Advertisements
Chapter 10 Reading KIRAN RABO BOOK1 CMPLT BY NANA HALEEMA BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

KIRAN RABO BOOK1 CMPLT BY NANA HALEEMA

Author :  NANA HALEEMA Category :  Complete Novels

Chapter   10 / 28

27K to 30K   out of 83.2K words

ce, "karɓi ki sha Nayla." Nayla kallon ta tayi sai
ta ɗan zabura Didi ta riƙe ta ta ce, "kar ki ji tsoro, babu abinda zai miki baya
cikin gidan ma gabaɗaya. Yi haƙurk ki sha ruwa." Ba musu ya sake karɓat ruwa ta sha
tana sauke numfashi kamar wacce tayi gudu.

Didi ta kalle ta ganin ta dawo nutsuwarta sai ta dafata ta ce, "ki yi haƙuri Nayla,
ban saka ki shigowa gidan nan dan ki shiga wannan yanayin ba, wallahi ban san zai
dawo ba da ban ce ki zo ba. Ki yi haƙuri don girman Allah, da na san hakan zai faru
da ban ce ki zo ba."

Nayla jin yadda take mata magiya cikin sanyim murya sai ta ce, "Haba Didi, don
Allah ki daina yi min magiya haka babu komai Didi."

"Dole na roƙeki ki yafe min ai Nayla, da ban je har gida na taho dake ba da haka
bai faru ba, tun farko kin nuna bakya so amma na takura miki. Gashi na saka ki a
halin tsoro da fargaba wanda ya kusa sakawa ki suma ki fita daga hankalinki, ki
yafe min kin ji? bazan sake takura miki akan zuwa gidan nan ba."

Nayla ta ce, "babu komai Didi, don Allah ki daina bani haƙuri." Didi ta sauke
ajiyar zuciya ta ce, "ransa ne a ɓace sosai kin tarar dashi akan gaɓa shiyasa, zaki
ga ni kaina bai ƙyale ni ba saboda in ransa ya ɓaci ya kan rasa hankalinsa na wani
lokaci sai daga baya yake fahimtar abinda ya faru. Bayan fitar ki baƙon da ya zo
shine silar ɓacin ransa, na tabbatar ba dan haka ba da bazai kalle ki ba, saboda
nayi masa magana ranar da ya yi miki wannan abun."

Nayla ta riƙe hannun Didi ta ce, "babu komai Didi ya wuce." Ta yi murmushi ta ce,
"na gode. Amma ki rage tsoronsa har haka, ki koyi dakewa koda zaku haɗu a wani
waje" tayi murmushi ta ce, "Dan na san baza ki sake shigowa gidan nan ba, Nayla ban
ga laifinki ba Omar abin tsoro ne a wajan wanda bai san shi ba, amma in ka san shi
normal mutum ne kamar kowa" ta faɗa tana ƴar dariya tana kallon Nayla da take yaƙe.

Didi ta ce, "ina jin aure zan masa wataƙila zafin kansa ya ragu." Nayla bata san
san da murmushi ya subce mata ba, ta wara ido ta ce, "Aure! Kuma sai a samu wacce
zata aure shi? Taɓɗi! amma sai dai mai taɓin hankali." Sai bayan tayi magana ta
fahimci a bayyane tayi maganar. Didi tayi dariya sosai ganin ta saka Nayla murmushi
ta ce, "Ni da nake cewa ƴar gida za a yi dake? Shikenan tuwo na mai na, Yayar
amarya kuma Yayar ango."

Wani irin numfashi Nayla ta sauke mai nuni da ta rasa abinda zata ce. Didi tayi
dariya ta ce, "wato kin kasa magana ma kenan?." Nayla tayi murmushi kawai bata ce
komai ba. Didi ta ce, "mu je na raka ki wajan Hajja in na soya awara sai na kawo
miki." Ai kamar jira Nayla take ta miƙe tana neman hijjabinta.

Didi ta bita da kallo dan ƙananun kaya ne a jikinta ta ɗora dogon hijjabi ta fito
ta ce, "Irin wannan kyau haka Nayla? gaskiya ina yiwa ƙanina kamu." Taɓe fuska
Nayla tayi ta kalle ta tace, "Didi wallahi kina saka zuciyata cikin fargaba, don
Allah ki daina faɗar haka bana so." Didi tayi dariya tana cewa, "na daina faɗa, yi
haƙuri." Nayla ta saka hijjabin ta, itama Didi ta saka suka fito.

Ganin tana dafe kai ya saka Didi ta ce, "ciwon kai ko?." Ta ɗaga mata kai alamun
eh, Didi ta ce, "sannu, Allah ya ye." Ta amsa da amin suka fita ƙofar gidan. Nayla
ganin Didi bata rufe gidan ba sai ta ce, "baki kulle ƙofar ba." Didi tayi murmushi
ta ce, "a tunanin ki za a shiga ayi mana sata ne? Gidan su Omar Damisa ne fa, gidan
nan ko almajiri baya shiga yayi bara balle ɓarayi." Nayla ta ce, "Ya ci suna Tiger
ɗin ai, ba shi da sabo." Didi ta yi murmushi Nayla ta girgiza kai bata kuma cewa
komai ba amma zuciyar ta tana jinjina girman baƙin halin sa.

A zaune suka samu su Hajja ita da Salma suna cin abinci. Didi ta ce,
"Hajja ga Nayla na dawo da ita na kuma yi mata laifi, a taya ni roƙon ta tayi
haƙuri." Hajja ta ce, "me ya faru ke da ƙanwarki?." Didi ta ce, "ita da Omar suka
gamu wallahi, gamuwar bata yi daɗi ba sam kuma duk ni ce sila. Ni nazo har goda
muka tafi, da ban mata dole ba da baza ta je ba, yanzu haka kanta ciwo yake yi."

Salma ta yi dariya ta ce, "Shiyasa ni da gidanki sai kallo daga nesa." Didi ta
zaunar da Nayla ta ce, "ki yi haƙuri Nayla." Nayla ta ce, "Haba Didi, tun a can ki
ke bani haƙuri, don Allah ki bari."
"Na bari, Na gode sosai Allah ya baki miji na gari. Zan koma gida yanzu amma zan
shigo anjima." Nayla ta ce, "to Didi." Didi ta fita zuciyar taduk babu daɗi akan
abinda Omar ya yi mata.

Ai Didi tana fita Nayla ta zare hijjabinta ta cillar ta ɗaga wuya sama ta kalli
Salma ta ce, "Salma duba wuya na ki ga babu yanka da wuƙa." Salma ta kalli wuyan ta
ce, "babu komai, Meye ya faru?." Nayla ta ce, "wannan mutumin an yi ɗan tijara kuma
ɗan bala'i. Ina shiga ban ma kula dashi ba fa, ina ganinsa sai nayi ta'awizi ashe
yaji haushi, wai korar shaiɗan nayi masa, to meye marabarsa da shaiɗan ɗin?."

Salma ta ce, "shine ya shaƙe ki?."
"Ke faɗar tashin hankalin da na shiga ai ɓata baki ne, ba na jin ma abinda yake
cewa saboda tsoro da fargaba. Kawai naga ya ɗora min wuƙa a wuya daga nan
ƙwaƙwalwata taje hutun rabin lokaci, dan numfashi na kaɗan ya rage bai ɗauke ba."

Salma ta ce, "to shi wai bashi da hankali ne ko ne? Faɗa masa aka yi in yayi miki
wani abun ƙyale shi za a yi?." Nayla ta ce, "shima ya san wasa yake yi ai, babban
abin mamakin ma wallahi har ita Didin bai bari ba, kin ji yadda yake zazzaga bala'i
kamar ba ita yayarsa ba?. Sai magana yake akan shi bashi da dangi da sauran su."

Salma ta ce, "wannn mutum dai ya zama annoba a unguwar nan, almajiri fa baya shiga
gidan saboda tsoro." Nayla ta ce, "haka Didi take faɗa min yanzu, ke ni naga bala'i
ai. Ruwa kuwa ina jin na sha yafi leda uku." Hajja da take jin ta tayi dariya ta
ce, "kin cika tsoro ne kawai Hauwa'u."
"Hajja tsoro halak ne, dan naji tsoronsa ai ban yi laifi ba, da tuni an kawo miki
ni ya yanka min wuya."
"Haba dai, shima ai bazai fara ba, tsorataki yake yi kawai."

Salma ta ce, "amma abin yayi yawa wuƙa fa? Wai bashi da dangi ne?." Hajja ta ce,
"kin taɓa ganin wanda bashi da dangi?." Salma ta ce, "to suna ina? Ai ko dan wannan
jagaliyancin da yake yi ya ci ace na gaba dashi sun tsawatar masa." Hajja ta yi
murmushi ta ce, "wai ba gidan babar ku Sa'adatu zaku je ba?." Nayla ta miƙe ta ce,
"bara na canja kaya mu tafi" ta faɗa tana shiga ciki dan ta canja kaya su tafi.

***** Didi haka ta koma gidan gabaɗaya zuciyarta da jikinta babu ƙarfi,
haka ta soya awarar da suka gama ta rage wata ta saka a fridge dan ta ga da yawa
sosai, ta zuba wata a food flakas ta zuba sauce ɗin ta fita da kanta ta kaiwa
Hajja, Hajja take sanar da ita su Nayla sun fita itama ta koma gida.

Kamar yadda baƙon ta ya ce zai zo bayan la'asar hakan ce ta kasance, ita ta
manta da zuwan na sa sai da yayi mata waya ya ce gashi nan ya tawo ta tuna. Dole ta
miƙe tayi wanka tana fatan Allah ya sa shine na ƙarshen masu zuwa neman aurenta. Ba
jimawa ta gama shiryawa ya zo ta sauke shi a harabar gidan dan bata shiga da baƙo
ciki saboda bakin mutane.

Sun jima suna tattaunawa kuma ta yaba da kalamansa da nutsuwarsa da alama da gaske
yake, ya kuma faɗa mata duk abinda ake faɗa a kanta shi kuma bai damu ba ya amince
da auren ta a haka. A nan ya yi masa kwantancen gidan Kawu da lambar wayarsa dan
yaje su tattauna inda dai gaske yake, bai jima sosai ba ya yi mata sallama ya tafi
da alqawarin zuwa gidan kawu.

Haka kawai ta ke jin kanta da farin ciki fiye da sauran masu zuwa neman aurenta,
zuciyarta lokaci ɗaya taji tayi na'am da shi sosai ta kuma ji daɗi da har ya tafi
Omar bai shigo ba, duk da ya san labarin Omar ɗin da komai amma a yanayin da Omar
ɗin ya ke a ranar tsaf zai kwafsa.

Bata da uwa kuma ta da abokin shawara a kusa sai Hajja, Hajja ce maƙociya, kaka,
uwa a gareta. Hakan ya saka ta gama abinda take yi ta rufe gidan ta shiga wajan
Hajja. Hajjan kawai ta samu a zaune tana jan carbi tana kallon tashar madina.

Didi ta ce, "Hajja ƴan matan basu dawo ba?."
"Ba su dawo ba Aisha, amma na san suna hanya tunda magriba ta taho."

Didi ta ce, "Hajja yau ma wani yazo da batun aure, abinda ban taɓa yi ba yau nayi,
domin na tura shi wajan Kawu su yi magan." Hajja fara'ar ta ta ƙaru ta ce, "Alhamdu
lillah! Aisha ai abinda ki ka yi daidai ne, shi kansa zai yaba da hankaliki da kika
tura shi wajan na gama dake."

Didi ta ce, "Hajja ban taɓa jin na gamsu da duk masu zuwa neman aure na wani lokaci
ɗaya ba sai shi." Hajja cikin farin ciki ta ce, "lokacin aurenki ne yazo Aisha
shiyasa. Duk masu baki da kunu da suke ta magana a kai in yanzu Allah ya rubuta
shine lokacin ki sai yanzun zaki yi aure."

Didi ta ce, "sunan saAbdulhamid kuma bashi da mata, ya sanar dani sun rabu matar da
yara biyu kuma suna hannunta. Ya ce a yi bincike akan rabuwarsu da matar indai
akwai damuwa a kansa bazai sake zuwa ba. Ma'aikacin gwamnati ne a wata babbar
ma'aikata."

Hajja ya ce, "Alhamdu lillah! In sha Allah komai ya zo ƙarshe. Ai dai ka miƙa
lamarinka ga Allah baka da sauran damuwa, Zaɓi na gari Allah ya yi miki shiyasa ya
jinkirta miki auren, ko bani da rai zaki ce na faɗa miki Aisha."

Didi ta ce, "Allah ya sa Hajja." Ta amsa da amin Didi ta ce, "Sai dai Omar nake ji,
in ya san na kai batun nan wajan Kawu babu zaman lafiya. Ɗazu ma fa shine yazo waje
na kawo min katin bikin Ramla ƴarsa shine Omar ya tarar dashi, Wannan tsinin ɓacin
ran Nayla ta tarar."

Hajja tayi dariya ta ce, "yayi faɗansa ya gama dole sai an nemi maganatan ki a
fannin aure, shi kansa da yake wannan abubuwan bara maganar auren na sa ta zo dole
sai ya neme su. Babu mutumin kirkin da zai bashi auren ƴarsa ba tare da ya nemi
danginsa ba."
"Hmmm! Ina jin wannan ranar a zuciyata Hajja, ranar da Omar zai je ya nemo dangin
mu saboda batun aurensa. Allah Hajja gani nake akan Omar ya neme su zai iya fasa
aure, zai iya zuwa ya nemi wacce ba zasu damu da danginsa ba ya aura."

Hajja tayi dariya ta ce, "haka ki ke gani, amma zai neme su da kansa. Ban da abin
Omar tunda har suka fahimci a baya basu kyauta ba kuma suke ƙoƙarin gyara laifin su
ai ya kamata ya yafe musu." Didi ta ce, "Omar da kafiya, taurin kai, zuciya, riƙo,
zafin rai, zafin zuciya ai aminan juna ne, Allah kaɗai ya san yadda zamu kwashe
dashi in yaji na tura shi wajan Kawu."

"To banda abin Omar in baki tura shi wajan Kawu ba wajan wa zaki tura shi?." Didi
tayi dariya ta ce, "ya ce an faɗa min shi bai yi hankalin da zai bada aurena ba."
Hajja tayi dariya sosai ta ce, "a shekaru dai yayi, amma ina hankalin da Ummaru zai
bada aurenki?."

Didi tayi murmushi Hajja ta ce, "ki cigaba da yi masa addu'a, kamar uwa ki ke a
wajansa, ki ta yi masa addu'a wata rana sai labari."
"In sha Allah Hajja, addu'akullum ana yi masa har taimakon malamai nake nema
akansa, in sha Allah canji zai zo. Ba dan malam Salahudden ya rasu ba ai da shine
maganin Omar, yana matuƙar girmama malamin." Hajja ta ce, "a yanzun ma zai dawo
hankalinsa in sha Allah, nan gaba shima mu sha biki."

Didi ta ce, "wai! Omar da mata." Hajja ta ce, "ba abun mamaki bane, kuma cikin ikon
Allah daƙyar in ba ta silar mace zai canja ba." Didi ta ce, "wai ta hanyar
soyayya?."
"Kina ganin bazai yu ba ne?."
"A'a, amma lamarin ne akwai firgici, wacce yarinya ce zata so Omar a haka?. Ga
halinsa na bayyane ga zafin zuciyar da yake da ita?."

Hajja ta ce, "kadai Allah ya bamu lafiya, Allah ya yafi gaban komai." Didi ta ce,
"Haka ne Hajja. Bara na koma magriba tayi in Nayla ta zo a gaishe su" Hajja ya amsa
tana sake yi mata addua'a tana amsawa ita kuma ta fita tana jin Hajja kamar
mahaifiyar ta saboda kirki da karamcin ta.

Nayla sai bayan i’sha aka dawo dasu daga gidan ƙanwar mahaifiyarta ya wacce suke
cewa Mama. Ɗanta mai suna Abbas shine ya dawo dasu har gida sannan suka shiga wajan
Hajja tare. Yana yin sallama Hajja ta ce, “wa nake ganin kamar Abbas?.” Yayi dariya
ya ce, “ni ne Hajiya Hajja, kin wuni lafiya?.”

“Lafiya lau mara kunya, baka zuwa ka gaida mutane sai dai in zaka kawo babbarka
sannan ake ganinka, yanzu ma na san saboda Nayla ne ka shigo ko?.” Yayi ƴar dariya
ya ce, “Haba Hajja, ni da nazo ki bani dambun nama sai ki fara ƙorafi?.”

Hajja ta ce, “nayi ɗin, baka zuwa gidan nan kai kwata-kwata sai da dalili.” Yayi
murmushi ya kalli Nayla da take jona chaji kasancewaar an gyara musu wutar gidan.
Hajja ta bishi da kallo tana kallon abinda yake kallo ta ce, “ya ƙannen naka da
Yayar?.”
“Lafiya lau Hajja, kowa yana gaisheki.”
“Ina amsawa da kyau.” Daga nan suka yi shiru ya sake kallon Nayla da take aikinta
ba ta shi yake yi ba.

Hajja ta ce, “Hauwa ga saƙo ki can Aisha ta kawo miki tun yamma.” Nayla ta kalli
Hajja ta ce, “to.” Abbas ya miƙe ya ce, “Hajja ni zan koma, sai Allah ya dawo
dani.”
“Allah ya kiyaye.” Ya kalli Nayla ta ya ce, “Hawwa zan tafi.” Ta kalle shi ta ce,
“To Yaya Ab ka gaida gida.”
“Bazaki raka ni ba?.” Ta shagwaɓe fuska ta ce, “na gaji Yaya.” Yayi murmushi ya ce,
“ki huta.” Itama murmushin tayi ya fita daga falon.

Salma ta bi shi da kallon ta kalli Nayla ta ce, “Nayla anya Yaya Abbas bai ƙyasa
dake ba?.” Nayla ta wara idanu ta ce, “rufa min asiri ki bar zancen nan.”

Hajja ta ce, “babu zancen a rufa miki asiri ai gaskiya ta faɗa, ni kaina na lura da
yana sonki Hauwa’u.” Gabanta ya faɗi ba tare da ta san dalili ba ta kalli Hajja ta
ce, “don Allah Hajja ki daina faɗar haka, ni ɗan uwana ne babu wannan batun a
tsakanin mu. Kuma kun san shi yana da wasa da dariya babu lallai abinda ki ke zargi
ne. Ga su Yaya Muhmmad da su Yaya Aliyu, da Yaya Khaleed duk ba a ce haka ba sai
shi?.”

Hajja tayi murmushi ta ce, “Mai Babban suna da Ali babu wanda ya nuna wani abu a
kan ki kamar yadda Abbas ya nuna, daman ni ina son auren zumunci kuma in sha Allah
a cikin zuri’ata sai an yi auren zumunci ba ɗaya ba ba biyu ba. Da kaina zan cewa
Abbas ya samu Daddyn ku da maganar ki.”

Nayla kamar tayi kuka ta ce, “Don girman Hajja ki bar zancen nan, wallahi ni bana
so” ta faɗa tana tashi ta shiga ɗaki dan ita in akwai abinda ta ƙi jini bai wuce
auren zumunci ba. Haka kawai baya burgeta balle tayi tunanin zata yi nan gaba.
Balle ma kuma Abbas da ya kasance mai ƙirar mazan da ta tsana, bana son namijin da
gym ya nuna shi, ita ta fito son mai normal ƙira ba murɗaɗɗe ba.
Didi tana zaune har takwas na dare Omar bai shigo ba duk sai ta damu ta
ɗauko waya tana kiransa amma wayar ma taƙi shiga. Ba jimawa sai gashi ya shigo da
sallama ta amsa tana kallonsa ganin fuskarsa tana nan kamar ɗazu a ɗaure tamau.
Didi ta ce, “ina ka shiga ina ta jiran ka tun dazu?.” Kamar ba zai ce komai ba sai
daga baya kuma ya ce, “ina nan.”

“Ka zauna kaci abinci.” Kai ya girgiza alamun baya ci sannan ya ce, “meyasa baki
kira ni ba lokacin da baƙonki yazo ba?.” Ta kalle shi ta ce, “na san ba zaka dawo
ba saboda ranka a ɓace yake sosai, Yanzu ka zauna kaci abinci.”
“Bana son cin komai.”
“Ko abincin rana baka ci ba na san kuma kai ba mai son abincin waje bane, ka zauna
na kawo maka awara nayi maka da kaina.”

Jin yadda take magana murya a sanyaye sai ya ɗago ido ya kalle ta ta ƙaraso inda
yake ta ce, “ka zauna don Allah, ba don ni ba.” Ba shi da mafita dole ya zauna ta
wuce kitchen sai gata ta dawo da lafiyar jollof rice da kuma ƙaramin plate na awara
ta ajjiye masa. Kallon shinkafar ya yi ya ce, “bazan ci shinkafa ba, wannan ya isa”
ya faɗa yana ɗaukar ƙaramin plate ɗin awarar ya riƙe a hannunsa ya ɗora ƙafa akan
ɗaya.”

Fara ci yayi kusan mintina biyar kafin ya kalle ta ya ce, “Amma ya yi daɗi sosai,
kuma babu yaji.” Didi tayi murmushi ganin ya sake ta ce, “na san baka son yaji ai
shiyasa sauce ɗin ma babu abinda zai saka ta yaji.” Kai ya girgiza cikin izza da
ƙasaita ya kalle ta ya ce, “ina jinki.”

Didi ta ce, “Kamar yadda kaji sunansa haka sunansa yake, ma’aikaci ne ya taɓa aure
amma basa tare da matar. Kuma alamunsa ba da wasa yazo ba gaskiya.” Ya girgiza kai
ya ce, “haka ake so. Yanzu ya maganar ta tsaya?.” Ido ta zuba masa sannan ta ce,
“ka san ba ni zan bayar da kaina ba ko? To na tura shi wajan Kawu.”

Cak ya dakata da abinda yake yi ya kalle ta suka haɗa ido tayi sauri ta ce, “babu
yadda na iya ne, ya nemi ganin dangin babana dole na yi masa kwatancen

10 / 28