Author : NANA HALEEMA Category : Complete Novels
gaisa da Hajja suma duk suka gaishe ta amsa da murmushi ta
ce, "Hajja mutuminki shine yake firgitata, na faɗa mata kuma ta daina jin tsorosa
babu abinda zai mata amma ta kasa. Kuma da zata zauna a garin nan na wani lokaci
suna sabawa shikenan. Wahalar sabo ne dashi kawai." Salma ta ce, "Didi ko iya
wannan idanun na sa ma ai ya isa ka ji tsoro balle ya buɗe baki."
Didi tayi dariya ta ce, "yanzu saboda shi sai ku daina zuwa wajan Yayarku?." Salma
ta ce, "ai Didi lamarin na sa ne akwai ban tsoro." Nayla ta ce, "Ke da bai taɓa
tarfa ki kamar yadda ya yi min bama kenan, ina jin in ke ya yiwa abinda ya yi min
suma zaki yi." Didi ta ce, "ai na faɗa miki shi zan saka yazo ya ɗauko min ke in
baki koma ba, zaki gani kuma."
Hajja ta ce, "wai! ranar sai Hauwa ta suma." Suka yi dariya gabaɗaya kafin Didi ta
ce, "Hajja dahuwar awara zaki koya min, wacce nake kaiwa ana yi min bata yiwa Omar
daɗi." Hajja ta ce, "shikenan kin kama Hauwa har wuya. Ja hannunta ki je ta dafa
miki, ta iya dafa awara nesa ba kusa ba. Itama irin Omar ɗin ce, tsabar son cin ta
da take yi sai da ta iya dafawa." Didi ta kalli Nayla ta ce, "Alhamdu lillah, ki ce
shiga gida ya kama ki."
Nayla ta wara ido ta ce, "ai gwara ki aiko min da kayan nayi miki a nan sai na aiko
miki da ita, kuma ban iya mai yawa ba ƴar kaɗan na iya dafawa." Didi ta ce, "ai
wallahi gida zamu je ki yi min nima na koya, babu wani na aiko miki dashi baki isa
ba."
"Allah Didi tsoronsa nake ji, in na ganshi hantar cikina kaɗawa take yi." Suka yi
dariya gabaɗaya Didi ta ce, "Tsoron nake so na cire miki, ki saba dashi shima
yayanki ne kamar yadda nake yayar ki."
Hajja ta ce, "ai na faɗa mata in da amana ai ruwa bazai dafa kifi ba, Ita da ya
saɓo ta a kafaɗa ko riga babu itace mai faɗar haka a kansa." Nayla ta dafe kai
cikin takaicin kalaman Hajja ta ce, "Wai Hajja don Allah meye haka?." Didi ta yi
dariya ta ce, "Hajja kina bata kunya."
"Kunyar ƙarya ce, ai ba ƙarya nayi ba a kafaɗar ya ɗauko ta ko? Kuma ai gaskiya ne
rigarsa ya saka mata."
Didi ta ce, "Gaskiya Hajja ki daina tuna mana maganar nan kunya mu ke ji." Hajja
tayi dariya ganin Nayla sai ɓata rai take yi, ita kuma tana sane take faɗa saboda
ta tunzura Nayla ɗin. Didi ta miƙe tana dariya ta ce, "Nayla ina jiranki." Nayla ta
ɗaga kai dan babu yadda zata yi ne amma bata son haɗuwa da Omar.
Bayan Didi ta fita Nayla ta kalli Hajja ta ce, "Haba Hajja! Meyasa zaki ce mata na
iya don Allah? Kin san tsoronsa nake ji." Hajja ta ce, "ke ni fa saboda
kyautatawarsa akan ki ne ce ki je, sannan Didi jikata ce kamar ki, tana sona tana
son ku gabaɗaya." Nayla ta kalli Salma ta ce, "Salma zamu je?." Salma ta wara ido
ta ce, "ai na rantse da Allah baza ni ba, Ke dai ki je." Nayla ta zauna kamar zata
yi kuka zuciyarta cike da fargaba.
Didi na rabon abinci a ƙofar gida ta hango Nayla tana tahowa a nutse sai tayi
murmushi tana kallonta, ita dai Nayla na matuƙar burge ta sosai, bata sani ba ko
dan tana kyau ne ya saka haka oho. Babban abinda yake burge ta game da Nayla shine
shigarta, bata taɓa yin shigar banza. Kayanta ta basa wuce doguwar riga, riga
doguwa har guiwa da siket, butterfly da sauran kayan mutunci na zamani. Wannan
dalili ya saka take sonta sosai, gata kirki.
Tare suka ƙarasa rabon abincin da Nayla suka shiga cikin gidan Nayla sai ɗari-ɗari
take yi. Didi ta kalle ta tace, "kwantar da hankalinki baya nan, ya kai yamma bai
dawo ba."
Ajiyar zuciya tayi Didi tayi dariya suka fara haɗa awara kamar yadda ta ce. Didi
tana gefe tana kallon ta har suka markaɗa a blender aka tace aka fara dafawa. Didi
ta ce, "bara na gyara kayan miyar nan mai sauce nake so nayi." Nayla ta ce, "ashe
kina son awara, nifa saboda son da nake mata ne ya da na iya dafawa, dan tunda na
taɓa ganin gashin kai a cikin wacce ake yi min a gida na daina bari masu aiki su yi
min." Didi ta ce, "ni bata dame ni sosai ba, mutuminki ne masoyin awara, bai damu
da nama ba kamar yadda ya damu da awara. Zai iya ci miki awara da safe da rana da
daddare, Sam shi nama bai dame shi ba, da rayuwar nama da babu duk ɗaya, har gwara
kifi ma."
_Shiyasa yake gabjeje mana ashe soya beans yake afakawa cikinsa_ Nayla ta faɗa a
zuciyarta. Didi ta ce, "kuma kar ki ɗauka da yawa yake ci, kin san ɗan iyayi ne,
ƴar kaɗan in ya ci zata ishe shi kawai sonta yake yi. Da ita da jollof rice mai
kifi, da noodles, da pasta and stew. Inda safe ne kuma doya da ƙwai in ta huce ya
ci ta da ketcup ko yaji, har mamakin inda ya iya cin ketcup yake yi. Noodles ma sai
ya ci ta tun safe har dare kamar yaro. Wani lokacin kuma baya cin ahinci sai dai ya
shafa coffee ko ya yini yana cin apple da kankana." Nayla ta yi murmushi kawai tana
mamakin ko ita ina ruwanta da abinda yake so.
Didi ta ce, "yau so nake yaci har ya barta, bara na haɗa sauce ɗin." Nayla ta ce,
"bar shi nayi miki kafin awarar tayi, tunda kin gyara kayan miyar bara ayi
blending, ni gyara su ne bana so." Didi ta ce, "yau Omar zai ci abincin ki kenan."
Tayi dariya kawai ta fara haɗa sauce ɗin tana yi suna hira.
Nan da nan suka gama Nayla ta tace awarar ta kalli Didi ta ce, "Zamu bar ta haɗa
jikinta sai mu soya. Ita kuma sauce ɗin in kina da mayonnaise ki zuba mata, ko in
kin zo serving ki zuba ni dai tana min daɗi." Didi ta ce, "ai kam na gode sosai
Nayla, Kin ga nima na koya saboda gaba, ashe ma babu wahala." Tayi murmushi ta ce,
"bara naje gidan Hajja."
"To ki dawo mu ƙarasa don Allah."
"Zan dawo yanzu Didi" ta faɗa tana fita da sauri.
Didi sallama ta jiyo daga tsakar gidan hakan ya saka ta kashe gas ta fito
tana amsawa. Gabanta sai da ya faɗi ganin wanda ya yake tsaye a tsakar gidan ta
daure tayi murmushi ta ce, "Kawu kai ne tafe? Sannu da zuwa." Wanda ta kira da Kawu
ya yi murmushi ya ce, "Yauwa Aisha, ke kaɗai ce a gidan?."
"Eh ni kaɗai ce Kawu, Omar bai dawo daga masallaci ba. Shigo kawu."
Kawu ya yi ajiyar zuciya dan yana daga cikin masu tsoron Omar ya shiga falon da
sallama. Didi ta amsa ya zauna suka gaisa ta ce, "Ya Mutanen gidan?."
"Lafiya lau Aysha. Daga masallaci nake na biyo mu gaisa na kawo miki kafin bikin
ƙanwarki" ya faɗa yana miƙa mata katin.
Didi da murmushi ta ce, "bikin wa za a yi Kawu?." Kawu ya ce, "Bikin Ramla." Jin
sunan Ramla sai da gabanta ya faɗi itama sai tayi murmushi ta ce, "Kai ma sha
Allah! Allah ya nuna mana lokacin."
"Amin ya Allah, Amma zaki zo ko?."
"Zuwa kai Kawu, in ban zo ba waye zai zo?." Yayi murmushi ya ce, "gaskiya ne, ku ne
yayyen amarya."
Tayi murmushi ya miƙe tsaye ta ce, "Kawu ko ruwa baka sha ba ka miƙe." Kawu ya ce,
"sauri nake yi, babu komai ba sai na sha ruwa ba. Na ce Omar bai shirya aure
bane?." Ta kalle shi ta ce, "Gaskiya bai shirya ba."
"In ya shirya akwai ƙannensa zai iya zuwa ya nema." Jin abinda Kawu yace sai tayi
murmushi tana murna da Omar baya nan da an shiga uku da wannan furuci na Kawu.
"Didi!" Omar ya faɗa yana shigo falon. Ganin wanda yake parlon sai ya tsaya cak
yana kallonsa kafin ya girgiza kai ya kalli Didi da ita kanta bata so ya shigo ba,
Kawu kuwa ya gamq tsurewa saboda tsoro.
Karaf Didi tayi ta ce, "Omar ga Kawu, ya biyo mu gaisa ya kawo katin biki ƙanwarka
Ramla." Idanu ya waro waje ya ce, "ni bani da wani Kawu a duniya, kuma bani da
ƙanwa, bani da ƙanwa a duniyar nan kar ki sake cewa ƙanwata!."
Kawu yayi tsitt bai ce komai ba zuciyarsa rawa kawai take yi saboda tsoro. Kallon
Kawu ya yi ya ce, "Baka san baƙi ba sa zuwar mana gıda ba?." Kawu ya ce, "Omar ni
ne fa."
"Kaine wa? Na ce kai ne?" Ya faɗa a zabure yana fito da idanunsa waje cikin fusata.
Didi ta kalle shi ta ce, "Omar meye haka?."
"Didi wai meyasa ki ke min haka ne? Su waye waɗannan da ki ke bari suna shigo mana
gıda?. Waye shi? waye na mu?" Ya faɗa yana ɗaukar iv da aka kawo ya watsar dasu a
tsakiyar falon.
"Omar Kawu ne fa."
"Ke ki ka san wani Kawu ni ban san shi ba, bani da wani Kawu a duniya" ya faɗa
idanunsa a waje yana karkaɗa yatsansa. Kallon Kawu ya yi ya ce, "ka manta abinda na
yi maka wancan lokacin ko? Baka ji ba ka sake zuwa gidan nan ko?. Shikenan zan maka
tabon da baza ka sake marmarin zuwa ba."
Kawu ya tsorata sosai ya ce, "ka yi haƙuri Oma...."
"Kar ka sake faɗar sunana, haƙuri kuma ban san shi ba!" Ya faɗa da ƙarfi yana
kallonsa. Didi ta kalli Kawu ta ce, "Kawu yi haƙuri, ka tafi kawai Kawu." Ganin
Omar zai fita ta ce, "Omar kar ka fita daga falon nan, Kawu mu je na rakaka." Omar
jikinsa rawa yake saboda ɓacin rai ya fita daga falon. "Omar! Omar ka dawo!" Ta
faɗa da ƙarfi amma ina ya fita daga gidan.
Kawu ya ce, "Aisha tsoro nake ji kar ya saka ayi min wani abun, haka kwanaki ya
saka aka kusa hallaka ni." Ganin Kawu ya tsorata sosai sai ta ce, "babu abinda zai
maka Kawu, tunda nace babu abinda zai yi babu ɗin, Kayi haƙuri."
"Ni zan bada haƙuri da na zo tunda na san baya so, ki yi haƙuri duk laifina ne ni
na jawo wannan tsanar da yake mana." Didi ta ce, "Mu je kawu." Har ƙofar gida ta
raka shi, ta ka ga su Bash kuwa suna jiran fitowarsa.
Kallon su tayi ta ce, "Kar wanda ya yiwa Kawu komai, in kuma wani abun ya same shi
duk sai ranku ya ɓaci, ku faɗawa Damisar na ku ni nace a ƙyale shi. Kawu shiga
motarka." Kawu jiki na rawa ya ce, "A'a Aisha."
"Kar ka damu Kawu babu komai." Kawu dai tsoro ne ya saka shi shiga motar ya bar
unguwar a guje.
Didi gidan ta shiga cikin ɓacin rai ta shiga falo tana mamakin baƙar zuciya irin ta
Omar da baya mantawa. Bai bar dangin uwa ba, haka ma dangin uban bai bar su ba. Har
gwara ma na uwa tsanar da ya yi musu bata kai wacce ya yiwa su Kawu ba. A lokacin
ya shigo tsakar gidan ya tsaya yana zagaye ransa a matuƙar ɓace zuciyar sawuya,
fuskarsa tayi wani irin ga jijiyoyin kansa sun tashi. Abokin karawa kawai yake nema
ya wuce a kansa.
"Assalamu alaikum, Didi na da......" Maganar Nayla ta maƙale saboda wanda suka haɗa
ido dashi a cikin gidan. "A'uzubillahi minal shaiɗanir rajim!" Nayla ta faɗa a
tsorace cikin gigicewa dan bata san ma ta yi ta'awizin ba. Omar ya sake wara ido a
kan fuskarta cike da mamaki da fusata ya ce, "Shaiɗan!" Ya faɗa yana kallon Nayla
tare da takowa zuwa inda take.
*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.
Nana Haleema❤️
*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025
©️*Nana Haleema.*
Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.
*Book 1*
*P 08.*
Nayla baya take ja yana takowa inda take idanunta a waje ƙirjinta yana up and down
saboda tsoro da tashin hankali. Shi kuma yana takawa inda take saboda ɓacin rai da
zallar haushi da takaici a zuciyarsa. Sai da ta jingina da bango ya dakata da bin
bayanta, jikinta na rawa kar kar kar bakinta na motsawa amma ta kasa magana.
"Ni ki ke yiwa korar shaiɗanu? Wacece ke! Waye ya turo ki gidan nan!?."
Tsawar da ya yi ya sake firgita Nayla ta runtse idanunta cikin fargaba da tashin
hankalin da bata taɓa shiga irin ta ba. Numfashita ya kusa ɗaukewa ganin ƙaramar
wuƙar da ya zaro daga ƙasan takalminsa ya ɗago ya ɗora wuƙar akan wuyanta yana sake
wara idanunsa waje ya ce, "Wacece ke!?."
Nayla bata taɓa shiga tashin hankali kamar yadda take a ciki yanzu ba, ƙafafunta
sai rawa suke yi saboda tashin hankali, zuciyar tacike da dana sanin abinda ya
shigo da ita gidan. "Omar!" Didi ta faɗa da hanzari tana zuwa ta janye Omar daga
kusa da Nayla da take zubar da hawaye. Sharaf Nayla ta faɗi a numfashi ta na sama
da ƙasa saboda tashin hankali.
"Baka da hankali ne Omar? Kashe ta zaka yi?." A fusace ya kalle ta ya ce, "Wacece
ita? Ban ce kar na sake ganinta a gidan nan ba?."
"Gidanka ne da sai wanda ka ke so ne zai shigo? Na ce gidanka ne!?."
"Ba gidana ba ne, amma ina da ikon hana duk wanda bana so shigowa cikinsa. Ban son
sake ganin wannan yarinyar a gidan nan, bana son sake ganin ta!" Ya faɗa da ƙarfi
yana nuna Nayla da take zaune a baya kamar sumammiya.
Didi ta fusata sosai ta ce, "baka isa ba, baka isa ka hana baƙina shigowa gidan nan
Omar. Wai kai Meya ke damunka? Meye a cikin kanka? Meyasa baka aiki da hankali ne
kai?." Idanu ya sake warawa waje yana kallon Didi jin kalamanta musamman na ƙarshe
ta ce, "eh na faɗa, Meyasa baka aiki da hankali? Meyasa ko yaushe zuciya ce take
sarrafa tunaninka ba ƙwaƙwalwarka ba?." Kai yake girgizawa Didi ta sake cewa,
"wacce irin zuciya ka ke da ita ne kai? Meyasa baka mantuwa baka yafiya?."
"Eh bana yafiya, kuma bazan yafe ba. Iya yau kin cece shi ya sha, amma wata rana
zamu haɗu a lokacin da babu ke ko?."
"Ƙanin mahaifinka ne, ko ka ƙi ko ka so dole ka kira shi da Kawu." Ƙasa ya yi da
muryar da yana girgiza kai cikin ƙunar rai ya ce, "Har abada bani da dangin
mahaifi, bani da dangin mahaifiya, kamar yadda na rasa iyayena suma ki ɗauka sun
mutu. Ke kaɗai na sani dangina, bayan ke babu wata halitta a duniyar nan da ta rage
da zan kalle ta matsayin dangi!" Ya ƙarashe maganar da ƙarfin gaske.
"Ƙarya ka ke Omar, ƙarya ka ke. Kawu ƙanin mahaifinka ne duk da abinda ya aikata
maka ba a canjawa tuwo suna. Baba Adamu Yayan mahaifiyarka ne, duk da abinda ya yi
maka ba a canjawa tuwo suna. In dai har ka manta da dangin iyayenka to zaka manta
da wanda suka haife ka Omar!."
Hannu ya saka ya daki kansa ya juya ya sake juyowa ya kalle ta ya ce, "iyayena sun
rasu dan haka bani da wani a duniyar nan in ba ke ba."
"Nima ɗin baka ɗauke ni komai ba Omar, tunda baka yin abinda nake so." Sake kallon
ta ya yi ya ce, "na rantse da Allah Didi, in na sake ganin ƙafar wani dangin Baba a
gidan nan ranar bazai kwana lafiya ba. Zan iya ɗagawa dangin Mama ƙafa, amma bazan
taɓa ɗagawa dangin mahaifina ƙafa ba. Ke kin san waye ni, kin kuma san abinda zan
yi da wanda bazan yi ba."
Didi sai ta kasa magana dan baza ta iya da taurin kansa ba, tayi murmushin takaici
kawai ta kalli Nayla da take zaune a wajan har lokacin kamar bata numfashi.
Da sauri ta ƙarasa inda take ta ɗago ta jikinta ta ce, "Nayla! Nayla buɗe idon ki
don Allah." A hankali Nayla ta buɗe ido tana kallon Didi sai jikinta ya cigaba da
rawa ta ƙanƙame Didi tana kuka sosai.
"Yi haƙuri Nayla, ki daina kuka don Allah ki yi haƙuri" ta faɗa tana shafa bayanta
a hankali cikin tausayinta da mugun takaicin halin Omar.
Omar takaici kamar ya kashe shi haka yake ji, cikin tsananin ɓacin rai da takaici
da tsawa ya ce, "in na sake ganin yarinyar nan a gidan nan bazan ƙyaleta ba." Cikin
ɓacin rai da fusata Didi ta ce, "Sai ta shigo! Omar sai ta shigo in ka dama ka
kasheta ka kaima ka ga in za a barka da rai. Na gaji da wannan shirmen na ka,
kullum kana girma amma kana cin ƙasa, sam baka aiki da hankali balle ka san abinda
zaka yi."
Runtse idanu yayi yana jin zafin kalamanta, Babban abin haushin ma a gaban yarinyar
da ta taɓa yi masa faɗa kwanaki a gabanta, yau ma gashi an maimaita har tana cewa
yana shirme baya aiki da hankali. To shi wanne gangancin ne ma zai bari ya bar
yarinyar da lafiyarta? ai in bai taɓa lafiyar jikinta ba bazai ji daɗi ba. Bai taɓa
jin haushin wata halitta kamar ita ba, saboda itace mace ta farko da aka yi masa
faɗa a gabanta.
Zai sake magan ta dakatar dashi cikin fushi ta ce, "Dallah Malam fita ka bani waje
kafin na tsinke ka da mari." Sak ya yi yana kallon ta jin wai zata mare shi, kallon
ta yake yi cikin mamaki dan abinda ta faɗa bata taɓa furtawa shi ba sai a lokacin.
Ganin kallon mamakin da yake mata sai ta ce, "ko kana ganin ban isa na mare ka ɗin
ba ne? In kana ganin ban isa ba ka cigaba da tsaya min kai wallahi sai na mare ka."
Kai yake gigirzawa yana kallon Nayla da take kwance a jikin Didi tana sauke
numfashi ya ce, "na gama haddace fuskarta, duk abinda ya faru tayi kuka da kanta"
yana faɗar hakan ya fita daga gidan cikin baƙin ciki da ƙunar zuciya. Wai kamar shi
Omar Tiger Didi take cewa zata mara a gaban wata yarinya, ƙarshe ma akan yarinyar
take zancen zata ta dake shi.
Didi ta kalli Nayla bayan ya fita ta ce, "Nayla yi haƙuri don Allah ki
nutsu, ki dawo nutsuwarki ji." Tashi tayi da sauri ta ɗauko mata ruwa mai sanyi ta
bata, ai kam Nayla ta sha ruwan nan sosai dan tana buƙatarsa. Hijjabin jikinta ta
cire mata ta riƙeta ta ce, "taso mu shiga ciki." Daƙyar Didi ta iya ɗaga ta suka
shiga falon Didi ta zaunar da ita akan kujera ta kunna mata fanka sannan ta zauna
kusa da ita tana yi mata firfita.
Bata sake magana ba sai da taga Nayla ta ɗan nutsu hawayen da take yi ma ya tsaya
sannan ta sake kawo mata ruwa ta