Author : NANA HALEEMA Category : Complete Novels
yake sonka ba amfani yake yi da kai. Da zarar ya ji ƴarsa
na sonka duk wannan zai gushe, saboda ba matsayin ku ɗaya ba."
A fusace Omar ya ce, "Saboda ita muslma ce ni kafiri shiyasa ki ke kiran ba
matsayin mu ɗaya ba?." Mamaki ya bawa Didi ganin yaji haushin abinda tace, har ya
kasa ɓoyewa ya nuna mata hakan. Didi ta ce, "a wajan su gwara kasancewar ka kafiri
akan kaje a yadda ka ke kace kana sonta Omar."
Didi ta ta sake tausasa murya ta ce, "Ni don Allah ka rufa min asiri kar ka bari
wannan kalaman nata ya yi tasiri a kanka, yadda na sanka baka bawa kowa ƙofa a
rayuwarka itama kar ka bata, ka ɗauka komai ba komai bane ka manta da ita, ka toshe
duk hanyar da zata bi wajan neman ka."
Omar ya zuba mata idanunsa yana zagawa dasu a fuskarta ya ce, "Yanzu kika gama faɗa
min baka sanin lokacin da soyayya take shiga zuciyarka, nima in soyayyarta zata
shiga zuciyata zan hana ne?."
Gaban Didi ya faɗi jin kalamansa, tsoron ta ɗaya kar taje ya fara son Narma ta
shiga uku. Didi ta ce, "Addu'a zaka yi Allah kar ya baka ikon fara sonta." Baice
komai ba ya fita yana mamakin wannan kalamai na Didi masu kama da rainin hankali.
Didi da kallo ta bishi a bayyane ta ce, "Wai Narma ke son Omar...Innalillahi
wa'inna ilaihir raji'un, ya Allah ka kiyaye min ƙanina daga faɗawa tarkon
soyayyarta, gwara ce itace take sonsa da ce shine yake sonta, gangancin fara son
Narma kamar ganganci da rayuwarsa ne. Ya Allah kar ka bashi ikon fara son wannan
yarinya" ta faɗa kamar zata yi kuka.
••••••
Narma da zazzaɓi mai zafi ta sauka a Abuja, ta kira Najwa ta ce tazo ta
ɗauke ta, ba jimawa sai gata ganin yanayin da take ciki sai ya bata tsoro ganin da
gaske bata da lafiya kawai ta wuce asibiti. Sai bayan sun je asibitin an bata
taimakon gaggawa sannan ta kira Mum ta sanar da ita.
Awa biyu tayi a asibitin suka koma gida an samu zazzaɓin ya sauka. Bacci tayi
sosai bayan sun koma dan har da maganin bacci aka bata, ta jima sosai tana bacci
har dare sannan ta farka, da yake ta san ba sallah zata yi bata yi ƙoƙarin yin
sallah ba tana kwance tana tuna kalaman Omar masu kama da sukar mashi a zuciyarta.
Tashi tayi ta tsaya gaban mirror tana kallon kanta, wai itace take son namiji kamar
Omar, ɗan daba wanda bashi da komai bai san komai ba sai riƙe wuƙa. Ita Barr Narma,
manager director ta kamfanin mahaifinta, ita Narma da take juya kuɗin mahaifinta da
suka haura billions wai itace take son wani da bashi da komai har yake mata
wulaƙanci. Turarukan da suka kan madubin ta watsar, ta jawo madubin ya faɗi kasa ya
tartwase a wajan, ta faɗa kan gado tana fashewa da kuka.
A guje Mum, Dad, Najwa da Nabil suka shigo daƙin. Dawowar Dad kenan sun rako shi
sama wajan ta suka ji sautin fashe-fashe daga ɗakin. Ganin yanayin da take ciki ya
saka su ƙarasowa da gudu kowa yana tambayarta abinda yake faruwa. Bata iya magana
ba sai kuka da take yi a jikin mahaifinta mai tsuma zuciya. Duk sun yi shiru suna
surarem kukan da take yi, sai da tayi mai yawa sannan ta tsagaita sai ajiyar zuciya
da take yi.
Najwa ta kawo mata ruwa Dad ya bata tasha yana kallon ta a nutse. Sai da yaga ta
nutsu sosai sannan ya ce, "Me yake damun ki Daughter? Me ya faru kika shiga wannan
yanayin?."
Narma murya a shaƙe ta ce, "I'm in love Dad." Dad ya kallo Mum ya sake kallon Narma
ya ce, "kina nufin ki ce duk wannan damuwar da kike ciki saboda soyayya ne? You're
in love, that's why you looks like this?." Bata yi magana ba sai lumshe ido ta tayi
a jikin Dad bata ce komai ba.
Dad ya yi shiru bai ce komai ba Mum ta kalle ta tace, "Narma taso mu je ki ci
abinci." Bata samu damar magana ba ta miƙar da ita tsaye suka fito falo ta zaunar
da ita. Tea ta zuba mata ta miƙa mata ta ce,"Oya take it." Narma a sanyaye ta ce,
"I want to brush my teeth first."
"Okay, Najwa kai ta bathroom." Najwa ta riƙeta ta miƙe tsaye, Dad ya ce, "take her
to my bathroom, sai an gyara ɗakin ta, ki buɗe drawer akwai sabon brush." Da to ta
amsa suka wuce zuwa ɗakin Dad.
Basu jima ba suka dawo, Narma ta zauna tana shan tea ɗin kaɗan-kaɗanan tana tunanin
yadda suka yi da Omar. Sai da shanye tea ɗin tass suna ta yi mata sannu. Sai da ta
gama ta nutsu sannan Dad ya ce, "akwai abinda ki ke so?."
Ta girgiza kai alamun babu ya ce, "okay, tell me your problems. Who is the guy you
are in love with?." Ta yi shiru bata amsa ba, Mum ta ce, "Narma Dr ya tabbatar mana
da kina cikin damuwa shine ya haifar miki da zazzaɓi ɗazu, yanayin muka same ki a
ɗaki ya tabbatar min da maganar Dr gaskiya ne. Waye wanda ki ke so haka?."
Shiru tayi bata ce komai ba, Nabil yayanta ya ce, "Narma feel free ki faɗi abinda
yake ranki, kar ki damu zamu yi supporting ɗinki hudrend percent." Narma tayi
ajiyar zuciya ta ce, "Dad ku taya ni da addu'a saboda kamar bazai karɓi ni ba." Mum
ta ce, "what! Kina nufin daman ke kike sonsa ba shi yake sonki ba?." Narma ta ɗaga
kai alamun eh. Mum cikin wani yanayi ta ce, "damn it! Ta ya hakan ya faru Narma?."
"I don't know" ta faɗa kamar zatayi kuka.
Dad cikin rarrashi ya ce, "ɗan waye? Ɗan sarkin Dubai ne?" Ya faɗa yana kallon ta,
dan a ganinsa duk wanda Narma zata so har haka kuma bai san tana yi ba, bai ma
karɓeta ba, a ganinsa sai dai ɗan sarkin Dubai. In ba haka ba to waye zata iya
wannan son da ya saka mata zazzaɓim damuwa? A ganinsa ko ɗan president albarka.
Narma ta katse shi ta ce, "Not at all. Dad...!" Ta faɗa tana jan sunan tare da
kallon sa. Ta ce, "promise me you will allow me to marry him at any cost." Dad ya
riƙe hannunta ya ce, "I promise you zaki aure shi indai yana sonki, abinda bazan
amince ba shine in baya sonki bazan yarda ki aura shi ba." Ta yi murmushi ta ce,
"Dad I'm Barr Nass don't forget, i will attract his attention."
Dad ya yi murmushi ya ce, "anything for you my daughter. Kema ki yi min alƙawarin
damuwarsa baza ta sake baki damuwa har ki yi ciwo ba." Narma ta girgiza kai ta ce,
"in sha Allah." Rarrashinta suka dinga yi suna bata baki har ta ware ana hira da
dariya da ita.
Bayan Kwana biyu.
Narma ta tabbatarwa da kanta Omar shine farin cikin ta dole ta san ya zatayi kafin
ta rasa ranta, duk da tayi ƙoƙarin ajjiye damuwar ta kamar yadda ta yiwa mahaifinta
alƙawari amma soyayyar tana nan a tare da ita. Ta daure bata nemi Omar a kwanakin
ba tana so taga zai kira ta ko bazai kira ta ba.
Abin mamakin bai kira ba kuma bai yi mata koda text ba, sai ta tabbatar da gaske
bai ɗauki maganar ta da mahimmaci ba tunda gashi ya share ta bai kira ya ji ya take
ba.
Shi kuwa Omar shi kansa ya san ya damu da lamarin Narma, daurewa kawai yake yi yana
nuna bai damu ba amma a zuciyarsa ya damu da ita sosai ma kuwa. Bai san dalilin da
ya saka ya damu ɗin ba, shi ba sanin so ya yi ba balle ya ce sonta yake yi. Bai
taɓa ƙoƙarin kiranta ba,
dan shi kansa ya san bazai iya neman ta ba ko meye zai faru, dalilin da ya saka ya
jure rashin jinta ya share ya bar tunaninta.
Kamar ko yaushe yana zaune cikin ƴan uwan sa ƴan daba ana meeting akan ƴan wata
unguwa suna faɗa kuma ana cewa ƴan unguwar su ne. Yana zaune yaji kiran waya amma
bai duba ba har suka gama meeting ɗin da bai ce komai ba, hankalin sa baya tare
dashi shiyasa bai ce komai ba. Ana gamawa ya tashi ya nufi gida. Yana shiga ɗaki
wayarsa sake yin ƙara ya ɗauko tare da zubawa number ido, har lokacin bai yi saving
ba dan baya so ba, kawai baya so ya bada wata ƙofa da wani abun zai shiga ransa.
Kamar bazai ɗauka ba sai kuma ya ɗauka tayi shiru bata ce komai ba shima bai ce
komai ba. Nunfashinta kawai yake ji yana sauka a hankali, saukar numfashinta sai ya
saukar masa da kasala sosai ya yi shiru bai ce komai ba.
"Da ban kira ka baza ka kira ni ba ko? Ka san damuwar da na shiga a kanka kuwa? Ka
san har asibiti na kwanta saboda kai?. Saboda Ina sonka ka ke min haka ko Faruk?
Shikenan na gode" ta faɗa a sanyaye.
Lumshe ido ya yi zuciyarsa na bugawa sosai, in ya ce bai ji daɗin maganarta ba
ƙarya yake yi, in ya ce bai ji maganar ta na shiga zuciyarsa ba ƙarya yake yi, in
ya ce bai ji rauni ya mamaye zuciyarsa ba ƙarya yake yi. Buɗe ido ya yi har lokacin
bata sake magana ba yana dai jin nunfashin ta kamar ɗazu.
Shiru ya rasta tsakani har mintina biyu sannan ta sauke ajiyar zuciya ta ce,
"shikenan ka gaishe da Didi."
"Ya hanya?" Ya tsinci muryarsa ya faɗa ba tare da ya shirya ba. Narma jin maganar
sai tayi ajiyar zuciya mai nauyi ta ce, "hanya ba lafiya ba, ni kaina ba lafiya
nake ba Faruk."
"Ayya Allah ya bada lafiya" ya faɗa a hankali.
Narma ta ce, "Amin,Thank you." Nan ma ya sake yin shiru bai ce komai ba, Narma ta
ce, "Okay byee" ta faɗa tana yanke wayar da sauri. Shiru yayi yana kallon wayar
yana mamakin kansa da ya tambaye ta hanya, to Ina ruwansa?. Numfashi ya sauke, ya
saka a ransa tausayinta yake ji shiyasa haka da wannan tunanin ya share wancan.
•••••••
Mutanen Saudia sun dawo Kaduna, Nayla har lokacin bata dawo daidai ba domin
abinda take ji yafi ƙarfin zuciyarta. Nauyi take ji kamar dutse aka ɗora mata a
ƙirjinta, wani lokacin numfashi wahala yake mata saboda nauyin da zuciyarta tayi
mata. Washe garin da suka dawo Twiny ta juya Kano saboda mijinta ya gama komai na
gida. Sai ta sake zama shiru-shiru bata da abokin shawara, gashi tana son zuwa Kano
amma tana tsoron Abiy kasancewar bata jima da dawowa ba.
Kamar yadda ta zaɓarwa kanta kullum tana ɗaki a zaune sai ga autan su ya shigo ya
ce Abiy yana kiran ta. Sai da ta daidaita nutsuwarta sannan ta fito ta same shi a
falon da shi kaɗai yana kallon tv. Da sallama ta shiga ya amsa yana bita da kallo
tare da tattara nutsuwar sa gabaɗaua a kanta.
Sai da ta zauna sannan ya ce, "Mamana dawo kusa dani" ya faɗa yana nuna amsa kan
kujerar da yake. Ba musu ta tashi dawo kusa dashi ya fuskance ta ya ce, "Mamana
baki da lafiya ne?." Ta girgiza kai alamun a'a ya ce, "bana son body language, ki
yi min magana."
"Lafiyata lau Abiy." Abiy ya ce, "ƙarya ki ke yi, tun a Saudia kika canja gabaɗaya.
A wancan lokacin na karɓi dalilinki ne kawai saboda kar na takura ki, amma ba dan
na amince da abinda ki ka ce ba. Me yake damun ki kika koma haka? har rama naga kin
yi, me ya faru?."
Nayla tayi shiru bata ce komai ba Abiy ya ce, "ban kai na ji damuwarki ba?." Da
sauri ta ce, "A'a Abiy."
"To faɗa min."
"Babu ne shiyasa."
"Kar ki yi min ƙarya Mamana, ƙarya ba halin ki bane. Ki faɗa min gaskiya kafin na
gano da kaina." Nayla ta ce, "da gaske nake Abiy, babu abinda yake damuna."
Abiy ya yi shiru yana kallon ta cikin nazari, bai yarda da abinda ta ce ba, ya san
kawai bazata faɗa bane amma zai san yadda zai yi mata. Ya sauke numfashi ya ce,
"shikenan. Ga offer ki" ya faɗa yana miƙa mata takarda.
Nayla murmushi tayi cikin farin ciki ta karɓa Abiy ya ce, "Federal inland revenue
service ne. Ranar Monday zaki je ki gama duk abinda ya kamata." Nayla cikin farin
ciki ta ce, "Abiy na gode, Allah ya saka da alkhairi ya biya ka da aljanna."
Murmushi ya yi ya ce, "Amin Nayla. Sai zancen shagon ku keda Twinyn ki, za a ƙara
muku jari ku cigaba da juya kuɗin, Kwana biyu ma ke bakya zuwa."
Nayla farin cikin samun aiki duk ya cika mata zuciyata, burinta a rayuwa kawai ta
yi aiki shiyasa Abiy ya samar mata. Ta ce, "Abiy ni na rasa me zance saboda murna."
Murmushi ya yi kawai yana kallon ta ya ce, "Nayla kenan. Akwai abinda ki ke so
bayan wannan?."
Nayla tana murmushi ta ce, "babu komai Abiy. Kawai Ina so na kaiwa Hajja tsarabarta
ne." Murmushi ya yi ya ce, "Nayla sarkin zuwa Kano, Ke dai kina son shiga Kano."
Tayi dariya ta ce, "Kano da daɗi Abiy."
"Shikenan, in kin shirya sai ki je gobe ki yi kwana biyu ki dawo."
Farin cikin da Nayla taji ko da ya miƙo mata offer bata ji ba, hakan ya bayyana a
kan fuskarta sosai da murya ta ce, "Na gode Abiy, Allah ya saka da alkhairi ya
jiƙan mahaifa, Allah ya jikan Ummana." Murmushi ya yi ya ce, "Amin. Bani offer ɗin
kinje ki shirya." A guje ta miƙe ta shiga ɗaki tana murna.
Cikin murna ta yi ajiyar zuciya ta zabura ta buɗe trolly bag ta fara zuba tsarabar
Hajja da ta Salma har da Didi ma. Wata maroccon jallabiya ta maza ta ɗauko kalar
baƙa mai kyau da santsi ta kalla ta ce, "zata yi masa kyau sosai." Murmushi take
kamar shashasha, tana hango in Omar ya saka rigar ya zai koma. Da haka ta gama zuba
kayan a jakar tafiya Kano.
Wayarta taji tana ƙara da ta duba sai ta ga Abiy ne, tana ɗauka ya ce, "Mamana ki
bar zuwa Kano gobe a gama settling aikin nan da kika samu, in aka gama kafin ki
fara aiki sai ki je ki dawo. Yanzu ake sanar dani gobe ake so ki je." Sai jikinta
ya yi sanyi ta ce, "to Abiy" daga haka ya yanke wayar ita kuma ta zauna gabaɗaya
murna ta koma ciki.
Nayla Anya kuwa🤔
*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.
Nana Haleema❤️
*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025
©️*Nana Haleema.*
Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.
*Book 1*
*P 22.*
Kwance tashi babu wahala a wajan Allah, a hankali zuciyar Narma ta fara rinjayar
zuciyar Omar, tun tana kira yana ƙin ɗauka har ta kai in bata kira shi bama baya
jin daɗi. Gashi da shegiyar izza shi bazai iya kiranta ba, in ta kira kanta ta
yiwa, in bata kira ba bazai kira ba.
Tun yana ƙaryata kansa akan yana sonrta har ya amince da gaske yana sonta, kuma
shima ya shirya auren ta kamar yadda ta shirya aurensa. Ranar da ya bayyana mata
kamar zata yi hauka saboda murna, duk da bai yi wasu dogayen kalamai ba, kawai ya
ce mata shima zai iya aurenta daga nan bai ƙara koda kalma ɗaya ba. Narma ta dinga
murna tana farin ciki, shi kansa farin ciki yake yi, duk da wani lokacin sai ya ji
kamar soyayyarta ta bar zuciyarsa, bayan kwana biyu sai ta dawo.
Duk da basa haɗuwa amma babu laifi sun saba a waya, da yake ba aikin yi ne dashi ba
in dai zata kira shi zata same shi, shine dai bai cika kiran ta sosai ba.
Yau ta kama ranar juma'a kamar ko wanne sati Didi ta kammala abincin sadaka ta
rabawa yara ta koma tana hutawa ya shigo bayan an sakko daga masallaci. Da kallo
take binsa ya zauna ta ce, "har an sakko?." Gira kawai ya ɗaga alamun eh kafin ya
kalle ta sosai ya ce, "Didi." Ta kalle shi ba tare da ta amsa ba, ya ce, "ta ya
zan iya gane Ina son wata?."
Da kallon rashin fahimta ta bi shi ta ce, "ban gane ba, me ka ke nufi?."
"Ina nufin in na fara son wata ta ya zan fahimci hakan?. A taƙaice ya ake gane
soyayya?."
Didi da kallo take bin sa cikin faɗuwar gaba, babban tashin hankalin ta bai wuce
kar ya ce yana son Narma ba, amma tunda ya tambaya zata faɗa masa dan tafi kowa
sanin bai san soyayya ba. Didi ta ce, "To nima Omar ba wani sani nayi ba ai."
"Amma baza ki kasa yi min bayani yadda zan gane ba ai ko?" Ya faɗa yana tsare ta da
ido. Didi ta ce, "Zuciyarka zata dinga bugawa a yayin da ka ganta, zaka dinga ɓata
lokacin ka wajan saurarenta, zaka dinga jin shauƙi sosai koda sautin muryarta ka
ji, zaka dinga jin zaka iya yin komai dan ka mallaketa. Sannan....." dakatar da ita
ya yi ya ce, "iya wannan da ki ka faɗa ma ya isa."
Kallon fuskar ta yayi, cikin rashin tsoro ya ce, "Hakan yana nufin ina son Narma,
daman na tambaye ki ne dan na tabbatar kuma na tabbatar ɗin."
Cikin tashin hankali Didi ta ce, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Omar ka san
abinda ka ke faɗa kuwa?. Kana son Narma ka ce fa? Don Allah ka faɗa min wasa ka ke
yi." Da mamaki ya ke kallon ta jin tayi dogon salati ya ce, "wannan salati haka
Didi na meye? Bata cancanci na sota ɗin ba ne?."
"Omar kai ne baka cancanci ka sota ba, Omar ita ba ajinka bace, don girman Allah ka
rufa min asiri ka bar maganar nan, Ina kai ina soyayya da ƴar gidan sanata Omar?."
"Kin zo a makare Didi, domin kuwa wannan asirin naki bazai rufu ba. Ina sonta kuma
zan je har gaban sanatan na faɗa masa."
Didi numfashi ta ja kawai tayi shiru bata ce komai ba, dan babu amfanin maganr, ta
san kuma wallahi sai ya aikata tunda ya faɗa. Hawaye yaga tana yi ya tausasa murya
ya ce, "don Ina sonta shine ki ke kuka?."
Didi ta ce, "Omar bana so wani abun ya same ka, Ina ji a jikina soyayyarta bazata
zama alkhairi a gare ka ba."
"Kin san gaibu ne Didi?." Jin tambayar da ya yi mata ya saka take kallon sa da
mamaki, kenan dai da gaske son Narma yake yi tunda gashi yana yi mata wata
bahaguwar tambaya.
"Ban san gaibu ba Omar, amma auren ka da ita da kamar wuya." Omar ya murmusa ya
jingina da kujera ya ɗora ƙafa kan ɗaya ya ce, "ki taya ni addu'a kawai, amma kin
san tunda na ɗauki hanya bazan karkace ba. Zan je har gidan su har gaban sanata na
nemi auren ta, kin san