Advertisements
Chapter 15 Reading KIRAN RABO BOOK1 CMPLT BY NANA HALEEMA BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

KIRAN RABO BOOK1 CMPLT BY NANA HALEEMA

Author :  NANA HALEEMA Category :  Complete Novels

Chapter   15 / 28

42K to 45K   out of 83.2K words

ya saka pcap wacce ta rufe fuskar sa.

Narma kuwa a ƙasan gadar ƙofar nasara motar da take ciki ta mutu, tayi-tayi ta
kunna ta kasa kunnawa gashi bata da number kowa balle ta kira azo a tafi da ita
gıda. Tsaki tayi ta fito daga motar tana kallon hanya, wajan babu mutane sai mota
da take wucewa kuma babu haske sosai hakan ya bata tsoro. Napep take so ta tare ta
hau ta tafi amma bata san ma ya ake tare mai napep ba dan ba taɓa hawa tayi ba,
bisa kuskure ko tsautsayi bata taɓa hawa napep ba. Shiyasa take kallon su ɗaya
bayan ɗaya suna wucewa ta rasa me zata yi.

Abu taji an saka mata a bayanta kamar wuƙa zata juya aka ce, "kina juyawa wallahi
sai na farɗe miki bayanki, kawo wayar hannunki." Narma jiki ya fara rawa hannu na
karkarwa ta kuma kasa miƙar wayar.
"Baza ki bayar ba sai na kashe ki?." Hannunta rawa yake yi garin ta miƙa masa wayar
garin ya yanke ya da wuƙar a hannuta. Narma tayi ƙara tana kallon hannunta, shi
kuma ya yi cikin duhu a guje bai sake waiwayen ta.

Hannunta jini yake yi tana kuka ga tsoron tashin hankali, sai rawa jikinta yake yi
dan bata taɓa tsintar kanta a irin wanna tashin hankalin ba sai a lokacin.

*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.

Nana Haleema❤️

*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025

©️*Nana Haleema.*

Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.

*Book 1*
*P 13.*


Omar tun daga nesa ya gane motar ya kuma ganta a tsaye a wajan, a hankali ya ƙaraso
kamar zai gifta sai yaji tana kuka tana cewa, "a taimake ni don Allah, a taimaka
min jinina zai ƙare."

Ɗaga pcap ɗin ya yi ya kalle ta suka haɗa ido ganinsa ta matso kusa dashi a gigice
da fitar hankali sosai ta ce, "Tiger sun ƙwace min waya, sun yanke ki a hannu,
jinina zai ɗare ka taimaka min zasu kashe ni." Ya kula gabaɗaya a gigice take har
tana riƙe shi bata san ma tayi hakan ba saboda tsoro.

Kallon hanyar ya yi ya sake kallon ta yaga yadda take hawaye shaɓe-shaɓe tana riƙe
da hannu kamar wacce aka guntulewa hannu, kallon ɗan yankan da yake hannun ta ya yi
tare da yin tsaki a bayyane har lokacin bata saki rigarsa.

"Take me to hospital please, ka kaini ayi min TT kar na samu ciwo." Kamar ba zai yi
mata ba magana ba sai yaji ta ce, "Don Allah ka ɗauke ni daga nan, tsoro nake ji,
ka taimaka min don Allah." Yadda take kuka tana ƙoƙarin shege masa jiki ne ya saka
ya riƙe hannunta ya janye ta ya buɗe gaban motar ya ce, "shiga." Ba musu ta shiga
jikin ta na shaking sosai ya buɗe mazaunin driver yana kunna motar ta tashi ya ja
motar ya nufi asibiti mafi kusa.

Wani private hospital suka ƙarasa ya ajjiye motar ya kalle ta yaga sai kuka take yi
ta riƙe hannunta, shi wallahi mamaki take bashi, ɗan wannan yankan take yiwa kuka
kamar wacce aka yanka sosai. Ya kalle ta ya ce, "Fita ki je." Ta buɗe murfin motar
ta kalle shi ce, "nayi bleeding sosai in na tashi jiri zan yi."
"Ko" ya furta a bayyane yana kallon ta.

Fita ya yi daga motar ya ce, "Fito" ya furta a kausashe dan ya ga tana neman mayar
dashi ɗan aikinta, jin yadda tayi magana ya saka ta sakko amma tana fitowa tayi
kamar zata faɗi, da hanzari kuwa ta riƙe shi tana cewa, "na ce maka i'm dizzy bazan
iya tafiya ba." Ɗan tsaki ya yi ya janye ta a jikinsa ya kalli bayan sa yaga
ma'aikatan asibitin nan ya yi musu magana suka riƙe ta suka shiga da ita.

Bai shiga ba ya tsaya a jikin motar sai ga wacce ta shiga da ita tazo tayi masa
magana dole ya shiga. Yana shiga ya ganta sai kuka take yi an ɗaure hannun da
bandage, likitan da ya gama yi mata dressing wound ɗin ya kalle shi ya ce, "Oga ka
taya mu rarrashinta taƙi yin shiru."

Kallon ta ya yi suka haɗa ido sai wani juya ido take yi kamar mage. Ƙaramin tsaki
ya yi Narma ta kalle shi ta ce, "kayi clearing bill ɗin, wayata da atm ɗina duk sun
ƙwace." Sai a sannan ya tuna ma da batun wayar ta bai ce komai ba ya yi musu
transfer a take suka fito tare da ledar magani a hannun nurse ɗin wai baza ta iya
riƙewa.

Sai tafiya take kamar mara jini ita a lallai an yanke ta, gabaɗaya haushi take
bashi yadda take langwaɓewa kamar wacce aka jiwa ciwon kirki. Suna zuwa gaban motar
ta shiga bayan motar shi kuma ya shiga gaba ya ja motar da gudun gaske.

Da yake kwanciya tayi bata san inda suka nufa ba sai da taji ya tsaya yana niyar
fita, ta miƙe ta gansu a wani waje mai duhu ta ce, "ina zaka je?." Kallon ta ya yi
jin yadda tayi maganar a firgice bai amsa ba, "don Allah ka je dani bazan iya zama
ni kaɗai ba, wallahi i'm scared." Nan da nan jikinta ya fara shaking cikin tsananin
tsoro tana ganin kamar abinda ya faru zai sake faruwa.

Narma ganin ya yi mata banza yana niyar fita sai itama ta fito da sauri ta ce,
"bazan iya zama ba, don Allah ka je dani tsoro nake ji."
"Inda zan je ba wajan zuwan ki bane" ya faɗa without looking her.
"Ni dai zan je, don Allah ka je dani." Kallon ta ya yi sai kawai ya yi gaba ta
bishi a baya, kanta har sarawa yake yi saboda ciwon da ya fara yi mata.

Wani waje taga sun shiga sai gasu a gaban dandazon ƴan daba sama da su ashirin a
wajan sun baje wayoyi da atm cards da kuɗi. Wajan banda warin wiwi babu abinda yake
yi, ga hayaƙin taba ya cika wajan.

Ganin an shigo suka miƙe duk suka fito da makamai ɗaya daga cikin yana cewa, "wanne
mai ƙarar kwanan ne yazo inda bazai fita ba?." Narma ta ɓuya a bayasa gabanta na
faɗuwa tana dan sanin shigowa wajan. Haske shi suka yi da fitila shi kuma ya ɗaga
pcap ɗin kansa, ganin fuskarsa ta bayyana sai suka haɗa baki suka ce, "Damisa!."

Babban cikin su ya ce, "Allah ya ja zamanın Damisa ƙi sabo, mu je madugu uban
tafiya, barkono ka fi ƙarfin shiƙa. Allah ya sa ba laifi mu ka yi ba, na ganka
kwatsam babu sanarwa." Omar ya bisu da kallo yana kallon wayoyin da suke ƙasa ya
ce, "waye ya ƙwace waya a ƙasan gada?." Ɗaya daga cikin su ya ce, "Madugu ai ƙasan
gada da yawa, daidai ina ka ke nufi?." Narma ya juya yana kalla ya ce, "fito." Sai
ta riƙe rigarsa tana kwanciya a bayansa jikinta na rawa sosai. Hannunta ya jawo
kafin ya saki hannun na ta ya ce, "waye ya karɓi wayarta?."

Wanda ya ƙwace mata wayar ya kalle ta ya ce, "afuwan Jan wuya ni ne." Da hannu ya
yi masa alamun da ya zo, ba musu ya taso yazo yana zuwa ya daki ƙewarsa ya ce, "Sai
ka ji mata ciwo?." Ya sunkuyar da kai ya ce, "afuwan madugu ban san antyn mu ba
ce." Harararsa ya yi ya kalli Narma da tayi tsuru ya ce, "bata haƙuri." Kallon
Narma ya yi ya ce, "ki yi hakuri Anty." Firgita tayi da maganarsa jin ta wani iri
kana ji ka san a buge ya ke, ta yi tsalle cikin tsoro ta koma bayansa ta riƙe shi
jiki na rawa.
Omar ya runtse ido jin jikinta a bayansa a kwance, wani iri yake ji baya so tana
riƙe shi ɗin nan, shi in ba Didi ba babu macen da ya taɓa haɗa jiki da ita, ko ita
tunda ya girma bai haɗa jiki da ita ba sai dai ya riƙe hannunta ko su gaisa da
safe, shiyasa yake jin wani iri a jikinsa in ta riƙe shi. Daurewa ya yi ya ce,
"ɗauko min wayar, sannan kar ka naga an taɓa mata komai."

Ba musu ya juya aka fara bincike wayar sai ga iPhone 16 kalar pink da atm ɗinta a
baya an ɗauko ya miƙa masa yana cewa, "wallahi Allah ne ya taimaka Magudu da yanzu
ba labarin nan ake yi ba, na je inda za a kwashe kuɗaɗen ciki baya nan." Omar ya
karɓi wayar yana kallon su ya ce, "sauran wayoyin fa?."

Wanda yake zaune ya ce, "Damisa ganimar yau ce." Ya bisu da kallo ɗaya bayan ɗaya
kana ya ce, "tattaro min su duka." A tare suka haɗa baki suka ce, "Haba Damisa
wannan yawa ka ke yi fa, wannan ba halin ka bane." Fuska ya sake ɗaurewa ya ce, "Ku
tattaro min ko na tattara har da ku." Babban ciki ya ce, "gaskiya Madugu hakan bai
yi ba, ka san wahalar da muka sha....." kallon da ya yi masa ya saka ya ce, "Kawai
dan kaine wallahi, amma da ka san babu wani da ya isa ya saka mu bada wayar nan
koda gwamna ne wallahi, ku bashi."

Tattaro wayoyin suka yi suka zuba a wata jaka aka miƙa masa ya karɓa yana kallon su
duk sun ɗaure fuska alamun basu ji daɗin hakan ba. Ya sake kallon su ya ce, "Ku
riƙe kawai" ya faɗa yana miƙa musu.
" ka je dasu kawai, amma kawai dan babu yadda zamu yi da kai ne."
"Ban son wannan ɗabi'ar da ku ke yi, in ba ku daina ba...." Sai ya katse maganar ya
karkaɗa musu yatsansa. Ya motsa zai bar wajan ta sake riƙe shi gam.

Tsaki ya yi ya ce, "Malama ki sake ni!." Yadda ya yi maganar a kausashe ya saka ta
sakinsa amma duk da haka tana rike da gefen rigarsa suka fita daga wajan. Bayan
motar ta shiga a tsorace ya cilla mata wayar ta ya ce, "Kano ba Abuja bane ki san
inda zaki dinga shiga." Bata ce komai ba ya ja motar kai tsaye police station ya
wuce.

Nan ma sai da ta bishi ya samu dpo yana niyar fita suka gaisa ya bashi wayar ya ce,
"wayoyin da aka ƙwace yau ne, ku saka a duniya a mene masu su a basu wayar." Dpo ya
kalle shi ya ce, "ina wanda suka ƙwace wayoyin su ke?."
"Ni dai wayoyin na kawo maka in na mayar shikenan." Ya karɓa ya ce, "amma samun
masu aikata laifin ya fi samun wayoyin amfani. Tiger da zaka taimaka a kama su da
kayi babban aiki."

Ya kalli Dpo ya kafin ya ce, "a fara bawa kowa haƙƙinsa tukunna, zan faɗa maka inda
zaka same su wani lokaci, amma ba yau ba." Dpo ya ce, "babu damuwa. Da za a samu
shugabanni kamar ka ai da Kano ta zauna lafiya. Ga ka dai kowa ya san ka amma baka
ɓarnar da ƴan uwanka suke yi, ban san meyasa ake kiran ka da ɗan daba ba, dai kai
ba shi ba ne." Bai ce komai ba ya fito ya shiga mota itama ta shiga ya ja motar ya
nufi gidan da Narma ta sauka.

Yana tsayawa a harabar ta buɗe motar ta fito jiki a sanyaye dan kanta ciwo yake yi
mata matuƙa saboda kukan da tayi. Fitowa Shima ya yi tana niyar shiga ya ce, "kin
ga." Ba musu ta tsaya cak ta jiyo tana kallon sa ya tako inda yake ya miƙa mata key
ɗin motar. Ta kalli key ɗin da yake bata ta kalle shi ta ce, "kaje da ita."
"Karɓi" ya sake faɗa yana miƙa mata fuskarsa a ɗaure yamau.

A shagwaɓe ta ce, "hannuna yayi nauyi bana iya ɗaukat komai, maganin ma wahala nake
sha wajan riƙewa." Ledar hannunta ya buɗe ya saka mata key ɗin ya juya ya fita daga
gidan. Ajiyar zuciya tayi bayan ya fita tana kallon sa ta ce, "kamar wani mai
hankali, ba dan shi ba da waya ta ta tafi kenan" ta faɗa tana shiga falo.

Kunna wayar tayi tana ajiyar zuciya kiran Dad ya shigo, ɗauka tayi daga can
Dad ya ce, "Narma ina kika saka wayarki? Ina ta kira tun ɗazu bana samun ki." Narma
ta ce, "Dad!" Sai ta saka kuka hankalinsa ya tashi ya ce, "me ya faru? Tiger ne ya
sake miki wani abun?. Talk to me mana kin saka ni a ruɗani."

"Dad tare ni aka yi a under the flyover, they snatched my phone and my atm card.
Dad sun yanke ni a hannuna jini yana ta flowing" ta faɗa tana jan kalmar ƙarshe
tare da fashewa da kuka.
"Innalillahi! Daughter me ki ke cewa? A ina haka ya faru? Ina shi Tiger ɗin yake?."
Ba ta yi magana ba sai kuka, kawai ya yanke wayar ya kira ta video call ta ɗauka ta
ganshi a zaune shida Mum harda Najwa a rikice suke ce mata ne ya faru.

Narma ta ce, "Dad ba da shi ne fita ba, ni kaɗai na fita."
"Are you mad Narma? Nace baki da hankali ne. Me na faɗa miki akan fita ke kaɗai?
Ban yi miki warning akan haka ba?." Ganin yana faɗa sai Mum ta ce, "My dear ka yi
mata a hankali baka ganin tana da ciwo ne?. Daughter calm down ki faɗa mana abinda
ya faru."

Narma ta ce, "na jira shi bai zo ba sai na hau mota na fita, ina cikin tafiya sai
motar ta tsaya na fito daga motar sai ga wani ya saka min wuƙa ya ce na bashi
wayata, da zai ƙwace wayar ne ya yanke ni....!" Ta faɗa tana hawaye.

Dad ya ce, "oh my god! Yanzu ya jikin naki?. Kin je asibiti?." Mum cikin faɗa ta
ce, "'ni banga amfanin wannan banzan Tiger ɗin ba, ban ga amfaninsa da ka bashi
ragamar kula da yarinya ta ba. How com yana matsayin driverta ya barta ta fita ita
kaɗai?. Gaskiya dear bazan iya tolerating wannan shirmen na sa ba, zan tura mata da
poliçe da zasu kula min da ita. Kalli hannunta fa, kalli girman ciwon da ka ji mata
akan wayar one million."

Narma ta goge ido ta ce, "No Mum, ya taimake ni. Ban san ya aka yi ba ina wajan sai
na ganshi yazo, he took me to the hospital and had my wound dressed, then muka je
har inda masu ƙwacen wayar suke zama ya kaɓo min wayar har suka bani haƙuri. Sai da
ya dawo dani sannan ya tafi."

Jin haka gently Mum ta ce, "kina nufin har inda wanda suka ƙwace miki wayar ya je
ya karɓo miki?."
"Yes Mum, har da atm card ɗina ma an bani. Ba ma iya phone ɗin ba duk wanda aka
karɓawa waya yau ya karɓa ya kaiwa police station za a neme masu shi." Dad ya kalli
Mum ya ce, "Now you understands why I have trusted him right? You should see the
benefit of being him with Narma?." Narma ta yi shiru ya kalle ta ya ce, "na
tabbatar da ace tare ku ke babu wanda zai ce zai miki wani abun."


"I see, Dan suma bashi respect sosai har mamaki nayi."
"You see. Kina ji, yanzu ki je ki huta ki yi bacci sosai da safe sai mu ƙarasa
maganar."

Narma ta ce, "but Dad I'm scared wallahi, please can you convince him to come and
stay with me? In yana kwana a nan zan fi samun tsaro sosai." Dad ya ce, "don't
worrry, yanzu ki kwanta." Amsawa tayi ta kashe wayar ta tashi ta sha magani ta
kwanta.

Dad bayan ya kashe wayar ya kalli Mum ya ce, "kin ga abinda nake faɗa miki
ko?. Ɗan iska sai da ɗan iska irinsa ake zama lafiya." Mum ta ce, "na fahimta, amma
ya cika zaƙewa ne da yawa baya bata girmanta." Dad ya yi murmushi ya ce, "ƙyale ni
dashi, tunda har ya taimake ta ai komai ya yi kyau."

Omar kuwa a haka ya koma gida jikinsa duk babu ƙarfi, ƙhamshin turaren Narma
ya gama kama kayan jikinsa gaba da baya. Duk ya takura ya kuma damu saboda turaren
ya ishe shi duk da yana da daɗin ƙamshi sosai, amma ya takura masa so yake ya cire
kayan ya huta.

Yana shiga gidan ya ga Didi a tsaye, ta ƙaraso inda yake ta ce, "Tun ɗazu nake
jiran dawowaka, ko abinci baka ci ba." Kallon rigarsa tayi kasancewar ta blue mai
haske ta ce, "Omar me nake gani a jikinka kamar jini?." Kallon rigar ya yi ya kalle
ta zai yi magana ta ce, "Omar kar ka ce min faɗa ka yi."

Omar ya ce, "Ban yi faɗa da kowa ba Didi, taimako nayi, kar ki damu." Kallon
fuskarsa tayi sai taga bai yi kama da wanda ya yi faɗa ba, dan ta san in faɗa ya yi
jiyoiyin kansa ma zasu tona masa asiri saboda ɓacin rai.

"Wa ka taimaka haka?."
"Wata yarinya aka ƙwacewa waya kuma aka yanke ta a hannu shine na taimaka mata." Da
mamaki take kallonsa ta ce, "ƙhamshin turarenta nake ji a jikinka haka?." Ɗan kulle
ido ya yi ya buɗe dan bai so ta ji ƙhamshin ba ya ce, "shi shine."

"Wanne irin taimako ne wannan da ƙhamshinta zai dinga tashi haka a jikinka?." Ya
kalle ta ganin tana kallon sa kamar bata yarda ba ya ce, "kin san bazan miki ƙarya
ba ko?." Didi ta ce, "na sani, ban ce kana ƙarya ba, ina so na tabbatar ne kawai."
"To ki yarda" ya furta mata a taƙaice ya wuce ya kyale ta. Mamaki abin yake bata,
taimako ya yi, taimakon ma mace ya taimaka kuma ga ƙhamshinta a jikinsa, wanne irin
taimako ne wannan haka?. Babu mai bata amsa hakan ya saka ta ƙyale shi da tambaya
ta shiga ciki.


Washe gari.

Da labarin abinda Tiger ya yi aka tashi, kusan duka mutanen da aka ƙwacewa waya a
daren jiya an basu kayar su, musamman wanda aka ƙwacewa a arear da ya karɓa. Ana ta
saka masa albarka dan an faɗi sunan sa ance Omar wanda aka fi sani da Tiger.

Nayla na zaune kusa da Hajja tana kallon labaran tana murmushi. Hajja ta kalle ta
tace, "ke lafiya ki ke murmushi?." Ta kalli Hajja ta ce, "Hajja Omar ƙanin Didi
shine ya karɓo wayoyin da aka ƙwacewa wasu jiya, Wallahi shine abin ya yi min daɗi
sosai."

Hajja ya ce, "indai irin wannan abubuwan ne ya saba, inda iya haka yake tsayawa da
ya zama mutumin kirki sosai, to shima shegen kansa ne. Lokacin da yake cikin ƴan
daban kaca-kaca baza ki so ki ji irin abinda yake yi ba, ya zubar da jinin mutane
da yawa ba kaɗan ba. Allah sarki Aisha, ya wahalar da baiwar Allah nesa ba kusa ba,
itace zuwa wajan ƴan sanda, itace zuwa prison, ita zuwa inda yake zama. Kaii...sai
dai Allah ya biyata kawai, amma Omar ya wahalar da ita har yanzu yana kan bata
ciwon kai." Nayla tana ji

15 / 28