Advertisements
Chapter 26 Reading KIRAN RABO BOOK1 CMPLT BY NANA HALEEMA BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

KIRAN RABO BOOK1 CMPLT BY NANA HALEEMA

Author :  NANA HALEEMA Category :  Complete Novels

Chapter   26 / 28

75K to 78K   out of 83.2K words

tana son Omar matuƙa Nayla, har nan tazo ta zube min akan na
saka baki Omar ya saurareta. Amma tsabar wulaƙanci irin nasa a gaban idanunta yake
cewa in ma yaudarar sa tazo yi yafi ƙarfinta. Shi da ita ya ce mata shi bazai yi
soyayya da ita ba kar ta sake gangancin furtawa, kuma fa ƴar manya mutane ce
wallahi, mahaifinta shine Senator Kano central a yanzu. Omar yana yiwa mahaifinta
aikin siyasa, kin san ƴan siyasa suna son irin su Omar a tafiyar su. To shine fa da
zata zo Kano ya ce Omar ne zai dinga kaita duk inda zata je saboda ya yaba dashi,
daga nan dai sai ta fara sonsa."

Nayla tana ji amma bata fahimtar me take cewa, tayi tsitt zuciyarta na bugawa a
guje, sai goge ido take yi bata so hawayen da ya taru a ciki ya zubo. Didi ta
cigaba da faɗin, "A hankali dai shima ya fara sonta, sonta ya fara dai ko ba so
bane shi ya sani. Ban da hauka irin na Omar ina shi ina wannan yarinyar? To baya
jin magana, ya ce min tunda ya ɗauki hanya bazai karkace ba, ni wallahi tsoro nake
ji kar a cutar dashi.."

Nayla bata iya magana ba tayi shiru zuciyarta na bugawa sosai har zazzaɓi take ji
yana neman rufe ta. Jin tayi shiru sai Didi ta ce, "ki daina tsoron sa don Allah,
abinda ya yi miki da yanzu bazai miki ba."

Nayla tayi murmushin yaƙe ta ce, "ba tsoron sa nake ji ba Didi, kawai na tafi
tunani da mamakin sa ne. Daman zai iya son wata mace? Lallai tayi sa'a ko wacece."
"Mtsww! Meye abin sa'a dan Omar yana son wata? Rashin sa a ne ma ai wata ta fara
sonsa ni a wajena. Meye abin so a Omar don Allah?. Farar fata ko kyaun fuska? Allah
dai ya shirya kawai."

Nayla tayi murmushi bata ce komai ba dan kanta ya yi mata nauyi sosai kwanciya take
da buƙatar yi. Miƙewa tsaye tayi ta ce, "Didi bara na koma wajan Hajja." Did ta ce,
"To Nayla. Na gode Allah ya bar zumunci. Zan aiko miki da mutuminki shinkafa da
wake shi nake dafawa." Nayla tayi murmushi ta ce, "to Didi" ta faɗa tana fita kamar
wacce ƙwai ya fashewa a ciki.

Tana fitowa tsakar gidan taji muryarsa ya yi ƙaramin tsaki ya ce, "to ni ƙaramin
yaro ne da wani abun zai same ni a hanya? Lafiya naje gida." Nayla tana takowa inda
yake tana jin zuciyarta na cigaba da bugawa dan ta san da budurwarsa yake waya.
Tana zuwa kusa dashi ta ji ya ce, "kar ki dame ni!" Sai ya yanke wayar fuskarsa ba
yabo babu fallasa.

Ya ɗago ido suka haɗa ido daidai lokacin da hawaye ya sakko daga idanun ta. Kallon
ta yake yi da mamakin abinda ya saka ta kuka tunda yaga tana hawaye a wajan Didi,
kusan ko yaushe in zai ganta kuka take yi bai sani ba ko kukan ne yake mata daɗi.
Da sauri tazo zata wuce doguwar rigar jikinta harɗe ta zata faɗi tayi saurin dafa
bango bata faɗi ba, yana tsaye shi dai yana kallon ikon Allah dan kallon ta yake
yi. Da sauri ta fice shi kuma ya yi tsaki ya ce, "tunda ba a nutse ki ke ba ai dole
ki nemi faɗuwa, yarinyar ta cika rawar kai" ya faɗa yana shiga ɗaki.

Nayla a guje ta shiga falon Hajja ko kula Hajja da Salma bata yi ba ta wuce
ɗaki a guje ta faɗa akan gado tana sakin kuka mai sauti. Hajja da Salma suna jiyo
sautin kukan nata Hajja ta kalli Salma ta ce, "Salma wai me yake damun ƙawar ki
ne?." Salma ta ce, "Wallahi Hajja ban sani ba, amma tun waccan tafiyar ta na lura
tana cikin damuwa, dana tambaya sai ta ce babu komai."
Hajja ta ce, "ki duba har rama tayi fa, gaskiya tana cikin damuwa ya kamata ki
tambayeta ki ji abinda yake damunta. Ko ki yiwa takwararta magana tunda ku biyu ne
ƙawayen ta." Salma cikin damuwa ta ce, "to Hajja. Amma tabbas tana da damuwa, ki
duba da farin ciki ta fita amma ta dawo a wannan yanayi. Gaskiya akwai abinda yake
damunta sosai." Hajja ta yi ajiyar zuciya bata ce komai ba amma tana tunanin abinda
ya damun jikar ta ta.

Nayla kuwa kuka take yi kamar ranta zai fita, in ta tuna Omar yana son wata mace
sai taji sabon kuka da hawaye yana ambaliya daga idonta. Zuciyarta fara harbawa
take yi kanta na juyawa, kanta ya yi nauyi haka ƙirjinta ma ya yi mata nauyi sosai.

Shikenan ita a haka zata gama rayuwa da dakon sonsa, tunda gashi yana da wacce yake
so kuma har yana cewa zai je ya samu mahaifinta. Shikenan ta ta ta ƙare, sai dai ta
mutu da sonsa ba tare da ya sani ba. Kalaman Didi take tunowa ta fara girgiza kai
ta ce, "Ko da zan mutu ni bazan ce ina sonsa ba, bazan faɗawa Didi Ina sonsa ba,
bazan faɗa ba" ta faɗa tana kuka sosai tana kwanciya a kan gadon jiki na rawa.

Sai da tayi kuka mai isarta sannan ta iya yin shiru ta tashi tayi alwala tayi
sallah sannan ta zauna tayi shiru tana salati. Wayarta ta ɗauko ta kira Baba Salisu
da ya kawo ta ta shaida masa gobe yazo ya ɗauke ta fasa kaiwa ranar Sunday.

Salma ce ta shigo bayan ta gama wayar ta zauna kusa da ita ta ce, "Nayla a duniya a
baki da ƙawaye masu baki shawara kamar ni da Twiny, ana kallon ki an san kina cikin
damuwa, ki faɗa min abinda yake damunki."

Kallon Salma tayi jin ta ce Twiny sai ta ce, "Sayyadi...Driver Hajja, yana nan ya
kai ku gidan Twiny?." Salma ta ce,"yana nan." Nayla ta miƙe ta yafa mayafin
doguwar rigar ta ce, "na fasa kaiwa jibi a garin nan gobe zan koma Kaduna, muje ya
kaimu ko zuwa anjima ne ma dawo." Tare suka fito suka faɗawa Hajja inda zasu je
tayi musu a dawo lafoya suka fita.

Jidda tayi murnar ganin Nayla a gidan ta suka baje a falo dan sun saba da Salma
sosai. Salma ta kalli Jidda ta ce, "Jidda wani abun da yana damun Twiny ki wallahi,
nayi-nayi ta faɗa min taƙi faɗa. Tsabar damuwa wai Nayla ce take cewa ta fasa yin
kwana biyu a Kano gobe zata koma Kaduna. Kowa ya ji wannan magana sai ya yi mamaki
sai kuma ya tambaya meyasa." Twiny ta kalli Salma ta ce, "tun a Saudia muka yi
maganar nan da ita, amma abin yawa yake sake yi yana bani mamaki" ta kalli Nayla ta
ce, "Nayla don ki faɗa min waye wannan da ki ke so."

Salma ta ce, "wai zaman akan soyayya ne? Da yake bata faɗa min ba ta ce kawai mu zo
nan." Jidda ta kalle ta ta ce, "akan soyayya ne Salma, wani take so shi bai ma san
tana sonsa ba."

"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Lallai Nayla tana cikin azaba mai tsanani."
Jidda ta ce, "tayi addu'a a Saudia amma ta ce soyayyar bata raguwa sai ma sake
sonsa da take yi, nace ta nemi zaɓin Allah in shine alkhairi Allah ya kawo silar da
zai fara sonta shima. Amma sai tayi murmushi ta ce ko da yana sonta auren sa da ita
da wahala ya yu."

Suka kalli Nayla a tare da take hawaye Salma a raunane ta ce, "Nayla waye wannan?."
Nayla ta goge ido ta ce, "Sanin waye bashi da amfani, ku taya ni addu'a kawai Allah
ya kawo min mafita. Twiny bani paracetamol kaina ciwo yake yi."

Ba musu ta tashi ta kawo mata haɗi da ruwa ta sha kafin Jidda ta ce, "amma faɗa
mana zai iya sakawa ki ji sauƙi a zuciyarki, kin san babu wanda zai ji labarin daga
bakin mu." Nayla tayi murmushi ta ce, "qaunar da zaku nuna min shine ku yi min
addu'a."
Ganin ta dage taƙi faɗar waye sai suka ƙyaleta suna ta hira har ita, dan ta ɗan
sake amma da ta tuna sai hawaye. Sai tara na dare suka baro gidan Twiny zuwa gidan
Hajja. A nan Hajja take faɗa mata ga abinci Didi ta kawo mata kaɗam ta iya ci ta
ajjiye ta kalli Hajja ta ce, "Hajja gobe zan koma Kano, na kira driver Abiy zai
mayar dani gida."

Hajja ta kalle ta tace, "Hauwa'u an fasa kaiwa jibin?." Ta yi ajiyar zuciya ta ce,
"Na fasa Hajja. Na tuna akwai abinda zan yi a gidan, kuma ranar ranar litinin Ina
da aiki." Hajja ta ce, "To Hauwa'u Allah ya kiyaye hanya ya nuna mana goben, Allah
ya yi miki maganin damuwarki." Ta amsa da amin daga nan bata sake cewa komai ba,
Salma tana kallon Labarina ita kuma ta miƙe ta shiga cikin ɗaki.

Kamar yadda ta fada washe gari da ƙarfe goma na safe driver ya zo daga Kaduna, sai
da ta bari ya huta ya ci abinci a wajan Hajja bayan sallar azahar suka ɗauki hanyar
Kaduna.

Ko a can kasancewar babu wanda ya san da dawowata, da yake ta asabar ce Abiy yana
gida shi da Yaya Ahmad tayi sallama a falon ta shiga. Yaya ya ce, "A'a, mutanen
Kano." Murmushi tayi ta ƙaraso ta zube akan carpet ta ce, "Abiy ina yini."
"Lafiya lau Mamana, ya kika baro Hajja?."
"Lafiya lau, tana gaishe ka. Ga saƙo ta ce a baka." Ya karɓa yana cewa, "Hajja bata
gajiya da hidima in dai aka je sai ta bayar? Na kuwa gobe sosai. Zan yi mata waya
na yi godiya."

Da Yaya suka gaisa kafin ya ce, "mutanen kano, ba sai gobe zaki dawo ba daman?." Ta
yatsine fuska ta ce, "Gajiya nayi kawai na kira Baba Salisu na ce ya zo ya taho
dani yau." Ya yi dariya ya ce, "ikon Allah, zaman Kanon ne kuma ya ishe ki?." Tayi
dariya kaɗan Abiy ya ce, "nima nayi mamaki, bata faɗa min ma zata taho ba, sai
Salisu ne yake cemin ita zai ɗauko tayi amsa waya jiya, na ce to sai ka dawo.
Gaskiya zan faɗawa Hajja taci tarar ki kin gudo kin barta."

Nayla tayi dariya ta miƙe ta shiga wajan Mama. Itama tayi mamakin ganin ta suka
gaisa daga nan ta koma ɗakinta tana sauke ajiyar zuciya. Zaman Kano ai ba nata
bane, indai tana son kanta da zaman lafiya dole ta bar shi.

Da daddare Mama ta shiga wajan Nayla ta same ta ta yi shiru ita kaɗai. Zama tayi
kusa da ita ta ce, "Nayla." Nayla ta kalle ta ta ce, "Na'am Mama."
"Tunanin me ki ke yi haka?."
"Babu komai Mama."
"Haba Nayla, kowa ya ganki ya san kina cikin damuwa mai yawa. Meyasa baza ki faɗa
min ba? Ko dan bani na haife ki ba?."

Nayla ta girgiza kai ta ce, "A'a Mama ba haka bane, babu damuwar ne shiyasa." Mama
ta zo kusa da ita ta riƙe hannunta ta ce, "uwa nake a wajanki, na haife ki na yi
jika dake Nayla. In baza ki iya faɗa min damuwar kiba wa zaki faɗawa? In baki furta
min abinda yake damunki ba wa zaki fadawa?. Uwa ce fa ni, ko bani da maganin
damuwarki in nayi miki addu'a Allah zai amsa." Nayla kalaman Mama suka karya mata
zuciya ta fara share hawaye. Mama ta sake nutsuwa ta ce, "faɗa min Ina jinki."

Nayla ta ce, "Mama babu komai, in akwai zan fada miki bazan ɓoye ba." Mama tayi
murmushi ta ce, "shikenan Nayla. Allah ya yi albarka, ki fito ki ci abinci" daga
haka ta tashi ta fita tana tabbatarwa da kanta ƙarya Nayla tayi mata, amma zata
tambayi Jidda dan ta san ita ta san dalilin damuwar Nayla.

••••••••

Washe gari Didi ta shiga gaishe da Hajja ta kuma yiwa Nayla sallama dan fita zata
yi kar ta shiga bata nan tarar da Nayla ta tafi, tayi mamaki sosai Hajja ta bata
labarin a yadda ta shigo gidan da yadda ta ce ita ta fasa zama. Didi ta ce, "Allah
ya sa ba Omar ne ya tsorata ta ba, dan ke baki ji ajiyar zuciyar da tayi da ta
ganshi ba. Ni wallahi tsoron nasa da take ji ya fara bani tsoro." Hajja ta dinga
dariya tana faɗin ba wani tsoro kawai akwai abinda yake damunta ne.

*Abuja*

Kamar ko yaushe suna zaune gabaɗaya suna hira Narma ta kalli Dad ta ce, "Dad." Ya
kalle ta ya ce, "Narma." Narma ta ce, "mun gama magana da Faruk ya ce zai zo ku
gaisa." Sai kuwa Najwa ta ce, "Awwnn! Ki ce shima dai yanzu da gaske yana yi ko
Sis?."

Aka yi dariya Dad da fara'a ya ce, "da gaske ki ke?." Ta ɗaga kai alamun da gaske
kafin ta ce, "yana so ka bashi date da time ɗin da zai zo." Dad ya ce, "wow! wannan
abin farin ciki ne sosai. Inda zai iya zuwa ranar Monday zan so hakan, zan kira
minister mu zauna tare domin mu tarbe shi" sai kuma ya kalle ta ya ce, "Ko kuma
ranar Monday da aiki?."

Narma ta ce, "Dad ko yaushe ne zai zo indai a kaina ne. Zan faɗa masa in ya amince
ranar monday ɗin zai zo." Mum da take dariya ta ce, "oh my god! Narma....." Narma
tayi dariya ta ce, "Mum I love him so much, my feelings for him are impossible to
hide" ta faɗa tana murmushin sannan ta ce, "then he loves me too." Nabil yayan ta
ya ce, "Ma sha Allah, muna taya ki murnar samun wanda ki ke so." Tayi murmushi ta
ce, "thank you bro, let me go and call him" ta faɗa tana tashi ta shiga ciki a
guje. Dad yayi dariya suna tattauna yadda za'a tarbi siriki in yazo.

Narma na shiga ɗaki Omar ta kira bai ɗauka ba, ta sake kira bai ɗauka ba sai
ta ƙyale shi dan baya son tana tara masa kira. Wajan mintina kaɗan da kiran ya kira
ta ta ɗauka da sauri ta saka a kunne sai ta ce, "kashe na kira ka."

Daga can ɓangaren Omar ya ji abinda ta ce ya maimaita a zuciyarsa, me take nufi
kenan? bashi da kuɗin da zai iya kiran ta kenan sai dai ita ta kira shi?. Kafin
tayi magana ya yanke wayar, Narma ta kira sau adadi yaƙi ɗauka.

Narma ta tayar da hankalinta ganin yaƙi ɗauka, ta je WhatsApp ta tara masa message
tayi masa text message shima ba reply. Tun tana kiran sa har ta gaji ta kuma kasa
gane laifin da tayi wanda ya saka ya yanke mata waya ya kuma ƙi ɗauka.

Shi kuwa Omar yayi haka ne dan ya koya mata hankali nan gaba bazata sake cewa ya
kashe ta kira shi ba. Yana ganin message ɗinta da kiran yayi banza ko kallo bai yi
ba dan ya yi alqawari bazai ɗauka ba, kuma bazai kira ta ba, zata san waye Tiger.

Sunday ta wuce, Monday ta wuce Omar baya ɗaukar wayarta kuma baya kiranta. Narma
hankalinta ya tashi sosai sai ƙarya ta yiwa Dad ta ce ya ce ranar Monday baya nan.
Sai ranar talata da yamma ya ga kiran na zuwa bai ɗauka ba sai da ta katse sai ya
kira ta da hanzari ta ɗauka, tana sakawa a kunne ta ce, "laifin me nayi maka haka?
Me nayi ka ke hukunta ni da wannan hukuncin Faruk?."

"Gobe in na kira ki sai ki sake cewa na kashe ki kira ni. Banda kin raina ni saboda
kinga ina surarenki har ke zaki ce min wai na kashe ki kira ni? Nuna min ki ke yi
bani da kuɗin da zan kira ki?." Jin yadda yake maganar da tsawa sai Narma ta ce,
"I'm sorry...." Cikin tsawa ya katse ta ya ce, "kin manta gargaɗin da nayi miki
ko?." Narma ta ce, "yi haƙuri, na saba da yin English ne ko yaushe shiyasa, Amma
zan dinga kiyayewa. Kayi haƙuri don Allah."

"Mtsw! Faɗi matsalarki" ya faɗa kai tsaye yana sauraren ta.
"Ka yi haƙuri, nayi kewarka, kuma Ina sonka, Ina ƙaunarka." Sai ya ɗan sassauta
murya bayan ya ja tsaki ya ce, "Ina jin ki."

"Daman tun ranar asabar na faɗawa Dad maganar zuwan ka ya ce in kana dama kazo
Monday...au litinin, shine na kira na sanar dakai a lokacin."
"Yanzu sai me?."
"In zaka iya zuwa gobe yana jiran zuwan ka."
Omar ya yi ajiyar zuciya ya ce, "bazan zo gobe ba, amma zan zo ranar alhamis hakan
ya yi?." Narma tayi murmushi ta ce, "Ya yi Faruk ɗina, na gode Allah ya barmu tare
na haifa maka yara masu kama da kai." Samun kansa ya yi da murmushi mai sauti har
taji murmushin nasa. Omar ya ce, "na faɗa miki ban shirya aure ba ko? Ban ma san
yaushe zan yi ba."

Narma ta ce, "ai fata nayi mana ko?" Ta faɗa cikin shagwaɓa tana narkar da murya.
Shagwaɓar da take yi yana ƙara masa karkasashi da yanayin da ya saba ji in suna
waya. Jin ya yi shiru sai Narma ta ce, "baka ce amin ba, baka so na haifa maka
yaran ne?." Murmushi ya sake yi har Narma tayi mamakinsa, dan ta san sai a gama
waya dashi bai yi maganar kirki ba balle murmushi. Ya ce, "Ki jira lokaci."

"Alhamdu lillah! Faruk yana son ya auri Narma har ya haɗa jini da ita. Wannan abin
farin ciki ne." Nan ma murmushi ya sake yi amma bai ce mata komai ba, tana ta yi
masa zance shi kam baya tanka mata sai ya ga dama, sai da ya gaji ya ce, "Zamu yi
magana anjima" daga haka ya yanke wayar yana shafa gajin fuskarsa yana murmushi.
Ajiyar zuciya ya yi ya miƙe ya shiga wajan Didi da niyar faɗa mata zai je gidan
sirikai.

*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.

Nana Haleema❤️


*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025

©️*Nana Haleema.*

Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.

*Book 1*
*P 24.*


A zaune ya samu Didi tana waya ya zauna a kujerar da ya saba zama ya harɗe ƙafa
yana kallon ta tana cewa, "Ya jikin na ki?." Shiru tayi ana bata amsa sannan ta ce,
"Allah ya ƙara lafiya Nayla, a gaishe da su Mama." Ta Amsa daga nan ta yanke wayar.
Ambatar Nayla da tayi ya saka shi ya tuna fuskar ta a lokacin da take hawaye, sai
ya samu kansa da jin wani iri a zuciyarsa ba tare da ya san dalilin haka. "Omar ya
aka yi?." Maganarta ta katse shi ya kalle ta ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Ranar
alhamis zan je Abuja wajan mahaifin Narma."

Didi ta kalle shi ta kasa cewa komai sai kallo, ta zuba masa ido bayan ta tallafi
haɓarta da hannayenta. Ta ce, "Omar!." Jin yadda ta kira shi ya saka ya kalle ta
sai ta ce, "Ka shirya aure ne? Yanzu in aka ce an baka aurenta kana da abinda zaka
aure ta?."

Ajiyar zuciya ya yi ya sauke ƙafasa daga kan ɗaya, ya sarƙe hannayensa

26 / 28