan tebur.
“Kana da yawan cika baki a magana. Amma ka sani mu ba da suna muke aiki ba. Idan suna ya bayyana, haske zai shigo. Idan haske ya shigo, tsarin ya lalace. Mu mune mazaunan ƙasa a ɓoye. Mu ne masu murɗa jijiyoyin gwamnati. Mu ne masu rubuta dokar da gwamnati ke karantawa.” Ya sake matsawa kusa kusa sosai.
“Yau shekaru takwas kenan muna kallonka daga nesa. Kana tunanin wannan gadarar taka ce ta baka wannan filin? Ko har yanzu gurɓataccen tunaninka na cigaba da baka wancan ƙarfin ikon da kake gadara da shi a baya har yanzu yana da tasiri? Ka manta cewa ƙasar nan tun kafin ka yi tunanin kare ta, mun riga da mun shafe shekaru muna sarrafa zuciyar manyan da kake kira shugabannin cikinta. Kalli kanka mana, har yau baka ɗauki darasi daga ikonmu bane?. Mu muka bar ka a nan. Mu muka hana a kashe ka. Mu muka hana a sake buɗe shafin ka. Ba wai saboda kana da muhimmanci a garemu bane. A’a…” Ya yi kakkarfan numfashi yana wani murmushi, ya cigaba da faɗin, “…saboda muna son ka zauna ka kalli yadda ƙasar da ka ɓata shekarun ƙuruciyarka a kareta ta koma filin WASAN ƘWALLON ƙafarmu. Da jinin abokanka, zuri'arka, ƴan ƙasar taka zata zame mana mai danshin da zamu ji daɗin gudu a kanta. Kaɗan da zamu rage a cikinsu