Author : NANA HALEEMA Category : Complete Novels
tare. Daga nan suka yi sallama ya kashe
wayar ya kwanta yana tunani, fuskar Narman yake gani a idonsa ya ja tsaki mai tsaho
ya kulle ido da ƙarfin gaske.
Kwana biyu bai je ba saboda Sen ya ce ya bari Ashraf ɗin ya dinga kai ta dan haka
kwana biyu babu inda yake sai dai ya fita ya dawo kawai. Ita kuwa Narma biki suke
sha Ashraf yana kai ta duk inda take so amma ta kasa daina tunanin Omar ko kaɗam,
da ta rufe ido shi take gani musamman lokacin da yake kallon idanunta.
Ranar asabar Ashraf ya koma Omar bai sani ba yana zaune a ɗaki ya ga baƙuwar number
tana kiran sa, ɗauka ya yi ya saka a kunne bai yi magana ba Narma ta ce, "Hello
Tiger, Narma ce." Jin hakan sai ya gane ta ya ce, "ina ji."
"Ashraf baya anjima zan je biki."
"Okay" ya furta mata kafin ta sake magana ya yanke wayar.
Saurin katse da wayar ya yi jin zuciyarsa na wani irin harbawa lokacin da Narma ta
fara yi masa magana, magana take cikin yanga da iyayi hakan ya saka yaji wani iri
har bai san ya yi hanzarin kashewa ba. Shin wai me yake Shirin faruwa dashi ne?.
Meyasa ya kasa daina tunanin ta? Meyasa yake jin wani iri da ta kira shi yanzu?
Lallai dole ya san dalilin hakan kafin abun ya yi nisa.
Ɓangaren Narma murmushi ta samu kanta da yi bayan ya kashe wayar a bayyane ta ce,
"muryarsa mai daɗi, zan so naga yana murmushi." Sai kuma tayi tsaki ta ce, "Ko Ina
ruwana ma oho, da ya yi murmushi da kar ya yi shi ya sani. Ni so nake na manta
dashi amma na kasa, ko meyasa na kasa mantawa dashi oho min" ta faɗa a bayyane tana
tashi ta shiga ɗaki har lokacin muryarsa take ji a kunnen ta.
Tofa, Omar da Narma, ga kuma Nayla a gefe.
*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.
Nana Haleema❤️
*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025
©️*Nana Haleema.*
Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.
https://www.tiktok.com/@nanahaleemawriter?_t=ZS-8zaZqblsrGp&_r=1
*Book 1*
*P 15.*
Nayla kuwa yanayin da take ji akan Omar ya fara damunta domin ko yaushe a cikin
tunaninsa take, ko yaushe a cikin ganin murmushinsa take da zarar ta kulle. Ga
faɗuwar gaba da take addaba mata, ko ya taji an kira wani mai irin sunansa sai
ƙirjinta ya buga. Ɗakyar ta jure kwanaki uku bata ganshi ba, a safiyar ranar bayan
tayi wanka ta shirya cikin riga da siket, rigar har guiwa ta saka mayafi ƙarami a
kanta ta fito falon.
Salma ta kalle ta tace, "Sai ina?." Ta kalli Salma ta ce, "Zan je gidan Mama
Zaliha." Hajja ta kalle ta ce, "Sai kin dawo, amma dai kar ki yi dare." Nayla ta
ɗaga kai alamun to, Salma ta ce, "Amma da kin faɗa min da na raka ki."
"Na ji jiya kina cewa bakya jin daɗi shiyasa, ni kuma tun jiya ta kira ni ta ce
nazo." Salma ta ce, "Da motar Hajja zaki je?."
Nayla ta ce, "A'a, napep zan hau." Hajja ta ce, "ke bana son shirme, kin san
babanki baya son kina hawa abin hawa na haya ko? Meyasa baza ki bari a kira Sayyadi
ya kai ki ba?." Nayla ta ce, "Hajja ai ba jima zan yi ba, yanzu zan dawo" ta faɗa
tana fita da sauri dan kar Hajja ta hanata.
Nayla tana fita daga gidan kallon ƙofar gidan Didi ta ta yi gabanta ya faɗi sosai,
a hankali ta fara takawa zuwa ƙofar gidan faɗuwar gabanta na tsannanta, wani irin
yanayi baƙo a gare ta yana ratsa ilahirin jikinta. Ƙofar ɗakinsa a buɗe take tayi
sallama ta shiga gidan amma shiru babu alamun motsi.
Tana gab da shiga falon ta ji an ce, "wace a nan!?." Da sauri ta jiyo suka haɗa
ido, Sarai ya gane itace tun wucewarta ya ganta, yana sane ya ce wace a nan dan
yarinyar ta soma zuwar masa wuya.
Nayla ta ce, "ni ce, ina yini." Bai amsa ba ya ce, "Haka ake shiga gidan mutane
babu sallama?." Nayla ta sunkuyar da kai ta ce, "nayi sallama."
"Mtsww! To me ya kawo ki?."
"Wajan Didi na zo."
"Tattara ƙafafunki ki bar gidan nan Didi bata nan." Jin abinda ya ce sai ta ɗago ta
ga shima ita yake kallo fuskarsa a ɗaure sosai. A hankali ta tako ta zo ta wuce shi
ya bita da harara ya koma ciki.
Haushin Didin ita kanta yake ji tun safe ta wani fita gidan biki, bikin ma kuma wai
gidan Kawu tsabar lalacewa. Ga Nayla da ta ke neman tunzura zuciya sa, ta dame shi
da shige da fice a cikin gidan su. A bayyane ya ce, "wannan yarinyar akwai nacin
tsiya."
Nayla ba ƙarmain daɗin ganinsa taji ba ta dinga sauke ajiyar zuciya tana tafiya
fuskarta da murmushi, ji take kamar an yi mata babbar kyauta mai matuƙar daɗi
kasancewar ta ganshi har sun yi magana. A haka ta hau napep ta tafi gidan Mama
Zaliha dan kar ta koma Hajja ta fahimci wani abun da baza ta je ba.
Omar shiryawa ya yi cikin manyan kaya na yadi baƙi mai gajeran hannu kansa babu
hula, gidan ya kulle da makulli sannan ya tafi wajan Narma da niyar kai ta inda ya
ce zasu je.
Narma tun shigarsa tana tsaye a balcony tana kallon sa, wara idanu tayi tana kallon
sa cikin shigar manyan kaya dan ya yi mata kyau sosai. Bata taɓa ganin sa da manyan
kaya ba, duk da ƙananun kayan suna karɓar sa kamar jarumin india, amma kyaun da
yayi a manyan kaya ƙarshe ne.
Gani tayi kamar kwanakin da ɗauka bata ganshi ba ya sake yin kyau ga wani class na
musamman da ya ƙaro, duk da fuskarsa babu annuri amma ya yi mata kyau sosai. Gazebo
ya shiga ya zauna akan kujerun da suke cikin ta. Yadda ya zauna ya ɗora ɗafa kan
ɗaya yafi komai tafiya da ita, bata san tayi murmushi ba a bayyane ta ce, "Tiger!."
Sakkowa tayi daga saman ta fito harabar gidan tana kallon inda yake, samun kanta
tayi da nufar wajan da yake cikin salon tafiyar ta ƴan gayu. Har ta isa bai sani ba
sai tsayuwarta ya gani da ƙhamshin turarenta. Ɗago ido ya yi ya kalle ta, ta yi
kwalliya cikin straight gown, ta kawo mayafi mai kauri amma mara girma ta saka,
tayi ɗauri da ta ja shi baya gaban gashin ta ya fito sai hakan ya ƙara mata kyau
sosai.
"Ina yini" ta furta tana kallon sa shi kuma tuni ya janye idanunsa dan ya kasa gane
abinda yake ji in yana kallon ta musamman in itama kallon sa take yi. Miƙewa ya yi
ba tare da ya amsa ba, a shagwaɓe ta ce, "na gaishe ka kayi min shiru, kuma saboda
kirkin da ka yi min ya saka na gaishe ka." Lumshe ido ya yi ya buɗe jin yadda
maganarta ta tatsa har cikin zuciyarsa, wani irin sanyi yake ji a jikinsa yanayinsa
na canjawa.
Sake haɗa ido suka yi ya janye ido bai ce komai ba. Narma ta ce, "baza ka amsa
gaisuwar ba?." Ɗan ƙaramin tsaki ya yi ya ce, "lafiya." Daga haka ya yi gaba ta
bishi da kallo duk sai taji haushin kanta da ta yi abinda ya dizaga ta.
A hankali take takowa dan ɗakyar take motsawa saboda yadda ta kamata rigar, daga
wajan guiwarta an kama rigar sosai ta tsuke. Baya ta juya tana yiwa mai gadi magana
a nan ya hango doguwar tsagar bayan rigar wacce ta bayyana farara digadiginta, har
abinda ya rab digaginta da cinyarta a bayyane yake. Ɗauke kai ya yi daga kanta yaja
dogon tsaki ba tare da ya san dalili ba, ta buɗe motar ta shiga shi kuma ya ja
motar suka fita.
Babu wanda yake magana a cikin su kamar ko yaushe, shi titi yake ita kuma danna
waya amma lokaci zuwa lokaci tana ɗagowa ta kalle shi sai ta cigaba da abinda take
yi. Shopping complex suka shiga kamar yadda ta ce, ya tsaya a harabar store ɗin ta
buɗe ta fita bata ce masa komai ba.
Fitowa ya yi shima ya shiga dan akwai abinda yake so ya siya. Bata san ya shigo ba
sai ganin sa tayi a ɓangaren turare ya ɗauki ɗaya na maza sannan ya ɗauki ɗaya na
mata. Ƙarasowa wajan tayi ta kalle shi shima ya kalle ta amma bai ce mata komai
kafin kuma tayi magana ya wuce. Wajan kayan shayi ya je ya ɗauki coffee sannnan ya
ɗaukarwa Didi milo dan ya san ta akwai son Milo, haka kawai ma sha take yi.
Kafin Narma ta gama shi ya biya kuɗi ya koma mota ya zauna yana duba turaren da ya
siya. Ba jimawa sai gata nan ta fito bayan ta da mai riƙe da ledar da ta yi
siyayya. Yana daga zaune buɗe baya aka saka mata sannan ta shiga motar suka tafi.
Jira yake yaji ta ce ga inda zasu je yaji tayi shiru shi kuma bazai tambaya ba.
Ta wani ƙaramin cafe suka zo wucewa Narma ta ce, "ɗan tsaya a nan zan siyi donut."
Faka motar yayi ta shiga ciki bata jima sosai ba ta dawo ta shiga motar. Wani
almajiri ne yazo wucewa yana bara Omar ya sauke glass ya miƙa masa kuɗi shi kuma
yana addu'a, Omar ya ɗaga glass ɗin bai ko kalle ya ba. Donut ɗin ta buɗe sai ta
kalle shi ta ce, "Ga donut" ta faɗa tana miƙa masa ledar. Kai ya girgiza mata kawai
ya ja motar suka tafi.
Wayarsa ce tayi ƙara ya kalla yaga Goje ne yake masa waya sai ya ɗauka ya saka a
kunne Goje ya ce, "Damisa babbar Yaya ce babu lafiya, yanzu ta dawo daga unguwa."
"Subahanallah! Me ya same ta?" Ya tambaya a gigice. Goje ya ce, "Bamu sani ba,
kawai mun ga saukarta daga napep tana jiri kamar zata faɗi."
"Gani nan" ya faɗq yana yanke wayar tare da ƙara speed ɗin motar.
Kallon sa Narma take tana mamakin Wacece babu lafiya haka ya damu?. Sannan mamakin
kanta take yi wai ita Narma itace driver yake amsa mata waya a mota bata ɗauki
mataki ba, ita kanta ta san ta canja.
Gani tayi sun wuce hanyar su ta kalle shi ta ce, "gida fa zan je." Ai ko kula ta ma
bai yi ba sai da ya ganshi a ƙofar gidan su ya fita a gigice ya shiga gidan. A
kwance ya samu Didi kana ganin ta ka san bata da lafiya, ya tallafo ta jikinsa ya
ce, "Sannu Didi, tashi mu je asibiti." Ta kalle shi ta ce, "A'a Omar, ba sai naje
ba."
"Wallahi sai kin je, ki tashi mu je ko na ɗauke ki wallahi." Jin abinda ya ce sai
tayi murmushi ta miƙe ya riƙe hannunta suka fito, gidan ma a buɗe ya barshi saboda
su Bash suna nan.
Motar da taga ya buɗe mata gaba ne ya bata mamaki, duk da tana cikin ciwo bayan ya
shigo sai sa ta ce, "Omar motar waye wannan?." Narma da take baya ta maimaita Omar
a zuciyarta tana cewa, _Dama sunan sa Omar? Suna mai daɗi. Shiyasa yake da fushi
mana da yawa masu suna Omar haka suke._ bai bata Didi amsa ba ya ja motar ta ce,
"wai yaushe ma ka iya mota Omar?."
Kallon ta ya yi ya ce, "Don Allah ki yi shiru baki da lafiya" ya faɗa yana taɓa
goshinta yaji zafi sosai. Narma da take baya ta ce, "Sannu, ya jiki?."
Didi kanta ciwo yake ɗakyarta iya waiwayowa bata ma iya gane wacece sosai ba, ta
ɗaga kai kawai daga nan tayi shiru. Narma dai mamaki take yi ko wacece wannan? Ya
ruɗe tunda aka ce bata da lafiya, gata kuma har yana haɗa ta da Allah akan tayi
shiru cikin rarrashi, lallai ko wacece tana da mahimmaci a gare shi.
Asibitin da suka je aka yiwa Narma dressing nan suka je ya fito da kansa ya riƙe
Didi suka shiga asibitin. Narma ganin yadda jikin Didi yake rawa sai ta bata
tausayi sosai daman ita akwai tausayin mara lafiya hakan ya saka ta fito itama ta
bi bayan su. Kwantar da Didi aka yi akan gado aka yi mata allura kafin a ɗauki
jininta a gwada a dawo a fara yi mata treatment ɗin malaria.
Ɗakin gado biyu ne a ciki amma Didi ce kawai a kwance, Narma tana jingine da bango
tana kallon Didi da aka gama saka mata ruwa bacci ya ɗauke ta. Hannun Didi ya riƙe
wanda aka sakawa ruwan ganin zai faɗi ya ajjiye a gefen ta ya zare mata hijjabin
jikinta ya sake taɓa wuyanta. Ƙaramin tsaki ya yi jin har lokacin da zazzaɓin ya
ce, "Sai da nace mata kar ta fita amma taƙi ji."
Narma ita dai kallon sa take yi domin mamaki yake bata sosai, gabaɗaya ya sauya
mata ya yi sanyi damuwar rashin lafiyar wacce bata san alaƙar su ba ta canja shi.
Kana jin yadda yake magana kasan ko wacece wannan ya damu da ita sosai. Kallon
gefen ta ya yi yaga tana kallonsa sai a lokacin ma shi ya tuna da ita dan wallahi
tunda yaga yadda Didi take ya manta da wata Narma a bayan mota. Sai Narma tayi
murmushi ta ce, "Zata samu sauƙi in sha Allah." Kai ya girgiza bai ce komai ba,
amma yaji ta burge shi sosai.
Awa ɗaya suka kwashe a asibitin dan shi bazai iya tafiya ya bar Didi ba, ita kuma
Narma duk ta gaji sosai. Bai ma lura da yanayin ta ba, abinda ya sani ko babanta ne
zai zo bazai bar Didi ya tafi wani waje ba. Ya kalle ta ya ce, "zan kira waya azo a
mayar dake gida yanzu." Narma ta ce, "A'a, ka bari ta farka sai mu tafi gabaɗaua,
jikinta bai yi worst ɗin da za'a yi addminting nata ba." Shiru kawai ya yi bai sake
cewa komai ba. Fita ya yi ya yi sallar magriba ya dawo a lokacin Didi ta buɗe ido.
Bayan ya dawo ya ƙaraso inda take ya riƙe hannunta ya zaunar da ita akan gadon ya
ce, "ya jikin?."
Didi ta ce, "na ji sauƙi sosai, ciwon kai ya rage sai rashin ƙarfin jiki da babu."
"Shima zaki daina ji in sha Allah." Ba sake magana ba ya fita jim kaɗan ya dawo ya
kalle ta ya ce, "zamu tafi gida, ga magani da allurai an bayar, ai kin ce jikar
Hajja ta iya allura ko?." Didi ta ɗaga masa kai, ya riƙota ta tashi tsaye ya saka
mata hijjabi da kansa ya riƙe hannunta ya ce, "Mu je gida." Kallon Narma tayi ta
ce, "Ka bar baƙuwar ta ka."
"Wacce baƙuwa?" Ya furta yana kallon Narma dan wallahi ya sake mantawa da ita.
Narma ta ɗan saki fuska kaɗan ta biyo bayan su. Yanzun ma Didi ya buɗewa gaba ta
shiga, Narma ta shiga baya suka sake komawa gidan Didi. Narma tana mamaki kenan
itace bazai buɗewa ƙofa ba tunda gashi yana buɗewa wacce bata sani ba. Suna tsayawa
Narma ta ce, "Allah ya ƙara sauƙi."
Didi ta kalle ta ta ce, "Amin. na gode Barr Nass." Narma bata yi mamaki yadda ta
santa ba tayi mata murmushi ta fita.
Bayan sun shiga Didi ta ce, "ka bar ni kaje ka mayar da ita gida, tayi ƙoƙari sosai
wallahi." Ya kalli Didi ya ce, "zan kai ta, so nake na tabbatar kin samu lafiya."
"Na samu lafiya Omar, ka je ka mayar da ita ba kowa ne zai yarda da irin haka ba."
Bai ce komai ba ya fita ya shiga motar bai ce mata komai ba har suka je gidan.
Fitowa yayi daga motar bayan ta fito ta kalle shi ta ce, "Allah ya ƙara lafiya, a
gaishe ta." Dan kawai kallon sa take yi ne ya saka taga bakin sa ya amsa da amin,
amma maganar ko kan harshensa bata zo ba balle laɓɓansa. Ya miƙa mata key ta
girgiza kai ta ce, "kaje da motar saboda kana da mara lafiya, kaje da ita kawai."
Kai ya girgiza ya ce, "bana buƙata" ya faɗa yana sake miƙa mata key ɗin.
"Ka je dashi." Ya girgiza kai ya ce, "bani da buƙata, na gode."
Murmushi tayi jin yana yi mata godiya ta karɓi key ɗin har ya juya ta ce, "Omar!."
Wani iri ya ji a jikinsa, ya waiwayo ya kalle ta ta ce, "Ranar da aka yanke ni a
hannu kaine ka biya kuɗin asibiti, na manta ban biya ka ba. Please ka bani account
number ɗin ka na tura maka."
Kamar zai yi magana sai ya fasa ya ɗaga kai kawai yana juyawa ya fita, ta bishi da
kallo tana murmushin da bata san dalili ba. Mai gadi ta kira ta bashi key ɗin motar
ta ce ya kwaso mata kaya ya shigar mata dasu ita kuma ta shiga ciki.
Omar kuwa haka ya koma gida sunansa da ta kira yake ji har cikin zuciyarsa
bai san lokacin ba, ya yi murmushi Didi ta kalle shi ta ce, "murmushin me ka ke
yi?." Ya ƙarasa shiga yana kallon ta ya ce, "ya jikin naki? Na ɗauka ma kin yi
bacci kin huta."
"Ban yi bacci ba."
"Abinci fa?."
"Na ɗan ci, Hajja ce ta ta aiko min da abinci yanzu." Ya girgiza kai yana kallon ta
ya ce, "To yanzu ki ki kwanta ki huta. Sai da nace miki kar ki je gidan bikin nan
kika ƙi ji, wataƙila wani abun suka yi miki dan ki yi rashin lafiya daman ba son ki
suke yi ba."
Tayi ƴar dariya ta ce, "naji, ko ma meye dai ƴan uwana ne." Ya taɓe baki bai yi
magana ba. Tana so tayi masa maganar Narma da inda ya koyi mota amma bata jin
ƙarfin jiki hakan ya saka ta tashi taje ta kwanta shi ma ya fita zuciyarsa cike da
tunani kala-kala.
Washe gari bai fita ba har yamma sannan ya je gidan dan yaga kiran Narma bai ɗauka
bane. Lokacin da ya je gidan shiru babu komai duk bai ga masu aikin ba bai damu ba
ya yi zamansa a inda ya saba zama. Ihu ya dinga ji daga cikin gida, da farko ya
ɗauka kunnensa ne amma sai yaji abun ya yi yawa ihu ake sosai ana neman taimako.
Kamar kar ya shiga sai kuma ya miƙe ya shiga falon gidan dan bai san abinda ya faru
a ciki ba, a daidai lokacin Narma ta sakko a guje daga ita sai towel ƙarami wanda
ko cinyar ta bai gama ɓoyewa ba, kanta babu ɗankwali tana ihu kamar wacce aka biyo.
Ganinsa a tsaye sai kawai ta yo inda yake ya yi saurin yin baya dan yaga ƙoƙarin
rungume shi take yi.
"Geckos a toilet ɗina, ka taimaka min ka kashe shi tsoronsa nake ji." Takaicin da
Omar ya ji ji yayi kamar ya tsinke ta da mari ya tsaya kawai