Advertisements
Chapter 11 Reading KIRAN RABO BOOK1 CMPLT BY NANA HALEEMA BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

KIRAN RABO BOOK1 CMPLT BY NANA HALEEMA

Author :  NANA HALEEMA Category :  Complete Novels

Chapter   11 / 28

30K to 33K   out of 83.2K words

gidan Kawu.
Kai ka san ai ba ni zan aurar da kaina ba dole a nemo ganin dangina.” Ajjiye plate
ɗin hannunsa yayi bai ce mata komai ba ya miƙe tsaye ya fita.

Daman ta san ƙarshen cin abincin na sa yazo kenan tunda ta ambato maƙiyansa, taji
daɗi da bai yi magana ba dan ta san da faɗa zasu yi dashi. Su Bashir ta kira ta
basu abincin sannan ta shiga tayi shirim kwanciya. Tunanin baya ne yake dawo mata
dawo mata cikin kanta, ta yi ajiyar zuciya tana tuna abinda ya wuce.

*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.

Nana Haleema❤️

*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025

©️*Nana Haleema.*

Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.
*Book 1*
*P 09.*


Ranar asabar da daddare Omar da Didi suna zaune a falo yana aikin danna waya ita
kuma tana kallon tv, bata ce masa komai ba ganin ya ƙi ya saki rai, sai ɗaure fuska
yake yi ba kamar jiya ba, bata so ta yi masa wata maganarta tsokano shi hakan ya
saka ta yi shiru. Shirun ne yayi yawa hakan ya saka ta kalle shi ta ce, "Omar." Ya
ɗago manyan idanunsa ya kalle ta sai ta langwaɓar da kai ta ce, "don Allah ka daina
buɗe idanunka akan fuskar mutane, wannan idanu naka sai ya firgita mutum cikin
dare."

Bai yi magana ba ta ce, "zan faɗa maka wata magana amma kar ranka ya ɓaci don
Allah."
"To" ya amsa a taƙaice kafin ta ce, "Ɗazu Kawu ya kira ni, maganar AbdulHamid ce.
Ya samu Kawu ɗazu da yamma, shi kuma ya ce ya bashi lokaci zasu ɗan yi bincike a
akansa."

Ta ɗauka da ta kira sunan Kawu ransa zai ɓaci kamar kullum amma sai taga yayi
murmushi mai ƙayatarwa da daɗin kallo. Murmushi yana yi masa kyau matuƙa, yana
fitowa da asalin kyaunsa da kwarjininsa. Ya ce, "Allah ya tabbatar da alkhairi."

Sai taji daɗi sosai a ranta ta har hakan ya bayyana a fuskar ta ta ce, "Amin
Habibin Mama. Yaushe zaka nemo taka matar? Kaga in Allah yayi aurena dashi sai a
haɗa gabaɗaya ko?." Kallon ta yayi tare da ɗaga yalwatacciyar gashin girarsa ya ce,
"Tare mu ka zo duniyar da zamu yi aure tare?."

"Ba tare muka zo ba, amma zan so mu yi aure tare."
"Ke kika fara zuwa duniya, ke zaki fara aure."
"Ai abin ba daga nan yake ba, yara nawa aka haifa a bayana duk suna yi aure har
yaran su duk sun girma?."
"Su daban Omar daban" ya faɗa yana kallonta.

Didi ta ce, "to naji, Amma ya kamata dai kaima ka fara neman matar aure, kaga in
nayi aure gidan nan bazai maka daɗi ba, waye zai maka girki ka ci da sauran su?."
Omar ya ce, "kin san dai na iya girki ko?."
"Na sani, amma yadda baka zaman nan zaka so ace kana dawowa abinci zaka ci ba sai
ka dafa ba."

"Ni wannan bai dame ni ba, ki yi auren dai kawai yafi komai a yanzu." Tayi murmushi
cikin tsokana ta ce, "faɗa min wacece budurwarka, baka ɓoye min komai amma baka
taɓa faɗa min wacce ka ke so ba." Murmushi ya saki mai sauti yana kallon ta ya ce,
"Ni aka ce miki ina da budurwa?." Didi ta harare shi ta ce, "Santalelen saurayi mai
kyau da kyaun zati kamar ƙanina ai bazai rasa budurwa ba. Ina jin ka ya sunanta."

"Aisha" ya faɗa cikin gatse yana kallon ta da murmushi. Dariya tayi jin sunan da ya
faɗa ta ce, "ka ce takwara ta ce ma, Yaushe zata zo na ganta?." Bai ce komai ba
kuma bai daina murmushi ba ta ce, "Wai! zan so naga mace da Omar zai so, zan so
naga lokacin da Omar zai fara soyayya. Allah ka bani aron rai da lafiyar da zan ga
Omar na matuƙar son wata mace bayan Didinsa. Wacce kalar mace ka ke so? fara ko
baƙa?."

Kallon ta yake cikin mamaki ganin yadda ta saka shi a gaba tana yi masa wannan
tambayoyi kamar wanda ya ce mata neman aure yake yi. Murmushi ya yi ya ce, "ni wai
na ce miki aure zan yi ne?."
"Ko baka ce ba na san zaka yi."
"To ba yanzu ba." Tayi murmushi tana kallon sa ganin shima murmushin ya ke yi ta
ce, "Allah ya kaimu lokacin, Allah ya kawo macen da zata gyara min kai ka hau kan
hanya mai kyau ka sauka daga wacce ka ke kai."
"Hmmm" shine abinda ya furta kawai amma murmushi yake yi. Sai kuma tayi ajiyar
zuciya alamun akwai abinda ta tuna amma bata ce komai ba.

Ganin yanayinta ya canja sai ya so ya kawar da damuwarta ya ce, "ai ki kiyaye ganin
matar da zan aura, sai na baki mamaki." Jin abinda ya ce sai fara'arta ta dawo ta
ce, "Allah ya nuna mana lokacin, Allah yasa baza a samu matsala a aurenka. Allah
yasa kar ka nemi wacce za a ce tafi ƙarfin ka."

Ga mamakin ta sai taga yayi dariya kaɗan ya ce, "har akwai macen da tafi ƙarfin
namiji ne a duniya?." Didi ta ce, "sosai ma kuwa, akwai inda kai baza kaje kace ma
a baka aurenta ba, saboda matsayin ku ba ɗaya ba ba." Ya girgiza kai ya ce, "ni kam
ban ga macen da za a ce tafi ƙarfina ba, sai dai in bana sonta." Kallon sa take yi
jin da gaske yake yi ta ce, "kai dai Omar ayi shiru kawai, amma akwai matan da sun
fi ƙarfin ka nesa ba kusa, tazarar ku kamar tazarar sama da ƙasa. Kyaun da ka ke
dashi ba komai ba ne."

Taɓe baki yayi kawai bai ce komai ba, amma shi kam a wajan sa bai ga macen da za a
ce tafi ƙarfinsa ba, in dai yana sonta tana sonsa to bata fi ƙarfinsa ba.

A wannan lokacin Nayla tana ƙofar gidan Hajja hannunta har rawa yake yi
wajan kiran number Salma, tana ɗauka ta ce, "Salma ya naga gate ɗin gida a kulle?."
Daga can ɓangaren Salma ta ce, "Wallahi mun fita, mun je dubiya kuma bamu taho ba."

Nayla ta ce, "Innalillahi na shiga uku, Salma fitsari nake ji kamar nayi hauka.
Yanzu ina zan shiga? Kin san ba kowa na sani a unguwar nan ba." Salma ta ce,
"Wallahi bamu taho ba, ki shiga gidan Didi kawai."
"Gidan Didi kuma? Ni ce zan shiga gidan Didi?."
"To ba lalaura ba ce? Ita kaɗai ki ka sani a unguwar kawai ki daure ki shiga."
Tsabar haushi Nayla kashe wayar tayi ta fara zaga wajan saboda fitsarin da take ji
kamar zai zubo.

Haka kawai ta shiga gidan Didi Omar ya ganta yayi mata tsawar da zata yi fitsarin a
wando, me ya kai ta shiga gidan Didi..? ai gwara ta yi fitsarin a wando ta san a
wandon ta yi. Runtse ido tayi saboda yadda take a matse sosai, kawai sai ta fara
hawaye cikin matsuwa da rashin mafita. Hango ƙofar gidan Didi take yi daga inda
take, kamar wacce aka bawa umarni ba shiri ta kwasa a guje ta afka gidan.

Kamar a cilla ta ta shiga falon da sallama, idon ta bai faɗa kan kowa ba sai
Omar da ya kalli ƙofar yana kallon wacce tayi sallama. Idanunta ne ya faɗa cikin
nasa, ga mamakinta murmushi yake yi kuma ganin ta bai saka ya daina ba sai ma ɗauke
kai da yayi daga kallon ta.

Didi ganin ta ƙame a jikin ƙofa sai ta miƙe ta ce, "Nayla lafiya na gan ki a
firgice haka?." Nayla a wahale ta ce, "Didi fitsari nake ji." Didi ta ce, "maza
shiga ki ciki mana" da sauri ta wuce ta shiga ɗakin Didi.

Didi ta koma ta zauna tana kallon Omar da har lokacin fuskarsa a sake take bai yi
wani abu da zai tsorata Nayla ba. "Ita wannan yarinyar kullum sai ta shigo ne?."
Jin abinda ya ce sai ta ce, "Eh mana, tana sona ne nima ina sonta, tana girmama ni
nima ina girmamata." Kai ya girgiza kawai, yana tuna a gaban ta Didi ta dinga yi
masa faɗa harda cewa zata mare shi.

Sallamar Nayla ya saka bai ce komai ba ta fito falon kamar munafuka tana kallon
Didi. Didi ta ce, "ƙaraso ki zauna." Zama tayi a tsorace ta kalli Didi ta ce, "Su
hajja ne basa nan, ni kuma naje gidan ƙanwar Abiy sai yanzu na dawo." Didi ta ce,
"Ayya. To ki shiga kitchen ki zuba abinci in zaki ci."
"Na ƙoshi" ta faɗa kanta yana ƙasa dan har lokacin yana zaune bai tashi ba.
Didi ta kalli Omar da ba su yake kallo ba ya dai hakimce ya ɗora ƙafa kan ɗaya yana
kaɗawa. Murmushi tayi tace, "Yayanki Omar ya ci awarar da kika dafa yana ta santi."
Nayla ta ɗago tana kallon Didi haka kawai gabanta yake faɗuwa, babban abin mamakin
faɗuwar gaban da take ji ta banbanta da irin wacce take ji in ta ganshi. Nayla dai
bata ce komai, Didi tayi murmushi ta kalli Omar da yake murmushi sosai da alama
akwai abinda ya bashi dariya a wayarsa.

Didi ta ce, "Omar!." Ɗago idanunsa yayi ya kalle ta suka sake haɗa ido da Nayla
tayi saurin kawar da kai jin faɗuwar gaban da take ji tana neman wuce tunaninta.
Hasken idanunsa kawai take a gani a idanunta, tana mamaki daman idanunsa suna da
haske haka ko kuma dan yau ransa ba a ɓace yake ba?.

Muryar Didi taji tana cewa, "itace fa ta dafa awarar da ka gama ci." Bai ce komai
ba,
amma yana mamaki meyasa Didi take son saka shi a lamarin yarinyar nan ne? Dan
tsabar neman waje irin na Didi wai Yaya Omar, shi kaf duniya babu wanda yake ce
masa Yaya.

Wayarsa take ƙara ganin mai kiran sai ya tashi ya fita daga falon. Didi ta bishi da
kallo sannan ta kalli Nayla da itama kallon sa take yi Didi ta ce, "Yau kin yi
mamakin mutumin naki ko?." Nayla tayi murmushi kawai bata san meyasa ta kasa furta
komai ba. Ji take kamar an ɗaure mata baki harshenta ya sarƙe ta saka cewa komai.
Didi ta ce, "wallahi ɗazu ya gama yabon awarar ki wai kar na sake kaiwa inda ake yi
na dinga yin irinta, yau tsokanarsa nake tayi shiyasa yake ta murmushi."

Nayla ta ce, "abin mamaki, ban ɗauka yana dariya ba." Didi tayi dariya ta ce,
"dariya har da ta ƙeta in dai Omar ne, kawai bashi da saurin sabo ne kwata-kwata,
amma da zaku saba ke kan ki da kinga canji daga halayensa. Yana da hira sosai in ya
so, zaku zauna ku yi hira cikin raha da wasa da dariya. Inda zaku saba murmushinsa
bazai miki wahalar gani ba, kafin a saba ɗin ne ana jimawa." Nayla ta girgiza kai
kawai ta sake kallon inda ya tashi sai take ji a zuciyarta dama ya dawo ta sake
gani yana murmushi.

Shi kuwa Omar ganin kiran Senator ya saka shi ya fita ya ɗauja da sallama,
suka gaisa Senator kamar ko yaushe ya ce, "Tiger gobe Narma zata sauka a Kano,
jirginta zai sauka bayana azahar in sha Allah. Akwai wanda na bashi number ka zai
kira ka ya kai ka airport ɗin, in ya nuna maka ita sai ka karɓi motar ku wuce. Zan
tura maka address ɗin gidan da zata sauka."

Omar ya ce, "Allah ya kaimu."
"Amin. Tiger please kar kayi wasa da wannan lamari, ka kula da Narma kar ka bar
wani wanda baka yarda dashi ba a kusa ita. Akwai wanda basa son su ga Narma a Kano,
na san baka da wasa shiyasa na zaɓe ka akan police."
"In sha Allah babu damuwa, sai dai in a samu damuwa daga wajanta."
"kar ka damu zan ja mata kunne sosai, in kaga abu ba daidai ba ka kira ni."
"In sha Allah" ya sake amsawa a taƙaice kafin su yi sallama ya kashe wayar.

"Zan wuce" yaji an faɗa daga bayansa muryata na rawa sosai alamun a tsorace take.
Juyowa yayi ya kalle ta kanta yana ƙasa jikinta na ɗan rawa kamar wacce aka jonawa
lantarki. Didi ya gano fito daga falo ta nufo inda Nayla take tsaye.

Bai ce komai ba kuma bai motsa ba har sai da Didi tazo wajan ta ce, "Omar ka bata
hanya mana." Magana yake so yayi amma sai ya fasa ya shiga ɗaki Nayla ta fita a
guje, Didi tana dariya ta bi bayan ta sai da ta ga ta shiga gidan Hajja sannan ta
dawo.

Tana shiga ta dinga yiwa Salma masifa akan me ta san zasu fita bata faɗa mata
ba, Salma ta ce, "Anty bala'i, na kira ki ban samu ba, kuma ba ga shi kin shiga
gidan su mai baki tsoro ba?."
"Ke kin san halin da nake ciki da na dawo? Fitsari kamar ya kashe ni bani da zaɓin
da wuce na shiga gidan." Salma tayi dariya tana bin ta da kallo ta ce, "ya ban ga
fitsari yana bin jikinki ba? Dan na san gamuwar ku dole ki yi fitsarin wando."

Nayla ta ce, "kee abin mamaki, yau bai min komai ba, hasalima da na shiga suna hira
da Didi murmushi bawan Allah nan yake yi. Wai daman yana murmushi?." Salma ta ce,
"mai zai hana ya yi? Kawai ba kowa yake yiwa bane." Nayla ta ce, "naga alama" ta
faɗa tana shiga ɗaki tana sake hango murmushinsa a idanunta.

Washe gari har rana ta fito Nayla ta kasa mantawa da fuskar Omar yana murmushi, da
ta rufe ido shi take gani da lokacin da suka haɗa ido hasken idanunsa ya shiga
cikin nata ido. Gabaɗaya ta kasa mantawa da abin ta kwana, tayi-tayi ta manta amma
abin ya ci tura.

Omar kuwa lokacin da driver ya kira shi ko Didi bai sanarwa ba ya fita, ya
same shi yana jiransa a mota ya shiga motar suka ɗauki hanyar airport. Mutumin yana
ta jan Omar da hira shi kuwa ba amsawa yake ba yayi shiru abinsa.

A cikin airport suka ajjiye motar Omar ya fito ya jingina da motar shima driver ya
fito yayi kamar yadda Omar ya yi. Kallon Omar ya yi ya ce, "Abokina sai kayi haƙuri
da yarinyar nan bata ji, tana da rawar kai sosai sannan tana da gadara duk abinda
yake so shi za a yi mata." Omar ya ɗago ido ya kalle shi mutumin ya ce, "Wallahi
sai kayi haƙuri dan bata da kunya ko kaɗan, mulki take ji dashi da isa, hatta buɗe
ƙofar mota zata ce kai zaka yi mata. Ga tsawa da kyara kamar waɗanda ta haifa."

Omar ya girgiza kai kawai mutumin ya sake cewa, "Ni ai naji daɗi da aka ce wannan
karon ba ni zan dinga kai ta inda take so ba, wallahi sai sha biyu na dare zata yi
min waya na baro gidana nazo na siyo mata pizza ko shawarma. Ta tara ƴan mata
irinta ƴaƴan manya a gidan suna ihuu kamar ba dare ba."

Omar duk yana jinsa kawai bai san me zai ce masa ba ne, amma duk abinda yake faɗa
baya tunanin ko babanta zai yi masa shi balle ita. Drivern ya ce, "Abokina gata nan
ta fito, Hajiya Narma kenan shugabar masu shigar banza nigeria."

Omar ya ɗaga kai yana kallon inda yake kallo, Narma ya hango cikin atamfa fitted
gown ta atamfa ta kama ta sosai ɗakyar take motsawa, mayafi ne siriri ta yafa shi a
kafaɗa, hannun rigar gabaɗaya da net aka yi shi hakan ya bayyanar da farin dantsen
hannunta, hatta pink colour ɗin bra ɗinta ana gani. Tahowa take fuskar ta ɗauke da
baƙin glasess, gabaɗaya ilahirin jikinta a bayyane yake, daga wrist ɗinta zuwa hips
ɗinta an kama shi ɗam, a kuma cike sosai. Duk yadda ka kai ga kushe sai ka yabi
surar Narma, dan Narma akwai sura ma sha Allah, shiyasa take ɗaukar hankalin maza
nan take.

Omar gani yayi wanda suke tsaye ya ƙarasa da sauri ya karɓi trolly bag ɗinta ya
saka a bayan mota, sannan ya buɗe mata bayan motar ta shiga. Omar ya bawa key ɗin
motar ya ce, "Allah ya fushsheka lafiya mutumina, ni daga nan zan wuce." Omar ya
kalle shi ya ce, "na gode. Amma kazo mu je gidan tare ban gane kwatancen ba."
"To mu je" ya faɗa yana buɗe motar ya shiga shi kuma ya shiga gaba.

Drivern ya kalle ta ya ce, "Hajiya barka da zuwa." Danna waya take yi ta ce,
"barka." Bata sake magana ba shima bai sake ba ya kunna motar suka bar cikin
airport ɗin. Tafiya suke babu wanda yake magana a ciki su, ƙhamshin turarenta ya
gama mamaye motar gabaɗaya.

Wayar Omar ce tayi ƙara ya duba yaga Didi ce ya ɗauka yana cewa, "Na fita zan dawo
anjima." Abinda ya ce kenan ya cire wayar daga kunnesa, hakan ya saka ta ɗago kai
tana kallon inda Omar ɗin yake.

"kai meye ma sunan ka?." Driver ya ce, "Yahya Hajiya,"
"Waye wannan muna tafiya yana amsa min waya?." Yahya ya ce, "baƙo ne Hajiya, bai
san dokokin ki ba."
"Ka sanar dashi" ta faɗa tana cigaba da danna wayarta. Omar bai ma kalle shi ba ya
cigaba da danna waya a haka suka isa katafaran gidan da yake cikin nasarawa gra,
mai gadi ya buɗe masu ƙofa suka shiga.

Yahya ya fito da sauri ya buɗe mata ƙofa ta fito ya ɗauki jakar ta yabi bayan ta a
guje. Omar ya bushi da kallon mamaki dan shi bai ga abu ɗaya da zai iya yi mata ba,
daga buɗe ƙofar da ɗaukar jakar. Yana nan tsaye Yahya ya dawo ya kalle shi ya ce,
"Abokina wannan matar bata da kunya na faɗa maka, gwara ka ja girmanka, in ba haka
ba zata yi maka abinda bazai maka daɗi ba. Ba a waya a mota in tana ciki, ka
kiyaye."

Omar ya girgiza kai ya ce, "wai abinda ka ke yi mata nima shi zan yi?."
"Fiye da haka ma."
"Ba a haifi yarinyar da zan yiwa wannan abun ba." Yahya yayi dariya ya ce, "Tunda
har ka karɓi aiki da Hajiya Narma sai kayi haƙuri kawai, duk abinda ka ke faɗa
yanzu a baki ne, amma zaka tabbatar da magana ta gaskiya ce." Kallon idon Yahya ya
yi ya ce, "nayi maka kama da wanda yake wasa?."

Kwarjini ya yiwa Yahya sosai sai ya girgiza kai ya ce, "A'a, amma ina baka
shawara." Omar ya ɗauke kai suka yi sallama da Yahya ya tafi.

Fanfo ya gani daga can gefen compound ɗin kuma yana fa buƙatar yin sallah, ya
ƙarasa yayi alwala, ya juya yana kallon gidan a nan ya ga wani ƙaramin masallaci da
mai gadin da ya buɗe musu ƙofa a ciki, Omar ya nufi wajan kai tsaye da niyar yin
sallah. Narma ce ta fito ta canja shiga zuwa riga mai jikin roba ta kama, sannan
daga sama wuyan a buɗe yake ana iya hango saman ƙirjinta. Narma ta ce, "kai!." Bai
ko kalle ta

11 / 28