Advertisements
Chapter 25 Reading KIRAN RABO BOOK1 CMPLT BY NANA HALEEMA BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

KIRAN RABO BOOK1 CMPLT BY NANA HALEEMA

Author :  NANA HALEEMA Category :  Complete Novels

Chapter   25 / 28

72K to 75K   out of 83.2K words

bana jin tsoro komai kuma bana tsoron kowa. Ki kwantar da
hankali ki daina kuka, babu abinda zai same ni sai alkhairi."

Didi tayi ajiyar zuciya ta ce, "ai shikenan" ta faɗa cikin rashin mafita dan ta san
bazai bari ɗin ba kamar yadda yace. Ganin ta a yanayin damuwa sai ya yi ƙoƙarin
kawar mata da tunani ya ce, "Ya zancen AbdulHamid? Kwana biyu bana ganinsa." Didi a
sanyaye ta ce, "Ta ya zaka ganshi kullum kana ɗaki kana soyayya?."
"Hmm! Saura wata nawa bikin?."
"Ban sani ba" ta bashi amsa a taƙaice tana miƙewa ta shiga ɗaki ta bar masa falon.

Murmushi ya yi dan ya san haushinsa take ji, shi kam tunda ya ɗaura ɗammaara bazai
kwance ba. Kiran Narma ne ya shigo wayarsa ya ɗauka ya ji ya ce, "Faruk na shigo
Kano, Ina so mu yi magana da gaggawa, kuma zuwa dare zan koma Abuja. Na karo Mum
gaisuwar rasuwa ne." Daƙyar ya ce, "maganar meye?."
"Ni dai Ina so mu haɗu, zaka zo ko nazo gidan ku?." Numfashi ya sauke kana ya ce,
"kina ina?." Narma ta ce, "Ina guest house, amma ba wanda ka sani ba. Ina zaka zo
zan baka address ɗin, ko kuma naje wancan da ka sani sai mu haɗu."

Shiru yayi yana nazari akan zuwan kamar bazai ce komai ba, ta san halinsa akan
wannan shirun yanzu sai ya ɓata mata lokaci har lokacin tafiyar su ya yi. Ta ce,
"please na faɗa maka da wuri zamu bar Kano."
"Zan zo" ya bata amsa taƙaice kafin ya kashe wayar. Ba jimawa yaji ƙarar messege ya
miƙe ya fita daga falon.

Da kayan jikinsa ya tafi tunda Didi ta laqaba masa saka mayan kaya ranar
juma'a. Bashir ne ya kai shi a machine ya kuma saka shi ya tsaya ya jira shi ya
fito su tafi. Kafin ya zo Narma ta sanar da zuwan da hakan ya saka kai tsaye aka
masa iso zuwa harabar gidan. Kiran ta ya yi a waya ya ce, "ki fito." Narma a
sanyaye ta ce, "don soyayyar ka da annabi Muhammad S.A.W ka shigo, ba don halina
ba" ta faɗa dan ta san zai ce bazai ce bazai shiga ba.

Jin magiya da tayi masa sai ya kashe wayar bashi da zaɓin da ya wuce shiga inda
nuna masa matsayin nan ne hanya. Tafkeken falo ne mai kyau da tsari, babu haukan
ado a cikin sa amma ya tsaru irin sa ake kira da luxury parlour. Tana tsaye a falon
cikin riga da siket na atamfa ta yi mata matuƙar kyau. Kasancewar atamfar baƙa ce
sai ta haska farar fatarta sosai.
Ta ɗame kamar ko yaushe, daƙyar take iya motsawa a cikin siket din. Rigar kuwa
tsabar kamata da tayi gabaɗaya ana ganin saman ƙirjinta, gashi bata da tsaho in ta
ɗaga hannu ana hango cibiyarta. Kallon farko in kayi mata zaka ga shigar ta ƙara
mata kyau, amma in ka nutsu zaka fahimci fidda tsaraici ƙarara a tare da ita.

Bai san yana kallon ta sai da yaji ta a jikinsa ta rungume shi da sunan welcome
hug. Shiru yayi kamar ruwa ya cinye shi, shi bai yi hugging nata ba kuma bai
ƙoƙarin cire ta a jikinsa ba. "Nayi kewar ka" ta faɗa tana kwance a jikisa tana jin
farin ciki da nutsuwa na shiga jikin ta. Maganar da ta faɗa ne ya saka shi janye ta
daga jikinsa yana binta da shegiyar harara. Da yatsa ya nuna ta ya ce, "gargaɗi na
karshe zan miki, kar ki sake aikata haka, kar ki sake cewa zaki riƙe ni, kar hakan
ya sake faruwa in ba haka baza ki sake ganina a inda ki ke ba!."

Narma ta shagwaɓe ta ce, "I'm sorry, I just missed you ne shiyasa." Ƙaramin tsaki
ya ja sai ta ce, "i'm apologize fa, smile please." Sake bashi haushi tayi dan shi
baya son magana da turanci, duk abinda ta ce yaji amma baya ra'ayin ayi masa magana
yaren. Murmushi tayi ganin ya sake tamke fuska, ita hakan ma yana matuƙar burge ta
wallahi, sake ƙara mata ƙaunarsa yanayin sa yake yi a zuciyarta.

"Have a seat" ta faɗa tana nuna masa wajan zama. Kallon ta yayi da birkitattun
idanunsa, yana ayyana dole ya taka mata burki akan turancin nan kafin hakan ya saka
ya tsane ta. Bai musu ba ya zauna ta zauna nesa dashi kaɗan ta ce, "kayi kyau
Faruk! Sai naga kamar ana ƙara maka kyau ne sosai." Kallon ta ya yi jin wata magana
mai kama da zagi dan ya wuce zolaya, shi bai ce tayi kyau ba sai ita zata faɗa? Ina
kyaun a wajansa.

Daman ta gama shirya center table ta kalle shi bata damu da rashin bashi amsa ba ta
ce, "bismillah." Kallon abinda ta nuna ya yi ya kalle ta ya ce, "ki faɗa min
dalilin ki na kira nan." Ta langwaɓar da kai ta ce, "Amma ka sha ko ruwa ne ko? Ni
wallahi kamar baka yi kewata ba sai ɗaure fuska ka ke, don Allah kayi murmushi."

Kallon ta ya yi suka faɗa ido ya ce, "zuwan da nayi bai nuna miki abinda kike
tunani ba?." Sai ta yi murmushi cikin zallar shagwaɓar da take sake canja masa
yanayi ta ce, "haka ne my Faruk. Da kace zaka zo naji matuƙar farin ciki, domin
kuwa na san tabbas na babban samu matsayi a wajan ka."

"To Ina jinki." Narma ta gyara zama ta ce, "Yaushe za ka zo Abuja ku haɗu da Dad
ɗina? Ba a matsayin Tiger ba, a matsayin Faruk inlwa ɗinsa. Yaushe zaka zo?." Bata
ji ya amsa ba hakan ya saka ta ce, "Ina so kaje don ya san da zaman soyayyar mu
Faruk, bana son yin aure da wuri, amma tunda na fara sonka nake ji a zuciyata ina
son yin aure da gaggawa."

Omar ya kalle ta yana wani tunani, ya rasa meyasa in ta yi zancen aure wani lokacin
zuciyarsa bata karɓa, sai ya dinga ji kamar shi bazai aureta ba, sai ya dinga ji
shi kamar ba aurenta yake son yi ba akwai abinda yake zuciyarsa ba aure ba. Ya
kawar da tunanin ya ce, "na faɗa miki na shirya yin aure ne yanzu? Kuma shi ne ya
ce nazo?."

"A'a, ni nake so kazo saboda ya san da kai ayi maganar aure a wuce wajan kawai."
Kai ya girgiza ya ce, "baza ki samu matsala ba?."
"Babu wata matsala."
"To zan duba na gani, in na samu lokaci zan sanar dake sai ki faɗa masa." Narma
tayi murmushin jin daɗi ta ce, "thank you my Husband to be. I can't wait to be your
wife, I feel like na jawo lokacin da zaka kasance miji a gare ni. Ranar da aka ce
na zama matar ka bazan iya bacci ba."

Gyara zama y yi ya ce, "Narma!." In ya faɗi sunan nan kamar ya soka mata abu a
zuciya haka take ji, bata taɓa jin wanda yake faɗar sunan ta daidai kamar sa ba. Ta
narke tana kallon sa ya ce, "kar ki sake yi min wani yare in ba hausa ba in muna
tare kin gane?." Jin yadda ya faɗa a kausashe sai ta nutsu sosai ta ce, "in sha
Allah bazan sake ba. I'm sorry..." hararar da ya yi mata ya saka ta tsorata sosai
ta ce, "ka yi haƙuri" ta faɗa a sanyaye. Bata taɓa zaton soyayya zata saka ta
tsoron wata halitta irin Omar ba, tsoronsa take ji matuƙa bata son abinda zai ɓata
masa rai ko kaɗan. Shiyasa take kiyaye dokikinsa dan a zauna lafiya.

"Yaushe zaka saba dani ne Faruk? Ka kasa sakin jiki dani har yanzu. Ina sonka, da
kai kaɗai nake so na rayu. Don Allah kar ka dinga amfani da rauni na akan sonka
kana cutar dani." Kallon ta ya yi bai san lokacin da ya yi murmushi ba, kamar
shashasha itama sai tayi murmushi ta ce, "na gode da wannan kyauta Faruk."

Miƙewa tsaye ya yi alamun zai tafi ta ce, "Zaka tafi ko ruwa baka sha ba."
"Zan sha wani lokaci" ya bata amsa ba tare da ya kalle ta ba, dan in yana kallon ta
wani ne yake shiga jiki sa take sai yanayinsa ya canja.

Miƙewa itama ta yi ta kalli window ta kalle shi ta ce, "Ga irin wajan zaman ka can
a wancan gidan, naga kana son zama a gazebo, dole gidan auren mu kasance da gazebo
saboda ka shiga ka huta" ta faɗa cikin son burgewa. Kallon ta ya yi kafin ya ɗauke
kai ya ce, "kina tunanin samunta a aurena?."

Narma jin ya bata amsa sai ta sake karya murya cikin iyayi ta ce, "ko ba yanzu ba
ko nan gaba. Kuma gidana da nake ginawa akwai."
"Gidan ki!" ya maimaita yana yi mata kallon bakin da hankali kafin ya sake cewa,
"kina tunanin in Allah ya ƙaddara na aure ki ni Omar zan zauna a gidan da yake
naki? Hmmm baki san Omar ba har yanzu, ki yi gaggawar canja tunaninki a kan hakan"
ya sake cewa, "In har da gaske kina son auren Omar ki san irin tunanin da zaki yi"
ya faɗa dan ya tuna mata, dan shi ba irin mazan da suke zama a gidan mata bane,
gwara ya yi mata gargaɗi da babbar murya.


Narma a sanyaye ta ce, "Ina yi mana fata a rayuwar auren mu mu samar da ita."
"Dakyau!" ya furta yana fita ta biyo bayan sa tana ta yi masa shagwaɓa yana sharewa
kamar bai gani ba ko kamar baya jin shagwaɓarta a jikinsa, yana ji kawai bazai nuna
bane, dan in ya nuna mata shine a ruwa. A haka suka yi sallama ya fita ya samu
Bashir na jiran sa suka koma gidan Didi.


Bayan fitar Omar Didi tana zaune rana ta buɗe sosai tana shan iskar fankar
solar taji anyi sallama. Amsawa tayi tana jiran mai shigowa sai kawai suka haɗa ido
da Nayla. Didi ta wara ido ta ce, "Nayla!." Nayla tayi dariya ta ƙaraso kusa da
Didi ta zauna ta ce, "Na'am Didi." Didi da farin ciki ta ce, "Saukar yaushe? Wannan
bazata haka."
"Saukar ɗazu. Ina yini." Didi ta amsa da fara'a tana tambayar ya mutanen gida ta
tabbatar mata da kowa lafiyar sa lau.

Didi ta ce, "wallahi nayi kewar ki Nayla, haka kawai nake ji bana so ki bar Kano."
Nayla tayi dariya ta ce, "wallahi nima bana son barin Kano Didi, amma ya zama dole
dan yanzu na fara aiki ma a can."
"Ma sha Allah, amma na taya ki murna Nayla. Allah ya sanya alkhairi ya kaɗe
fitina."
"Amin ya rabbi. Na gode sosai Didi."
"Amma kwanaki zaki mana ko?." Nayla tayi dariya ta ce, "Ranar Sunday da safe zan
tafi, kin manta na ce Ina aiki?." Didi ta ce, "kai! Wallahi ban ji daɗi ba. Amma
babu komai in sha Allah ɗan Kano zaki aura, kin ga sai dawo Kano gabaɗaya mu dinga
ganin ki."

Nayla tayi murmushi amma a zuciyar tana aiyana in sha Allah ƙaninki zan aura Didi,
amma a bayyane sai bata ce komai ba. Didi ta kalle ta tace, "an sha saudia. Ina
fatan kin roƙawa mutumin ki shiriya a wajan Allah kamar yadda na ce, kin yi min?."
Wani iri taji a zuciyarta, domin kuwa babu ranar da zata fito ta koma bata ambaci
sunan Omar a addu'arta ba, ba wai tana cewa Allah ya bata shi bane, tana roƙon
Allah ya shirya shi ya cire masa dukkan abinda yake yi ya dawo mutum kamar kowa.
Ita kanta bata san sau dubu nawa tayi masa addu'a ba. Har ɗawafi ta yi akan Allah
ya canja Omar, ta yi ɗawafi bama sau ɗaya ba.

A bayyane ta ce, "Nayi masa sosai Didi, ba ma shi kaɗai ba har da ke. A jikina nake
jin Allah zai amsa da gaggawa." Didi ta ɗaga hannu ta ce, "Allah Amin" ta kalli
Nayla ta ce, "na gode Nayla, Allah ya bar zumunci." Nayla tayi murmushi ta amsa da
amin. Didi ta kalle ta tana murmushi ta ce, "wallahi Nayla haka nan Allah ya saka
min ƙaunarki, Ina jinki kamar ƙanwata." Nayla ta murmusa ta ce, "nima Ina jinki
kamar yayata Didi."

Didi tayi murmushi ta ce, "Amma Nayla naga kin rame, kin yi rashin lafiya ne?."
Nayla ta girgiza kai ta ce, "haka ake cewa na rame amma ni bana gani, lafiya ta lau
kawai kiɓar nake so na rage." Didi tayi dariya ta ce, "ai baki da kiɓa Nayla, gaki
nan ƴar chubby dake in kika rame ai baza ki yi kyau ba. Gaskiya ki daina." Nayla
tayi dariya kawai bata ce komai ba sai ledar da ta shigo da ita ta miƙawa Didi ta
ce, "ga tsabar ki."

Didi ta karɓa ta ce, "Nayla harda tsaraba? Ai ni iya addu'ar da kika yi min itace
babbar tsaraba a wajena." Didi ta buɗe ta ga doguwar riga irin mai babban mayafin
nan da ake yayi, original ƴar Saudia dan a yanayin jikinta ma zaka tabbatar da ba
fa irin ƴan Nigeria ba ce. Sai zamzam da chocolate da kuma cross shoe. Didi ta fara
godiya Nayla ta ce, "Didi yanzu ki ka ce ni ƙanwarki ce ko? Don Allah ki bari."

Didi bata daina ba ta cigaba da addu'a tana yi mata godiya. Nayla ta sake bata leda
ta ce, "Ga na...." Sai ta rasa wanne suna zata kira shi, Omar zata ce ko Tiger?
Didi kallon ta take yi tana so ta ji na waye, Nayla ta ce, "Na Yaya Omar."

Didi tayi dariyar tsokana ta ce, "A'a, harda su kaza a cin danƙoo? Kuma yaushe Omar
ɗin ya zama Yaya Omar?." Nayla tayi murmushi ganin tana tsokanarta, ta karɓa ta
buɗe taga doguwar riga irin ta maza mai dogon hannu, ga wata cover ƙarama mai kyau
a ciki, ta ɗauko ta buɗe idon ta ya faɗa kan lafiyayyar azurfa mai bala'in kyau.

Didi ta kalle ta a sanyaye ta ce, "Nayla duk wannan na Omar ne? Azurfa da take da
tsada a nan ƙasar ma balle a Saudia?. Bayan azurfa ma harda doguwar riga ga wani
abu ma a ciki ina ji" ta faɗa tana fito da ƴar ƙaramar kwalba ta oil perfume ta ce,
"ga turare. Nayla hidimar bata yi yawa ba?."

Nayla ta ce, "Haba Didi wallahi babu komai, an zama ɗaya kar ki damu." Didi tayi ta
ce, "To Nayla, mun gode Allah ya saka da alkhairi ya bar zumunci, Allah ya baki
miji na gari." Nayla ta amsa da amin kafin Didi ta ce, "Su Omar an samu azurfa,
daman hannun nasa babu komai kamar ba saurayi ba, kin taimaka kin fito dashi ya
zama mutum shima kamar kowa. Kwanaki ya je kasuwa zai siya aka ce masa azurfa mai
kyau daga ko dubu talatin ta fara, ya dawo na ce ya baka siyo ba wai ai ba hauka
yake yi ba, ta sha zaman ta." Nayla tayi murmushi kamar yadda Didi take murmushin
itama tana sake yiwa Nayla godiya.

Basu ji sallama ba kawai sun ganshi ya shigo falon, Didi ta kalle shi ta ce,
"shigowa babu sallama Omar?." Kallon Didin ya yi kafin ya kalli wacce take zaune a
kusa da ita yana aiyana wacce baƙuwa ce tazo musu gida. Nayla tunda taji an shigo
an kuma ce Omar ta nutsu ta sunkuyar da kai ƙasa.

Sake kallon Didin ya yi ya ce, "Nayi sallama baki ji ba ne." Ajiyar zuciya Nayla
tayi jin murya sa a kunnen ta, ido ya cikowa da ƙwallar kewarsa da take ji. Didi
jin ajiyar zuciyar da tayi sai ta kalle ta a tausashe tace, "Nayla ki bar jin
tsoron Omar don Allah, wannan ajiyar zuciya ta meye haka? Kar ki dinga cutar kanki
fa." Nayla bata ce komai ba domin Didi baza ta gane ba, ita ba ajiyar zuciyar
tsoron sa take yi ba, ta soyayyar da take yi masa ce.

Ta kalli Omar ta ce, "ga tsaraba Nayla ta kawo maka daga Saudia." Sarai ya gane
Nayla ɗin ya haddace sunanta tsaf a wajan Didi, har mamakin haddace sunanta da yayi
yake yi, da zarar ta ce Nayla fuskarta zata zo idonsa. Bai san me yasa hakan ba
amma ya ɗauki hakan a yawan kiran sunanta da Didi take yi ne, da kuma faɗan da ta
yi masa a gabanta. Basarwa yayi kamar bai gane ba ya ɗage gira sama ya ce, "Wace
haka?."

Wani iri Nayla taji a zuciyarta, amma jin muryarsa na kore waccan damuwar. Didi ta
Harare shi bata yi magana ba ta ce, "ga tsarabar sai kayi mata godiya, nima ta
gwangwaje ni da doguwar riga. Kuma irin ta jikinta sak, ni sai yanzu ma na lura" ta
faɗa tana nuna masa.

"Kin gode" ya faɗa yana niyar juyawa. Didi ta ce, "kai baka gode ba?." Ya kalli
Didi ya kalli Nayla da take zaune kamar munafuka, shi fa wallahi haushi take bashi
ba kamar in ya tuna faɗan da Didi tayi masa a gabanta, tayi masa faɗa tana wajan
kuma ta hana shi ɗaukar mataki sannan ta shigaba da shigowa gidan su. Lokaci ɗaya
yaji haushinta na sosa zuciyarsa. Ya ce, "ai ban roƙa ba ko?." Didi taji babu daɗi
cikin takaici da jin kunya take kallon sa, in da ba a gabanta bane ba da sauƙi,
amma a gaba idon mutum akwai cin fuska sosai.

Sai ya samu kansa da kallon Naylan da take zaune, baƙin gani ya yi domin kuwa
murmushi take yi ga kuma hawaye yana sakkowa daga idanun ta. Ƙaramin tsaki ya yi
dan haushi yaso ya bata, duk da yaga hawaye amma hawayen bai kama da na jin haushi
ba. Ganin kallon da Didi take yi masa sai ya ce, "an gode" daga haka ya fita ta
harari bayansa ta ce, "kaji dashi bahagon mutum kawai. Ni mamaki ma nake yi da
Narma ta iya dakon soyayyarka zuwa yanzu, ko da wanne yanayi ka ke soyayyar oho."

Dam gaban Nayla ya buga bata san ta ɗago tana kallon Didi ba, ganin tana hawaye
jikin Didi ya yi sanyi ta ce, "yi haƙuri kinji Nayla, don Allah ki yi haƙuri."
Nayla bata ce komai ba dan labarin soyayyar tasa take so taji.

Ganin Didi bata sake cewa komai a kai ba sai Nayla ta ce, "Didi yana da budurwa
ne?." Didi ta ce, "yana da wahala dai, Omar Ina ga wata budurwa kema ban da abin
ki. Ɗazu dai ya gama furta min da gaske yana son yarinyar kuma ya shirya aurenta ta
ko wanne hali. Ko waye zai bashi auren ƴarsa oho."

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!" Nayla ta faɗa a bayyane ba tare da ta sani
ba.


*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.

Nana Haleema❤️

*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025

©️*Nana Haleema.*

Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.

*Book 1*
*P 23.*


Jin dogon salatin da Nayla tayi Didi ta kalle ta da mamaki, Nayla tayi saurin cewa,
"Kuma itama tana sonsa? Taɓ bata san waye shi bane." Jin abinda ta ce sai Didi tayi
dariya ta ce, "wallahi

25 / 28