Advertisements
Chapter 18 Reading Kida A Ruwa Book 2 Complete Hausa Novel Hausa Novels
Advertisements

Kida A Ruwa Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Billyn Abdul Category :  Action Novels

Chapter   18 / 24

51K to 54K   out of 71K words

kan ƴaƴan titi yake sauke lalurarsa ya samu wannan ƴar shilar ai ya gama nasara. Dan tabbas zai sheƙe ayarsa gwargwadon iko...

       Ƙarƙarewar zancen ta katse masa tunani, dan Oga ya bashi damar zuwa su samar da wanda zai musu aiki ta bayan fage daba a cikin gidan yake rayuwa ba. Sai Mole ya kula da komai. A karo na farko ma Oga Jush ya bada damar Dagger ya kawo masa Mole gabansa da yana son ya gana da shi. Duk da Dagger yaji wani iri a ransa baiƙi amsa umarnin ogan ba. Amma zuciyarsa sai faman kai-kawo take akan miyasa oga Jush ɗin ke son ganin Mole a karo na farko? Shifa koma mi za'ayi ayi amma kada ace za'a shiga al'amarinsa da Nimrah, dan bazai iya ɗauka ba.

      A zahiri dai baice komai ba. Ya amshi maƙudan kuɗaɗen da basa gajiya da bashi yay musu sallama ya tafi ransa fal wasi-wasi.........✍️

      

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*

*_+227 98 94 12 81_*

*_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*

*_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899*

*_Moniepoint MFB_*

*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_*

*_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_*

*_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_*

*_Chapters & Audio_*

@BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276*

*_Access Bank_*

*_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_*

*_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_*

*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_*

*+234 805 568 7449*

*_Telegram Number👇_*

*+234 903 234 5899*

*_Maza ku matso MASOYAN Bilyn Abdull da IDANU suka hana karatun novels...._*

*_Tofa Bilyn ku ta samo muku hanya mai sauƙi da kina aiki, ko kina kwance kina hutawa, ko kina inda baki son yawan surutu earpiece ɗinki kawai zaki maƙala a kunne ko Bluetooth kisha sauraren littafin KIƊA A RUWA.... Cikin sauƙi.... 💃_*

*_Kar dai na cika ku da zance. Zamu fara saida littafin KIƊA A RUWA.... Na saurare (Audio) kenan akan farashi mai sauƙi da rahusa._*

*_Akwai VVIP AREWAPEN kenan 💃_*

*_Akwai VIP Telegram 💃_*

*_(Ƴan WhatsApp ku haƙura kawai ƴan ta'addar bati sunfi yawa a cikinku gaskiya tsoron rashin m ɗinku nake 😂🤣)_*

*_Telegram Audio 2k ne kacal ba tsada 💃. Sai kusaka ta wannan account ɗin👇_*



_(2k)_

*9032345899*

*_Moniepoint MFB_*

*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (2k)_*

*_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_*

*_Telegram Number 09032345899_*

*_Ƴan NIGER🇳🇪 kuma bazamu barku a baya ba in sha ALLAHU zaku biya (Telegram vip 1,500 CFA) domin littafin KIƊA A RUWA..... na ji Audio-vocal. Sai ki biya tanan👇_*.

_(1,500 CFA)_

*_+227 98 94 12 81_*

*_My NITA_*

*Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 1,500 CFA vip telegram*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*

*_+227 98 94 12 81_*

*_AREWAPEN (Vvip)_*

*_Chapters & Audio_*

@BilynAbdull

*_Ƴan WhatsApp kuzo muyi shawara idan zaku iya amana ayi harkar nan daku 😂, dan bana son a barku a baya duk da dai bakwa ji, ba raga min zakuyi ba na sani duk da ƙaunar da nake muku 🤣😂._*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💦KIƊA A RUWA...!!💦_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*

_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_Masu fama da matsalar idanu kuma naku ya fara sauka a AREWAPEN faka-faka AUDIO da zafinsa. Book 1 zaku sameshi a cikin book 1. Book 2 na tare da book 2 shima. 💃💃😘😘😀_*

*_GENERAL FICTION_*

_Wannan labari ƙirƙirarre ne. Sunaye, wurare, da abubuwan da suka faru duk ƙirƙira ne, ba su da alaƙa da gaskiya ko wani, koda Bilyn Abdull ce 😂._

*_BOOK 2_*

_Chapter 23_

__________________

IMZEEDVENTURE

✨ Duniyar luxury kayan kitchen & kayan yara masu kyau, unique, kuma classy ✨

Wai har yanzu kina nan a GWAMMA ɗinki ba Hajiya Bilqees ba madam😱?.

Yo ba dole na kiraki gwamma ba kitchen kamar na zamanin kakaninmu ba gyara ba kayan ƙawa 💃.

Mufa matan zamani daga kitchen ake fara gane mun kai ƴan gayun zamani💃🏼🤸. Dan haka maza garzayo na nuna miki hanyar da kema za'a fara kiranki Hajiya Bilqees ba Bilki ba 😀.

IMZEED VENTURA shine kankant a wajen maida mata ƴan ƙwalisa da kayan ado na kitchen harma dana jiki. Ga na yara gana manya kai komai mun haɗa sai wanda ya gani 💃💃.

Kina neman kayan kitchen masu kayatarwa?

Ko kayan yara na yan gayu, masu kama da sabo?

✔️ Siyan nan take

✔️ Order kayan gonjo

✔️ Adashe GATA don kayan kitchen

Shiga group ɗinmu ki gani da idanunki 👀👇

👉

https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt

📩 DM: https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1

📞 Call/WhatsApp: 07077532253

🎵 TikTok: Imzeedventure https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1

Kada a yi babu ke 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 ki shigo yanzu. Muna aika kaya ko ina kike cikin salama da kwanciyar hankali.🥰

Mu da kayanmu duk naku ne. Maza kuzo ku tattaremu a saka muku a mota ko Jirgi😂💃💃.

__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

.........A wannan rana ƙarfe sha biyu na rana jirgin su Mammah ya sauka, tare take da Ammar ɗinta sai ƙaninta Tasi'u da Ammar ke kira Uncle. A tsakkiya suka sakata har inda motoci suke. Aiko cikin sa'a sukai arba da tagwaye biyu Yaya Ma'aruff da Ja'afar da suka zo ɗaukarsu da kansu. Sai dai me suna yunƙurowa a tare suka koma suka ƙame kamar gunkinaye idanunsu akan Uncle Tasi'un. Dan duk da suma suna yara sosai ya aikata abinda ya aikata hakan bai sa sun mance wannan fuskar tasa ba. Dan bayan mahaifin Biebah shine mutum na biyu daya bar musu tabo a zuciya na zahiri. Abinda dangin mahaifinsu suka aikata duk a labari suka sanshi, a labarin ma ba komai ba daga bakin Mammah ko Dadansu. Gwaggo Alawiyya ce ta gaya musu komai.

    Ganin yanda sukai ɗin ya saka Mammah cikin dakewa furta, “Oh bakwa farin ciki da ni na koma kenan ko?”.

     Jikinsu ne yay sanyi, cikin dauriya da danne zukata suka nufota, batare da ko kallon Uncle ɗin nasu sun sake yi ba suka rungumeta ita da Ammar suka manta da shi. Ammar daya tsargu da abinda ya farun da ƙyar ya iya dannewa yana murmurshi. Haka suka kama Mammah a tsakkiya har mota. Sai da ta shiga suma suka shiga Ammar ya shiga, ganin Uncle Tasi'un bai shigo ba Mammah tace su masa magana ya shigo. Kallonta sukai kamar zasu fasa kuka. Amma kallon da itama tai musu na gargaɗi ya sasu risinar da kawuna Ja'afar ya fita yay masa magana. Sum-sum kamar munafuki ya shiga kusa da ita suka sakata a tsakiya shi da Ammar......

       Sun iso gida da yake shiru kasancewar basawan cikinsu duk ana makaranta. Masu aiki ne kawai sai Aunty Shariffa da Aunty Lailah da yay basu je gidan haihuwa ba saboda dawowar Mammah. Hasalima da kansu suka shiga kicin yi mata abincin da suka san tafi so da ƙauna. Masu aiki da suma ke farin ciki da dawowarta na tayasu da ƙananun ayyuka. Daga Aunty Shariffa har Aunty Lailah kowace fama take da ƙaramin ciki, dan cikin ikon ALLAH kamar yanda sukai haihuwar su Abees a tare da tasu Afrah da Ayyan haka wannan cikin ma basu da nisa a samu. Sai dai Aunty Lailah ce ta fara samu kafin Shariffa. Dan haka nata yafi fitowa sosai har ana iya gani.

      Mu'azz ya fita akan batun karatunsa dan Imam ne yazo har gida suka fita a mashin ɗinsa. Wannan ya ƙara haifar ma da gidan shiru. Motar su Mammah na gama tsayawa Lailah da Shariffa suka fito cike da ɗoki da farin ciki dan Mammah uwa ce a garesu ba uwar miji ba. Itama fuskata ƙawace da murmushi ta fito da taimakon Ammar. A tare ta kamosu jikinta ta rungume tana mai jin farin cikin ganinsu da sanya musu albarka. Yayinda suma suka zame suka zube cike da girmamawa suna mata barka da dawowa. Ta amsa musu da kulawa tana kamasu ta miƙar.

      Cike da tsokana Ammar ya ce, “Wato kunga Mamanku ni in ma na ɓata a can babu ruwanku ko Auntys?”.

     Yanda yay maganar yana cika baki da iska har su Ma'aruff dake faman haɗe fuska saboda Uncle Tasi'u Sai da suka dara. Suma cike da tsokana sukace, “Mu mun isa muso kawun yara ya ɓata. Ai sai suyi mana bore suma Yaya Ammar”.

        “Ato naga ba'a wani ji dani ne sai Mammah kawai”.

      “To ayi haƙuri, kasan rashin ta ya maida mu kamar marayu a gidan cike muke da ƙaguwar son ganinta. Kaima bari kaga ƴaƴanka su dawo duk kanka zasuyi”.

     “Ai shiyyasa ma ban damun ba. Dan da kaina zanje na ɗakkosu a schools”.

      Duk hirar da suke zugawa Uncle Tasi'u na kallonsu ne kawai cikin damuwar kallon banzar da su Ja'afar ke masa a kaikaice. Su ko su Lailah basu lura da shi ba sai daga baya. Kamaninsa da Mammah dake a bayyane ya sakasu kasa jurewa suka bishi da kallon sakanni. Sai kuma suka duƙar da kawuna cikin ƙaulani da rashin tabbaci suka shiga masa barka da zuwa. A karo na farko yaɗan sauke ajiyar zuciya. Dan koba komai girmamawar tasu ta ɗan sakashi jin sanyi a ransa. Ya amsa musu da kulawa shima.

      Mammah ta katse su da faɗin, “Kumuje ciki kun san fa ni bana jurar tsaiwa”.

      Da to suka amsa mata suna sakata a tsakkiya, dai-dai nan kuma maigadi da sabon driver suka iso wajen cike da girmamawa suka duƙa har ƙasa suna gaida Mammah. Tabbas Mammah zata iya haihuwarsu idan muka musalta da yanayin auren da na ƙarancin shekaru musamman ma itama da akai mata tana ƴar 14. Dan driver dai zai iya zama sa'an Dada, maigadi ko bai wuce sa'an su Yaya Ja'afar ba, idan ma Dada zai girme ma sabon driver ɗin kaɗan ne, sai dai yanayin jin daɗi ba ɗaya ba, duk da a yanzu basu san yaya Dadan yake ba amma ya fishi ƙyawun jiki da ƙuruciyar zahiri. Dan shi wannan ma har furfura ta cika masa gemu duk da dai kansa akwai hula tashi da ƙwaƙwa baƙa data ɓoye gashin kan nasa, sai na iya fuskar zaka shaida zuwa gemu dan yana da saje...

        “A'a bawan ALLAH tashi-tashi kaji, mun sameku lafiya ko Almu. Ka yi baƙo ne?”.

     Maigadi ya bata amsa da mata bayanin ba baƙonshi bane su Yaya Ma'aruff ne suka kawo shi. Kafin tace wani abu sabon driver wanda shima a karo na biyu fuskarsa da murmurshi ya amsa mata, kafin ya miƙe yana sake mata barka da dawowa da sannu da jiki. Sannan ya juya yana gaida Uncle Tasi'u da Ammar. Ma'aruff ne ya juyo yana kallon Mammah ya ce, “Sabon driver ne daya maye gurbin Baba Ari. Sunansa Buba kwana uku da tafiyarku ya fara aiki”.

       Fuskar Mammah da fara'a sosai ta ce, “Masha ALLAH. Sannu da zuwa Malam Buba. ALLAH yasa zamanmu tare ya zama alkairin da zamu shiga aljanna gaba ɗaya. Ina dai fatan babu wani damuwa a zamanka tare da mu ɗin?”.

          “Amin Hajiya. Amin Amin. Babu wata damuwa sai godiya tsakanina da ku. Dan kuwa kwanakin da nai kawai na shaida alkairin mutanen wannan gida.”

      “To Alhamdullahi ALLAH yasa mu dace. Bari naje na huta munsha zaman jirgi zuwa anjima ka shigo mu ƙara gaisawa?”.

     “To to shike nan Hajiya, ALLAH ya huta gajiya nagode sosai.”

     Fuskar Mammah da murmushi ta amsa da amin Kafin su Shariffa su kamata har zuwa ciki. Shi dai Uncle Tasi'u na biye da su sum-sum kamar munafuki, sai dai harga ALLAH yayi matuƙar girgiza da ganin irin wannan katafaren gida mai kama da wani ƙaramin estate wai duk mallakin Adda A'isha ne da zuri'arta. Addarsa fa dake wujiga-wijiga akan marayun ƴaƴanta dana gayyar soɗi na kishiya data kama ta riƙe ita mai son miji. Addar nan tasa dai daya damfara gida ya gudu ya batta da sanin bata ga tsuntsu bata ga tarko a lokacin, amma a yanzu sai gasu a wannan ƙosashen gidan a babban birnin tarayyar ƙasa da dukkan alamu suka nuna nasu ne, kai shifa tun a motar dasu Ja'afar ɗin suka ɗakkosu dama zuciyarsa ke bugawa, yanzu kuma da suka shigo gidan ma sai yaga motocin da sukafi wadda suke ciki, sannan ba ɗaya ba a ƙalla motoci sun kai bakwai a gidan harda wadda suka dawo ta takwas.

     Bai ji zuciyarsa na tsitstsinkewa ba sai da suka shiga cikin katafaren sashen Mammah ita ɗaya, dan dama sashenta dana Dada sunfi kowanne girma a gidan. Kafin kace mi kuma ƴan aiki har uku sun zagayeta suma da tasu gaisuwar girma. Ga waɗan nan tsala-tsalan matan daya fahimci matan su Ja'afar ne sai rawar jiki suke akanta kamar wata uwarsu mahaifiya...

     

.....★DUBAI★.....

       

    “Inaga a wannan gaɓar zan saka a kashe mijin nata, dan hakan ne kawai zai saka ta yarda ta saduda ta mallaka min kanta”.

       A wani irin firgice Hajiya Hasiba ta ɗago tana kallon Adeel mai maganar. Mamawo kuwa abincin da suke ci ne ya nema ƙwareta. Sai da ta ɗauki ruwa tasha da sauri.

    Shi ko ko'a jikinsa, dan tamkar ma bai ga halin da suke ciki ba ya cigaba da maganarsa.

         “A karo na farko ina son sanin wanene shi mijin nata? Miya taka a ƙasar taku? Ɗan wace zuri'a ce? Miye ƙarfin ikon sa?”.

      Su duka biyun rasa mai bashi amsa akayi, dan dama daga su sai shi ne a dining room ɗin. Su Ismat sunbi Nabeeha sun fice a gidan tun da sukaji zancen zuwansa. Ɗan dukan table ɗin yayi ta yanda suka dawo hayyacinsu firgigit. Da ƴar tsawa da raini da wulaƙanci ya ce, “Ko kuma kuna bin bayan wulaƙanta ni da take ne....?”

       “A'a wlhy bama bin bayanta. Da muna da iko da zuciyarta ma da tuni kun jima da zama ma'aurata maybe ma kun haihu. Mijinta ba kowa bane, ba ɗan kowa ba, baya da komai, baya taƙama da komai. Kawai soja ne a ƙasar mu, kamar yanda muka sanar maka tun farko kuma yana prison yanzu haka, shekaru ashirin da biyar kuma aka yanke masa a can”.

      “What! Shine kuma take tunanin zaman jiransa?”.

     “Shirmenta ne kawai Prince, amma tun kan ya shiga prison ma ita ta bar masa gidan sakamakon auren yarinya ƴar shekara 7 da yayi saboda ya ɗakota a wajen yaƙi. Daga ƙarshe ma mukaji ashe shine ya kashe mata iyaye dan ya aureta, da alama wani laƙanin asirin aka bashi dan dama yanda yake juya sojojin da wani gadararsa har manyan suna tsoronsa kai ka san ba haka kawai bane, dole akwai aikin asiri a ciki”.

       “Woow naji daɗin wannan labarin ƙwari da gaske. Yanzu ita yarinyar tana ina ne?”.

    “Tana a gidansu tare da ahalinsa. Sai dai a yanzu takai kusan 15years da wasu watanni”.

       Komai bai sake cewa ba ya miƙe kawai, da kallo suka bishi yana tafiya cike da ƙasaita da gadara, sai da yaje gab da fita a dinning room ɗin sannan ya juyo yana kallonsu. “Zamuje ƙasarku tare da ɗaya a cikinku”. Daga haka ya fice abinsa batare da jiran amsarsu ba.........✍️

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*

*_+227 98 94 12 81_*

*_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*

*_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899*

*_Moniepoint MFB_*

*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_*

*_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_*

*_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_*

*_Chapters & Audio_*

@BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276*

*_Access Bank_*

*_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_*

*_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_*

*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_*

*+234 805 568 7449*

*_Telegram Number👇_*

*+234 903 234 5899*

*_Maza ku matso MASOYAN Bilyn Abdull da IDANU suka hana karatun novels...._*

*_Tofa Bilyn ku ta samo muku hanya mai sauƙi da kina aiki, ko kina kwance kina hutawa, ko kina inda baki son yawan surutu earpiece ɗinki kawai zaki maƙala a kunne ko Bluetooth kisha sauraren littafin KIƊA A RUWA.... Cikin sauƙi.... 💃_*

*_Kar dai na cika ku da zance. Zamu fara saida littafin KIƊA A RUWA.... Na saurare (Audio) kenan akan farashi mai sauƙi da rahusa._*

*_Akwai VVIP AREWAPEN kenan 💃_*

*_Akwai VIP Telegram 💃_*

*_(Ƴan WhatsApp ku haƙura kawai ƴan ta'addar bati sunfi yawa a cikinku gaskiya tsoron rashin m ɗinku nake 😂🤣)_*

*_Telegram Audio 2k ne kacal ba tsada 💃. Sai kusaka ta wannan account ɗin👇_*



_(2k)_

*9032345899*

*_Moniepoint MFB_*

*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (2k)_*

*_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_*

*_Telegram Number 09032345899_*

*_Ƴan NIGER🇳🇪 kuma bazamu barku a baya ba in sha ALLAHU zaku biya (Telegram vip 1,500 CFA) domin littafin KIƊA A RUWA..... na ji Audio-vocal. Sai ki biya tanan👇_*.

_(1,500 CFA)_

*_+227 98 94 12 81_*

*_My NITA_*

*Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 1,500 CFA vip telegram*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*

*_+227 98 94 12 81_*

*_AREWAPEN (Vvip)_*

*_Chapters & Audio_*

@BilynAbdull

*_Ƴan WhatsApp kuzo muyi shawara idan zaku iya amana ayi

18 / 24