Author : NANA HALEEMA Category : Complete Novels
magana kayi min banza."
"Me zan ce miki? Kin nuna waccan abar ta fi ni" ya faɗa cike da jin haushi.
"To haka kawai daga ganin yarinya sai ka fara yi mata ihu baka san ta ba baka san
daga inda take ba? kai baza a yi baƙi a gidan nan ba kenan?."
Ya kalle ta ya ce, "duk wanda zai zo gidan nan munafuki ne, yana zuwa yaga ya muke
rayuwa ni dake." Didi ta ce, "in ma hakan ne babu ruwan ka, kar wata baƙuwata ta
sake zuwa kayi mata abinda ka yi yanzu, Wajena suka zo ba wajanka ba." Ya kalle ta
ya taɓe baki ya nuna kansa da yatsa ya ce, "ni ki ka yiwa faɗa a gaban wata
yarinya, ni kika yiwa tsawa har ki ka ce na bar miki falo kuma duk a gabanta. Ni ko
Didi?."
Didi ta kalle shi dama ta san zai ji haushi ta ce, "kaine ka jawo, lokacin da ka
shigo da kun gaisa ka shiga ɗaki inda nake ai da hakan bai faru ba." Ya girgiza kai
cikin ƙunar rai, baƙin ciki yake ji zuciyarsa, kamar shi tiger Didi ta yi masa faɗa
akan wata banzar yarinya wacce bai ma santa ba. Ya kalli Didin da take kallon sa
cike da ɓacin rai ya ce, "ni wai kika kora a gaban wata, ni Omar hmm....." ta kalle
shi ta ce, "meye hmmm? Kar ka cutar da ƴar mutane, kar ka saka a zubar mata da
jini."
"In ki ka ce kar ayi ɓata bakinki ke yi, zata san ta shigo gidan mu ta saka
chaji har an yi min faɗa a gabanta. Nan gaba aka ce ta shigo baza ta yi wannan
marmarin ba."
Ganin yadda yake cize baki yana maganar ya saka Didi ta ajjiye abincin da ta taho
masa dashi ta riƙe hannunsa ta ce, "Omar kar ka saka ka cutar da ita, na faɗa maka
kar ka yi mata komai." A fusace ya cire hannunsa daga nata ya ce, "to meyasa zaki
yi min faɗa a gabanta? Meyasa?. daga wani gari na dawo ko tsayawa baki yi mun gaisa
ba ki ka fara yi min faɗa." Didi ta ce, "shikenan nayi kuskure, amma kar ka yi mata
komai na sake faɗa maka."
Kai ya girgiza dan maganar bata wani shige shi ba ganin haka Didi ta ce, "wai baka
gane ta ba ma?." Kallon ta yayi alamun na san ta ne daman, ta ɗaga kai dan tana
fahimtar saƙon ido in ya yi mata tunda ya saba ta ce, "ka san ta mana, Nayla ce fa
jikar Hajja. Yarinyar da aka taɓa ƙoƙarin yi mata fyaɗe ka cece ta ka dawo da ita
wajan Hajja?. Ka tuna har ka dinga yiwa Hajja faɗa akan ne aka barta ta fita ita
kaɗai bayan a san baƙuwa ce bata san gari ba, ka tuna?."
Kallon Didi yayi jin abinda take cewa dan ya tuna abinda ta ce ɗin tsaf a ransa,
har hango lokacin yake yi a idanunsa da yadda komai ya faru. Amma bazai gane ta ba,
dan a yanzu ma ba ganin fuskarta ya yi sosai ba, gwara ma a da ɗin ya san fuskarta
saboda suna haɗuwa bayan abin ya faru tana yawan zuwa wajan Didi kafin ta bar
garin. Bazai manta da ita ba dan ta silar ta ya fara yankewa wani ɗan yatsa a
duniya, tabbas a kanta ya fara zubar da jini saboda ceto. Batu ake na shekara tara
zuwa goma baya ta ya zai gane ta banda abin Didi?.
"Ni ban san ta ba, ina kallonta a matsayin wacce ki ka yi min faɗa a gabanta"
Abinda ya ce kenan ya wuce ya barta a wajan tayi dariya tana jinjina son girma, da
son mulki, da zafin kai irin na ƙanin nata, abincin ta shigar masa dashi ɗakim
sannan ta koma wajan Nayla.
*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.
Nana Haleema❤️
*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025
©️*Nana Haleema.*
Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.
https://chat.whatsapp.com/K8IEI39TB803y9pEtzMmdp?mode=ems_copy_t
*Book 1*
*P 05*
Didi da ta bar wajansa wajan Nayla ta koma ta zauna kusa da ita ta ce, "na bar ki
ke kaɗai ko?." Ganin Nayla a tsorace har lokacin sai ta tausasa murya ta ce, "har
yanzu a tsorace ke ki ke? Ki nutsu mana." Nayla ita dai gaban ta faɗuwa yake saboda
duk abinda suke faɗa tana ji, tana ji Didi tana ce masa kar ya yi mata komai duk
shine ta sake firgita. Dana sanin shigowa gidan ta mamaye mata zuciya, ji take ina
ma bata shigo ba ta haƙura da chajin wayar.
Didi ta kalli Nayla ganin har lokacin tsorace ta ke sai tayi dariya ta ce, "Wallahi
dariya ki ke bani, yadda ki ka firgita haka kamar kin ga wani abin tsoro, In kina
nuna kina tsoronsa har haka sai ya fi cewa zai latsa ki. Omar fa yana da sauƙin
kai, kawai shi bashi da saurin sabo ne, amma na tabbatar miki kafin ki bar Kano
zaku saba, Zaki yi mamakin yadda yake da hira da kuma yawan murmushi." Murmushin
yaƙe kawai Nayla tayi dan kawai tana jin ta ne, amma ta yaya zasu saba da dashi
bayan abinda ya faru.
Didi ganin tayi shiru ta dinga jan ta da hira kaɗan-kaɗan tana amsawa duk da har
lokacin a tsorace take matuƙa. Agogo ta kalla sai ta kalli Didi ta ce, "Didi bara
na ɗauki wayata na tafi saboda zan kira Abiy na ji ya koma gida lafiya." Didi ta
kalle ta tace, "Ko dai kina so ki gudu saboda Omar?."
"A'a Didi, Abiy zan kira na tabbatar yana jiran kira na."
"To Shikenan. Ina jiranki da daddare ki zo ki taya ni hira." Nayla ta ɗaga kai
kawai ta tashi ta ɗauki wayarta da charger tayi hanyar fita Didi na bayanta.
Tana fitowa daga falon yana shigowa gidan idanunsa ya faɗa cikin na ta. Nayla bata
san lokacin da wayar charger sun suɓuce a hannunta ba, wayar ta faɗi ta ɗan yi ƙara
amma bata duba ba jikinta ya cigaba da rawa. Hannunta Didi ta riƙe ta bayanta,
Nayla ta sunkuyar da kai cikin tsoro. Didi ta kalle shi bata ce masa komai ta kalli
Nayla ta ce, "Nayla don Allah ki kwantar da hankalinki, kin ga kin yar da wayarki"
ta faɗa tana sunkuya ta ɗauki waya da charger ta riƙe mata hannunta har suka bar
cikin gidan.
Ai Nayla bata iya cewa Didi komai ba, tana bata wayar ta kwasa a guje ta yi hanyar
gidan Hajja. Didi tayi dariya ta dawo cikin gidan tana dariya suka sake haɗuwa da
shi cikin dariya ta ce, "Kaji tsoron Allah ka daina tsorara yaran mutane don Allah,
haba wannan bala'i daga haɗa ido da kai duk ta ruɗe?. Ni ban ga meye abin tsoron a
nan ba." Bai ce komai ba ya sake shiga cikin gidan tayi dariya ta bi bayansa tana
jinjina ƙarfin tsoron da Nayla take masa.
Nayla a haka ta faɗa cikin gida a firgice Hajja da Salma da suke zaune a
falo suka ganta kamar an cillo ta Hajja ta ce, "ke lafiya?." Nayla ta sauke ajiyar
zuciya ta ce, "Hajja har abada bazan sake shiga gidan Didi ba, na gama shiga gidan
ko me za a bani." Salma ta wara ido ta ce, "shiyasa daman da Hajja ta ce min kina
can nace wallahi bazan je ba, in yaga ka shiga gidansu kamar zai yanka naman ka
haka yake ji. Sam baya so ya ga an shiga gidan, ba ya ƙaunar kowa ya shiga gidan su
daga shi sai Didi."
Nayla ta ce, "wallahi Salma fitsari ne kawai ban yi ba, yau ni naga bala'i ganin
idona. Salma duba min wayar nan ki ga ko screen ɗinta ya samu damuwa, dan yadda ta
faɗi a hannuna da na ganshi na tabbatar daƙyar bai fashe ba. Wannan halitta ta
mutumin nan akwai ban tsoro, ga ido kamar na aljanu." Salma ta karɓi wayar da take
miƙa mata dubawa kana ta ce, "Wallahi ya tsage. Wannan bala'i har ina? daga gidan
su ya jawo miki asarar sama da naira dubu ɗari biyu. Dan screen ɗin wayar ki in bai
yi haka ba ya kusa."
Nayla ta faɗi akan kujera ta dafe kai ta ce, "gabaɗaya ban shigo Kano da ƙafar dama
ba, da fari gidan nan babu haske, ga tashin hankalin da na haɗu dashi sannan ga
asara." Hajja da take jin ta take kallon ta tayi dariya ta ce, "wai duk tsoron
Ummarun ne ya saka ki ka firgice haka?." Salma ya ce, "ba dole ba Hajja, wannan
mutumin kallon sa ma tsoro yake bawa mutane balle kuma ya harare ka ko yayi magana.
Ni na jima ban ga mutum bai baƙin hali kamar sa ba, sai kyaun fuska kamar shi ya
tsara kansa, amma zuciya da hali baƙaƙe."
Hajja ta ce, "ai kam yana da kirki sosai, kaf unguwar nan ni kaɗai ce nake kiransa
da Ummaru ya amsa har yayi min magana. Duk da nima ɗin kafin ya amsa sai ya ce bana
son sunan amma sai na faɗa, kuma zai gaishe ni wani lokacin da fara'a sannan ya
tafi. Kawai shi baya so a raɓi yayarsa ne saboda mutanen unguwar nan suna yi musu
wata fassara mara daɗin ji. Shiyasa sa baya son kowa ya shiga gidan su dan baya
ƙaunar munafurci da gulma."
Nayla ta ce, "to mu ina ruwan mu da wata fasaara da ake musu Hajja? Shima ya san in
ba dan Didi ɗin ba waye zai shiga gidan nan? To Didi tana da kirki sosai, tun ɗazu
naso fitowa amma ta hana ni ta ce sai yanzu zan fito, shima ƙaryar zan kira Abiy ne
ma ya saka ta ƙyale ni. Har tana cewa na dawo da daddare, to in ba aljanna ake
bayarwa ba me zai kai ni gidan nan na ta?."
Salma ta ce, "bashi da mutunci bai san mutunci ba, ai ko dan yayarsa ya kamata ya
dinga ɗagawa mutane ƙafa. Ni fa shiyasa wallahi bana ma shiga gidan dan bana so na
haɗu dashi kwata-kwata, In ta shigo gidan nan ta dinga yi min mitar bana shiga inda
take, kin san ni babu ɓoye-ɓoye kai tsaye na ce mata Omar yana gidan bazan iya
shiga ba.." Nayla ta ce, "ina yaga kirki? shi ai abin alfaharinsa ne ma a shiga
gidan su. Nima ba dan chaji ba da sai dai ta shigo ta ganni, duk abinda zata ce
bazan je ba."
Hajja tayi dariya ta ce, "ke dai kawai ya firgita ki ne Hauwa'u."
"Wallahi sosai Hajja, haka na saka Didi a gaba ina kuka tana rarrashi." Hajja tayi
dariya sosai ta ce, "ke fa babu abinda zaki cewa Omar wallahi, ya taimake ki a
lokacin da ake gab da tuntsurar miki da budurcinki. Ba dan shi ba da yanzu ana
zancen an yi miki fyaɗe shekarun baya."
"Hmmm!" Shine abinda Nayla tace kawai tana sauke numfashi. Salma ta ce, "Kai Hajja!
daman wai shine ya taimake ta?." Hajja ta ce, "Ke duk labarin da ake yi baki sani
ba?."
"Ban taɓa tsayawa na fahimta ba ai."
"Shine wallahi. Haka ya ɗauko ta kamar jaririya saboda a tsorace take sosai sai
kuka take yi daman ita sarkin shagwaɓa. Gashi babu riga a jikinta sun yaga rigar
atamfar da take jikinta, hakan ya saka shi ya cire rigarsa ta sama ya saka mata
sannan ya dawo da ita."
"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Don Allah Hajja ki daina faɗar haka bana so
wallahi" Nayla ta faɗa da ƙarfi tana runtse ido. Salma ta sake cewa, "Hajja wai
kina nufin rigarsa ya sakawa Nayla?." Hajja ta ce, "ƙwarai kuwa."
"Tab! amma ya cuce ta wallahi."
"Meye na cuta shi da ya yi taimako? Kuma magana ake ta shekaru takwas ko tara
baya."
"To Hajja shekara tara baya a ƙalla tana da shekara sha uku ko sha huɗu."
Hajja ta kalli Nayla da har lokacin idon ta yake a kulle ta ce, "Kuma da yake tana
da girman jiki ƙirjinta a cike yake shiyasa ma suka so lalata ta." Nayla tashi tayi
ta bar falon cikin takaici da baƙin cikin wannan labari, ta tsani ta ji ana bada
labarin nan ko kusa.
Salma ta ce, "Gaskiya Hajja ki daina bada labarin nan, hakan yana nufin fa ya gama
ganin halittarta tun shekarun baya. Yanzu kallon raini yake mata shiyasa ma yake
tsoratata."
Hajja ta ce, "to sai me? Da ya gani ɗin wani abun yayi mata? Da ya barta a wajan su
da ba lalata ta zasu yi ba?. Ni tun daga lokacin nake ƙaunarsa saboda abinda ya yi
mata, daga ranar ya fara riƙe amfani da makami dan a kanta ya fara zubar da jini,
akan taimakon ta ya fara saka makami a jikin mutum. Haka yazo gidan nan yana faɗa
kamar ƙanwar sa aka ao cutarwa. Ni yayi min, kuma har gobe ina kallon sa da wannan
ƙimar."
Salma tayi shiru bata ce komai ba Hajja ma tayi shiru dan da alama tana taya ƴar
uwarta kishi dan ance ya ɗauko ta babu riga. Ita kuma bata ga abin fushi ba,
taimako ne kuma ya wuce wataƙila ma shi ya manta.
Omar kuwa bayan Nayla ta fita shima fita ya yi bai dawo ba sai bayan an
yi sallar magriba as usually shi da mutanen sa. A falon ta suka baje suka ci abinci
kamar yadda ya saba ciyar da su kafin ya sake fita. Bai dawo ba sai tara na dare ya
same ta a zaune da waya a hannunta tana dannnawa.
Kallon sa tayi bayan ya shigo ta ce, "baka faɗa min me ya faru a Abujaa ɗin ba."
Zama yayi ya kalle ta ya ce, "wani ɗan aiki zan yi zuwa wani satin."
"Allah yasa ba harkar siyasa ba ce ba." Murmushi yayi kaɗan amma bai ce komai ba.
Ta kalle shi ta ce, "ina so ka gane ƴan siyasar nan amfani suke yi da ku wajan
lalata rayuwarku su kuma su inganta ta ƴaƴan su, ku ɗauki makami ku je ku yi musu
yaƙi su kuma su gina yaran su da ilimi. Kuna nan kuna wahalar banza kuna haƙilo
ƴaƴan su suna gida cikin ac da kwanciyar hankali, ku kuma sun mayar da ku ƴan
wahala waɗanda ba su san darajar kan su ba. In da gaske yaƙin neman zaɓen su ke yi
su fito a yi da ƴayan su mana. Baza su yi ba saboda rayuwar ƴaƴan su ba irin ta ku
bace, aikin ku ku salwantar da rayuwarku a kan su, su kuma su gina na su." Kallon
Didin yayi ya ce, "Didi kenan."
"Ko nayi ƙarya ne?."
"A'a" ya faɗa yana ɗauko wayar sa ƙirar iphone yana dannawa.
Didi ta kalle shi ta ce, "Ni wai ya aka yi ka ke iya operating ɗin waya? Gashi ko
labarai ne da turanci sai na ji ka karanta ka faɗa min, ya abin ya ke?." Ya kalle
ta da mamaki ya ce, "Oh dan bana so ana yi min magana da turanci shiyasa ki ke yi
min kallon ban iya ko?." Ta yi ƴar dariya ta ce, "A'a ban ce ba. Kawai dai na san
ko secondary school baka yi handling ba, duk da ka ce jarabawa ce baka yi ba."
Ya kalle ta ya ce, "Ai kin san jarabawar ce ban yi niya ba, kuma mutum nawa na
rubutawa waec ana biyana?. Ko ke da ki ke taƙama da wani NCE ko diploma sai mu
zuba, wallahi sai na kai ki ƙasa ko motsi baza ki iya ba. In kina mamaki a feɗe
biki biri har wutsiya." Ta yi dariya sosai ta ce, "Wane mutum! Ku ai gifted ne, ku
karatu yake bi kuna guduwa. Da ka tsaya ka yi karatu ko Omar, da ba ƙaramin amfana
za a yi dakai a ƙasar ka ba."
"Babu niya, tunda sai wanda yake da ilimin boko ne yake zama wani a duniya zan ta
zama a yadda ku ke kallona."
Didi ta ce, "Allah ya ke bawa kafirai arzuƙi a duniya balle musulmi mai bauta
masa?. Allah yana bada duniya ga wanda yake da wanda baya so, lahira ce sai rabo.
Ba sai mai karatun boko ne yake zama wani ba Omar, in dai Allah ya saka maka
albarka zaka iya zarce wanda ya kai matakin professor. Ilimin yana da amfani ne
saboda goyayya da mutane."
"Mutane haka suke ɗauka, wanda bai yi boko ba babu shi babu arzuƙi a duniya.
Turanci ne kaɗai ilimi a nigeria, duk ilimin ka in baka iya shi ba a banza ake
kallon ka. Mu baza mu yi karatun ba, kuma baza mu yi turancin ba, in Allah ya ce
yes sai na ga ɗan shegiyar da zai ce no. Ko yanzu in niya zan je a bani takardar
da ku ke taƙama da ita, kawai babu niya ne."
Didi ta yi dariya cikin tsokana ta ce, "Ni dai ina so naji ya akayi ka ke iya
karanta turanci? Ko duk zaman social media ɗin ne ya kawo haka?. Yadda ka ke zama
ko yaushe cikin danna waya da kuɗi ka ke samu da ita da ka ji daɗi." Murmushi ya yi
kaɗan bai ce komai ba.
Ta ce, "tsokanarka nake, ko a shekarun baya kana cikin wanda makaranta take ji da
ku." Bai bata amsa ba sai girgiza ƙafa da yake yi, ta kalli ƙafar ta sa ta ce, "wai
ni meye benefit ɗin wannan baƙin abun da ka saka a ƙafarka? Gashi dai yana yi maka
kyau sosai, amma adon mata ne."
Taɓe baki ya yi bai ce komai ba ta ce, "ko da yake ko mace aka gani da sarƙar ƙafa
wata fassara ake mata daban."
"Ni kam yana burge ni."
"Sai matarka ta saka." Bai ce komai ba cikin tsokana ta ce, "Wai kuwa ka san me
aure yake nufi?." Wani kallo ya ɗago ido yake mata na kin raina min hankali, Didi
ta sheƙe da dariya ta ce, "to kai ba abokai ne da kai ba, ba wani waje ka ke zuwa
ba ta ya zaka fahimta daidai?." Murmushi ya yi bai kula ta ba dan bazai kulata ba.
Kira ne ya shigo wayar Didi ganin sabuwar number sai ta ɗauka masu siyan abincin ta
ne, ta saka a speaker daga can ɓangaren aka yi sallama jin muryar namiji sai ta
amsa a sanyaye kafin ya ce, "don Allah da Aisha nake magana?." Didi ta ce, "eh
itace. Wake magana?."
"Sunana Abdulhamid."
"Allah sarki!."
"Aisha ina so ki bani lokaci ina so zan yi magana dake." Didi ta kalli Omar da ya
kafa mata idanu ta ce, "Magana da ni? Akan me?."
"Alkhairi. Magana a waya baza ta yu ba ikon ganin ki nake so ki bani." Didi tayi
ajiyar zuciya ta ce, "To san sanar da kai."
"Yauwa na gode, don Allah ki saka lokaci mafi kusa in hakan zai samu."
"Shikenan, zan maka text."
"Na gode sosai, ki kwana lafiya" Didi ta amsa shi kuma ya kashe wayar.
"A ina ya samu number ki?" Omar ya tambaya yana kallonta.
"Omar ta ya zan sani? Ni dai kawai ya kira ni ne."
"Me ya ke