Advertisements
Chapter 27 Reading KIRAN RABO BOOK1 CMPLT BY NANA HALEEMA BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

KIRAN RABO BOOK1 CMPLT BY NANA HALEEMA

Author :  NANA HALEEMA Category :  Complete Novels

Chapter   27 / 28

78K to 81K   out of 83.2K words

waje guda ya
kalle ta ya ce, "ni ai na faɗa mata ban shirya aure ba, tana so iyayenta su san da
ni ne kawai." Zuba masa ido tayi tana kallonsa, a tausashe ta ce, "Omar anya baka
yi ganganci da rayuwarka ba? Anya baka saka zuciyarka a tsaka mai wuya ba?. Sai
nake ji kamar akwai wani shiri da yarinyar ta shirya maka Omar."

"Didi babu wani shiri sannan babu abinda zai faru, Ina sonta kuma zan je wajan
iyayenta matsayin mai sonta."
"Omar kenan, ta ya iyayenta zasu karɓe ka a matsayin mai son ƴar su?. Tausayi ka ke
bani wallahi, domin wanna hasashe naka ba mai yuwa bane Omar." Kallon ta ya yi ya
ce, "Didi bana so kina ce min haka, wai ita wacece da zaki dinga cewa tausayi nake
baki a kanta?."

"Ita ba tsarar ka bace ba Omar, ita ba daidai da kai ba ce ba Omar." Kallon Didin
ya ke yi na wani lokacin kafin ya ce, "Didi!."
"Omar."
"Bakya son abinda nake so ne?."
"Omar Ina so mana."
"Meyasa ki ke faɗar abinda ki ke faɗa indai haka ne."
"Hmmm!" Didi ta faɗa a taƙaice bata ce komai ba. Omar ya ce, "kawai ki ta ya ni da
addu'a." Didi ta ce, "Omar addu'a ko yaushe Ina yi maka ita ai, Allah ya baka
abinda ka ke so in alkhairi ce."

Shiru ya yi Disi ta ce, "kuma kaima ka dinga addu'a, kana da ƙoƙarin ibada na sani,
amma ka ƙara daga yadda ka ke Omar. Ka cigaba da yaƙi da shaiɗan kana tashi cikin
dare, wani lokacin shaiɗan yana galaba a kanka. Ni shiyasa nake son ka samu mace
nutsatstsiya mai ilimi wacce zata cigaba da taimaka maka wajan bunƙasa ibadar ka."

Kallon Didi ya ke yi har ta gama magana kafin ya ce, "oh kina nufin dai ban cikin
masu ibada? Kina so ki ce mace ce zata saka na yi ko ta hana?."
"Ni ban ce baka yi, in na ce baka ibada ai ƙarya nake yi. Ko a unguwar nan an
shaida sallah bata wuce ka a masallaci, sannan ni shaida ce, tunda ni nake rayuwa
da kai. Ko a gaban Allah zanyi shaidar kana da ibada daidai gwargwado. Ina so ka
ƙara ne kawai Omar, amma batun mace zata saka ka yi ko ka bari wannan zai faru."
Taɓe baki ya yi bai ce komai ba ya yi shiru, ya lura adawa take yi da Narma shiyasa
bai tanka ba.

Didi ta ce, "To a yadda ka ke ɗin nan Omar in ba dan kana ibadar ba ai da ban san
ya zaka zama, Allah sai ya dubi maraicina ya taimake ni ya saka maka son ibadar a
zuciyar. Malam Salahudden kuma shine sila, shi ya ɗora ka a kan hanya gashi yanzu
baya duniya ka ɗore akan abinda ya ɗora ka a kai. Inda ace ibadar ma bata dame ka
ba ai da yanzu ka kashe ni da raina." Ƙala bai ce ba, ya share ta yana kallon wani
waje daban kamar ba da shi take maganar ba.

•••••••

Nayla lokacin da Didi ta yanke wayar taji sallamar Omar hakan ya saka ta yin shiru
tana sauke numfashi a hankali. Dawowar ta daga office kenan ta samu kiran wayar
Didi. Tashi ta yi ta shiga banɗaki tayi wanka lokacin har anyi magrib, ta fito ta
yi sallah sannan ta fito falo. Tana fitowa Auta ya tare ta ya ce, "Anty Nayla ki zo
in ji Mama."

Da to ta amsa tabi bayan sa zuwa ɗakin Mama ta shiga da sallama. Amsawa tayi tana
kallon ta har ta shiga kafin ta ce, "Abiy ya ce a sanar dake kina da baƙo in anyi
sallar i'sha." Nayla ta ce, "To" ta faɗa a sanyaye tana juyawa zata fita, Mama ta
ce, "Nayla bakya son faɗa min damuwarki ko?." Nayla ta kulle ido ta buɗe ta juyo a
hankali ta ce, "Mama ki yi haƙuri, ba na ƙi faɗa miki bane, kawai babu damuwar ne
shiyasa." Mama ta ce, "Shikenan jeki."

Nayla ta fito zuwa falo ta zuba abinci tana ta jagalgala shi amma ta kasa ci.
Daƙyar ta iya cin kaɗan kafin ta tashi ta shiga ɗaki ta zauna kawai babu abinda
take yi. Cikin wannan tunani har aka yi sallar i'sha ta tashi tayi sallah bayan ta
idar hijjabi ta saka kawai akan kayan jikin ta dan na shan iska ne ba canja kaya
zata yi ba.

Sallama akayi a ɗakin nata ta juyo taga Yaya da kansa ya kalle ta ya ce, "Nayla ga
baƙon ki can a babban falo, ki yi sauri yana jiran ki."

Kai ta ɗaga kawai bata ce komai ba. Ya kalle ta sosai ya ce, "Nayla wai me yake
damunki ne?." Murmushin ta ƙaƙalo ta ce, "Yaya na gaji ne kawai, zaman office ko
wahala." Dariya ya yi ya ce, "Yanzu kika fara aiki ai Nayla, maza ki zo yana jiran
ki." A hankali take takowa zuwa babban falon gaban ta yana faɗuwa sosai.

Da sallama ta shiga kanta ta na ƙasa ya amsa har ta ƙaraso ciki ta zauna. Kanta
yana ƙasa ƙafarsa kawai ta iya gani ta haka ta fahimci a inda yake zaune. Nayla ta
ce, "ina yini." Murmushi ya yi ya ce, "kin yini lafiya Nayla?."
"Lafiya lau" ta amsa a taƙaice.
"Ya aiki?."
"Alhamdu lillah" ta sake bashi amsa tana wasa da hannun ta. "Ma sha Allah. Sunana
Omar ...." Bata bari ya ƙarasa ba ta ɗago da sauri suka haɗa ido dashi. Saurin
ɗagowar da tayi ne ya saka shi ya dakata daga maganar da yake yi yana kallon ta.
Ajiyar zuciya tayi ta sauke ido ƙasa ganin ba wancan Omar ɗin bane suna ne yazo
ɗaya.

Murmushi ya yi ya ce, "me ya baki mamaki?." Kai ya girgiza alamun babu komai ya ce,
"Sunana Omar Mansur Garkuwa, ni ɗan garin Kaduna ne iyaye da kowa nawa yana cikin
garin nan. Amma Ina aiki da NCC a Abuja a can make da zama." Nayla jin sa take ba
fahimta take yi ba, shi kam yana ta magana yana gabatar mata da kansa amma ba ji
take yi ba saboda hankalin ta baya tare da ita.

"Nayla!." Jin ya kira sunanta ta ɗago suka haɗa ido ya ce, "Ina sonki, auren ki
nake da burin yi shiyasa na samu mahaifin ki da maganar ya ce nazo na same ki yau.
Ina fata zaki amince dani."

Ajiyar zuciya ta yi ta ce, "Allah ya zaɓa mana abinda yafi alkhairi." Murmushi ya
yi ya amsa da amin ya ce, "ki saka min number wayarki" ya faɗa yana miƙa mata
wayar. Karɓa tayi ta saka number ta miƙa masa wayar. Ya ƙarba ya ce, "na gode sosai
Nayla, na gode da damar da kika bani." Murmushi tayi kaɗan kafin ya bata kuɗi ta ƙi
karɓa tace ta gode. Babu yadda bai yi ba amma ta ce bazai karɓa ba dole ya haƙura
ya ƙyaleta suka yi sallama ta koma cikin gida.

A falon cikin gida ta tarar da Abiy ana zaune kamar ko yaushe shida Yaya da Yaya
Jawad da Auta da kuma Jalila da Mama. Abiy ya kalle ta ya ce, "baƙon naki ya
tafi?."
"Eh Abiy, ya tafi." Abiy ya kalli Yaya ya ce, "A NCC yake aiki kuma bazai wuce
sa'an ka ba, na san mahaifinsa a nan Kaduna suke gabaɗayan su. Familyn Mansur
Garkuwa ne. Yaron babu laifi gaskiya, yana da hankali ana ta yabonsa sosai."

Yaya yace, "Family Garkuwa Abiy? Lallai manyan mutane."
"Sosai kam. Amma ni yadda ake yabon kirkin yaron ne ya burge ni ba familyn sa ba."
"Ita samarin ma har sun yi mata yawa Abiy. Wannan shine na huɗu kenan fa, ga cousin
ɗinta Abbas."

Abiy ya murmusa ya ce, "bari kawai Babana, ka san bana son wannan yazo wannan ya
tafi. Abinda ya jawowa Jidda aure ba tare da Nayla ba kenan" ya kalli Nayla ya ce,
"Nayla bana son tara samari, bana son wannan saurayi yazo wannan saurayi ya tafi
kema kin sani, kamar yadda na bawa wannan Omar ɗin dama zan bawa sauran dama a ciki
ki zaɓi wanda ki ke so ki yi auren ki. In kuma Yayanki Abbas ki ke so shikenan."
Nayla ido ya ciko da hawaye ta turo baki ta ce, "To Abiy." Yaya J ya ce, "ke dallah
meye na wani hawaye?." Ta goge ido tana kallon sa, Abiy yana dariya ya ce, "Nayla
ce fa. Tunda kin fara aiki Nayla aure zaki yi, in Abuja kika tafi sai a nemi
transfer ki koma can, in Kano ne sai ki koma can, in a nan ne dai duk ɗaya." Kanta
na ƙasa sai ajiyar zuciya da tayi, ta miƙe Jalila na ta tsokanarta, Nayla ta harare
ta ta miƙe ta shiga ɗaki.

Mama ta bita da kallo ba tare da ta tanka ba. Familyn Garkuwa kawai take maimaitawa
a zuciyarta, ta ya zata bar Nayla ta auri ɗan Familyn Garkuwa?. Kaf wanda aka
lissafa a cikin masu neman aurenta wallahi baza ta bari ta aure su ba, har cousin
ɗinta Abbas bazata bar auren ya yu ba. In ma ta bari ta aure su taje ta huta kenan
taji daɗin zaman aure, ai wallahi yadda bata ji daɗin zaman aure ba Nayla ma baza
ta ji daɗin zaman aure ba, duk yadda zata yi zata yi don ganin Nayla ta sha wahala
a gidan aure, baza ta bari a kai Nayla inda zata ji daɗi ba wallahi. In ta bar
hakan ya faru mahaifiyar Nayla ta ci bulus kenan, ita ta wahalar da ita a gidan
aurenta kuma sai ta bar ƴar cikinta ta ji daɗi...? Wannan ai ba abu ne da zai yu ba
wallahi. Kai ta girgiza tana cize baki tana tunanin abinda ya kamata ace ta yi.


•••••••
Thursday
10:00am

Didi kallon Omar take yi ganin ya sha kwallaiya cikin manyan kaya riga da
wando da hula, ya yi matuƙar kyau kamar ba Omar ɗinta ba. Omar ya kalle ta ya ce,
"Didi mun shirya sai Abuja." Didi jikinta gabaɗaya a sanyaye ya ke ta ce, "to Omar,
Allah ya kiyaye hanya."
"Amin. Don Allah ki daina sanyin jikin nan bana so."
"Omar ji nake kamar akwai abinda zai faru wallahi, bana so ka tafi Omar."

Ajiyar zuciya ya yi ya ce, "Babu abinda zai same ni, kar ki damu." Kai ta girgiza
ta ce, "kai da wa zaku je? Kana da abokan da zasu raka ka?."
"Ni ina da abokai ne? Sai dai yara su Bash."
"Dasu Bashir ɗin zaku je?" Ta tambaya da mamaki tana kallon sa. Gira kawai ya ɗaga
mata sai gasu sun shigo kowa ya ci manyan kaya, Bashir da Goje ne, daman sune na
hannun damansa, ba kamar Bashir.

Da kallo take bin su sai suka bata dariya ganin yadda suka yi wani iri dasu harda
kwalli suka ranbaɗa su a lallai za a je gidan sirikai. Ganin Didi na dariya sai
suna suka yi dariya dan sun fahimci canjin da suka yi take yiwa dariya.

Didi ta ce, "lallai su Bashir an ci kwalliya. To ina Tukur?
"Babbar Yaya ai baza a barki ke kaɗai ba."
"Shi zai yi gadina kenan. To a mota zaku tafi?." Omar ya ce, "eh a mota zamu je."
"Allah ya kiyaye" ta faɗa tana kallon su kafin su fita ita dai gani take wani abun
zai faru dasu dukkan su.

*Abuja.*

Ana ta shirye shiryen tarbar in-law, Dad ko fita bai yi ba yana gida saboda tunda
ya ga Narma tana matuƙar sonsa ya san ba ƙaramin mutum ta ɗauko ba. Ya gayyato
Minister don tarbar sa suna zaune a falo suna hira. Narma ta ci kwalliya sai
murmushi take yi, bata kawo matsala a zuciyarta ko kusa, a ganin ta tunda tana son
Omar dan yazo gidan sunba abin damuwa bane ba.

Narma ta sakko daga sama Mum ta bita da kallo tana murmushi ta ce, "my daughter,
kin yi kyau." Tayi murmushi ta ce, "thank you Mum. Yau rana ce mai mahimmaci a
wajena shiyasa nayi kwalliya." Mum ta ce, "dukkan mu rana ce mai mahimmaci, ko
haɗuwarki da Asharaf baki wannan farin cikin da ki ke yi yanzu ba."
Jin Mum ta ambaci Ashraf sai ta murmusa kawai tana tuna yadda suka ƙare dashi jiya,
yana jajjada mata wallahi sai ya aureta babu wanda ya isa ya aure ta in ba shi ba.
Dad ne ya shigo yana kallon Narma ya ce, "Daughter bai zo bane?." Narma ta kalli
Dad ta ce, "bai ƙaraso ba Dad."
"Okay zamu yi sallah." Ta amsa Dad ya fita don su yi sallah.

Su Omar basu suka shiga Abuja ba sai ƙarfe uku na rana, duk sun jigata saboda zama
mota, kai tsaye hotel suka je suka kama ɗaki a nan suka huta zuwa la'asar suka yi
sallah kowa ya sake gyarawa sannan suka nufi gidan su Narma.

Lokacin da su Omar suka je ƙofar gidan Narma ya kira a waya ya ce mata gasu sun zo.
Mai gadi ta kira a waya ta bashi umarnin buɗe musu su shigo. Mai gadi ya kalli su
Omar bayan sun gama waya da Narma ya ce, "Hajiya ta ce ku shiga." Ya faɗa yana bisu
da kallon mamaki.

Yadda ake ta zuzuta su, tun safe aka ce musu za a yi baƙi ya ɗauka zai ga motoci
sun cika estate ɗin sai ya gansu taxi. Buɗe musu ya yi suka shiga gate ɗin farko
suka shiga na biyu. Narma ya gani a tsaye da alama jiran su ta ke yi,da sassarafa
ta ƙaraso inda suke dan takalmin ƙafarta ma silifa ne, tana zuwa ta kalle shi da
murmushi ta ce, "Barka da zuwa Faruk."

Su Bash dai sunan tsaye suka yi, basu ɗauka inda Ogan nasu ya kawo kansa ya kai
haka ba. Duk da sun san gidan, suna zuwa tare dashi wani lokaci. Kenan a gidan
Sanata yake neman aure? Kuma wannan kyakykyawar budurwar ita yake so?. Gaskiya sun
jinjina ƙarfin guiwa irin ta Omar, gashi babu damar magana balle su tanka, sun san
halinsa. Narma ta ce, "mu je falon." Bayan ta suka bi tana tafiya tana yiwa
ma'aikatan gidan faɗa, su kuma sai gaishe su suke yi suna ana bata haƙuri.

A babban falon ta kalli Omar ta ce, "Dad sun je masallaci, tun ɗazu suna jiran
zuwan ka baka zo ba, yanzu zasu dawo." Omar ya girgiza kai ya zauna ko ɗar a
zuciyarsa baya ji. Yadda ya zauna ya harɗe ƙafa sai ka ɗauka Sen ɗin ne da kansa,
su Bashir kallon ikon Allah kawai suke yi, basu ɗauka lamarin ogan nasu ya kai haka
ba.

Nan take aka cika gaban su Omar da abin sha da abin motsa baki. Narma ta fita ta
koma cikin gida dan ta sanar da Mum zuwan su. Bash ya kasa haƙuri bayan ta fita ya
ce, "Sai da kai Tiger, wallahi Madugu ƙwarin guiwar ka yana burge ni sosai. Allah
ya bani ikon koyi da kai, Allah ya zamanin Jan wuya na mu." Omar bai ko kalle shi
ba kaɗa ƙafa kawai yake yi, babu abinda suka taɓa abinda aka kawo musu. Su Bashir
suna son cin koda Apples ɗin da aka ajjiye ne, amma waye ya isa ya taɓa bayan ga
Boss a gefe bai taɓa komai ba? Sai dai kallon.

Dariyar Dad suka jiyo suna shigowa falon shi da minister. Turus suka yi ganin su
Omar a zaune a kan kujera suna kallon masu shigowa. Kallo ɗaya Sen ya gane Omar ya
kalle shi da mamaki ya ce, "A'a Tiger, saukar yaushe? Zuwa babu notice?" Ya faɗa
yana ƙarasowa fuskarsa ba yabo babu fallasa.........

Senator ya haɗu da In law😂😂

*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
wa.me/701 809 8175
Dm to subscribe yours.
Nana Haleema❤️


*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025

©️*Nana Haleema.*

Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.

*_Godiya ta musamman ga waɗannan mutane masu karamci, kirki, daraja da kuma
alkhairi._*

1-Halimahz
2-Oum Nabil
3-Jamila Umar Janafty
4-Oum Mumtaz
5-Maryam Kitty
6-Aisha Muhammad Alto
7-Autar Manya
8-Mai Dambu
9-Maryam Jumare
10-Maryam Hadeja
11-Zainab Kano
12-Aunty Nice
13-Gureenjoh.

_Ina miƙa godiyata a gare ku, Allah ya saka muku da alkhairi, Allah ya bar zumunci
ya cikawa kowa burinsa na alkhairi amin._❤️❤️

*Book 1*
*P 25.*


Omar bai tashi tsaye ba kuma bai ce komai ba, su ma su Bashir ganin Boss bai tashi
tsaye ba sai suka gyara zama. Sen ya ƙaraso yana bin su da kallo, ransa ya ɓaci
ganin su a zaune akan kujera kamar wasu baki masu mahimmaci.

Minister ya kalli Omar ya kalli Sen ya ce, "Ina baƙin da aka ce mana sun zo?." Sen
ya ce, "to nima dai ban ga kowa ba, nayi tunanin zan ga Bakuwar mota a car park
amma ban gani ba."

Kallon su Omar ya yi ya ce, "ku jira ni daga waje zan gana da baƙi yanzu. Bana son
irin wannan zuwan babu notice, ni ban san ma ya akayi aka bar ku kuka shigo ba
wallahi. Mtsww..." Sai kuma ya ɗaga murya ya ce, "Auwal!." Da sauri wanda aka kira
da Auwal ya shigo, Sen ya kalli su Omar ya ce, "kai su BQ, in na gama ganawa da
baƙi sai su zo. A taƙaica waye ya bar su suka shigo? Irin waɗanan baƙin ba ni nake
faɗa muku zuwan su ba?. Waye ya shigo da su?."

"Hajiya Narma ce" ya bashi amsa da girmamawa.
"Narma!" Ya maimaita cikin mamaki.
"Itace.." Sen ya tafi tunani, ya kalli Omar ya sake kallon Auwal ya kuma maimaita
sunan Narma. Omar da ya ke jinsa yake kuma kallon reaction ɗinsa ya murmusa ya ce,
"babu wasu baƙi da zasu zo Sen, mu ɗin nan dai mu ne baƙin." Da sauri Sen ya juya
yana kallon Omar ya ce, "ban gane ba."

"Ba kana jiran zuwan sirikan ka bane?" Omar ya faɗa yana kallonsa kamar yadda shima
shi yake kallo. Kasa magana Sen ya yi sai kallon Omar da yake yi cikin mamaki. Omar
ya ce, "to ai ni ne." Sen ya yi ƙaramin tsaki tare da tamke fuska ya ce, "kai kar
ka ga Ina wasa dakai, Ina baka damar zuwa gidan nan ko yaushe ka raini ya shigo
tsakaninmu, ka tsaya matsayin da na baka. Ku tashi ku bar min falo!."

Narma ce ta shigo falon ta ce, "Dad!." Kallon ta ya yi cikin fusata ya ce, "Ina
baƙin naki suke? Sannan kece kika buɗewa waɗanan falon nan suka shigo?." Narma
cikin shagwaɓata ce, "ni ce mana. Kuma Dad ai sune baƙin nawa, Tiger shine Faruk
ɗina, your inlaw."
"What!!" Sen ya faɗa da ƙarfin gaske yana kallon Narma da take kallon sa, ya kalli
Omar da yake zaune har lokacin kamar falon babansa, ya kuma kalli minister da yake
tsaye ya rasa ma abinda zai ce.

Kallon Narma ya sake yi cikin wani irin yanayi ya ce, "kin san abinda ki ke faɗa
kuwa? Are you out of your senses Narma?."
"Dad da gaske nake, he's your son in-law." Sen ya nuna Omar da ya miƙe tsaye a
lokacin bakinsa har rawa yake yi ya ce, "Wai wannan?." Narma ta ce, "yes Dad, I
love....."
Ai bata ƙarasa ba ya tsinke ta da marin da sai da ta koma ta daki bango.

"Narma!!" Ya faɗa da ƙarfin gaske yana riƙe kafaɗunta

27 / 28