Author : Billyn Abdul Category : Action Novels
ai kai ka tafi, tunda baka san inda za'a cillaka karatun ba”.
Kallon Aunty Shariffa mai maganar yayi da faɗin, “Kai Mamy banda fata, kin san bakin iyaye da saurin kama ɗa, in sha ALLAHU nikam ina nan cikin garin nan babu inda za'a kaini”.
Mammah dake fitowa a ɗaki ta ce, “Ni dama za'a kaika wani ƙasan da yarana sun huta da damun su da kakeyi babban banza”.
“ALLAH Mammah na tafi kema sai kinyi kewata. Suma haka kuma, dan sun san ina rufa musu asiri a gidan nan. Amma tunda kun shigar musu yara duk zaku gane kuran ku. Daga yanzu ko tarin banza kukayi zan fara rubutawa ne, kuma Dada zan ajiyewa yanda zaku fi caskaluwa dan na Daddy mai armashi ne yanzu”.
A tare suka kwashi fillo suka shiga jefa masa. Gashi sun kasa tashi saboda ƙafafinsu sunyi dayin wahalar aiki. Aiko mi za'ai in ba dariya ba. Da ƙyar Mammah ta raba faɗan nan ta hanyar janyesu ta shafa musu man zafi a ƙafafu. Ga shi lokacin yin girkin rana yayi. Haka suka shiga kitchen ɗin suna sharɓar hawaye, ga camaras da suke ji kamar su fincike su su yardar su samu a tayasu. Amma ba dama, dan duk bayan wani ɗan lokaci sai Daddy Imran ya kira waya ya tabbatar musu duk yana kallonsu dan yayi connecting da wayarsa, suma kuma sun san haka ɗin ne tun ma ba yanzu ba..........✍️
Gaskiya kuzo muje balling Trouble Buddy da Trouble Queen kafin Daddy Imran ya kaisu gadon asibiti🤣🤣.
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number👇_*
*+234 903 234 5899*
*_ASSALAMU ALAIKUM MUTANE NA MASU ALBARKA_*
*_Maza ku matso MASOYAN Bilyn Abdull da IDANU suka hana karatun novels...._*
*_Tofa Bilyn ku ta samo muku hanya mai sauƙi da kina aiki, ko kina kwance kina hutawa, ko kina inda baki son yawan surutu earpiece ɗinki kawai zaki maƙala a kunne ko Bluetooth kisha sauraren littafin KIƊA A RUWA.... Cikin sauƙi.... 💃_*
*_Kar dai na cika ku da zance. Zamu fara saida littafin KIƊA A RUWA.... Na saurare (Audio) kenan akan farashi mai sauƙi da rahusa._*
*_Akwai VVIP AREWAPEN kenan 💃_*
*_Akwai VIP Telegram 💃_*
*_(Ƴan WhatsApp ku haƙura kawai ƴan ta'addar bati sunfi yawa a cikinku gaskiya tsoron rashin m ɗinku nake 😂🤣)_*
*_Telegram Audio 2k ne kacal ba tsada 💃. Sai kusaka ta wannan account ɗin👇_*
_(2k)_
*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (2k)_*
*_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*
*_Ƴan NIGER🇳🇪 kuma bazamu barku a baya ba in sha ALLAHU zaku biya (Telegram vip 1,500 CFA) domin littafin KIƊA A RUWA..... na ji Audio-vocal. Sai ki biya tanan👇_*.
_(1,500 CFA)_
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*
*Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 1,500 CFA vip telegram
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_AREWAPEN (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull
*_Ƴan WhatsApp kuzo muyi shawara idan zaku iya amana ayi harkar nan daku 😂, dan bana son a barku a baya duk da dai bakwa ji, ba raga min zakuyi ba na sani duk da ƙaunar da nake muku 🤣😂._*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
11
.........Kwanaki kusan biyar su Nimrah na cin ƙaniyarsu da aiki, sun jikatu matuƙa sunyi laushi, kuka da roƙo babu kalar da basuyi ba, hakama kawunansu sun bama Daddy Imran haƙuri amma yace idan suka bar aikin nan Boarding fa babu fashi. Da ga ƙarshe dai suka zagaye suka kira Aunty Ummie a waya suna mata kuka suka sanar mata. Dama kwana biyu bata leƙo gidan ba saboda aiki. Aunty Mommy kuwa basa ƙasar ita da mijinta sai a satin nan zasu dawo. Ita ko Aunty Mimi ciki gareta tsoho haihuwa ko yau ko gobe shiyyasa Mammah ta hanata zuwa gidan.
Alhamdullahi zuwan Aunty Ummi da suke kira da Big Mah-mah ne ya cecesu a hannun Daddy Imran. Dan bayan an sako massalacin juma'a yazo gidan gaida Mammah ta tareshi da daɗin baki da ban haƙuri har ya haƙura masu aiki su dawo gobe. Amma duk da haka da sharaɗin daga yanzu kullum dasu za'a dinga shiga kitchen yin girki. Da wannan ALLAH ya ƙwacesu. Masu aiki suka dawo, su kuma suka samu sauƙi. A cikin satin ma suka koma zuwa islamiyya dan suspension ɗin ta ya ƙare, sai kuma karatun da akayi basa nan ya sakasu a gaba. Sati ya zagayo suka koma boko ma, amma duk da haka sai da akai zama da Hajiya ta kafa sharaɗin babu su ba yarinyar ta, dole kuma a raba musu wajen zama sannan case ɗin ya mutu. Dan an dai gane ƴarta na kalle-kallen banza a waya da gaske kamar yanda su Nimrah ɗin suka faɗa......
>>>>><<<<<<
Yau ta kasance juma'a, dan haka an tashesu da wuri. Sai dai shiru babu drivern su babu alamarsa. Sun san maybe ya fara zuwa ɗaukar su Abees kafin yazo nan, duk da kuwa a kulum su yake fara zuwa ya ɗauka kafin su ƙarasa makarantar su Abees ɗin saboda suna rigansu tashi. Tun suna kallon agogo har suka sare, ga mafi yawan ɗalibai duk sun wuce anzo an ɗaukesu. Makarantar su nada doka kuma ma tilas zuwa ake ɗaukar kowane ɗalibi bawai buɗe musu gate ake su fito ba kawai.
Sun gaji ga Ruky na ciwon mara, dan ita in zatai period ba ƙaramin jikata take ba. Ganin ta fara kuka hankalin Nimrah ya tashi. Ofishin Principal ta nufa amma ta tasar baya nan wai sun shiga meeting da malamai. Da gudu ta dawo wajen Ruky, ta sameta durƙushe azaba ta isheta, bata son suje clinic ɗin cikin makaranta dan an riga an tashi. Idannunta na cika da ƙwalla itama ta kamata ta miƙar. “Tashi muje wajen security ko zai taimaka ya barmu mu fita kawai, amma shima Baba Driver bai ƙyauta mana ba”. Da ƙyar da ƙyar Ruky ta iya miƙewa suka isa gate ɗin, cikin sa'a suna isowa sai ga motar Yaya Ammar na isowa. Ajiyar zuciya Nimrah ta sauke, dai-dai Mu'azz na fitowa daga motar, ya ƙaraso inda suke da sassarfa yana faɗin, “Lafiya kuwa? Miya sami Ruƙayyan?”.
“Yaya ciwon mara, muyi sauri mu tafi kasan idan ya fara tsanani sai suma. Amma Yaya driver fa?”.
Sai da ya buɗe musu suka shiga yake bata amsa yana reverse. “Baba driver accident yayi, yanzu haka ma yana asibiti”.
“Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un, badai da su Aheel ba?”.
“A'a bada su ba, shi kaɗai ne yaje ɗakko motar Ummie (Aunty Lailah suke cema Ummie, Shariffa Ammie) daga wajen wanki”.
“Ya rabbi, ya jikin nasa?”.
“Gaskiya yaji jiki sosai, dan har yanzu ma ba'a bari an gashi ba. Motar kuwa tama tashi aiki, dan babbar mota ce ta haye shi”.
Gaba ɗaya jikin Nimrah ya ƙara sanyi, ita kanta Ruky dake fama da kanta hankalinta ya sake tashi, a haka suka iso gida ciwon marar ya ƙara tsanani, dole ma sai Mu'azz ɗaukarta yayi. Gaba ɗaya hankalin ƴan gidan a tashe yake da hanlin da baba driver ke a ciki, dan mazan gidan duk suna can. Ganin hanlin da Ruky ke ciki kuma duk sai suka maida hankali a kanta. Babu bata lokaci aka kira family doctor ɗin su, da yake ya san matsalarta yana zuwa allurai yay mata....
Basu sami ganin Baba Driver ba sai ranar Lahadi da yamma. Gaba ɗaya gidan suka shirya suka je suka duba shi. Yaji jiki kam kwari da gaske, amma Alhamdullah yana samun dukkan kulawar data dace. Ga matarsa an ɗakko tana jiyyarsa. Komai na asibitin Kuma su Yaya Ja'afar ne suka biya. Sosai matar ke godiya akan yanda suka bama al'amarin mijinta muhimmanci, inda wasu ne ko'a jikinsu, ƙilama suce sai an biyasu motar miliyoyin kuɗin data tashi aiki. Amma su bata motar suke ba ta lafiyarsa sukeyi.
Shima Baba Driver kallonsu kawai yake yana hawaye, dan baya iya magana har yanzu. Su duka sun ɗauka yana kuka ne kawai akan halin da yake ciki. Dan haka Mammah tai masa nasihar haƙuri da tawakkali akan ƙaddara. Kusan awar su ɗaya suka koma gida suna sake jimanta al'amarin. Satin baba driver biyu ya fara samun sauƙi, zuwa yanzu kuma Mu'azz ke jigilar kai su Nimrah makaranta da ɗakkosu kullum. A haka kwanakin tafiyar Mammah da Yaya Ammar suka cika zuwa Egypt ganin likita. A tare suka mata rakiya airport cike da kewa, dan Ruky da Nimrah harda kukan su. Ƙarshe Uncles ɗin nasu suka koma lallashinsu da tabbatar musu ai sati biyu kawai zatai ta dawo. Haka suka dawo gida. Tafiyar Mammah da Yaya Ammar da kwanaki biyar al'amarin karatun Mu'azz ya taso, dole su Yaya Ma'aruff suka fara batun neman driver, dan su basu da isasshen lokaci, wani lokacin ma da ƙyar suke ƙulla sati uku a ƙasar. Ammar yana fama da aikinsa, ga Bilal ma baya ƙasar, ko yana nan aikinsa shima ya ishesa, bazasu so kuma matansu kullum na gantalin kai yara makaranta da ɗakkosu ba, balle Biebah da bata da magana yanzu sai ta project ɗinta. Sunata tunanin ina zasu samu sabon driver mai amana kamar Baba amma sun rasa makama.
Shawarar kota hanyar Baban za'abi Yaya Ma'aruff ya bayar, dan haka suka amince da hakan. Bayan sun taso kasuwa suka nufi gidansa dake can wani ƙaramin ƙauye, sai dai atanan yankin babban birnin yake. Sun sameshi jikinsa Alhamdullah, sai dai ƙafa data samu nakasa sosai har yanzu anata fama. Sun sake jajanta masa da ajiye masa alkairin da basa gajiyawa wajen yi masa sannan suka sanar masa abinda ya kawosu. Cewar suna son ya sama musu wani drivern mai amana kamar shi dan sun yarda da shi. Da farko shiru yayi idanunsa na cika da ƙwalla. Sai da Ja'afar ya ce,
“Baba wannan ai ba abin kuka bane. Mun yarda da kai ne da amanar ka shiyyasa muka sake biyowa ta kanka, kuma in ma ALLAH ya baka lafiya muna maraba da dawowarka cikinmu”.
Hawaye Baba ya share, “Na sani ku mutanen arziƙi ne masu tarin alkairi, har abada kuma bazan manta da tarayyata da ku ba. Amma mizai hana ku cigaba da kai yaran makaranta da kanku?”.
“Baba bazai yiwu ba, kasan yanda uziriri sukai mana yawa dai, idan muka ce mune zamu kaisu za'aita samun matsala. Ga boko ga islamiyya, ga cefanen gida kai Mammah anguwa da iyalanmu”.
Baba yay shiru zuciyarsa na kai-kawo, dan yasan bazasu fahimci mi yake nufi ba daman kai tsaye, shi kuma tsoro bazai barshi fitowa ya buɗe musu komai ba kai tsaye, sai kawai yace to su bashi lokaci zai kira a waya. Cikin gamsuwa sukai musu sallama suka tafi. Cikin damuwa matarsa ta ce, “Wai miyasa kake ta musu kwana-kwana malam? Mutanen nan mutanen kirki ne, banyi zaton zasu zo da damuwa kanada damar musu maganinta ka kasa ba”.
“Ba kasawa nai ba Tabawa, kawai ina duba al'amarin ne dai kawai, kin san yanda rayuwa ta lalace yanzu ba kowa ke raɓarka da ƙyaƙyƙyawar zuciya ba. Ko ni ɗin ma alkairin su da hukuncin UBANGIJI ne ya sauya ni daga dalilin raɓarsu”.
Cikin rashin fahimta ta ce, “Kamar ya? Ban gane ba malam!”.
Murmushi kawai yayi bai sake cewa komai ba ya barta da wasi-wasi. Awa ɗaya ba'ayi da tafiyar su Yaya Ma'aruff ba Baba Driver yayi baƙo. Kasancewar matarsa tasan mutum ya saba zuwa wajensa bata kawo komai a ranta ba ta shiga ciki gida ayyukanta ta basu waje. Dan yana jiyyar a ɗakin soro ne...
“Rabe! Kana ganin taurin kanka zai cigaba da baka nasara ko? Halin da kake ciki bai zame maka aya ba kenan?”.
Murmurshi Baba Driver yayi mai ciwo, idanunsa cike da ƙwalla ya ce, “Ba darasi ne ban ɗauka ba Ari, ina tausayin bayin ALLAHn nan ne. Wlhy mutanen nan munanen kirki ne su da mahaifiyarsu. Sannan ya kamata mu yarda ba laifinsu bane akan abinda ya faru baya, shima kansa wanda ake son azabtar da su ta dalilinsa mufa sani rayukanmu ya jajirce wajen karewa, ALLAH ne ya ƙaddara za'a tarwatsa mu a ƙauyukanmu har mu watse irin haka. Hasalima mutanen nan dake munana shi a garemu sune silar faruwar komai akan waɗan can abubuw......”
“Rabe! Kana nufin wuyanka yayi kaurin bijirema su Oga Dagger ko? Amma kasan minene hukuncin yin hakan a gareka ko? Karka manta kana cikin ƴantattun da aka bama damar zuwa su rayu a cikin mutane har suyi aure su hayyafa cikin ƴanci. Baku san wahala da azabar da mu dake cikin jeji kullum a ɓoye muke sha ba. Mutanen nan da kake ƙoƙarin karewa ance maka kaje kai musu wani abu ne? Information ɗin abinda ke gudana a rayuwarsu kawai akace ka dinga kawowa. Musamman ita wannan yarinyar Nimrah, amma taurin kai yasa ka zauna kana kawowa mutane ƙauli da ba'adi, gashi nan har sai da ka jama kanka zaman guri ɗaya, da da ƙarar kwana ma yanzu wani labarin ake ba naka ba. Ni dai yanzu ga saƙo, Oga Mole da Oga Dagger sunce gobe zasu turo sabon driver ka turashi ga mutanen nan ya maye gurbin ka, zaɓi ya rage naka kayi koka kuskure kai ne zakai kuka, dan a yanzu ba kai za'a hara ba ƴaƴanka ne ko matarka”...
Yana gama faɗa ya miƙa batare da ya saurari magiya da roƙon Baba Driver ba.....
★>><<<<★>>>><<★
★DUBAI★
Ganin yanda Nabeeha ke faman haɗa kaya ya bama Ismat data kawo mata breakfast har ɗaki tsoro. Duk yanda taso daurewa saita kasa. Cikin damuwa ta ajiye tray ɗin da take ɗauke da shi ta nufeta. Hannunta ta riƙe cikin rauni da damuwa ta ce, “Aunty wai mi kike yi haka ne? Ina zaki kike haɗa kaya?”.
Hannun nata ta fisge, kukan da take faman riƙewa tun daren jiya saboda taurin zuciya a karo na farko ta fashe da shi..........✍️
12
.........“Ismat zan koma ƙasata, wlhy na gaji da wannan rayuwar, bazan iya ɗaukar huɗubar Momy ba, gara na koma gidan mijina nai zaman jiran dawowarsa ko nan da shekara hamsin ne ma ba ashirin da biyar ba”.
Ajiyar zuciya mai ƙarfi Ismat ta sauke, dan koba komai itama an taɓo mata inda ke mata ƙaiƙayi dama. Ta kama hannun Nabeeha suka koma bakin makeken gadon ɗakin da yaji shinfiɗu na alfarma, dan duk da haɗuwar gidan da komai na cikinsa ɗakinta na musamman ne. Gyara irin na ƴar gata Adeel yasa akai mata. Hannayenta duka a cikin na Ismat ta ce, “Aunty wlhy koni ina bayanki ki koma gidanki, dan ita Momy idannunta sun rufe da son kuɗi bata duba abinda muke so koya dace damu. Ita kawai tafi kallon abinda zata samu. Gamu dai a cikin ƙaton gida a kuma ƙasa irin ta Dubai da kowa ke buƙatar yazo, amma wlhy Aunty Jiddah ta fimu kwanciyar hankali, tana rayuwar auren ta ga yaranta abin sha'awa, shiyyasa wlhy nima na fara ji a raina zanyi na nata na koma gidan Abba na bashi haƙuri na samu miji nayi aure. Dan in har muka cigaba da rayuwa da Momy anan wataran sai mun lalace, dan waɗan nan shaggun mutanen babu abinda suka iya sai son mata kamar su babu matan a cikin nasu ƙabilar”.
“Ismat wlhy ni duk bama wannan ba, babban abinda ke bani mamaki da Momy itafa kawai na kashe aurena saboda wannan mutum yace mata aurena yake son yi, haba miyasa ba zatai tunanin daya dace ba, dukiya irin ta mutumin nan, da nasaba ta gidan mulki, mulkin ma mai ƙarfin gaske ne zai zauna wani auren baƙar fata ƴar Africa saboda rainin hankali da ɗaukar mutane jakai. Kiga yanda suke wulaƙanta matan African fa kamar wasu dabbobi dan ko bayi na baya sun fi matan da ake kawo musu suna iskanci da su a yanzu mutunci da daraja. Wlhy Ismat ina son mijina, duk da ina jin takaicin auren shegiyar yarinyar nan har yanzu a zuciyata....”
“Na sani Aunty, ki share wani batun yarinya kawai muyi tafiyar mu, dan uwarta mune zamu miki maganinta, da ƙafarta zata bar gidan batare da kowa ma ya sani ba ta koma ƙauyen su, idan tace ita ƴar hau ce mu ƴan hau-hau ne to”.
Ajiyar zuciya mai ƙarfin gaske Nabeeha ta saki, tana mai jin nutsuwa da gamsuwa da zancen autar tasu. A gefe zuciyarta na jin matsanancin kewar mijinta da buƙatar son kasancewa da shi da akoda yaushe take yaƙi da kanta a kai, sauƙi-sauƙin ma da take samu kullum cikin mafarkinsa da yanda yake tafiyar da ita a shimfiɗa take, shiyyasa take samun sassauci da jinsa kamar a kusa da ita har yanzu.....
Da baya-baya Hajiya Hasiba tabar bakin ƙofar ranta a matuƙar ɓace da tattaunawar