Advertisements
Chapter 11 Reading Kida A Ruwa Book 2 Complete Hausa Novel Hausa Novels
Advertisements

Kida A Ruwa Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Billyn Abdul Category :  Action Novels

Chapter   11 / 24

30K to 33K   out of 71K words

ke ɗawainiya da ita ba sai gata da ƙuruciya. Dan kuwa kowa ji yake da su ita da hassanarta kamar tsoka ɗaya a miya a gidan nan”.

      Mutumin da tunaninsa ya katse saboda maganar maigafi ya ɗan murmusa yana sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya da kaiwa zaune. Sai kuma ya kalla maigadi yace, “Ƴan biyu ne kenan?”.

    Kai tsaye maigadi ya ce, “Eh tana da hassana kwarai da gaske. Sai dai sam basa kama da juna sai a hallaya, Hassanar ma fara ce, ita kuma ka ganta baƙa. Fitinannun yara ne na bugawa a fasta. Sai dai akwai tarbiyya da girmama na gaba dasu. Dan ni dai tsakanina da su wlhy sai sambarka. Hakama sauran ma'aikatan gidan nan babu wanda zakaji yace musu ALLAH wadarai. Rashin jin su da sa'anninsu ne a makaranta. Wannan kam kullum cikin kawo ƙararsu ake gidan nan. Abin mamakin kuma su yayyen nasu babu mai dukansu akan hakan balle ƙwaƙwƙwaran tsawa. Dan ita wannan ɗin ma tsabar rashin ji ZAKANYA ake ce mata, ita kuma Hassanar DAMISA”. Sai kuma yay ƴar dariya da tura masa abincin gaban sa. “Uhm kaga ci abinci nabi na cika ka da surutu. Tunda dai kana nan ai a hankali zaka gane komai in sha ALLAHU. ALLAH dai ya bamu haƙurin zama da juna. Amma zakaji daɗin zama da waɗan nan mutanen saboda mutanene na kirki masu karamci da ƙyaƙyƙyawar zuciya. Damma naji sunce babban gidan baya ƙasar, akoda yaushe zaka same su cikin begensa, narasa mi yake zaman yi a wata ƙasa shekaru masu zurfi haka”.

      A karo na farko mutumin da alamu ya nuna bashi da yawan magana ya ce, “Ƙila aiki yake ko? Kasan masu kuɗin nan da son ƙasashen ƙetare kamar talaka da son gidan alfarma ne”.

    Dariya maigadi ya tuntsure da ita yana cika baki da abinci. Shima mutum sai ya murmusa kawai yana cin abinci nasa. Sai dai gaba ɗaya zuciyarsa tayi nauyi sosai, kaɗan-kaɗan kuma sai ya kalla hanyar da Nimrah ta shiga yana jan ajiyar zuciya.........✍️

Tofa waye a South Africa? Waye kuma a gidan su Nimrah?. Mutane na yanzu fa za'a fara wasan😎💃.

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*

*_+227 98 94 12 81_*

*_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*

*_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899*

*_Moniepoint MFB_*

*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_*

*_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_*

*_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_*

*_Chapters & Audio_*

@BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276*

*_Access Bank_*

*_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_*

*_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_*

*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_*

*+234 805 568 7449*

*_Telegram Number👇_*

*+234 903 234 5899*

*_ASSALAMU ALAIKUM MUTANE NA MASU ALBARKA_*

*_Maza ku matso MASOYAN Bilyn Abdull da IDANU suka hana karatun novels...._*

*_Tofa Bilyn ku ta samo muku hanya mai sauƙi da kina aiki, ko kina kwance kina hutawa, ko kina inda baki son yawan surutu earpiece ɗinki kawai zaki maƙala a kunne ko Bluetooth kisha sauraren littafin KIƊA A RUWA.... Cikin sauƙi.... 💃_*

*_Kar dai na cika ku da zance. Zamu fara saida littafin KIƊA A RUWA.... Na saurare (Audio) kenan akan farashi mai sauƙi da rahusa._*

*_Akwai VVIP AREWAPEN kenan 💃_*

*_Akwai VIP Telegram 💃_*

*_(Ƴan WhatsApp ku haƙura kawai ƴan ta'addar bati sunfi yawa a cikinku gaskiya tsoron rashin m ɗinku nake 😂🤣)_*

*_Telegram Audio 2k ne kacal ba tsada 💃. Sai kusaka ta wannan account ɗin👇_*



_(2k)_

*9032345899*

*_Moniepoint MFB_*

*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (2k)_*

*_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_*

*_Telegram Number 09032345899_*

*_Ƴan NIGER🇳🇪 kuma bazamu barku a baya ba in sha ALLAHU zaku biya (Telegram vip 1,500 CFA) domin littafin KIƊA A RUWA..... na ji Audio-vocal. Sai ki biya tanan👇_*.

_(1,500 CFA)_

*_+227 98 94 12 81_*

*_My NITA_*

*Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 1,500 CFA vip telegram

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*

*_+227 98 94 12 81_*

*_AREWAPEN (Vvip)_*

*_Chapters & Audio_*

@BilynAbdull

*_Ƴan WhatsApp kuzo muyi shawara idan zaku iya amana ayi harkar nan daku 😂, dan bana son a barku a baya duk da dai bakwa ji, ba raga min zakuyi ba na sani duk da ƙaunar da nake muku 🤣😂._*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💦KIƊA A RUWA...!!💦_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*

_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_GENERAL FICTION_*

_Wannan labari ƙirƙirarre ne. Sunaye, wurare, da abubuwan da suka faru duk ƙirƙira ne, ba su da alaƙa da gaskiya ko wani, koda Bilyn Abdull ce 😂._

*_BOOK 2_*

_Chapter 14_

__________________

https://chat.whatsapp.com/HKCgesG0ua47qN8hwnCNAo

Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu

Muna muku marhabun lale da shigowa wannan group din mai albarka

Muna saida turaruka na arebiyan perfumes da kuma designer's perfumes dana gida dana motar dana office dana labile da turaren kujeru da kuma by oils masu na mata dana maza masu sanyaya zukatan ma'abota san kamshi ,munada kayan kitchen masu kyau cikin sauki sai kunzo

https://chat.whatsapp.com/HKCgesG0ua47qN8hwnCNAo

https://telegram.org/dl

https://www.tiktok.com/@yusufjummai?_r=1&_t=ZS-91wLXnmiIIa

https://www.instagram.com/jummai342?igsh=dTQ0bnZobTRwN3Vm

07061352952 or 08034528104

__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

.........Shekaru sun ja, ƙungiya ta ƙara bunƙasa da cikar samuwar sabbin members. A hasashe na hankali zuwa yanzu zamu iya cewa duk abinda ƙungiyar duhu ke buƙata na dukiya da mamaye babba da jaka na ƙasar sun same shi. Tama kai hatta nauyin masu faɗa ajin da hukunci da zartarwa yanzu a hannunsu yake sakamakon kafa mutanensu a dukkan madafun iko. Sun ɓatar da mutane da yawa da suka ƙi basu haɗin kai a cikin masu mulki da jami'an tsaro harma da sarakunan gargajiya. Kai hatta malamai basu ɗagama ƙafa ba da ma'aikatan gwamnati. Idan ka yarda ka bisu kuwa shike nan ka tsira da rayuwarka da dukiya anan duniya sai kuma jiran sakamakon shugaba mai hukunci akan hukuncin wawaye na irinsu.

       Abinda zai baka mamaki daga sakaye Zak-Shadow da suka ruruta wutar tabbatarsa zuwa yanzu babu wani harin ta'addanci daya sake wanzuwa a ƙasar, hakan kuma wani shiri ne nasu na musamman da manufar cimma buri a ƙasar dama wajen ƙasar. Zamu iya cewa sun samu, dan wani ɓangaren samuwar zaman lafiyar yasa hatta suma talakawan sun fara mantawa da wani batun Zak-Shadow balle gwagwarmayar sa a kansu. Yara masu tasowa ma kuwa basu san labarinsa ba sam balle jarumtarsa. Kowa ya shagaltu da neman dukiya da son jin daɗi. Hatta ƴan gudun hijira da suka baro ƙauyukan Bankaura da sauran su zuwa yanzu wasu a ciki sun koma. Sai dai su bazasu ce sun manta komai ba, dan da yawansu an bar musu tabo a zuciya da gangar jiki da har abada bazasu manta ɗin ba. A kowanne family zaka samu an rasa wasu a ciki ta hanyar mutuwa a wancan lokacin ko ɓata na rashin tabbacin ina su wane suke. Wasu ma babu kowa a gidajen nasu da dama sun rushe wanda suka dawo ma sai da suka dinga sake sabon gini sannan garuruwan suka farfaɗo. Wasu ko zaman birni da cikin ƙauyukan da suka koma ya riga yayi tasiri a jikinsu sun haƙura bazasu iya komawa ƙauyukan nasu ba.

    Haƙar ma'adanai kam zuwa yanzu sai abinda ma yay gaba. Dan tuni sauran ƴan ƙauyukan sun zama suke wahalar haƙo musu, wasu sukan mutu a cikin rami ƙasa ta rufesu wasu wahala ta yau da kullum kan kwantar da su ciwo har su rasu suma. Amma hakan baya hana matasa masu tasowa amsarsu da cigaban wahalar dan ta zama itace mafi sauƙi da girman hanyar cin abincinsu a yanzu. Yau da kullum takai ba mutanen yankin kawai ba har wasu matasan na zuwa da ga wasu yankunan suma yin aikin haƙar matsayin balaguro. Dan haka da yawan matan garin suka maida hankali kan sana'o'in abinci da kayan ciye-ciye yaransu ƴammata da masu tasowa na ɗaukar talla zuwa wajen. Ta haka ne kuma yara da yawa ke rasa budurcinsu sakamakon yaudarar da mazan ke musu da kuɗaɗen da suke samu na wahalar ayyukansu. Wasu iyayen basu sani ba, wasu ko son duniya da yaudarar kai ta rufe ganinsu sunyi tamkar basu fahimci halin da yaran nasu suke ciki ba. Sai tsautsayi yasa ciki ya bayyana jikin yarinya kaji iyaye na kuka da kururuwa mara amfani dan aikin gama dai ya riga ya gama. Daga haka wasu kan zauna har su haifi cikin idan cikin yaran garin ne a tilasta su aure su, idan ɗan balaguro ne kuwa ya gudu ya barsu da ƴaƴan shegu. Tsangwama da habaici irin na mutanen ƙauye kan saka yarinya ta gagara jurewa ta gudu ta bar gida ta shiga yawon duniya a cigaba da buga harka acewarsu aljanna ta mai rabo ce (Hummm). Tun iyaye na damuwa da sauran jama'ar gari akan irin waɗan nan sabbin abubuwan har zuwa yanzu ya zame musu jiki koda ta fasu ma babu mai nuna damuwa sai kalmar ALLAH ya ƙyauta daga haka kowa yaja bakinsa yay shiru. Dan kuwa a cikinsu suma ɗin kaɗan ne da basu da irin wannan kashin a ɗuwawu tunda al'amarin ya zagaye kusan kowacce zuri'a ta ƙauyukan yankin a yanzu....

     An buga tambarin siyasa, lokacin sabon campaign na sake matsowa. Hakan ya saka members na ƙungiyar duhu dake cikin ƙasa da wajenta fara hallarowa babbar mahaɗa domin fara tsare-tsare da sabbin shiri kamar yanda suka ambata a watanin baya da sukai zaman ƙarshe.

       Idan oga Jush yay kira babu makawa sai an amsa saboda tsabar bin dokarsa da tsoron hatsabibancinsa kasancewarsa ɗan ƙetare mai ƙarfin faɗa aji da ƙarfa-ƙarfar madafun iko da aka san ire-iren su dayi a yankunan mu na masu ƙaramin ƙarfi da rashin gata da tun iyayenmu da kakanni suke bautar da mu.

    Kamar yanda suka saba haɗuwar cikin dare a wannan karon ma bata canja zani ba. Sun cika sabon meeting room ɗinsu taf da baka jin komai sai ƙarar ac's dake a kowanne bango, ɗakin mai cike da ƙarancin haske kamar yanda suka saba. A gaban kowa akwai mabanbanta abubuwan kaiwa baka. Wasu giya ce, wasu lemo, wasu abin motsa baki na nau'in abinci saboda ƙaracin cikakkiyar lafiya basa iya shan giyar ko lemon da akai dan more rayuwa. Wasu ma sigari suke busawa abinsu wasu ko ruwa ne kawai da suke ganin ya fi musu komai na kwanciyar hankalin jiki sai dai zukatan babu ƙyau da nagarta a cikinsu.

      Bayan oga Jush ya gama shan ƙamshinsa da bushe-bushen ƙatuwar sigarinsa ya fuskancesu cike da gadara da nuna isa irin ta shugabanci. “Da farko ina ma kowa barka da zuwa wannan kira da bin doka da oda. Anyi kira kun amsa, wannan kuma shine ke tabbatar mana da kowa matsayin abokan tafiya. Ƙungiyar duhu na alfahari da ku ƙwarai da gaske”.

      Tafi ɗakin ya saki raf-raf-raf. Sai da sukai na fin sakan biyar suka tsagaita shi kuma ya cigaba da magana. “Shekaru takwas kenan da sakaye rasa kunya ɓeran tanka mai karambani akan isar da bashi da ita cikin ɗakin duhu. Hakan ya samu tsagaita dukkan ayyukan mu sai na nema da tara dukiya kawai. Ina da tabbacin kuma zuwa yanzu bamu da muka fara tafiyar ba hatta da sabbin members na ƙungiya sunci sunyi nak da abinda suka samu da har jikokin jikokinsu bazasu taɓa talauci ba”.

       “Yes boss!!”.

   Suka faɗa cike da tabbatarwa kowa bakinsa a washe. Shima murmurshin yayi yana sake gyara zama da kunna sabuwar sigarinsa ya kai baki. Sannan ya cigaba da faɗin, “To lallai idan har munci mun ƙoshi, kuma mun gamsu da ƙoshinmu inaga lokacin fara sabon wasa yayi. Lokacin tunawa taƙadarin nan Zak-Shadow yake ko mi alƙawarinmu na fasa zuciyarsa yayi. Lokacin da zai san duk DUHU sunansa DUHU koda na rufe idanu ne yayi. Sannan duhun dare abin tsoro ne koda da hasken farin wata a cikinsa. Zamu cika dukkan alƙawarin mu a kansa da kan mutanen da yake tunanin yana da jarumtar zamewa garkuwa. Sai mun kumbura zuciyarsa, sannan mu huhhudata mu tsiyayar da jinin cikinta ya koma ƙarƙashin na'urar likitoci tsakanin rayuwa da mutuwa. Dan haka zamu fara sabon mission, batch a, season one episode one”.

       Raf-raf-raf wani mahaukacin tafi da yafi na farko ya gauraye hall ɗin. Bai hanasu ba sai da sukai iya son ransu fuskokinsu cike da farin ciki sannan suka tsagaita. Yanzu kam gefensa ya kalla, inda mataimakin shugaban ƙungiya ke zaune wato Mr Specter. Wani murmushin ƙasaita da isa yayi, dan tunda aka bashi wannan shugabancin girman kansa ya sake ƙaruwa. Sai da ya maida fuskarsa ya tsuke kafin ya fara magana cike da izza da isa.

       “Tabbas maganganun oga duk haka suke. Kuma muna matuƙar farin cikin kasancewarsa jagoran wannan tafiya a garemu. Muna fatan rayuwa mai tsaho a garesa da cikakkiyar lafiya. Ya cigaba da janmu daga nan har ƙarshen duniya”. (Hummm, tunda ta ubanku ce duniyar ba🥱)

     Nan ma tafin suka shiga rabgawa kamar yaran nursery da basa gajiya da tafi da waƙoƙi🙄😏. Mr Specter ya cigaba da faɗin, “Kamar yanda ya faɗa zamu tafi batch a season 1 episode 1 a sabon mission ɗin mu. Dan haka a wannan karon zamu kasa shugabancin ƙasar uku ne. Mu ɗauki kaso ɗaya, sauran kashi biyu a bawa sabbin fuska ta yanda aiki zai tafi dai-dai. Hikimar haka zai sa talakawa dinga mararinmu da ganin mune muka dace da shugabantar su waɗan nan sun kawo musu azabobin rayuwa. Hakan kuma zai bamu damar baza ayyukan mu yanda muke so muke buƙata. Sai dai fa mun sani dama waɗan can kaso biyun dama suma a ƙarƙashin ikonmu suke ta ƙarƙashin ƙasa batare da sun fahimta ba, dan dukansu dai yaran da kuka raina ne da hannunku akan siyasa zaku bamu. Hakanne zai bamu damar mamaye su tamkar hadari a tsakiyar hasken rana. Dan haka kowa yaje ya kawo sunan wanda yake buƙata da shugabancin da za'a bashi”.

    Sosai yanzu kuwa ɗakin ya hargiƙe da farin ciki. Duk da kuwa zukatan wasu sun sosu matuƙa gaya. Musamman ma waɗanda zukatansu suka kwaɗaitu da son a basu kujerar shugaban ƙasa da wasu manyan kujeru. Sai dai jawabin na yanzu ya tabbatar musu da suɓucewar wannan ƙudiri da burin nasu.......

∆∆∆∆∆∆★∆∆∆∆∆∆

      ★PRISON★

Ɗaki ne ƙarami dan gaba ɗaya faɗinsa da tsayi bai wuce girman ƙaramin kitchen na mai ƙaramin ƙarfi ba. Babu wani kayan alatu a cikinsa balle ƙyale-ƙyale dan hatta fentinsa ma duk ya dushe wani gurin ma ya ɓare. Babu window sai wasu ƙananu guda kusan goma dake can sama gab da silin da bazasu wuce faɗin ƙofofin bulo na gini ba, tanan hasken rana ya haske ɗakin har ake iya tantance abubuwan dake ciki. Akwai katifa ƙarama irin ta makaranta a saman gadon ƙarfe shima dai irin na ƴan makarantar ne, gadon da bedsheet, da filo sai bargo suma dai madaidaita. Sai ɗan table dake jikin gadon ƙarami da ƴan tarkace a kansa na jaridu da jug na ruwa sai ƙaramar kula da flaks ƙarami irin na silver ɗin nan. Sai ƙaramar kula itama ta silver ɗin dai. Ta ƙasan table ɗin akwai kwali mai ɗan girma dake rufe bamu san mike ciki ba, sai samansa da Alkur'ani ajiye, da wasu littatafan addu'oi harma dana ilimi da hadith. Daga can ta gaban gadon randa ce ta ƙasa mai ɗan girma tanata raɓa alamar akwai ruwa a cikinta, a rufe take da plate na roba da kofin ruwa ƙarami da ake kira moɗa. Sai ƙarfen gadon ta can ƙarshe an rataye sallaya. A ƙasan ɗakin tils ne daya tsufa sosai irin na da ɗin nan da sai a gidan masu kuɗi kake ganinsa, amma duk da haka fes yake kamar kaci abinci a kansa. Akwai ƙofa guda ɗaya a ɗakin dake tabbatar da toilet ne sai dai a rufe take. Ba ƙamshi a ɗakin ba kuma wari, kamar yanda babu wadataccen haske babu kuma duhu. Ba sanyin ac ko fanka, babu kuma zafi mai cutarwa.........✍️

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*

*_+227 98 94 12 81_*

*_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*

*_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899*

*_Moniepoint MFB_*

*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_*

*_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_*

*_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_*

*_Chapters & Audio_*

@BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276*

*_Access Bank_*

*_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_*

*_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_*

*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_*

*+234 805 568 7449*

*_Telegram Number👇_*

*+234 903 234 5899*

*_Maza ku matso MASOYAN Bilyn Abdull da IDANU suka hana karatun novels...._*

*_Tofa Bilyn ku ta samo muku hanya mai sauƙi da kina aiki, ko kina kwance kina hutawa, ko kina inda baki son yawan surutu earpiece ɗinki kawai zaki maƙala a kunne ko Bluetooth kisha sauraren littafin KIƊA A RUWA.... Cikin sauƙi.... 💃_*

*_Kar dai na cika ku da zance. Zamu fara saida littafin KIƊA A RUWA.... Na saurare (Audio) kenan akan farashi mai sauƙi da rahusa._*

*_Akwai VVIP AREWAPEN kenan 💃_*

*_Akwai VIP Telegram 💃_*

*_(Ƴan WhatsApp ku haƙura kawai ƴan ta'addar bati sunfi yawa a cikinku gaskiya tsoron rashin m ɗinku nake 😂🤣)_*

*_Telegram Audio 2k ne kacal ba tsada 💃. Sai kusaka ta wannan account ɗin👇_*



_(2k)_

11 / 24