Advertisements
Chapter 19 Reading KIRAN RABO BOOK1 CMPLT BY NANA HALEEMA BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

KIRAN RABO BOOK1 CMPLT BY NANA HALEEMA

Author :  NANA HALEEMA Category :  Complete Novels

Chapter   19 / 28

54K to 57K   out of 83.2K words

fiki matsayi shi zaki tausayawa ba shi ƙasƙantacce ba.
Aikin driving ɗin ma da ya samu daga gare ni ina da dalilina, ke kin san da ko mai
gadin gidan da ki ke bai isa ya zama ba."
"Is okay, I'm sorry."
"Sorry for yourself. Dan haka ranar Monday ki siyo ticket ki dawo gida. Ki zo ayi
maganar auren ki kawai, akwai mutane da yawa suke so su aure ki." Narma ta ce,
"Okay."
"Ki je ki ci abinci sannan ki kwanta." Ta sake amsawa sannan ta kashe wayar tana
turo baki ta hau sama. Shirin kwnaciya tayi amma babu bacci a idanun ta hakan ya
saka ta tsaya a varander tana kallon motoci zuciyarta cike da tunanin Omar.

Omar a irin yanayin Narma ya ke tafiya, zuciyarsa gabaɗaya ta cushe babu abinda
yake gani sai ita, kuma ta burge shi sosai zuwan ta gidan su ba ƙaramin girma ya
bata a idanunsa ba, duk wanda ya san da Didi bata da lafiya har yazo ya duba ta ai
abin ka girmama shi ne balle ita ga yadda matsayinta yake, ga kuma yadda ake faɗar
rashin kırkinta. Kuma batu ake na Didi rabin ransa aka zo akazo dubawa, dole ya ji
daɗi. Gaskiya in ya ce bai ji daɗin zuwanta gidan su ba ya yi ƙarya, har zuciyarsa
ya ji daɗi haka ya samar mata da matsayin sosai a wajan sa. A karo na farko a
rayuwarsa wata mace ba Didi ba ta burge shi, a karo na farko ya ji yana ganin
girman wata mace ba Didi ba a zuciyarsa.

Koda ya shiga gida Didi ma zancen ta take yi, tana aikin faɗar ashe tana da kirki
har haka ake mata kallon mara kirki, shi dai bai ce mata komai ba dan shi kaɗai ya
san abinda yake ji a jikinsa a haka ya tafi ya kwanta, sai dai babu bacci babu
alamun sa saboda tunani.

Nayla ma a irin yanayinsa take, gabaɗaya murmushinsa take gani a idanun ta
zuciyarta na bugawa sosai, ajiyar zuciya tayi a bayyyane ta ce, "wannan wanne irin
yanayi ne?." Babu mai bata amsa, ta sake yin shiru tana kallon bangon ɗakin, ta
kulle ido ta buɗe tana jin sautin muryarsa da yadda ya amsa gaisuwarta. Murmushi
tayi ta ce, "he's so handsome." Salma da ta shigo ta kalle ta ta ce, "waye ya kama
zuciyarki haka?."

Nayla ta kalle ta Salma ta ce, "tun ɗazu na shigo kina tunani kina ta murmushi
alamun kin faɗa soyayya, sai naji kina yabon kyaunsa, waye shi?." Gaban Nayla ya
faɗi, sai a lokacin ta farga da hakan yana nufin soyayya, kenan son Omar take yi?.
Tuna hakan sai ta wara idanu waje Salma ta ce, "meye na buɗe idanu, ai duk wanda
yaga yanayinki a kwanakin nan ya san akwai bayani. Kenan ɗan Kano kika samu ko?
Yaya Abbas yana can yana haukan sonki wani ya ɗauki zuciyarki."

Nayla ta haɗɗiye yawu ta ce, "Salma ba haka bane."
"To faɗa min ya ne?." Shiru tayi bata ce komai ba, ta juya baya ta kwanta tana
tunanin lallai dole ta bar Kano tun kafin dare ya yi mata.


Hajiya Nayla ita soyayya ai duk inda ki ke yana tare dake. lol 😝😂

*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.

Nana Haleema❤️


*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025

©️*Nana Haleema.*

Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.

https://chat.whatsapp.com/K8IEI39TB803y9pEtzMmdp?mode=ems_copy_t

*Book 1*
*P 17.*


Nayla haka ta tashi sukuku ta rasa abinda yake yi mata daɗi, zuciyar tayi mata
nauyi sosai yanayin ta gabaɗaya ya canja. Kallo ɗaya zaka yi mata ka hango canji a
yanayinta, kasancewarta ba mace bace mai nuƙu-nuƙu ba, ko ya yanayinta ya canja
zaka fahimta, kana ganinta ka san ta canja. Tana zaune a falon Hajja tama juya
cokalin a cikin tea ita bata sha ba kuma ita bata daina juya cokalin ba. Hajja ta
kalle ta ta ce, “Hauwa’u lafiya ki ke kuwa?.”

Ta kalli Hajja ta ce, “Lafiya lau nake Hajja, Kawai yau na tashi bana jin daɗi ne.”
Salma da take gefe tayi dariya ta ce, “ba wani nan, Hajja soyayya ta fara shiyasa
yanayinta ya koma haka.” Nayla ta ce, “Samla ki ji tsoro Allah, ni dai ban ce miki
ba.” Hajja tayi dariya ta ce, “rabu da ita Hauwa, in ma da gaske soyayyar ki ka
fara meye a ciki ai kin kai ki yi ne.”
Nayla ta ce, “balle ma ba haka bane” ta faɗa tana ɗaukar wayarta jin tana ƙara.

Abiyna shine ya bayyana akan screen ɗin, tayi murmushi ta ɗauka ta saka a kunne ta
ce, “Abiy barka da safiya.” Daga can ɓangaren Abiy ya ce, “Kin tashi lafiya
Mamana?.”
“Lafiya lau nake Abiy, ya su Mama?.”
“Lafiya lau kowa yake, sai kewar ki mu ke yi.”

Tayi murmushi kafin ta yi magana ya ce, “Ya Hajja tana Lafiya?.”
“Lafiya lau Abiy.”
“Ki gaishe ta da kyau.” Ta amsa kafin ya ce, “yaushe zaki dawo ne? Sati ɗaya na ce
ki yi amma naga kin yi shiru ban ji kina zancen dawowa gida ba.” Haka kawai gabanta
ya faɗi ta ce, “Abiy na ɗauka sai nayi sati biyu.” Abiy ya ce, “A’a baza ki ba
Mamana, ki zauna cikin shiri ko yaushe zan iya ce miki zan turo a ɗauke ki. Ki zo
gida ki fara aiki ki in makaranta zaki koma ki makaranta in aure zaki yi ki yi
aure.”

Nayla da zuciyar take harbawa ta ce, “To Abiy.”
“Yauwa, ki zama cikin shiri zan turo a taho min dake hutun ya isa.” Nayla ta amsa
kafin Abiy ya yanke wayar.

Hajja ta kalle ta ta ce, “Hauwa kina son zaman Kano baban ki yana son ki zauna a
kusa dashi. Yaushe ya ce zaki tafi?.” Nayla a sanyaye ta ce, “yace na zauna a shiri
ko yaushe zai turo a ɗauke ni. Wallahi Hajja bana son tafiya.” Hajja tayi murmushi
ta ce, “haƙuri zaki yi ko koma, nima bana son tafiyar ki amma mahaifinki shine yake
da iko akan ki sama da kowa, ki koma ɗin wani lokacin sai ki dawo.” Ajiyar zuciya
tayi kawai tuna tunanin in ta tafi Kaduna ya zata yi da ganin Omar kenan?.

Ɓangaren Abiy yana yanke wayar Mama da ta shigo ta zauna ta kalle shi ta
ce, “Abiy kana son Nayla ta dawo sai, na ɗauka zaka barta ta sake yin kwana biyu.”
Ya kalle ta ya ce, “iya hakan da na bari ma nayi ƙoƙari, ke kin san bana barin yara
su je wani waje, ba wai dan ba yarda da tarbiyyar wajan da zasu je ba sai dan kawai
bana so. In ba Hajja ɗin ba babu inda zan iya barin Nayla ta je yayi wannan
kwanakin.”

Mama ta girgiza kai ya ce, “haka ne, amma da ka bari ta sake kwana biyu Itama tana
son zaman Kanon. Kuma yanzu bata fara aiki ba kuma ba karatu take ba, tana da
lokacin da zata zauna wajan Hajja.” Abiy ya ce, “na yi iya yina ai, gwara ta dawo
gida wani lokacin ta koma.”

Mama ta ce, “haƙuri zaka sake yi, itama Naylan tafi jin daɗin zaman can akan zaman
nan.” Da mamaki Abiy ya kalle ta ya ce, “Haka Naylan ta ce miki?.” Mama ta ce, “eh
haka ta ce. Ta ce min ita da zaka barta ta koma Kano ma tafi son haka.” Abiy ya
zuba mata ido yana kallo cikin mamaki kafin ya ce, “na tambayeki.”
“Ina ji.”
“Meyasa bakya son zaman ta a gidan nan ne? Akwai abinda take tsare miki?.” Mama ta
wara ido cikin tsoro ta ce, “Abiy yau ni ka ke faɗawa haka? Me Nayla zata tsare min
a gidan nan saboda Allah?.”
Abiy ya ce, “to meyasa ko yaushe in ina zancen zata dawo ki ke so na barta ta
zauna?.” Mama ta ce, “ba haka bane, kawai ina duba yadda kakarta take sonta ne, da
kuma yadda ita Naylan take son kakarta. Kuma kar ka manta Hajja mahaifiyar Nayla ta
rasa, Nayla take kallo a matsayin ƴarta da ta rasa shiyasa kawai.”

Abiy ya ce, “nima uwar gidana na rasa, Nayla nake kallo a matsayin matata da muka
zauna tare tun auren saurayi da budurwa. Nayla kaɗai Allah ya bata matsayin ƴa
kafin ta bar duniya, ita nake kallo nake a madadin matata. Dan haka Zeena kar ki
sake yi min magana irin wannan, a duk lokacin da nayi maganar Nayla ta gida dawo in
baza ki taya ni cewa ta dawo ba ki kar ki sake saka min baki kin gane?.”

Ganin ya fusata sosai sai ta ce, “Allah ya baka haƙuri, ba da wani abun nake faɗ
ba.”
“Na dai faɗa miki” yana gama faɗar hakan ya tashi ya bar mata falon ta bishi da
kallo. Kai ta girgiza dan wallahi sai ta samu makamin da zata nisanta Nayla da
mahaifinta, dole ma tayi wani abun kafin lokaci ya ƙure mata.


•••••• Omar kuwa da safe wajan Didi ya shiga ya tabbatar da lafiya lau
take ya hanata dafa abinci da kansa ya dafa musu noodles suka ci, bayan sun kammala
ne ta kalle shi ta ce, “Yaushe zaka gama aiki da Barr Nass?.” Omar ya kalle ta
cikin rashin fahimta ya ce, “Wace haka?.” Ta harare shi ta ce, “ban sani ba.
Yarinyar da ka ke kaiwa unguwa mana.”

“Oh! Ni in kika ce Barr Nass ɗn nan ɓatar dani ki ke yi. Ban sani ba, amma na san
cikin kwanakin nan ne.” Didi ta girgiza kai ta ce, “to Allah ya taimaka, ni so nake
ayi a gama lafiya kar a samu matsala da kai.” Ya yi murmushi kawai bai ce komai ba
alokacin wayar sa ta ɗauki ƙara.

Number ce ya kalli wayar sosai kamar ya santa number hakan ya saka ya ɗauka ya saka
a kunne, “Hello Tiger.” Narma ta faɗa daga cikin wayar, lumshe ido ya yi jin
muryarta mai daɗi a kunnesa ya ce, “ina ji.” Narma tayi murmushi ta ce, “Daman na
san abinda zaka ce kenan. Na kira ka ne in kana da time zuwa bayan azhar zamu
fita.”
“Okay, Allah ya kaimu.”
“Amin. A gaishe da Sister ace ina yi mata ya jiki.”
“Okay” ya sake furtawa a taƙaiice, Narma tayi dariya ta kashe wayar.

Kallon Didi ya yi da take kallon sa kafin ya yi magana ta ce, “Omar kafin ita ka
taɓa waya da mace kuwa?.” Ya girgiza kai ya ce, “Gaskiya ban taɓa ba Didi, sai dai
masu rubuta wrong number su kira ni suna neman wani. Itace mace ta farko da na taɓa
waya da ita gaskiya.” Didi ta ce, “koda na ji, shiyasa ka ke mata magana a daƙile
kamar kai ne oga itace driver ta ka.”
“Bana son rainin wayo ne, kin fi kowa sanin haka.”
“Nafi kowa sani kam Alhaji Omar.” ya yi murmushi mai sauti kafin ya tashi ya bar
mata wajen.

Sai da yayi sallar azahar ya shirya cikin ƙanunun kaya masu kyau wanda suke
masa jikinsa sosai. Kiran Narma ne ya sake shigowa wayarsa ya kalli number dan daga
ɗazu zuwa yanzu ya gane number, ya ɗauka ya saka a speaker ya ajjiye a kusa dashi
bai ce komai ba. Narma ta ce, “Tiger ina jira.”
“Okay” ya amsa a taƙaice kafin ta kashe wayar ma ya yanke wayar.

Wajan Didi ya shiga ya samu bacci take yi ya fito ƙofar gidan yana ƙoƙarin kiran
Bash a waya. Ba jimawa Bash ya zo ya ɗauki shi a machine suka wuce gidan. A ƙofar
gidan ya ajjiye shi ya ce yaje kawai zai taho ya tafi shi kuma ya shiga cikin
gidan.
Da su Yahya ya gaisa da masu gadin gidan kamar ko yaushe, bayan sun gaisa ya
hakimce a inda yake zama. Ga mamakinsa sai gata ta fito fuskarta ɗauke da murmushi
tana nufo shi.

Kasa ɗauke ido ya yi daga kanta, tayi matuƙar kyau cikin lace ja mai adon duwatsu.
Riga da siket ne a jikinta ta yafa mayafi a kafaɗa ɗaya da wayarta a hannu. Kafin
ta ƙaraso ƙhamshinta ya zo inda take, ya miƙe ta kalle shi ta ce, “Zamu iya
tafiya?.” Kai ya ɗaga mata ta bashi key ɗin wata motar daban ba wacce suke hawa ba
ya ƙarasa ya kunna motar yana jira ta shiga.

Ga mamakin sai yaga ta buɗe gaban motar ta shiga, bai yi magana ba ya ja motar suka
fita ma’aikatan gidan sai kallon ikon Allah suke yi. Titi ya hau ba tare da ya san
inda zasu je ba,
kallon fuskar sa take yi cikin tsantsar shauƙin da bata san daga inda yake zuwa ba,
wani irin bugu zuciyar ta take yi ba tare da ta san dalili ba.

A haka ta kwana ta tashi cikin wannan yanayi na bugawar zuciya, tsananin kewarsa da
take take ji ya saka ta ce zasu fita da wuri ba dan ta san inda zata je ba, yanzu
gashi gata amma sai take jin yanayin kamar ya fi na baya shiga rai.

“Ina zamu je?.” Jin muryarsa ya saka ta janye ido daga kansa ta jingina da kujera
ta sauke ajiyar zuciya tare lumshe ido, a hankali ta buɗe ta ce, “nima ban sani
ba.” Kallon ta ya yi da mamaki suka haɗa ido sai ta ce, “mu je gaba akwai wani
restaurant sai mu shiga, yunwa nake ji.”

Bai sake magana ba ya cigaba da tafiya har suka zo inda take nufi. Shiga suka yi ya
ajjiue motar yana jira ta fita. Kallon sa yake ji tana ji a jikinsa shiyasa yaƙi
kallonta, bai san meyasa ta canja haka ba. Narma ta ce, “mu je tare.” Kai ya
girgiza bai kalle ta ba ta ce, “Don Allah.” Kallon ta yayi ya rasa meyasa ta canja
gabaɗaya, ya rasa meyasa take masa irin wannan abubuwan kamar wacce take tare da
wani mijinta.

“Bazan je ba” ya faɗa kai tsaye. Narma taji babu daɗi a zuciyarta, ta buɗe ta fita
ya bita da kallo dan iya tafiyarta ma abar ɗaukar hankali ce.

Ba jimawa sai gata da wani waiter a bayan ta da ledoji, ta shiga motar sannan ta
karɓa ta kalle shi ta ce, “mu je.” Fita suka yi ta sake kallon shi ta ce, “Zaka kai
ni zoo park? Amma mu shiga tare kaji!” Yadda tayi maganar kaɗan ya rage bai saki
motar ba, amma kasancewar sa akwai dakiya da basarwa bai nuna ba ya ce, “ni bazan
shiga ba.”
“Don Allah Omar!.” Ajiyar zuciya ya yi bai ce komai ba ya ɗauki hanyar Zoo park.

Ba ya cewa komai yana ji tana kallonsa ya rasa meyasa take son kallon sa haka
kawai. Narma kuwa tunani take yi, ko shima yana jin irin abinda yake ji akan sa
oho. A haka suka ƙaraso bakin zoo park, ta kalle shi ta ce, “mu je don Allah.” Yana
kallon gabansa ba tare da ya kalle ta ba ya ce, “babu inda zan je.”

“Don Allah” ta faɗa tana kallonsa.
“Bazan je ba!.”
“Ba don ni ba, don Allah, don Annabi.” Numfashi ya sauke ya kalle ta, baya son
magiya ko kaɗan, magiya tana daga cikin abinda Didi take masa ta cuce shi ya yi
abinda ba ya so. Ba tare da ya kalle ta ba ya buɗe motar ya fito ta biyo bayan sa
tana murmushi.

Shi ya biya kuɗin ticket suka shiga ciki. Tafiya suke yi tana gaba yana baya, sam
yaƙi yarda su jera su tafi tare, da tazo kusa dashi zai ɗan tsaya har sai ta wuce
sannan zai biyo ta. A haka ta suke ta tafiya, suna zuwa waje-waje baya cewa komai
dan shi kam ya gaji. Mamaki yake yi ma da ya amince ya biyo ta, mamakin kansa yake
yi kamar ba shi ba wani abun yana niyar canja shi. Da aka zo wajan tiger sai Narma
ta yi murmushi ta kalle shi sai ta ga ba wajan ma yake kallo ba.

Ta yi murmushi ta ce, “Tiger i like your acting” daga haka tayi gaba. Bai yi
tunanin me ta ce ya wuce shima.

Waya ya tsaya yana amsawa hakan ya saka ta tsaya tana kallon sa cikin annushuwa mai
yawa, ko tare da Ashraf take bata jin wannan abinda take ji a kansa, shiyasa ta
kasa fassara shi har yanzu. Basu jima ba suka fita suka mota tare da ɗaukar hanya.
Har lokacin bai ce mata komai ba itace dai take kallon sa kamar ta cinye shi.
Lokacin sallah ne yayi hakan ya saka yake gudu har suka ƙarasa gidan ya tsayar
motar.

“Na gode.” Kai ya ɗaga kawai bai ce komai ba. Ta yi gyaran murya ta ce, “Gobe zan
koma Abuja.” Kallon ta ya yi ta ɗaga masa kai ta ce, “Daddy ya ce na koma ni kuma
ban gaji da Kano ba.” Maimakon ya amsa mata abinda ta ce sai ya ce, “Allah ya
kaimu.”
“Amin ya rabbi. Ƙarfe sha biyu jirgina zai tashi, zaka zo ka kaini airport?.” Yadda
take maganar a shaƙe ya saka shi ya kalle ta, sai ta marairaice ta ce, “please!.”
“Allah ya kaimu” ya sake faɗa a taƙaice. Ta amsa da amin ta ajjiye masa abinda ta
siyo ta ce, “ga naka nan, in baka so ka kaiwa Sister. Sai gobe” ta faɗa tana buɗe
motar ta fita. Kafin ta shiga gidan ya fito ya ce, “Makullin.”

Tsayawa tayi tare da dawowa, ta karɓi key ɗin tana kallon sa bata ce komai ba ta
wuce ciki zuciyar tahar zillo take yi daga ƙirjin ta saboda bugawar da take yi. Bai
bar gidan ba sai da yayi sallar la’asar sannan ya fita daga gidan ya nufi gidan
Didi.

Narma tana kallon sa har ya fita ta jingina da bango idanunta a lumshe ta ce,
“Wayyo Allah, ne nake ji haka akan wannan mutumin? Meyesa bana so ya yi nisa dani?
Meyasa nake so naji yayi magana? Ina haushinsa da nake ji a baya ya tafi?.” Babu
mai bata amsa ta buɗe idanunta a bayyane ta ce, “me hakan yake nufi?.” Gate ɗin
gidan take kallo kamar shi take kalla kafin ta ja baya ta ta koma ciki.

Omar da ya koma ya bawa Didi kayan gabaɗaya, Didi ta karɓa tana godiya
dan shi kam ta san ba ci zai yi ba. Didi tana ta yabon Narma shi dai bai ce komai
ba ya yi shiru yana kallon wani waje daban yana mamakin yanayin da yake ji a kanta
da abubuwan da take yi masa ita kanta Narma. Bai bari tunanin ya yi tasiri a kansa
ba ya tashi ya fita daga gidan domin samu ya manta da maganar.

Washe gari.

_Tiger don’t forget my flight is at 12pm._ abinda ya gani kenan a wayar ɗsa, ya
sake maimaitawa karantawa ya fahimci abinda take nufi. Sake karantawa ya yi a karo
na uku sai ya ja tsaki ya cillar da waya ya ce, “iyayi, baza a yi magana da hausa
ba sai da turanci, sai ka ce an faɗa mata na iya oho.”

Wanka ya yi ya saka manyan kaya daman ya sanar da Didi zai mayar da ita bai shiga
wajan

19 / 28