Author : NANA HALEEMA Category : Complete Novels
shiga ɗaki sai gata
ta fito da jaka ta tafiya ta kalli Mama ta ce, "Mama zan tafi" ta kalli Jalila
ƙanwarta da Jalil ɗan autan su da suke fito tace, "zan tafi."
"Allah ya kiyaye" suka faɗa a tare. Jalil ya ce, "Ya Nalya kar ki daɗe, in bakya na
gidan nan babu daɗi." Murmushi ta yi ta shafa kansa tace, "an gama auta. Me zan
taho maka dashi?."
"Wannan donut ɗin da muka taɓa ci...." Ya faɗa yana jan sunan dan ta tuna. Ta yi
dariya ta ce, "kar ka damu auta in sha Allah."
Jalila ta ce, "Ya Nayla ni dai kunun Hajja nake so." Nayla ta yi dariya ta ce, "tun
daga Kano zan yi dakon kunu...? Lallai sannun ki Jalila."
"Allah ba don school ba sai na biki."
"Wani lokacin sai mu je tare."
Mama ta ce, "Nayla har na fara kewarki." Nayla ta ce, "Nima haka Mama" ta faɗa tana
Rungumeta. Abiy da yake kallon su cikin murmushin haɗin kan ƴaƴan na sa ya ce, "to
mu je." Nayla ta saki Mama tana cewa, "Abiy motata fa?."
"A Kano zan bar ki ki ja mota? Gaskiya Nayla da sauran ki baki san ina ne Kano ba."
Tayi dariya suka fito har harabar gidan ta shiga mota tana ɗagawa Mama hannu suka
fita.
Mama ta girgiza kai tana kallon bayan motar har suka fice ta ce, "Nayla lokaci dai,
ki jira ki sha mamaki dan wallahi! wallahi! sai ma farraƙa wannan soyayyar da yake
miki. Ki je ki dawo, sai na tabbatar da kin je gidan auren da zaki sha wahala, So
nake ki ƙare a wahala har abada, bana so ki san daɗin aure ko kaɗan. Ina nan ina
jiran ki!."
*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.
Nana Haleema❤️
*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025
©️*Nana Haleema.*
Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.
https://chat.whatsapp.com/K8IEI39TB803y9pEtzMmdp?mode=ems_copy_t
*Book 1*
*P 04*
Nayla da Abiy tafiya suke a mota a hankali kafin ya kalle ta ya ce, "Ummina." Ta
kalle shi ta ce, "Na'am Abiyna."
"In kin je Kano ban da yawo kin ji?." Ta ɗaga kai sannan ta ce, "in sha Allah
Abiy."
"Kin ga abinda ya taɓa faruwa dake a shekarun baya shiyasa na tsani zuwan ki kano,
ki kula ba ko yaushe zaki gida fita ba."
Nayla ta ce, "zan kiyaye in sha Allah Abiy."
"Yauwa. Allah ya yi miki albarka ya jiƙan Ummanki." Ta amsa da amin kafin ya kalle
ta ya ce, "zan saka miki kuɗi a account ɗinki duk abinda ki ke so sai ki siya."
Tayi murmushi ta ce, "Thank you Abiy." Shima murmushin ya yi kana ya ce, "Ya batun
Sadiq ne? Ban ji kin ce komai ba." Ta turo baki tace, "Abiy ya cika takura, kuma
shi wai in na aure shi bazan yi aiki ba ni kuma gaskiya a'a" ta faɗa da shagwaɓa
tana juyar da fuska gefe tana ƙifta idanu.
Murmushi ya yi cikin ƙaunar ɗiyar ta sa ya ce, "Gaskiya bazai yu ba, ya kamata ki
turo min shi mu tattauna." Ta sake ƙifta idanu wanda hakan ya zama ɗabi’arta tace,
"A'a Abiy, ka ƙyale shi kawai."
"To na ƙyale shi. Sai waye kuma?." Tayi dariya ta rufe fuskar ta alamun kunya ya
sake yin murmushi suka cigaba da tafiya.
Awa biyu da mintina ne suka kawo su Kano, har ƙofar gidan Hajja ya faka motar ya
kalli Nayla bayan ya tsaya ya ce, "Ki shiga ki sanar da Hajja zan shigo mu gaisa."
Nayla ta amsa ta fito ta ɗauki jaka ta shiga gidan dan ta sanar da Hajja zuwan Abiy
ɗin.
Da sallama ta shiga cikin muryar ta mai zaƙin gaske, Hajja da take alwalar sallar
azahar ta amsa yana kallon wacce ta shigo. Nan da nan fuskar Hajja ta washe Nayla
ta tafi a guje ta faɗa jikinta ta ce, "Hajja ta."
Hajja tayi dariya tace, "Hauwa'u ke ce da ranar nan? Sannu da zuwa mutanen zazzau.
To ɗaga ni kar ki karya ni." Nayla tayi dariya ta ce, "Abiy yana waje zai shigo ku
gaisa." Hajja ta tashi daga inda take ta ce, "maza jeki ki ce ya shigo, ai ban san
shi ya kawo ki ba." Nayla ta juya ta fita ba jimawa suka shigo tare da Abiy.
A falo suka same ta Abiy ya zube a kan carpet ya gaishe ta. Hajja ta amsa da fara'a
suka ta ce, "ya yara?."
"Lafiya lau Hajja."
"To ma sha Allah, Allah ya taimaka ya tsare." Ya amsa da amin kafin Hajja ta kalli
Nayla ta tace, "Hauwa'u maza kawo masa ruwa a fridge, Yau Salma bata nan ta shiga
kasuwa sai zuwa anjima zata dawo." Nayla ta ce, "Hajja ni fa shiyasa bana son zuwa
wani lokacin, Na faɗa miki ki daina ƙara u ɗin nan a gaban sunana bana so." Hajja
bata kula ta ba saboda sirikinta da yake wajan.
Abiy ne ya yi murmushi ita kuma ta tashi ta ƙarasa wajan fridge ta kawowa Abiy
ruwan roba harda lemo. Ya ɗauki ruwan ya riƙe a hannun sa. Hajja ta ce, "Na gode fa
Abdullahi da ka kawo min ƴar rigimata." Abiy yayi murmushi cikin girmamawa ya ce,
"Babu komai Hajja, Allah ya ƙara lafiya."
"Amin ya Allah, Allah ya gafartawa Bilkisu."
Da Abiy da Nayla suka amsa da amin kafin Abiy ya ce, "To Hajja zan wuce, ina so na
shiga Kaduna kafin duhu ya yi." Hajja ta ce, "Da wuri haka? Na ɗauka sai anjima har
zan yi waya a kawo maka gurasar Kano ka kaiwa yara." Yayi murmushi ya ce, "Babu
komai Hajja, a kan hanya nake daman ita kawai na sauke zan koma." Hajja ta ce,
"ikon Allah, daga zuwa har zaka koma kamar ba waje mai nisa zaka koma ba? Baza ka
zauna ka ci abinci ba?." Murmushi ya sake yi ya ce, "Hajja kamar wani baƙo? Babu
komai wallahi" ya faɗa yana saka hannu a aljihu ya ajjiyewa Hajja kuɗi sannan ya
fita Nayla ta bi bayan sa.
Yana jin godiyar da Hajja take yi yana murmushi har ya fita. Nayla da take bayansa
ta tsaya kusa da shi ta ce, "Abiy Allah ya kiyaye hanya, Allah ya sauke ka Lafiya."
"Amin Mamana, ki kula kin ji? Banda yawo. Kin ga yadda gari yake babu tsoro ƙwacen
waya yayi yawa, duk inda zaki je kar ki yi dare kuma ki sanar dani. Ki kuma
tabbatar driver Hajja ne ya kai ki ban yarda da hawa keke ba kin ji?."
"İn sha Allah Abiy, Kuma daman Hajja bata barin fita da daddare."
"Yauwa."
"Allah ya kiyaye a gaishe da Mama" ya amsa yana shiga mota ya tafi.
Wajan Hajja ta koma tana cewa, "Hajja me ki ke dashi a gidan nan? yunwa
nake ji wallahi." Hajja ta ce, "Sarkin ci, shiyasa ki ke ƙiba ai. Duba Salma tayi
abinci kafin ta shiga kasuwa." Falon Hajjan ta shiga dan a ciki kitchen yake dan
gidan Hajja gidan ƴan gayu ne. Hajja ta biyo bayanta sai ta same ta ta shiga da
kayan ta ɗakin da take sauka in tazo sannan ta fito.
Hajja ta kalle ta tace, "Baki zuba abincin ba?."
"Sallah zan fara yi tukunna, wai Hajja ya gidan yau babu wuta ne?."
"Wata waya ce ta solar ta katse har yanzu dai ba a zo an gyara ba." Nayla ta wara
idanu ta ce, "wai kina nufin babu wuta a gidan nan?."
"Eh yanzu dai kam babu, Wataƙila sai gobe ko jibi." Nayla ta ce,
"Innalillahi! Wallahi da na sani bazan zo ba sai an gyara, Ga wayata babu chaji ina
zan saka?." Ta faɗa ido na cikowa da hawaye cikin shagwaɓa. Hajja ta harare ta
tace, "Sarkin shagwaɓar tsiya, gabaɗaya Abiy ya shagwaɓaki. Ki yi sallah tukkuna
sai a san abinda za a yi." Nayla ta ce, "wallahi Hajja gabaɗaya raina ya ɓaci, bana
son zama babu chaji" ta faɗa tana komawa cikin ɗakin tana mita ta yi alwala ta fito
tayi sallar azahar sannan ta ci abinci.
Kallon Hajja tayi da take kallon ta itama ta ce,"babu masu chaji a unguwar
nan na kai?." Hajja ta ce, "a sace miki wayar ai." Nayla ta ce, "ni fa shiyasa ban
cika son zuwa Kano ba wallahi, da na san babu wuta ai da na taho da power bank
ɗina. Yanzu tsakani da Allah ta ya zan iya rayuwa babu chaji?."
Hajja ta ce, "In kin huta zuwa la'asar sai ki shiga wajan Aisha ki saka chaji."
Nayla ta ce, "wace haka?." Hajja ta kalle ta tace, "Didi." Nayla ta wara ido ta ce,
"wannan mutumin yana nan zan shiga gidan? A'a rufa min asiri kar ya naushe ni,
Itama Didin in ta shigo gaiahe ki ma gaisa." Hajja tayi dariya ta ce, "babu abinda
zai yi miki, ki huta sai ki shiga."
Nayla ta ce, "ni tsoronsa nake ji Hajja, Zuwana na ƙarshe harara ta ya dinga yi dan
kawai ina hira da Didi. Didin ta fishi kirki shi bashi da mutunci, daman gashi da
zubin abin tsoro." Hajja ta ce, "ke dai baza ki ce bashi da kirki ba, dan ya
taimake ki taimakon da babu wanda ya taɓa yi miki shi a rayuwa." Ta turo baki ta
ce, "ni wallahi ban so kuna tuna min wannan maganar" ta faɗa tana tashi ta shiga
ɗaki. Hajja tayi dariya zuciyarta cike da farin cikin ganin jikarta ta.
Didi kuwa cikin lokaci kaɗan ta kammala sana'ar abincin da mutane suka
saka order, mai delivery ya tafi kaiwa kowa tayi wanka ta gyara gidan kamar ba ita
ce tai aikin ba. Sana'arta karɓe ta, tun tana yi da kaɗan-kaɗan har ta kai ta kawo
wata ran sai ta yi abinci pack ɗari da hamsin ko ɗari biyu. Sosai ta ke samun
alkhairi tana kashe matsalolin gabanta, babu abinda zata cewa Allah sai godiya.
Shiyasa kullum in ka ganta fes da ita, daman ga ta ƴar gayu in ta yi kwalliyya sai
ka kalle ta ka sake kallo saboda babu abinda ya fi ƙarfinta.
Tana zaune bayan ta idar da sallar la'asar tana ta zullumin rashin kiranta da Omar
bai yi ba tunda ya tafi Abuja, ta kuma san hakan ba halin sa bane ba. Sallama aka
yi ta amsa tana jiran a shigo. Nayla ta shiga falon bayan ta sake yin sallama Didi
ta amsa tana murmushi kafin ta ce, "kaii Nayla! Saukar yaushe?."
Nayla tayi murmushi ta ƙarasa ta zauna ta ce, "ɗazu da azahar nazo Didi, Ina yini."
"Lafiya lau Nayla, ya hanya?."
"Alhamdu lillah."
"Ma sha Allah, sannu da zuwa. Tunda kika koma Wancan lokacin baki sake dawowa ba,
na cewa Hajja Nayla tayi mana yaji kenan."
Nayla tayi murmushi ta ce, "Wallahi Abiy ne sam baya son zama na a Kano, kuma ga
makaranta shiyasa dole ina can. A cikin kwanakin nan na kammala tahfiz ɗin da na
shiga shiyasa." Didi tayi dariya ta ce, "baya so ki yi nisa dashi ne." Nayla
murmushi ta yi kafin ta ce, "Didi don Allah zan saka chaji." Didi ta ce, "Kamar
wata baƙuwa Nayla? Jeki ki saka mana." Nayla ta tashi ta saka chaji ta dawo ta
zauna.
Didi ta kalle ta ganin sai murmushi ta yi sai tayi murmushi itama ta ce, "kwanaki
na ga kun sha biki sai rawa ki ke, na ce Nayla akwai son rawa." Nayla ta kulle
fuskar ta tana dariya ta ce, "Didi ashe kin ga status ɗin."
"Na gani tunda gashi na faɗa miki." Nayla ta sake yin dariya amma bata ce komai ba.
Didi ta ce, "yanzu kuma na gama aikin abincin order bara na duba miki abinci."
Nayla ta ce, "Na ƙoshi Didi, ina zuwa gidan Hajja na ci abinci." Didi ta ce, "Daman
ke ai bakya cin abincina, baki taɓa ci ba, kullum kin ƙoshi ki ke cewa."
"Ba haka bane ba wallahi, ina zuwa na ci abinci bana jin yunwa."
"Amma dai zaki mana shekara ko?." Nayla ta wara ido ta ce, "taɓ! Ai ko sati biyu
bana tunanin zan yi a nan." Didi tayi dariya ta ce, "Abiy yafi so ya dinga ganin ki
kullum, da gaskiyarsa."
Nayla ta murmusa tana jin daɗin zama da Didi, saboda mace ce mai fara'a da wasa ga
saurin sabo. Ta zama tamkar jikar Hajja itama, tana matuƙar girmama Hajja sosai, ko
me yake damunta Hajja take iya faɗawa ta bata shawara. Shiyasa duk wani mai zuwa
gidan Hajja ya san Didi saboda gidan zuwan ta ne, ko biki ake a ɓangaren Hajja Didi
na zuwa kuma an santa sosai. Didi ta miƙe ta shiga ɗaki tunawa akwai abinda zata yi
tabar Nayla a zaune tana ƙarewa falon kallo.
“Wacece ke!?.”
Abinda taji an faɗa kenan cikin kakkausar murya. A hankali ta juyo a firgice suka
haɗa ido nan take gabanta ya yanke ya faɗi. Kafin ta tattaro abinda zata ce ya ware
murya cikin tsawa ya ce, "Nace Wacece ke!? Me kika yi a zaune a na wajan?." Nayla
tsabar tsoro bata san ta miƙe tsaye ba, jikinta na rawa nan da nan ido ya cika da
hawaye abin ka da ƴar shagwaɓa.
"Goje!, Tk!, Bash! kuna Ina!" Ya faɗa da ƙarfi yana kallon ƙofa, sai gasu sun shigo
falon da hanzari. Nayla ya nuna musu ya ce, "ya akayi wannan ta shigo gidan nan?
Wacece ita? Kenan in bana nan barin kowa ku ke yi ya shigo!?." Goje ya kalli Nayla
da har lokacin jikinta yake rawa cikin tsawa ya ce, "Ke daga ina ki ke!? Waye ya
baki izinin shigowa gidan nan?."
Numfashi take ja daƙyar hawaye na sakkowa daga idonta, ta saka magana balle ta iya
cewa wani abun. "Ba magana ake miki!?."
"Cha....ji....na....ka...wo..." a fusace Omar ya ce, "Nan gidan kawo chaji ne? Ku
fitar min da yarinyar nan yanzu."
Didi da take banɗaki take jiyo amon maganarsa da hanzari ta fito dan da tasan zai
shigo baza ta bar Nayla ita kaɗai ba, ta san sai an yi haka. Tana fitowa falon ta
ce, "Kar wanda ya taɓata."
Cak suka tsaya da ƙarasowa inda Nayla take ta jawo hannunta zuwa kusa da ita sai
kawai ta fashe da kuka ta kwanta a jikin Didi. Didi ta shafa kanta ta ce, "yi
haƙuri Nayla, da na san zai dawo yanzu da ban barki ke kaɗai ba, Zauna" ta faɗa
tana zaunar da ita akan kujera.
Omar ta kalla fuska babu walwala ta ce, "kai wai meyasa ka ke haka ne? kenan bazan
yi baƙi ba sai wanda ka sani?. Haka kawai daga dawowarka kazo ka fara yiwa ƴar
mutane ihu ba tare da ka santa ba? Kenan bazan yi baƙuwa ba lallai sai ka santa?
Meye haka ne?."
Kallon Didi yayi amma bai ce komai ba ta kalli su Goje ta ce, "kenan ku ne masu yi
masa gadina, sai baƙin da ku ka ga dama sannan zasu zo su ganni ko?." Zasu yi
magana ciki tsawa ta ce, "ku fice ku bani waje!." Dole suka cika umarninta suka
fita. Didi ta dawo da kallonta gare shi ta ce, "kar ka sake ganin baƙuwata ka sake
yi mata ihu, in kai baka buƙatar baƙi ni ina buƙatarsu, wajena tazo ba wajanka ba
dan haka babu ruwanka da ita."
Wani irin yake ji a jikinsa da zuciyarsa, ya zubawa Didi ido cikin abubuwan da suka
tarar masa a ƙirji. Na farko kukan da Nayla take yi yana daga cikin abinda yake
sake harzuƙa shi, a ganinsa dan shagwaɓa shi zata saka a gaba tana yiwa kuka, me
aka yi mata?. Na biyu faɗan da Didi take masa a gaban baƙuwa yafi komai ɓata masa
rai. Ta fi kowa sanin baya so ayi masa faɗa a gaban mutane balle kuma mace baƙuwa
wacce bai santa ba, babban abin haushin ma ko gaisawa bata tsaya sun yi ba ta fara
yi masa faɗa akan wata wacce bata da alaqa da ita.
Kallon Nayla ya yi a fusace ya ce, "dalla malama ki yiwa shiru ko na yanka bakin
ki!." Wata irin firgita Nayla tayi sai gata ta dawo ƙasa daga kan kujera ta cure
waje ɗaya jikinta na tsuma. Babu zato babu tsammani ta ji maganar shiyasa ta
gigice.
Didi ta sake fusata ta kalle shi ta ce, "Omar fita ka bar min falo." Ido ya waro
waje jin mamakin abinda tace, a daidai lokacin da Nayla ta kalle shi sai ta sake
gigicewa ganin idanunsa kamar za a saka hannu a cire saboda girma. Kafin ya yi
magana ta sake cewa, "na ce ka fita ko!?." Bai ce komai ba ya juya ya fita a
zuciyarsa yana tabbatar da dole ma ya hukunta Nayla duk da bai santa ba.
Didi ta koma kusa da Nayla ta riƙe ta ta ce, "yi haƙuri Nayla, taso ki zauna." Ta
faɗa tana taso da ita ta zaunar da ita akan kujera ta kawo mata ruwa mai sanyi ta
ce, "sha ruwa." Ba musu ta karɓa tasha tana sauke ajiyar zuciya. Didi ta kalli
gaishe ta sai ta bata dariya ganin hawaye shaɓe-shaɓe fuskarta har tayi ja kamar
wacce aka yiwa duka.
"Yi haƙuri kin ji, haka nan yake shi in yaga baƙo ko baƙuwa in bai san su ba
shikenan sai faɗa. Ki nutsu ai ya tafi ki goge hawayen nan."
Nayla ta goge idanunta tana jan numfashi amma har lokacin a tsorace take. Sai da
Didi taga ta nutsu sosai sannan ta sake cewa, "kar ki damu bazai sake yi miki haka
ba." Nayla ta ce, "ai bazan sake zuwa ba ma Didi, bara na ɗauki waya
ta na tafi."
Didi tayi dariya ta ce, "Wallahi babu inda zaki je, kuma in baki shigo gidan nan ba
shi zan saka ya ɗauko min ke a wajan Hajja." Nayla tayi gum bata ce komai ba amma
zuciyarta cike take da tsoron sa, bata taɓa ganin halitta ta mutane wacce take
tsoro kamar sa ba.
Ganin ta yi shiru sai Didi ta tashi ta shiga kitchen ta ɗauko abincin da ta dawo
kusa da Nayla ta ce, "ko zaki kai masa abincin?." Yadda Nayla tayi da idanu cikin
firgici ya bawa Didi dariya ta ce, "wasa nake kwantar da hankalinki" ta faɗa tana
fita tana dariya dan wallahi yadda ta tsorata dariya ta bata.
Setroom ɗin da yake gidan wanda ya kasance ɗakinsa ta nufa, kafin ta ƙarasa ya fito
har yayi wanka ya canja kaya zuwa na shan isa, dan rigar jikinsa ko hannu bata
dashi sai wando wanda ya wuce guiwa da kaɗan. Kallon sa tayi ta ce, "sai mu koma ka
ci abinci." Bai kula ta ba sai ma sake tamke fuska da yayi yana kallon ƙofar ɗakin
da alama tana ciki tunda ga takalmin ta nan.
Didi ta ce, "Magana nake maka Omar." Nan ma ya share ta dan tsakani da Allah in ba
dan ita bace da yanzu ba wannan labarin ake yi ba, ta bashi haushi sosai. Itama sai
ta ɗaure fuska ta ce, "ina yi maka