Author : NANA HALEEMA Category : Complete Novels
tayi shiru amma Allah ya sani ya yi bala'in burgeta, haka
kawai taji tana so ta ganshi ko da kuwa zai yi mata tsawa.
Hajja ta sake kallon ta taga sai murmushi take yi ta ce, "Wai murmushin ne har
yanzu?." Nayla ta ce, "wani abun na gani a wayar." Hajja ta ɗauke kai sai Nayla ta
ce, "Hajja an ce Didi ma tayi rashin lafiya, bara naje na duba ta." Hajja ta kalle
ta ta ce, "Keda bakya son shiga gidan?."
"Hajja ai lalura ce kuma tana da kirki sosai."
"Ki jira Salma ta dawo sai ku je."
"A'a Hajja, kamar wata baƙuwa?, bara naje dai" ta faɗa tana ɗaukar hijjabi ta saka,
ta ɗauki wayarta fita Hajja ya bita da kallon mamaki.
*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.
Nana Haleema❤️
*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025
©️*Nana Haleema.*
Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.
https://www.tiktok.com/@nanahaleemawriter?_t=ZS-8zaZqblsrGp&_r=1
*Book 1*
*P 14.*
Nayla sai da tazo ƙofar gidan Didi sai kuma gabanta ya faɗi matuƙa, ta runtse ido
tare da ajiyar zuciya ta shiga gidan da siririyar sallama. Yana tsaye a tsakar
gidan dube-dube da alama akwai abinda yake nema, jin anyi sallama ya juya kai tsaye
suka haɗa idanu da Nayla.
Sanye yake da riga mai siririn hannu kamar singlet amma tafi singlet girma da rufe
jiki. Sai dogon wando mai jikin Damisa dan sai ka ɗauka da fatar Damisa aka yi shi.
Murɗaɗen jikinsa duk a bayyana haka farar fatansa a bayyane take tana ɗaukar ido,
ga wanda bai san shi ba dole in yaga fatarsa sai ya tsaya yana kallo saboda
haskenta.
A cikin sakan biyar ta ƙare masa kallo har lokacin kallon ta yake yi duk da tana
jin tsoro amma ta daure ta ce, "ina kwana." Bai amsa ba bai kuma daina kallon ta ba
yana mamakin wannan yarinya da shegen naci take, bata jin magana duk da ya yi mata
warning bata daina zuwa gidan ba.
Janye idanunsa ya yi bai ce komai ba, jin bai amsa ba sai ta ce, "Didi tana nan?."
Nan ma yayi mata banza sai jikinta ya ɗan yi sanyi, daman gashi a tsorace take
dashi gashi yayi mata banza. Kallon inda take ya yi yaga tana tsaye ya ce, "in zaki
shiga ki shiga, in fita zaki yi ki bani waje!" Ya faɗa da ƙarfi bata san ta wuce
shi a guje ba sai sautin tsakinsa taji tayi ajiyar zuciya.
Bata tarar da Didi a falo ba sai ta zauna kamar munafuka ta kasa sakewa, motsin
shara taji ana yi sai ta miƙe ta kalli window ga mamakin ta shine yake share gidan
a nutse, sai ta tsaya tana kallon sa tana murmushi wanda bata san tana yi ba. Didi
da ta fito ta ga Nayla na kallon window sai ta yi murmushi tana daga bayanta ta ce,
"Nayla." Firgigit tayi ta kalli Didi ta ce, "Didi yaushe ki ka fito?."
"Ta ya zaki san lokacin da na fito kina kallon mutumin ki yana shara? Ya baki
mamaki ko?" Ta faɗa suna zama a kan kujera. Nayla sai taji nauyi kallon sa da ta
tsaya yi amma bata nuna ba ta ce, "Sosai ma kuwa, kawai ji na yi ana shara sai na
leƙa ashe shine, kawai sai na tsaya ina kallonsa."
Didi tayi dariya ta ce, "ai dole ki tsaya, In ya so ya ga dama shi yake yin komai a
gidan nan hatta girki, har inda na kwanta shine zai gyara kuma baza ki ce namiji ne
ya yi ba. Amma in bai ga dama ba abinda ya ci abincin ma ni zan ɗauke." Nayla tayi
murmushi tana kallon Didi ta ce, "shi dai sai ka rasa ka gane wanne iri ne, in ya
yi gabas sai ya karkace."
Didi ta ce, "shiyasa nake faɗa miki yana da kirki fiye da tunaninki, yana da hira
sosai. Kawai bashi da saurin sabo ne kuma baya son baƙi kwata-kwata."
Nayla daɗi take ji a zuciyarta ana hirar Omar hakan ya saka ta sake gyara zama ta
ce, "ina fa kirki a nan Didi, har gaishe shi nayi yayi min banza." Didi ta ce,
"bazai amsa ba ai, in kinga ya amsa to tabbas kun sana dashi matuƙa. Naga alama dai
tsoron na sa ya ɗan ragu a zuciyarki."
Nayla ta ce, "hmm ina fa, wallahi akwai daurewa nayi nazo na gaishe ki, kwana biyu
kin yi rashin lafiya." Didi tayi dariya ta ce, "ai kuwa na gode sosai Nayla, Naji
daɗi matuƙa Allah ya bar zumunci." Nayla ta amsa da amin amma a zuciyarta kawai so
take a cigaba da zancen Omar. Ƴar hira Didi take janta da ita akan labarin mutanen
Kaduna da Hajja tana amsa mata da lafiya kowa yake.
Shigowarsa suka gani ya canja kaya zuwa jeans blue da farar riga mai layi-layi a
jikinta, riga ta mai dogon hannu ce, sai ya tattare hannun rigar zuwa guiwarsa
hannun, farin hannunsa da gashin da yake a kwance a hannun ya bayyana sosai, hakan
da yayi sai ya ƙara masa kyau sosai. Nayla kallon sa take yi kawai cikin burgewa,
daga sama yana da faɗi duk da ba faɗi sosai ba, amma daga ƙasa ɗan ƙarami dashi
kuma a tsuke kana ganin sa kaga halittar cikakken namiji jarumi.
"Ina zuwa haka Alhaji Omar?." Didi ta tamabaya tana kallon sa da murmushi. Ya kalle
ta bayan ya ɗage gira ya ce, "Yaushe ki ka fara sanin inda zan je?." Tayi dariya ta
ce, "abin ne da mamaki, naga ƙarfe sha biyu ma bata yi ba ka shirya. Ko wajan
yarinyar nan zaka je?." Agogo ya kalla ya ce, "A'a sai anjima."
"To ina zuwa ko abinci baka ci ba?."
"Bana son cin komai, zan je wani waje wataƙila bazan dawo ba sai dare." Didi ta
girgiza kai ta ce, "Allah ya kiyaye Alhaji Omar Faruk." Murmushi ya yi yace,
"Amin."
Murmushin da ya yi shine ya saka narkar da Nayla a kogin kallonsa har bata san ta
tallafi haɓar ta tana kallonsa ba, ya gama tafiya da ita daga shigarsa, da
maganarsa, uwa uba murmushin da yake sakawar Didi.
Sai da ya fita sannan ya kalli Didi taga tana neman wayarta sannan ta miƙe ta ce,
"Didi bara na koma." Didi ta ce, "da wuri haka? Na ɗauka sai anjima." Nayla ta ce,
"zan dawo anjima in sha Allah, ai yanzu na rage tsoronsa." Didi tayi dariya ta sake
yi mata godiya ta raka ta har waje sannan ta dawo.
Nayla sai da ta tsaya a gate ɗin gidan Hajja ta dinga sauke ajiyar zuciya. Namiji
mai murɗaɗɗen jiki irin na sa sam basa burgeta, hasalima itace mai kushe duk wani
namiji mai irin wannan jikin, bata ƙaunar su tafi son namiji mai normal jiki ba
wannan murɗewar ba. Wannan halitta tana daga cikin dalilin da ya saka bata so ace
Abbas yana sonta, dan ta san baza ta so shi ba saboda jikinsa dan shi ya fi Omar
murɗewa. Amma yau Omar ya burgeta, ya tafi da imaninta fiye da tunanin ta har
mamaki abin yake bata. Har hango kanta take yi ta kwanta a ƙirjinsa tana hasahen
wanne irin yanayi zata ji a wannan lokacin.
Da ta rufe ido murmushinsa take gani, sau biyu kenan taga yana murmushi, hakan ya
shiga cikin tarihin ta dan tun daga murmushin farko da ta gani ya yi komai ya
canja, faɗuwar gaban da take ji akansa ta canja salo zuwa harbawar zuciya a duk
sanda tayi araba dashi. A haka ta shiga gidan zuciyarta na bugawa sossi.
Shi kuwa Omar yazo zai fita sai kiran Sen ya shigo wayarsa ya ɗauka yana
shiga ɗakin sayana amsawa. Gaisawa suka yi Sen ya ce, "Tiger Narma ta faɗa min duk
abinda ya faru jiya, gaskiya i'm so proud of you, naji daɗin taimakon da ka yiwa
Narma sosai." Omar ya ce, "babu komai. Amma ka ja mata kunne Kano ba Abuja bane,
akwai masu ƙwace sosai wanda za su yi mata illa ma kafin su ƙwace ɗin. Ta kula in
zata fita ta daina kaiwa dare, in ta kai dare ma kar ta sake ta tsaya a ko ina.
Allah ne ya taimaka da har motar zasu ƙwace musamman in suka lura da bata san gari
ba."
Sen ya ce, "ai ganganci ne irin nata, na faɗa mata duk inda zata je ta kira ka amma
bata ji." Omar ya ce, "tafiyar mu baza ta zama ɗaya ba, ni bana son ɓata lokaci ko
kaɗan, kuma dai yanayinta bai yi daidai da nawa ba." Sen ya ce, "kar ka damu yanzu
ta fahimci abinda nake nufi." Omar ya ce, "babu komai."
"Yau zata je biki zata kira ka."
"Allah ya kaimu."
"Amin. Akwai saƙonka na kyautatawar da ka yi mata jiya, naji daɗi sosai."
"Na gode" ya bashi amsa a taƙaice kafin Sen ya kashe wayar.
Ɓangaren Narma a daren sai da tayi mafarkin Omar, da ta farka sai kawai ta
ɗauka taimakon ta da ya yi ne ya saka haka. A haka ta tashi ta shirya dan a ranar
zasu fara bikin Samra. Ƙawayenta guda uku ne suka zo gidan, ganin hannunta a ɗaure
suka dinga yi mata sannu kafin ta sake a fara hira.
Da wuri mai kwalliya tazo aka fara yi musu kwalliya, sai da aka yiwa duk ƙawayenta
sannan aka yi mata a lokacin an idar da magriba. Narma tayi kyau cikin ankon kamu
dukkan su dogayen riguma suka yi marasa kama jiki, amma Narma fitted gown tayi
wacce ta kama ta matuƙa, sannan saman rigar gabaɗaya net ne a jiki ana ganin
jikinta.
Ganin yadda tayi kyau duk suka ruɗe suna zugata ita kuma tana jin daɗi tana fari da
idanu. A lokacin Ashraf ya zo gidan haɗa ido da ya yi da Narma ji ya yi kasala ta
saukar masa lokaci ɗaya, ya haɗɗiye yawu ya bita da kallo ya ce, "Beb ke ce?."
Gira ta ɗaga masa ya ce, "you look so magnificent." Mursmushi tayi ya matso aka
fara yi musu hotuna masu kyau.
Ashraf ya ce, "Amma dai ni zan kai ki ko?." Narma ta ce, "Dad ya ce Tiger ne zai
kai ni."
"Tiger again?."
"Yes, sai dai mu haɗu a can." Ya girgiza kai ya ce, "Okay normal, sai mun haɗi
din." Daga nan suka yi sallama ya fita su kuma suka fara sallar i'sha. Narma dai
sai da ta cire rigar gabaɗaya sannan ta iya sallah bayan ta idar ta mayar.
A cikin ƙawayen ta wacce suke kira da Safna itace babbar ƙawar Narma, ta kalle ta
taɓe baki ta ce, "Narma ya kamata ki daina wannan ɗinkin fa, yanzu an daina wannan
matsewar musamman ke da kike da halitta irin wannan."
Narma ta ce, "kina da matsala Safna, to in ban nuna halittar da Allah ya yi min ba
meye amfanin ta?."
"Ki adana sai ki yi kwalliya a gidan mijinki."
"Ke baki ga yadda Ashraf ɗin ya ruɗe da ya ganni haka ba? Da iya surata nake sake
kama zuciyarsa. Kuma in bai ga abinda nake dashi ba ta ya ya zai yi mararin
aurena?."
Safna ta ce, "amma hakan ba daidai bane, wannan shigar zata iya jawo miki abinda ba
kiyi tunani ba Narma. Ina yawan faɗa miki wannan maganar amma bakya ji, su Nasreen
su daina zugaki, wallahi cutar ki suke yi. Da wannan shigarta ki babu lallai ki
samu wanda zai aure ki saboda Allah."
Gabaɗaya suka yiwa Safna can akan abinda ce ita dai tayi musu banza suka ƙaraci
surutun su. Ɗaya daga cikin su da ta fita ta shigo yana cewa, "Nass yanzu da
bouncers ki ka dawo yawo?." Narma ta ce, "a ina?."
"Gashi nan" ta faɗa tana nuna musu Omar ta window wanda ya ke tsaye yana amsa waya.
Narma ta kalle su ta ce, "shine Tiger fa, na san kin san sunan na sa ko?."
"Ni kuwa na san sunan, ban dai san fuskarsa ba amma na san sunansa ko ɗazu media
akan maganarsa ta yamutse."
"Yes shine. Ai na baku labarin abinda ya faru jiya, shiyasa Dad yake so ya dinga
kai ni duk inda nake so."
Safna ta kalle shi ta ce, "amma kin cuce shi, a ina ya yi kama da bouncers don
Allah? Ki ga mutum ɗan daidai dashi ki haɗa shi da waɗanan jibga-jibgan halittar?."
Suka yi dariya gabaɗaya Nasreen ta ce, "Gaskiya dai ta cuce shi, wannan ai ko rabin
bouncers bai kai ba, yanayin jikinsa ma sha Allah."
Safna ta ce, "kuma gashi bai yi kama da yadda ake faɗarsa ba. Kalle shi fa fari
kyakykawa mai zubin buzaye." Nass ta ce, "ni kaina mamaki nake yi anya kuwa ɗan
daba ne kamar yadda ake faɗa?. Amma jiya na gani da idona." Narma ta sake cewa, "mu
je mu tafi, ɗan rainin hankali ne yanzu sai na neme shi na rasa." Ɗaya daga cikin
su tace, "Dan ya raina miki hankali?." Nasreen ta ce, "baki yi maganinsa bane." A
haka suka fito harabar gidan ko wacce ta sha makeup kuma duk sun yi kyau.
Dukkan su da mota suka zo, ko wacce ta shiga motarta suka fita ita kuma ta shiga
bayan motar. Bai ce komai ba ya buɗe mazaunin gaba ya shiga ƙhamshin turarenta ya
sake kai amsa ziyara a hancinsa. Kamar zatayi masa magana sai ta kasa shi kuma yana
so yaji inda zasu je.
Narma da ta fahimta sai ta faɗi sunan event center ɗin da location ɗin, bai ce mata
komai ba ya kunna motar suka fita. Kallon gefen fuskarsa ta samu kanta da yi yana
kallon gabansa hankali kwance fuskar sa babu fara'a ko kaɗan.
"Na gode" taji bakinta ya furta ba tare data sani ba. Kamar bai ji ta ba haka ya
yi, ya cigaba da tafiya har suka zo inda ta ce kafin a buɗa masa gate ya shiga ta
fito daga motar.
Har zata wuce taji ya ce, "zaki gama yaushe?." Kallonsa tayi suka haɗa ido ta ga
fuskarsa babu alamun wasa ta ce, "nan da two hours." Bai sake cewa komai ba ta
tsaya tana kallonsa ganin hakan sai ya kalle ta sai ta wuce shi ta shiga ciki.
Samun kansa ya yi da kallon ta tana tafiya, ya yi saurin janye idanunsa jin baƙon
yanayi ya na kawo masa ziyara.
Bai zauna a wajan ba fita ya yi ya koma gida a yadda ya lissafa ƙarfe goma kenan
zasu gama. Ƙarfe goma da wani abun kuwa ya dawo ya samu ƴan mata suna ta fitowa
ƴaƴan manya kai da ka ga yaran ka san yaran masu kuɗi ne manya ba ƙananu ba. Hango
ta ya yi tana tahowa tana dariya gefen ta Ashraf ne shima dariyar yake yi.
Dauke kai ya yi ya kawar da fuska daga kallon ta ya lumshe ido, ido ya sake buɗewa
a lokacin ta zo wajan, kallon motar tayi ta gane ta sai ta ce, "Ka je kawai zamu
tafi da Beb." Kallon baki da hankali Omar ya yi mata ya kalli Ashraf da shima shi
yake kallo yana mamakin daman wannan ne tiger ɗin.
Narma ta sake cewa, "ka je kawai." Wani irin kallo yake mata alamun bazai ma yi
magana ba ganin hakan Ashraf ya ce, "kai ba Drivern ta bane? To ta ce kaje zan
kaita ka tafi mana." Kallon Ashraf ya yi bai ce komai ba dan bashi da lokacin sa.
Narma ta ce, "ƙyale shi Beb, mu je ka kai ni na gaji....." bata ƙarasa ba maganar
ta maƙale jin ya ce, "Ko ki zo ki shiga ko na ɗauko ki."
Mamaki suka juya suma kallon sa ganin kamar ba shi ya yi maganar ba, ya ɗago ido
yana kallonta ta ƙasan ido ya ce, "bana son ɓata lokaci, ki zo ki shiga ina da
abinda zan yi. Ni ba ɗan aikin ki bane da zaki ajjiye ni ina yi miki magana kina
yin banza ba!." Yadda ya yi maganar a kausashe ya saka Narma ta ɗan ji tsoro amma
ganin Ashraf na wajan sai ta danne ta ce, "ba fa zan shiga ba, a motar mijin da zan
aura zan tafi."
Ashraf ya ce, "malam ka tafi daman ai aikin ka kenan ko? To Narma tace bata so ba
sai ka ƙyale ta ba?." Kallon Narma ya yi yana cize baki ya sake kallon Ashraf ya
ce, "in na sake magana ka saka min baki sai kayi dana sani. Wallahi sai na saka ka
haɗɗiye haƙorinka."
"Me zaka yi?." Omar bai bashi amsa ba dan yadda yake jin zuciyarsa zai iya karya
shi wallahi.
Fitowa ya yi daga motar ya matso kusa dasu ya ce, "ka sake yin maganar zaka ga
abinda zan yi. Ke kuma kafin na irga uku ki shiga mota in ba haka ba wallahi sai na
mare ki!" ya faɗa yana nuna ta da yatsa idanunsa a waje. Tsoro ya bayyana a tare da
ita bata san ta buɗe motar ta shiga ba ya bar Ashraf a wajan ya shiga motar suka
fita.
"Wai kai meye haka ne? Ina ruwanka da ni, bani nace ka bari ya kai ni ba?. Biyan ka
ake yi, ina da ikon da zan ce bana son abu kuma dole ka yi min. Haba duk kabi
takura min, ni wallahi na gaji." Tsayawa ya yi ya jiyo yana kallon ta kafin ya duƙa
ƙasa ya ɗauko wata wuƙa mai madaidaicin girma, ya buɗe motar ya fito ya buɗe bayan
motar inda take ya saka mata wuƙar a wuya kamar yadda ya yiwa Nayla ya ce, "in kika
sake yi min magana wallahi sai na yi miki illa. Ni zaki dinga yiwa ihu? Sa'an ki ne
ni?."
Ɗiff Narma tayi tana tuna yankan jiya ma taji azaba balle ya yanke ta a wuya.
Kallon idonsa take yi yana kallon nata ya sake cewa, "in kika sake magana wallahi
da ƙafa zaki koma, In na yi rantsuwa bana karyawa, ki kiyaye ni duk lokacin da na
ce wallahi!."
Shiru tayi bata ce komai ba yaja tsaki ya ce, "stupid girl" ya faɗa yana barin
wajan ya sake komawa motar ya ja motar suka tafi. Har suka je gıda Narma bata ce
komai ba a tsorace take dashi ko motsin kirki ta kasa, ya buɗe motar ya fita ya
barta a cikin motar bai sake kallon inda take ba ya fita daga gidan.
Narma haka ta koma gidan jikinta duk a sanyaye a daren ta kira Dad ta faɗa masa
abinda ya yiwa Ashraf sannan ta kwanta amma zuciyarta cike yake da tunaninsa, wai
wanne irin ƙarfin guiwa yake da ita haka?. Da wannan tunanin bacci ya ɗauke ta.
Shi kuwa Omar yana komawa text ya rubutawa Sen dan wallahi ya cigaba da zama
inda Narma take bai dan adadin abinda zai aikata mata ba, gwara kawai su nemi wani
shi kam ya gaji.
Sen yana ganin text ɗin sa ya kira shi ya faɗa maaa abinda ya faru shi kuma ya nuna
jin daɗin sa akan hakan, dama amfanin kula da ita ɗin kenan, kuma shi Omar bai san
Ashraf ba dole a samu damuwa in ya gansu