Advertisements
Chapter 23 Reading KIRAN RABO BOOK1 CMPLT BY NANA HALEEMA BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

KIRAN RABO BOOK1 CMPLT BY NANA HALEEMA

Author :  NANA HALEEMA Category :  Complete Novels

Chapter   23 / 28

66K to 69K   out of 83.2K words

ce, "kamar ya kenan?."

"Ina nufin ko wacce mace ma zata iya son namiji kamar ni?." Didi ta ce, "ita
soyayya ai baka sanin lokacin da ka ke fara ta Omar. A yadda ka ke a haka in
ƙaddarar soyayya ta gifta sai ka fara son ƴar gwamnan garin, kuma so bana wasa ba
na gasken gaske, kuma dai kaga a zahiri ka san tafi ƙarfinka amma soyayya bata duba
wannan Omar. Ko kuma ita ƴar gwamna ta fara sonka so mai tsananin gaske, so na
gaskiya ba wai na wasa ba, saboda ba ita ta yi sonka a zuciyarta ba Allah ne da
kuma taimakon zuciya. To soyayyar ce yanzu duk ta gaskiya ta gushe sai dai sama-
sama, kafin a samu soyayyar gaskiya a yanzu an samu ta ƙarya sau dubu, kuma da yawa
yaran manyan mutane yanzu ƙwarya tabi ƙwarya ake yi, me ka kai me za a kawo maka. A
dah dai ɗan mai kuɗi ya auri ƴar talaka, ƴar mai kuɗi ta auri talaka kuma an zauna
lafiya. Amma yanzu wannan zamani ya gushe Omar."

Yayi shiru jin kalaman Didi sai ya kalle ta ya ce, "misali ace ƴar mai kuɗin
unguwar nan ta ce tana sona zaki amince da gaske takr?." Didi ta yi dariya ganin da
gaske yake maganar sai bata saka wasa a ciki ba ta ce, "zan amince mana Omar, ai ba
ita ta halicci kanta ba, kuma ba ita ta saka son naka a zuciyarta ba, babu yadda
Allah baya tsarawa ɗan adam ƙaddara da rabonsa. Allah ne ya kaddara hakan kuma
babu wanda ya isa ya canja faruwar sa. Kuma da yawa in yaran masu kuɗi mata suka
fara soyayya da wanda bai kai matsayin su ba yawanci soyayyar gaskiya ce, saboda
mata rauni gare su, soyayya tana saurin kama zuciyarsu."

Shiru ya yi kawai bai ce komai ba yana tunanin kenan dai da gaske Narma zata iya
fara sonsa ko dai hasashen Didi ne kawai?.

Didi ta ce, "kai dai ka bar so kawai Omar, nima ba wai sanin soyayyar na yi ba,
amma so babban abu ne. Kai ta addu'a Allah kar ya ɗora maka son wacce tafi
ƙarfinka, daga lokacin da ka fara son wacca tafi ƙarfinka daga lokacin zaka san
meye azabar so. So ai mugun abu ne wani lokacin."

"Ni ai Didi na faɗa miki bana tunanin akwai wacce tafi ƙarfina a duniya, in har
akwai ɗin sai dai in bata sona." Didi tayi dariya tana jinjina maganar sa ta ce,
"ko tana son naka iyaye da ƴan uwa sai sun dakusar da soyayyar."

Ya yi shiru bai ce komai ba yana ɗan girgiza kai ba dan ya yarda ba. Disi ta ce,
"wai me ya kawo wannan maganar ma yau?."
"Zan faɗa miki" ya fɗa yana tashi ya fita ya barta da tunani dalilin yin wannan
maganar, ita da ta san baya magana akan soyayya, ko akan mace baya magana balle
irin wannan ta soyayya. Ko tsokanarsa ta yi wani lokacin ko tanka mata baya yi,
amma tunda ta ji ya yi wannan maganar tabbas akwai dalili.

Yana fita yaga message ɗin Narma ta rubuta, _Daman na san baza ka zo ba, in
na rasa raina kaine sila Faruk! Da Ina da iko da na cire son da make maka tuni na
ajjiye shia a gefe. Amma babu komai na gode._

Sai yaji wani irin abu ya tsirga masa mai kama da tausayi sosai, ya sauke ajiyar
zuciya yana jin zuciyarsa na bugawa sosai cikin rashin sanin dalili. Shi dai bazai
je inda Narma take ba gaskiya, in ya je dagula masa lissafi zata yi ya rasa abinda
zai ce mata gwara ya ƙyale ta in ta gaji ta koma gida.

"Kenan in da gaske so na take su masu kuɗi babu ruwan su da cewa in mace ta fara
cewa tana son namiji zubar da aji ne? Tunda gashi tun daga Abuja ta ɗauko ƙafa tazo
Kano saboda ta furta min tana sona. In kuma yaudarata take yi ta taro match
wallahi, za tayi dana sanin aikata abinda ta aikata. Amma taya zan gane soyayyar
gaskiya ce ko ta ƙarya?." Shafa kansa yake yi ya kasa gane inda zai kama dan ya
kamo bakin zaren.

"To wai ni me nake ji a kanta?" Ya faɗa yana shafa ƙirjinsa daidai inda zuciyar
take, yana jin wani irin abu yana fizgarsa daga ta ciki. Da wannan tunanin ya
kwanta yana ta juyi ya rasa abinda yake damun sa.

Narma yanayin ta babu daɗi, raba dare tayi tana kuka zuciyarta ma bata
shawara kala-kala, har shawarar kashe kanta tayi ta fasa, tayi shawarar fita taje
gidan su Omar ta kasa. Ta jima tana kuka daƙyar ta samu bacci ya ɗauke ta.

Ya jima yana bacci har goma na safe sannan ya tashi, bai fito ba sai da ya
yi wanka jikinsa duk a sanyaye yake ya rasa abinda ya kamata ace ya yi. Lokacin da
ya shiga wajan Didi ta idar da sallar walha ta kalle shi ta ce, "yau ka sha bacci,
da fari na ɗauka ka fita ashe kana nan." Ya girgiza kai ya ce, "na jima ban yi
bacci ba ne jiya, daƙyar na iya tashi sallar asuba."

Didi ta ce, "ga idanunka nan har yanzu da sauran bacci. Ga abinci can in zaka ci."
Ya girgiza kai ya ce, "bana son cin komai gaskiya."

Didi ta ce, "na lura gabaɗaya a sanyaye ka ke, me ya faru ka koma haka?." Ya bita
da kallo yana tunani. Bashi da aboki a duniya sai ita, babu mai bashi shawara sai
ita, babu wanda yake iya faɗawa damuwarsa sai ita, babu da wanda ya saba sai ita
ɗin dai. Itace kawai mafitarsa, dole ya faɗa mata abinda yake faruwa ko zai samu
wata makama a wajan ta.

Niyar zama yake yi aka shigo falon sai ya fasa zama yana kallon wacce ta shigo.
Didi ta miƙe tsaye ganin wacce ta shigo cike da mamaki, shi kansa sai da gabansa
ya faɗi balle Narma da take kallon sa. Didi ta ce, "Barr Nass."

Wajan Didi ta ƙarasa ta ce, "Sister laifi ne dan mace ta fara soyayya? Laifi ne dan
ma fara son wani a lokacin da ban shirya ha? Laifi ne dan na fara son wani ba tare
da na san hakan ba?."

Didi da mamaki take jin abinda take cewa ta girgiza mata kai ta ce, "A'a." Ta nuna
mata Omar ta ce, "Amma Faruk ya kasa gane da gaske ina sonsa, wallahi sister daga
Abuja na taho nan akwai dan na furta masa kalmar Ina sonsa. Ina sonsa da gaske, ki
faɗa masa ba yaudararsa nake yi ba. In ya cigaba da tafiyar dani a haka a yadda
nake jin sonsa zan iya mutuwa!" Ta ƙarasa faɗa a sanyaye tana kwantar da kanta a
kafaɗar Didi.

Didi suman tsaye tayi tana jin sautin kukan Narma a kunnenta, tunani take yi wai ko
dai mafarki take yi? Sai kuma taga ai ko a mafarki abinda take ji bai kamata ace
yazo gare ta ba. Omar ɗin ta ake magana akai, kuma ƴar Senator ɗan takarar gwanma
ce take wannan maganar. Tabbas wannan maganar indai ba mafarki bane to tabbas wasan
kwaikwayo ne.

Bata iya bata amsa ba ta ji Narma ta ɗago daga jikin ta ta ce, "Sister bazan yi
ƙarya dan na yaudare shi ba, ki kalli idona wallahi da gaske Ina son sa. Tun farkon
ganina dashi na fara jin wani abun a kansa, da ya zo ɗauka na a Airport a nan na
sake jin abinda naji. Da ya taimake ni a lokacin da aka ƙwace min waya a nan na
tabbatar da ya shiga zuciyata. Ba wasa nake yi ba, ba yaudara na shirya ba, gaskiya
nake faɗa Sister."

Shi dai Omar yana tsaye kaiwa bai fita ba kuma bak ce komai ba yana kallon ikon
Allah. Didi sai a lokacin ta samu damar kallon Narma ta ce, "Wai Omar ɗina ki ke
so?." Ta ɗaga mata kai alamun eh, Didi ta zuba mata ido kafin ta kalli Omar da yake
kallon su sannan ta ce, "Narma kalaman naki ne kamar a mafarki, Omar ɗin ki ke so?"
Ta faɗa tana sake nuna mata shi da yake tsaye.

Narma tayi murmushi ta lura sun kasa gane abinda yake ji a kansa, ta ce. "Shi nake
so, saboda son da nake masa aka fasa maganar aurena da Ashraf ɗan gov katsina
state, na faɗawa iyayena Ina da wanda nake so su bani lokaci, yanzu sun bani lokaci
suma jira na kai musu shi matsayin wanda nake so. Wallahi a yadda nake ji bazan iya
auren wani in ba shi ba, ki taimaka min, kece kawai hope ɗina Sister. Nazo har nan
jiya na bayyana masa amma ya ce min A'a!."

"Tirƙashi!" Didi ta furta tana sake kallon Narma dan ta tabbatar a hankalin ta
take, sannan ta kalli Omar da yake jin su bai ce komai ba.

Motsawa yayi zai fita Didi ta ce, "Ina zaka je?."
"In na tsaya me zan yi Didi? Me zan ce in na tsaya? Gwara na tafi" ya faɗa yana
kallon ta.

Narma ta kalle shi ta ce, "kana ganin kamar wasa nake yi ko?" Sai tayi murmushi ta
ce, "dole zaka ji haka saboda a saba namiji ne yake bayyana cewa yana son mace
kafin ita tace, ni kuma sai gashi nice nazo ina yin abinda mazan ma baza su yi ba.
Ni ban iya ɓoye abinda yake raina ba, in dai akwai zan faɗa ne kawai na huta. Kuma
ban ɗauki dan nazo har gidan ku na ce ina sonka da wani abun ba, gaskiya na faɗa ba
ƙarya ba. Amma wallahi ko dm namiji ya yi min a social media sai na shekara ban
buɗe ba, namiji sai ya shekara biyu yana so nace masa hii amma ban ce ba. Duk
wannan ajin da nake dashi soyayyarka ta kawar da ita Faruk!. Kuma har yanzu kace
kana tantama? Didi kina ji fa" ta faɗa tana kallon Didi da take ganin abun kamar
almara.

Didi ta ce, "Ko da gaske ki ke, ko da wasa kike Narma kin fi ƙarfinki ce kina son
Omar, ke ba irin matan da ya kamata ace suna son Omar bace. Kuma amsar da ya baki
ta a'a itace daidai Narma, dan ke ba daidai dashi bace, ki tuna matsayin ki dana
mahaifinki."

Narma ta ce, "ni dai in har yana sona duk wannan ba damuwa ta bace, iyayena suna
son duk abinda nake so, ko yanzu na kai musu shi nace shi nake so zasu yi maraba da
zuwan sa. Kuma na sanar dasu ma fara sonsa kuma sun yi min fatan alkhairi." Didi ta
ce, "Omar ɗin ki ka ce kin fara so?." Narma tayi murmushi ta ce, "Didi kema ɗauka
ki ke ƙarya nake ko?."
"A'a Narma ban ce ba, amma maganar ce dole ta saka mana shakku a zuciyar mu."

Narma ta ce, "me zan yi da zai goge shakkun? Na shiga social media nayi video ce
Ina sonsa? Ko gidan tv zan je ma bada labarin yadda ma fara son sa?. Ko kuma na
sanar da iyayena su zo su nemana min auren sa?. Wanne zan yi da zai tabbatar da ba
ƙarya nake ba?."

Didi ganin Narma ta gigice sai ta kwantar da murya ta ce, "Ki kwantar da hankalin
ki Narma, yanayin matsayin da kike dashi ne dole ya saka mu tantama a kan ki."
"Shiyasa nace me zan yi ya goge?." Didi ta ce, "babu ko ɗaya da kika lissafa. Na
amince da gaske kina son Omar so na gaskiya kuma so na aure."

Narma a sanyaye ta ce, "Amma shi ya ce ƙarya nake yi." Didi ta sauke ajiyar zuciya
ta ce, "Narma ban san me zance miki ba a yanzu, amma ki koma gida zan yi ƙoƙari na
shawo kansa ya faɗa min abinda yake ji ransa a kanki, in yana ji zai karɓi soyayyar
ki shikenan, in baya ra'ayin hakan sai dai ki yi haƙuri."

Narma ta goge idon tana murmushi ta ce, "Hakan ma na gode. Amma Didi in kika samu
labarin wani abu ya faru dani wallahi Faruk ne sila, soyayyarsa itace silar da zata
jefa ni ko wanne irin yanayi. Yin acting ɗin ƙarya akan soyayya ba ajina bane,
bazan taɓa iya furta ina son mutum ba indai ba da gaske nake ba Didi. Abu ɗaya
kawai na sani, ina sonsa koda shi baya sona, zan rayu dashi koda baya sona."

Kallon Omar Narma tayi ta matso kusa dashi ta ce, "zan koma gida, zan je na samu
likitoci naji zasu canja min zuciya. Indai zasu iya zan amince a cire tawa a saka
min wata indai zan rabu da abinda nake ji. In kuma baza su iya ba ina tabbatar maka
wani abun zai same ni akan abinda nake ji a kanka. Na tafi, amma ka sani zan dawo,
zan dawo dan jin amsarka. Bazan iya rayuwa da wani in ba kai ba, bazan taɓa iya
rabuwa da kai ba" ta faɗa tana ficewa a guje kamar walƙiya.

*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.

Nana Haleema❤️

*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025

©️*Nana Haleema.*

Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.

*Book 1*
*P 21.*
Didi tana kallon ta har ta fice ta dafe ƙirji ta kalli Omar da yake tsaye har
lokacin ta ce, "wai da gaske ba mafarki nake yi ba?." Ƙoƙarin fita ta ga yana yi ta
ce, "Ina zaka je?" ya juyo yana kallon ta ta ce, "Dawo, ai fita bata kama ka ba
Omar. Daman shine silar magangangun da kayi min jiya? Daman akan Narma ne Omar?."

Yana daga wajan da yake tsaye ya ce, "na rasa abinda zan ce ne Didi, ban san me zan
yi ba, ban kuma san a wanne matsayi zan ajjiye hakan ba."

Didi ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Omar ni na amince da gaske Narma tana sonka." Ya
kalle ya ce, "ta ya kika tabbatar a lokaci ɗaya haka?."
"Kalamanta, yanayinta, matsayinta. Omar a matsayin da Narma take dashi a Nigeria
baka kai matsayin wanda zata yiwa wasa da hankali ba, ko ta yaudare shi ba. Soyayya
bata duba cancantar mutum ko kuɗi ko mulki, dan zuciyarta faɗa a soyayyarka abu ne
mai sauƙi tunda ba itace tayi kanta ba. Mace kamar ta baro Abuja kawai saboda ta zo
ta ce maka tana sonka daga ji ka san wannan abin ya kai zuciya."

Kallon Didi yake yi har ta gama magana kana ya ce, "in kuma film aka shirya fa? Ni
Ina ganin kamar da wata manufa hakan ya faru. Ta ya za a ce lokaci ɗaya ta baro
garin su tazo ta ce tana sona? Har yaushe ta sanni? Yaushe muka yi sabon da zata
fara sona? Yaushe muka yi mu'amala tare da hakan zai faru?."

Didi ta murmusa ta kalle shi ta ce, "Wacce manufa kenan? Me ka ke dashi da Narma
zata yaudare ka Omar? kai waye a Nigeria da za a yi amfani da ita wajan
yaudararka?. Da gaske na san ana amfani da mace a yaudari mutum amma sai mutum ya
kai inda ya kai ake aika masa haka. Allah na tuba kai wanne matakin rayuwa ka taka
da za a yi amfani da ita a cuce ka? Ai in ma cutar taka za a yi sai dai ayi amfani
da mata irin na lunguna ba dai ita ba."

Ganin ya yi shiru bai ce komai ba ta kuma cewa, "Zancen yaushe ta fara sonka duk
daga baya ne, zuciya tana fara son wanda mutum bai taɓa gani ba, ana fara soyayya a
iya jin murya kawai. Mace na fara son namiji in taji muryarsa a tv ko radio, haka
namiji yana fara son mace in yaji muryar ta koda a hanya ne."

Shi Omar mamaki abin yake bashi shiyasa ya kasa magana, ya sake kallon ta ya ce,
"wai da gaske yana faruwa a gaske ko sai a film? Ni ban amince da soyayyar ba, ban
amince akwai wani abu soyayya a duniya ba. Ina jinta tamkar tatsuniya, ina jin
labarin soyayya kamar iska da zata zo ta wuce ba tare da ka ganta ba, ina jin
labarinta tamkar tafiyar ruwa. Ban amince akwai soyayya ba Didi, ni ban yarda akwai
ta ba balle har na yarda da son da wata take min."

Didi tayi murmushi tana girgiza kai ta ce, "Zaka amince da akwai soyayya Omar, zaka
tabbatar da soyayya gaskiya ce a lokacin da ka fara son wacce ka ke so, daga wannan
lokacin zaka tabbatar da soyayya ba film bace ko wucewar iska. Yanzu babu abinda ka
sani sai ni, soyayyar Yaya da ɗan uwanta kaɗai ka sani, baka san ko wanne irin so
ba sai ita, baka san son ko wacce mace ba sai ni, baka jin ko wacce mace a
zuciyarka sai ni ɗin. A yanzu baza ka gane ba, sai zuciyarka ta fara son wata mace
sannan zaka tabbatar. Yanzu meye mafita akan Narma?."

"Mafita kamar ya?."
"Ya zaka yi da ita?. Misali ace da gaske tana son naka, ya zaka yi mata?."
"Haƙuri zata yi Didi, me zan yi mata?." Didi ta ce, "Haka nake so naji ka ce, domin
Narma ba kalar wacce zaka yi gangancin fara so bace, in ka bari zuciyarka ta
yaudare ka ka fara sonta wallahi kaine a ruwa domin kaine zaka sha wahala. Mallakar
Narma abu ne mai wahala a wajan namiji irinka, in kuma kaga hakan ya faru to sai
dai tsananin rabo."

Omar ya murmusa kaɗan ya ce, "ban san meyasa kike faɗar wannan maganar ba, ni ban
cancanci a soni ko a aure ni bane?." Didi ta girgiza kai ta ce, "ka cancanta mana,
ka cancanta a wajan wanda ka cancani kaso a soka. A wajan Narma, ko a wajan masu
matsayin na ƙasa da ita wallahi baka cancanta ba Omar. Ba maganar hasken fata ake
yi ba, ba maganar kyau ko sajen fuska da ƙirar jiki ake ba Omar. Magana ake ta
karatu da kuma kuɗi, magana ake ta asali mai kyau, in ma asali na kuɗi ko na
sarauta. Omar duka wannan baka dashi, kaga kenan a wajan ta baka cancanta ba, ba
ita kaɗai ba har masu biye mata."

Ransa yaji ya ɗan sosu akan maganar Didi, ya zuba mata ido yana kallon ta kafin ya
ce, "Shi mutumin da bashi da karatu ko bashi da kuɗi ba mutum ba ne?." Didi ta ce,
"Mutum ne mana Omar, amma a gidan Senator Kano central ba mutum bane wallahi."

Kallon Didi yake yi kawai bai ce komai ba, kamar zai yi magana sai ya fasa bai ce
komai ba ya kawar da kai gefe. Didi ta tausasa ta ce, "Ka bata haƙuri Omar, in
mahaifinta yaji tana sonka ma wani babban tashin hankalin ne, kar kaga kuna waya
dashi ko kana zuwa inda yake yana yi maka dariya. Wallahi dariyar nan ta manufa ce
Omar, ba tsakani da Allah

23 / 28