Advertisements
Chapter 28 Reading KIRAN RABO BOOK1 CMPLT BY NANA HALEEMA BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

KIRAN RABO BOOK1 CMPLT BY NANA HALEEMA

Author :  NANA HALEEMA Category :  Complete Novels

Chapter   28 / 28

81K to 83.2K   out of 83.2K words

ya jijjigata cikin fusata ya
ce, "kalle ni, ki dawo hankalinki, ki kalli waɗanda suke gabanki ki daina furta min
shirme. Narma ki dawo hankalinki!" Ya faɗa yana sake jijjigata da ƙarfi. Narma da
ta dafe kunci tana kallon mahaifin nata cikin gigicewa, bai taɓa dukanta ba a
rayuwarta ba sai a wannan lokaci. Omar da yake tsaye ya gaji da wannan surutun ya
ce, "tana cikin hankalinta, da gaske take ni ɗin sirikin ka ne."

Da wata irin fusace Sen ya juya ya nuna da yatsa Omar ya ce, "kar ka sake saka min
baki, da ƴata nake magana" ya jiyo ga Narma ya ce, "faɗa min prank ki ke yi ko? Ko
kuma April fools joke ne?."
Narma in her trembling voice ta ce, "Dad it's not a pranks, da gaske nake maka ni
na gayyato shi. Shine wanda ku ke zaman jiran zuwansa. He's my Faruk!."

Muryar Mum Narma taji ta ce, "Narma what are you saying?." Ta kalli Mum da take
tsaye tashin hankali ya gama bayyana a tare da ita, Narma ta ce, "Mum da gaske
nake, shine Faruk ɗina, kuma shi nake so. Sannan....." Ai bata ƙarasa ba Sen ya
sake tsinke ta da marin da sai tayi ƙara saboda shigarsa jikintq. Minister ne ya
riƙe shi ya ce, "easy mana, control yourself. A kan wannan zaka dinga dukan Narma?
Haba kamar ba kai ba" ya faɗa yana nuna Omar shima ransa a ɓace.

Kallon Omar ya yi da yake tsaye ƙyam yana kallon su one by one. Sen ya girgiza yana
nuna Omar ya ce, "meye ma sunanka?." Omar ya bishi da kallo cikin ko in kula ya ce,
"ka fini sani." Sen ya kalle shi ya ce, "shaye-shayen da ka ke yi ya taɓa maka
ƙwaƙwalwa ko?. Dan in ba mara hankali ba babu wanda zai yi abinda ka yi. Har kana
da zarrar ɗauko ƙazaman ƙafafunka kazo gidana da sunan neman aure?. Na jima Ina jin
ana cewa kawai mahaukatan da haukan su ya wuce ace musu mahaukata sai dai dadbobi,
ban yarda ba sai yanzu. Look at you..." Sai kuma ya dafe kai ya rasa ma abinda zai
ce.

Narma da take kuka ta ce, "Dad ni ce na gayyato shi, kuma ni sonsa nake yi...."
Maganar ta maƙale saboda zaburar da Sen ya yi zai yi kanta Minster ya riƙe shi, Sen
ya kalle shi ya ce, "kana jin abinda take faɗa? Kana jin abinda take cewa?."

Minster ya ce, "ba itace mai laifi ba ai, ga mai laifi nan a tsaye a gaban ka. Ita
meye nata da zaka dinga dukanta? Shi zaka daka ai ba ita ba" ya faɗa yana nuna
masa Omar da yake tsaye yana kallon su. Minister ya sake cewa, "Akwai abinda ya
shirya shiyasa ya yi amfani da asiri wajan mayar da Narma haka, don't judge her
Sen, bata san tana faɗa ba, it's the spell he cast on her that's working."

Narma ta ce, "Ni bai yi min ko wanne asiri ba, ni ce na fara sonsa kuma har yanzu
ina sonsa. Babu wani abu da ya shirya a kaina, yana sona kamar yadda nake sonsa" ta
faɗa da ƙarfi tana daga inda take.

Sen ya rasa abinda zai yi ya kalli Omar da yake tsaye yana kallon sa ya ce, "kai
kuma ka san ƴata ce ka amince har ka ke sonta?."
"Ga zahiri kana gani" Omar ya faɗa yana kallon sa kamar yadda yake kallon sa. Kasa
magana Sen ya yi na wani lokaci kafin ya ce, "ƴar tawa ka zo nan da ka ce min kana
so. Ƴata zaka yiwa asiri? Saboda na haɗa ka zama da ita a waje ɗaya shine ka samu
damar yi mata tsafi?."

Omar ya ce, "ƴarka zaka tambaya, in asiri nayi mata ma ta sani."
"Shut up! Ina magana kana magana dan ka raina ni?."
"Kaine ka haife ni?" Omar ya bashi amsa kai tsaye yana kallon sa kamar yadda yake
kallon sa.

"Ko a matsayin diver Narma baka isa ka zo ba, haɗa numfashin ka da na ta babban
zunubi ne saboda tazarar ku kamar sama da ƙasa ne. Na baka ita ne saboda wani buri
nawa har ka dinga yawo da ita a mota na wani lokaci, amma ba dan haka ba ko a mai
aikin gidan nan baka isa kazo ba. Bana ɗauka mutum aiki sai yana da matakin diploma
a karatu, kai kuwa fa?." Omar ya kalle shi ya ɗora yatsun sa biyu akan goshin sa
kamar ko yaushe ya ce, "ban zo a mai aiki ka ba, amma nazo a sirikinka."

Ai Sen ji ya yi kamar ya zuba masa ruwan zafi, jikinsa har rawa ya ke yi, ya zare
ido ya ce, "me ka ke dashi? Waye kai a duniya?. Ko matsayin mai gadin gidan nan
baka dashi, mai aikin gidan nan dukkan su graduates ne, meye matakin karatun ka?
Faɗa min me ka ke dashi a duniya?.." Omar ya ɗan yi murmushi kalle shi ya ce,
"abinda nake dashi ka ke so ka ji?" Ya kalli Narma da take wajen tana kuka ya sake
kallon Sen ya ce, "zuciyar ƴarka, ita nake dashi."

Fusata Sen matuƙa ya yi ya kai hannu kamar zai mare shi amma sai ya fasa yana jin
zuciyarsa kamar ana zuba masa ruwan zafi saboda ɓacin rai. Minster ne ya ƙaraso
yana kallon Omar ya ce, "Dan kaji last time na yabe ka sai aka ce maka ka kai
matsayin da zaka zo gidan nan neman aure?. Kana da hankali kuwa?."

Omar shima shi ya ke kallo ido cikin ido ya ce, "babu tabbacin kowa yana da hankali
tunda ba ganin hankali sa ake yi ba." Sen ya zabura ya yi kan Omar Minster ya riƙe
shi Sen yana cewa, "ka barni nayi maganin wannan mahaukacin, bar ni na kashe shi
kuma na kashe banza wallahi. Ni zai dinga yiwa hauka a cikin gida? Kalle shi fa?."
Minister ya ce, "ba class ɗin ka bane."

Ya kalli Omar cikin ƙunar rai ya ce, "baka da maraba da dabba a idona, amfanin ka a
gare ni na biya ka kaje ka sadaukar da rayuwarka domin cigabana da na ƴaƴana.
Saboda wannan kawai nake nuna maka so a baki dan bai kai zuciyata ba, in ba dan
haka ba baka ka kai ka ce kana son mai aikin cikin gidan nan ba. Jahili ne kai baka
da ilimin komai, babu inda zaka je a rayuwa a haka zaka ƙare rayuwarka a gagari
akan titi. Ko riƙe gidan ku baka iya yi, Yayarka itace take ciyar da kai ba kaine
ka ke citar da ita ba. A haka ka samu zarar ratso cikin gidan nan ka ce kana son
Narma!? Ka san wacece Narma?."

Omar ransa ya ɓaci sosai, tunda aka fara maganar sai yanzu ransa ya ɓaci hakan ya
saka shi zubawa Sen ido bai ce komai ba. Ganin ya yi shiru Sen ya ce, "Ni Senator
ne, Mahaifiyar Narma tsohuwar ƴar majalisa ce. Narma lawyer ce, ta kai matakin
masters a karatu, tana kuma riƙe da company guda a ƙarƙashinta. Tana juya biliyoyin
kuɗaɗe wanda sai ta saka hannu kuɗin zasu fita. Tana aiki da babban kotun Nigeria,
tana da ikon da zata yi ko wacce irin shari'a a faɗin ƙasar nan. Faɗa min kai
waye?. Ɗan daba ne, mai garari akan titi, ɗan shaye-shaye, jahili, wanda bashi da
ilimi balle a saka ran zai kai wani mataki a nan gaba?. Ko kana so kace ban san
labarin uwarka hiv ce ta kashe ta ba...." Ai bai ƙarasa ba Omar ya damƙi wuyan Sen
jikin sa na rawa.
Narma da take gefe ta yi tsalle ta zo wajan, Nabil da Minster suke ƙoƙarin cire
hannun Omar daga wuyan Sen amma sun kasa. Wani irin wuci Omar yake yi, ransa bai
taɓi ɓaci a duniya kamar yau ba, bai taɓa jin tsanar abu lokaci ɗaya kamar tsanar
Sen ba, bai taɓa ji zai iya aikata komai ba kamar yadda yake ji zai iya shaƙe Sen
har sai ya daina numfashi.

Daƙyar suka cire hannun Omar daga wuyan Sen. Sen yana fitar da numfashi daƙyar Omar
ya nuna shi da yatsa ya ce, "ka san irin kalaman da zaka faɗa a kaina, in ba haka
zaka fara dana sanin sanin Omar a rayuwarka." Minister mamakin ƙarfin halin Omar
yake yi ganin ko tsoro ma shi baya ji. Har gidan Sen yazo ya shaƙe masa wuya kuma
yana faɗar magana mara daɗi.

Sen da ya kammala dawowa hankalinsa ya nuna ya ce, "kaine zaka yi dana sanin sani
waye ni a duniya, zan nuna maka banbancin dake tsakanin aya da tsaƙuwa, zan nuna
maka banbancin da yake tsakanin sama da ƙasa. A yau zaka tabbatar da ka tafka
babban kuskure a cikin rayuwarka, zan shafe danginka kaf da kai kanka."

Waya Sen ya ɗauko yana dannawa hannunsa har rawa yake yi saboda ɓacin rai. Narma ta
riƙe hannu Omar tana ja cikin fitar hayyaci ta ce, "Faruk ka zo mu tafi, ka zo mu
tafi kawai ni zan bika duk inda zaka kaini. Ni Ina sonka har yanzu kuma zan aure
ka. Ka zo mu tafi, na zaɓi na zauna da kai akan zama a gidan nan."

Marin ta Nabil ya yi, ya janye ta gefe tana kuka ya riƙeta gam yadda baza ta iya
ƙwacewa ba. Omar ya kalli Sen muryarsa ta koma can ƙasa saboda ɓacin rai ya ce, "ka
ce babu inda zan iya zuwa ko?" Sai ya girgiza kai ya ce, "zan tabbatar maka da zan
iya kaiwa irin matakin da ka ke kai a yanzu, zan iya zuwa inda kai baka isa ka je.
Abinda nake so da kai ka kasance a raye."


"Har abada! Kai da zuwa irin matsayin da na taka a rayuwa har Allah ya tashi
duniya. Ko da ace a lahira ana mulki baka isa kayi irin abinda na yi ba, a lahirar
ma baka isa ka zo inda nake ba. Aljanna ma akwai irin ta mu, akwai irin ta ku. In
ka ci sa'a ka shiga aljanna ko a cikin ta baza ka hangi inda nake ba, na yi maka
nisa mai tsahon gaske a lahira balle kuma a duniya. Kana jahili wanda ko jss bai
kammala ba wanne mataki zaka je? A haka rayuwarka zata ƙare, daman domin ku yi mana
amfani Allah ya halicce ku, kuma kun yi mana amfani rayuwar mu ta yi kyau. Sai kaje
ka cigaba da zaman chamber ana shan wiwi."

Kallon sa yake yi shima kallon sa yake yi, kowa ransa a ɓace yake ba kamar Omar da
yake yi kamar ya murƙushe Senator.

Sen ya ce, "Narma ba daidai dakai take ba, kar kayi mafarkin mallakarta a cikin
rayuwarka domin daga yau zaman duniya bazai sake yi maka daɗi ba, zaka koma rayuwa
irin ta gidan yari har ƙarshen rayuwarka. Zan iya kashe ka kuma na kashe banza
wallahi, bana son aikata hakan ba dan ina tausayin ɗaukar ranka ba, sai dan nafi so
wahala ta yi ƙasa-ƙasa da ƙasusuwan jikinka. Wahala da baƙin ciki nake so su ga
bayanka ba bindiga ko wuƙa ba. Sai ka yi dana sanin wannan rana a rayuwarka, sai
kayi dana sanin sanin waye Senator Sagir a cikin rayuwarka."

Omar ya yi murmushi yana kallonsa ya ce, "wahala bata kisa, babu wahalar da zaka
bani wacce zata kashe ni Sagir!. Babu inda zan je, zan kasance da raina, zan cigaba
da rayuwa fiye da yadda na yi a baya. Zan kuma kai matakin da kai baka kai shi ba a
rayuwarka, abinda nake so da kai kawai ka kasance a raye Sagir!" Ya faɗa yana
girgiza kai yana kallonsa.


A lokacin ƴan sanda suka shigo Sen ya kalle su ya ce, "yayi attacking ɗin kashe ni,
sannan ya yi ƙoƙarin sace Narma. A tabbatar da rayuwarsa ta ƙare a prison" ya faɗa
yana kallon Omar da shima shi yake kallo.

Narma ta fincike hannunta daga na Nabil tayi inda Omar yake a gigice, Sen ya riƙeta
gam tana kuka tana ƙoƙarin ƙwacewa tana cewa, "A'a Dad! kar ka aikata haka, ka ƙale
shi don Allah. Ni nace yazo ba shi ya zo da kansa ba, ni ce nake sonsa Dad, ni nake
so na aure shi. Don Allah kar ka yi masa komai Ina sonsa...!!" ta faɗa cikin kuka
sosai tana ƙoƙarin fincikewa.

Ƴan sandan wajan Omar suka nufo shi kuma kallon Sen ya ke yi, ya kalli Narma da
take kuka ya sake kallon Sen ya ce, "zan tabbatar maka da abinda na faɗa, in har
kana so ka tabbatar kar ka bari ka mutu! Ka kasance a raye, sai na shayar da kai
mamakin da baka taɓa shiga irinsa ba a rayuwa." Sen a fusace ya ce, "ku tafi dashi
daga gidan nan!" Ya faɗa cikin tsawa matuƙa.

Kallon Narma Omar ya yi itama shi take kallo tana faɗin, "please Faruk!." Ɗauke kai
ya yi daga kanta, ya sake kallon mahaifinta kafin ya girgiza kai akwai bai ce komai
ba. Fita aka yi da su Omar aka saka su a mota, fitar motar daga cikin gidan ya yi
daidai da zubewar Narma a ƙasa ta faɗi summiya.

End of book 1!

_To fa Book 1 ya tiƙe a nan!!. Ya ku ke ganin abin zai kasance? Omar zai auri Narma
bayan duk abinda ya faru? Nayla fa? Omar zai aureta ko kuma zata cigaba da dakon
soyayyarsa?. Burin Maman su Nayla zai cika ko bazai cika ba? Shin Omar zai kai
matakin da ya faɗawa Sen ko bazai kai ba?. To wai meye asalin su Omar? Meyasa ya
tsani danginsa? Meyasa ya tsani dangin uwa da uba?. Didi zata yi aure ko baza ta yi
ba?. Wanne irin rabo ne zai kira Omar? Wanne irin Rabo ne zai kira Nayla? Wanne
irin rabo ne zai kira Narma?._

_Duk amsoshin tambayoyin nan suna cikin Book 2&3, labarin yana da tsaho doguwar
tafiya ce, zamu shiga jirgin book 2&3 ya lula damu cikin duniyar KIRAN RABO dan jin
abinda zai kasance. Free ya ƙare book 2&3 naira 500 for regular group, vip kuma
naira 1000 ne kacal. Akwai vip2 zai zo a arewabooks in sha Allah. domin biyan kudi
ka tuntubi wannan number via WhatsApp wa.me/2349030398006 wa.me/234701 809 8175 Dm
to subscribe yours._

_Na gode da soyayyarku a gare ni da littafin nan, Allah ya ƙara zumunci. Allah ya
sa ku nuna min ƙauna ku gigita ni da shiga paid group._😩❤️❤️

Nana Haleema❤️

28 / 28