Advertisements
Chapter 12 Reading KIRAN RABO BOOK1 CMPLT BY NANA HALEEMA BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

KIRAN RABO BOOK1 CMPLT BY NANA HALEEMA

Author :  NANA HALEEMA Category :  Complete Novels

Chapter   12 / 28

33K to 36K   out of 83.2K words

ba balle ya saka ran dashi ta ke, ta sake cewa, "da kai nake."

Nan ma Omar bai kalle ta ba sai ma cigaba da tafiya da yayi, mai gadin da yake
zaune a cikin masallacin ya taso da sauri ya tari Omar ya ce, "Abokina magana
Hajiya take maka." Omar ya kalle shi ya ce, "magana?."
"Eh, gata can tana magana."
"Ba da ni take ba." Muryar Narma ya ji a bayansa ta cewa, "Waye kai ina yi maka
magana baza ka amsa ba?." Nan ma bai motsa ba balle ya kalle ta.

Shan gabansa tayi tana kallonsa daga sama har ƙasa ta ce, "ba kai ne Tiger ba? Kana
ji ina yi maka magana zaka yi min banza waye kai?." Ganin yayi shiru bai amsa ba ya
dai zuba mata ido har hakan ya saka ta janye idanunta ta ce, "charger zaka je ka
siyo min yanzun nan, ka bar shiga masallacin ka je ka siyo min."

_Tashin hankali, haka za a yi da yarinyar nan?, ni zata tsayarta ce zata aika? Ni
take yiwa tsawa? Lallai kafin na gama aiki da ita sai dai a kai gawar ta Abuja._
Abinda yake aiyanawa kenan yana ƙare mata kallo cikin ɓacin da ya baya bayyana akan
fuskarsa.

Ta buɗe baki zata yi magana ya ce, "in kika sake yi min magana sai na yi ball dake
a wajan nan, sa'anki ne ni ko yaron ki ne..? bani waje!?" Ya faɗa da tsawa idanunsa
na waje yana kallon ta.

Narma bata san ta daka tsalle ta koma gefe ba sai sautin tsakinsa ta ji ya shiga
masallaci yana ayyana dole ma ya kira baban yarinyar nan bazai juri wannan shirmen
nata ba, ko ya ajjiye aikin da ya karɓa ko a wayi gari yayi mata illa.

*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.

Nana Haleema❤️

*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025

©️*Nana Haleema.*

Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.

*Book 1*
*P 10.*


Narma suman tsaye tayi ta bishi da kallo cikin faɗuwar gaba, ba a taɓa yi mata
tsawa ba sai yau, tsawar ta ratsata sosai shiyasa bata san ta koma gefe ba. Sai da
ta dawo hankalinta ta kalli ma'aikatan gidan ta ga kowa kallon ta yake yi rai a
ɓace ta wuce cikin gidan a guje. Tana shiga babban falon gidan ta ɗauki waya hannu
na rawa ta kira mahaifinta.

Yana ɗauka kafin ya yi magana ta ce, "Dad waye wannan ka haɗa ni dashi? Dad tsawa
fa yake yi min ina yi masa magana yayi min banza. Kuma tun airport ko sannu da zuwa
bai yi min ba, kamar ma bai san ya ɗauko ni a mota ba. Gaskiya Dad bazan jure zama
da wannan mutumin ba na gaji."

Senator da yake sauraren ta sai da ta gama ya ce, "ƙyale ni dashi zan kira shi
yanzu a waya, kin sauka lafiya?." Da shagwaɓe ta ce, "lafiya lau Dad. Charger na ce
ya siyo min na bar tawa a gida kaga yadda ya yi min tsawa kamar ni ce nake aiki a
ƙasansa? Babban abin ɓacin ran a gaban maids ɗin gidan nan. Gaskiya Dad i can't
toleret this kind of nonsense." Dad ya ce, "don't worry my dear, zan kira shi
yanzu."
"And let him come and say sorry to me Dad." Senator ya yi murmushi ya ce, "hold on,
i'm coming." Kashe wayar tayi ta nemi waje zauna tana lissafa kalar wulaƙancin da
zata yi masa.

Omar kuwa tun yana sallah yake jin kiran waya na shigowa wayarsa, bai
katse sallar ba sai da ya idar sannan ya duba wayar ganin mai kiran sai yayi
ƙaramin tsaki ya taso ya fito daga masallacin. Car park ya ƙarasa, daga gefe akwai
madaidaiciyar gazebo ta shan iska da kujeru a ciki nan ya shiga ya zauna, yana zama
wayarsa ta ɗauki ƙara ya ɗauka ya saka a kunne.

Daga can ɓangaren Sen ya ce, "Tiger." Omar ya amsa suka gaisa kafin ya ce,
"Tiger Narma ta kira ni ta ce kayi mata tsawa dan ta ce a siyo mata charger." Omar
ya ce, "ba ɗan aiken ta bane ba ni, haka zalika ni ba yaron ta bane. Saboda kai na
karɓi aikin nan, kai ta wajan da take so shine abinda ka ce zan yi, amma ba wai dan
ta saka ni a gaba tana yi min ihu ba. In a haka za a tafi gaskiya zan ajjiye aikin
nan sai a samo wani, ni bazan jure ba."

Senator ya ce, "bata san waye kai bane shiyasa, Amma zan mata magana za a samu mai
yi mata aike da siyo mata abinda take so, kai dai kai nake so ka dinga kai ta inda
zata je." Omar ya ce, "bazan dinga zama a nan ba gaskiya, zan dinga tafiya in zata
fita sai ta sanar dani nazo na kaita." Senator ya ce, "Daman ni abinda nake so
shine ka kaita ka kula da lamarinta a duk inda take." Omar ya yi shiru Sen ya ce,
"ina zuwa" ya faɗa yana yanke wayar.
Omar yana nan zaune bai san me ya faru ba sai yaga Yahya wanda suka rabu ya dawo ya
shiga gidan ba jimawa ya dawo ya hau mota ya fita. Taɓe baki yayi dan a kaf duniya
bai ga macen da zata aike shi ba in dai ba Didi ba. Tsabar raini shi zata dinga
yiwa tsawa ta ɗauka shi yaron ta ne?. Bai jima sosai a zaune a wajan ba kawai ya
tashi bayan ya bawa Yahya key ɗin motar da ya bashi ya fita daga gidan.


A can Abuja kuwa Dad yana yanke wayar Mum ta kalle shi a fusace ta ce, "ni fa tun
asali ban so ka haɗa riƙaƙƙen ɗan daba da ƴata ba, ta ya ya za a ce kaf jami'an
tsaron da suke Kano ka rasa da wanda zaka haɗa ta sai da ɗan daba?. Waye shi da zai
mata tsawa har yake ganin yafi ƙarfin ta aike shi? Ba a ƙarƙashin ka yake ba?."

Nabil da yake zaune shima rai a ɓace ya ce, "abinda zan ce kenan Mum. Ta ya zai
mata tsawa har kuma Dad ka biye masa ka ce wai in zata yi aike ta aiki Yahya? Kenan
shi ya fi ƙarfin ta aike shi ko me?. Gaskiya Dad wannan ba wanda za a zauna dashi
bane, ina bayan Mum ka salleme shi kawai a tura mata wani ya dinga kaita duk inda
yake so. Wani ƙazami dashi har yana da bakin da zai ce wai baza ta aike shi ba?
Waye shi?."

Mum ta kuma ɗora da cewa, "ba kowa bane face ɗan iska gari na banza da wofi,
matsayin numfashi su ma ba ɗaya bane amma Dear ya saka tana shaƙar gurɓataccen
numfashinsa a mota ɗaya. Tsakanin ta dashi shine mahaifinta ya biya shi ya ne ya
tayar da hayaniya a wajan zaɓe da sauran su, amma matsayin ya haɗa mota ɗaya da
Narma sam-sam bai tashi ba."

Dad yayi murmushi yana kallon su ya ce, "na fi ku tsanar kusancin da ya samu da
Narma saboda bashi da wannan matsayin kuma bazai taɓa samun sa ba har abada.
Tsakanin Narma dashi kamar tazarar sama da ƙasa, turaren da Narma take sakawa sai
ya siyi danginsa kaf balle kuma agogon da take ɗaurawa a hannunta. Ban haɗa shi da
Narma dan ya yiwa Narma wani abun ba, na haɗa ta dashi ne na ɗan lokaci saboda
lafiyar ta da zaman ta lafiya a Kano. Ke kin san wancan lokacin abinda ya faru da
ita, tare musu hanya aka yi ana ƙoƙarin saceta in ba dan Allah ya tsare ba da yanzu
wataƙila bata gidan nan. Shi kuwa kaf kano a san shi, in baka san shi ba ka san
sunan shi, ana faɗar sunansa shikenan duk iskancin da ka ke ki dashi ka ajjiye.
Saboda haka kawai na bashi Narma ya dinga kai ta duk inda zata je, in ba dan haka
ba haɗa ido ma bai kai matsayin da Narma zata yi dashi ba."

Nabil ya ce, "Amma Dad akwai police a Kano da zaka ɗauka a haɗa ta dasu ta je duk
inda take so, suna da bindiga shi kuwa bashi da ita, sun san aikin su shi kuwa me
ya sani ban da wasa da wuƙa?. Gaskiya Dad ban ji daɗi ba, wani ƙazamin bagidaje
dashi har yana da zarrar da kana yi masa magana yana cewa wai zai ajjiye aikin
saboda baya son raini? Just Imagine, wani banza shashasha talaka ne yake faɗawa ƴar
senator haka."

Dad ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "kar ka damu Nabil na san abinda nake yi, kar ka
samu damuwa, wani lokacin yawo da irin su Tiger yafi amfani akan yawo da police. Na
san abinda nake yi fa kar ka samu damuwa." Mum dai kawar da kai tayi zuciyar ta
cike da haushin wannan hukunci na senator, gashi wani banza talaka yana wulaƙanta
mata yarinya.

Wayar Narma ce ta sake zuwa ya ɗauka ya saka a speaker muryarta karaɗe falon
ta ce, "Dad zan fita da daddare amma an sanar dani ya fita, Dad i'm so done with
his attitude, Ko 24 hours ban yi ba ya fara bani cikon kai? Gaskiya i can't." Dad
ya ce, "whice time you want to go?."
"By 8."
"Alright, i will let him know, i will send you his number in kina son fita ko
yaushe you can give him a call." Narma ta ce, "Dad what's so special about this guy
that you're willing to share my contact info with him?."Dad ya ce, "kar ki damu"
abinda ya ce kenan ya yanke wayar yana kallon irin kallon da su Mum suke masa amma
bai kula su ba dan shi kaɗai ya san amfanin Tiger su baza su gane abinda yake nufi
ba shiyasa.

Shi kuwa Omar ko da ya bar gidan a napep ya koma unguwar su ya sauka a
bakin layin ya shiga ciki a ƙafa. Babu wanda yake yiwa magana kamar yadda babu mai
yi masa magana tafiya kawai yake yi cikin takun isa da ƙasaita da nuna zallar izza.

"Ummaru wucewa zaka yi? To na gode." Kallon inda aka yi maganar yayi yaga Hajja da
hijjabi zata shiga gidan ta da alama dawowar ta kenan daga wani waje. Zai yi magana
ta ce, "in baza ka shigo mu gaisa ba na gode" ta faɗa tana shiga cikin gidan.

Shi fa wallahi baya son shiga gidan mutane, ga Hajja yana ganin kırkinta da
mutuncinta amma shi gabaɗaya baya son shiga gidan. Ƙaramin tsaki ya yi ya shiga
gidan fuskarsa a ɗaure ya yi sallama a car park ɗin gidan. Nayla da ta ji sallama
ta amsa tana juyowa ido ta ya faɗa cikin nasa, bata san ta saki tea flaks ɗin da
yake hannunta ba sai sautin fashewar kwalba tayi.

Ido ta wara waje tana kallonsa shi kuma kallon sencond biyar ya yi mata ya ɗauke
kai ya jiyo muryar Hajja tana cewa, "Ummaru shigo mana." Shiga falon ya yi Hajja
tana cewa, "na ɗauka ai baza ka shigo ba, ko gaishe ni ɗin da ka ke yi yanzu ka
daina."
"Ina yini" ya furta a taƙaice ta amsa ta ce, "lafiya lau Ummaru, ya gida?."
"Lafiya" ya amsa a taƙaice yana kallon ƙasa.

Hajja ta ce, "Hauwa'u filas ɗin shayin ki ka fasa? Naji ƙarar fashewar kwalba. Ki
saka shi a shara kawai, Allah ya sa baki ji ciwo ba" Hajja ta faɗa yadda Nayla zata
ji.

Maganar da Hajja tayi ne ya dawo da ita hankalinta, ta ɗauki flakas ɗin ta saka a
shara ta taho a hankali zata shiga falon shi kuma zai fito. Ɗifff tayi ta ja
numfashi mai nauyi, ƙiris ya rage ƙirjinsu ya haɗu waje ɗaya, ya kalli fuskarta na
wasu sacanni murya a can ƙasa ya ce, "ki ƙauracewa ganina" abinda ya ce kenan tayi
saurin yin baya shi kuma ya fita yana ji Hajja tana yi masa magana.

Nayla ta shiga tana sauke ajiyar zuciya ta ce, "na shiga uku, Hajja daman
yana shigowa gidan nan?." Hajja ta ce, "yana shigowa mana." Nayla ta ce, "Allah ya
taimaki Salma da take bacci bata ganshi ba, wai har da ce min na ƙauracewa ganinsa.
Ni dai ban san ƙaddarar da take haɗa mu ba wallahi, gabana sai faɗuwa yake yi."

Hajja ta ce, "shiyasa ki ka fasa min filas ɗin shayi ai, sai ki kira babanki Daddy
ya bayar a kawo mana sabo saboda gobe zaki azumi." Nayla dai numfashi take sauke a
hankali, abinda yake bata mamaki faɗuwar gaban da take ji ba ta tsoro ba ce kamar
wacce take ji farkon haɗuwarsu, muryarsa take ji a kunnenta tana hango yadda
ƙirjinsu da ya kusa haɗewa da na juna. Lumshe ido tayi ta buɗe a bayyane ta ce,
"Allah mai iko." Hajja ta kalle ta sai tayi tsaki ta cigaba da kallon tv tana
kallon tashar saudia.

Omar yana shiga gidan a tsakar gidan ya samu Didi ta juyo tana kallon sa
ta ce, "shigowa ba sallama kuma Omar?." Bai amsa mata ba ta kalle shi ta ce, "ina
kaje ne?." Bai ce komai ba ya shiga falon ya zauna, itama bata bi bayan sa ba sai
da ta gama abinda take yi sannan ta shiga ta samu yana cin abinci.

Bata yi masa magana ba har ya gama dan ta san shi ba mutum ne mai son yin magana in
yana cin abinci ba, sai da ya sha ruwa ya sauke numfashi kaɗan sannan ta kalle shi
ta ce, "ina ka je?." Kallon ta yayi ya tashi zaune sosai ya ce, "na fara wani aiki
ne, amma ina ganin dole na ajjiye shi kafin na shaƙe yarinyar." Didi ta ce wanne
aiki ne?."
"Zan faɗa miki, na karɓi aikin saboda ke ne kawai, na san aikin zai kawo kuɗi sosai
ga hidimar bikin ki tana zuwa."
"Waye ya ce maka hidimar bikina tana zuwa?."
"A jikina naji hakan."
"Allah ya sa. Amma ka faɗa min wanne irin aiki ne?."

Bai ɓoye mata ba ya faɗa mata komai da kuma wacce aka haɗa shi da ita, ya ɗora da
cewa, "ni wai yarinyar nan zata yiwa tsawa" yayi wani murmushi ya ce, "ko babanta
bana tunanin zai yi min tsawa na ƙyale shi balle ita, a kaf duniya ke kaɗai zaki
aike ni naje bayan ke babu wata halittar."

Didi da ta saki baki tana kallon sa cikin mamakin da ya sumar da ita a wajan ta ce,
"Omar Senator Sagir ɗan takarar gwamnan Kano kuma sanata mai ci yanzu! Omar Meyasa
ka kai kanka irin wannan wajan don Allah?. Na san halin ka baka da haƙuri ko kaɗan,
kar zuciyarka ta kai ka ga aikatawa yarinyar nan wani abun na shiga uku."

Ya kalle ta ya ce, "kema kin san bazan ɗauki raini ba ai ko? Kuma bazan ɗauki
iskanci ba. Ko Wacece ita daidai nake da ita wallahi, dan ubantq sanata ne hakan
bazai hana na tsaga mata fuska ba da aska ba. In ta ja mutuncinta zamu zauna
lafiya, in bata ja ba sai dai ko yi haƙuri kawai zaki ji labarin ina prison."

Didi a ruɗe ta ce, "Omar don girman Allah ka ajjiye aikin nan ka rufa min asiri,
shi uban yarinyar wanne ganganci ne ya saka ya haɗa ka da ita? Omar ya san halin ka
kuwa? Ya san baka da juriya kuwa? Ya san kana ɗaukar makami kuwa Omar?." Ganin Didi
ta ruɗe hankalinta ya tashi sai ya ce, "kar ki damu Didi, babu abinda zai faru, in
kin ga wani abu ya faru yarinyar tazo da rainin hankali ne wanda kin san bazan jure
masa ba. Ko da ita nake yiwa aiki bata isa ta yi min abinda bai yi min balle
babanta nake yiwa aiki, Kuma shima baban nata alfarmata ya nema a wannan ɓangaren,
sai da na amince zan yi sannan ya turota."

Ganin ya miƙe tsaye Didi ma ta miƙe ta ce, "Omar ka yi masa waya ka ajjiye aikin
nan."
"Didi ki nutsu don Allah, babu abinda zai same ni."
"Wallahi a jikina nake ji haɗuwarka da ita bazai zama alkhairi ba wallahi, don
Allah ka ajjiye aikin nan." Ya bita da kallo ya ce, "Didi yarinyar da ki ke gani ce
a social media fa, wacce ki ke cewa tana burge ki kin ganeta?." Didi ta wara ido
waje ta ɗauki wayarta da sauri ta dubo page ɗin Barr Nass ta nuna masa ta ce,
"wannan ce?."

Hoton Narma ya gani cikin kayan lauyoyi sun yi mata kyau matuƙa fuskar ta sai sheƙi
take yi da annuri, wani iri yaji a jikinsa ya janye idanunsa ya kalli Didi ya ce,
"ina faɗa miki itace kuma kina nuna min hotonta."

Didi ta ajjiye wayar ta ce, "na shiga uku, Omar don Allah ka ajjiye aikin nan ka
ji? Yarinyar nan kowa ya yi mata shaidar bata da kunya, a social media ma faɗa ake
yi da ita balle kuma a zahiri, kuma kai ka ga tana ganin a ƙasanta ka ke aiki."

Murmushi ya yi ya ce, "Didi kar ki damu babu abinda zai faru." Didi a sanyaye ta
ce, "Tsoro nake ji Omar, bana son wani abu ya same ka shiyasa."
"Babu komai." Shiru tayi bata ce komai ba shi kuma ya fita ya bar mata falon tana
kallon sa. Tana mamakin wannan ƙarfin hali na Omar, yarinya kamar wannan ƴar manya
ita yake cewa in tayi masa wani abun sai dai ta samu labarin yana prison kenan
bazai ƙyaleta ba, ta san daman bazai ƙyale ɗin ba wallahi sai dai a kulle shi. Ita
dai duk fargaba ta gama cika mata zuciya, saboda babu wanda ya san halin Omar kamar
ta, tsaf zai jawo mata maganar da zata kwana tana kuka. A haka ta koma ta zauna
jiki babu ƙwari.

Narma kuwa bacci ta yi sosai bata tashi ba sai magriba tayi sallar la'asar
sannan tayi magriba, sakkowa tayi ƙasa ta samu har mai aiki ta haɗa mata abinci ta
zauna taci abinci, ta ɗauki waya tana amsawa kafin ta tashi ta koma sama.
Ta window ta leƙa ta ga Yahya a zaune ta ɗaga murya ta ce, "kai!." Ɗago kai yayi ya
kalle ta ya ce, "Hajiya." Narma ta ce, "ina sabon driver nan yake?." Yahya ya ce,
"Hajiya ai tun ɗazu da ya tafi bai dawo ba." Kai ta girgiza ta koma tana mamakinsa
da ƙarfin hali irin nasa. Shi ba kowan kowa ba amma ya dinga yi mata iskanci kala-
kala.

Sai da tayi sallar i'sha sannan ta fara shiri, sun yi da ƙawayenta zasu ne yawo
hakan ya saka ta shirya cikin doguwar riga wacce jikinta take kamar roba mai tsaga
a baya, daga hips ɗin akwai wani maɗauri kamar mayafi daka ɗaure shi aka ɗaura a
tsakiyar rigar. Rigar baƙa

12 / 28